AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Su waye suka mutu su waye zasu rayu? Kun yarda rayuwa bata da tabbas? Kun yarda ba abinda yake dorewa banda ikon Allah? Idan kun yarda da hakan to yanzu muka fara labarin Aalimah.!SumayyahAbdulkadir na tafe da cigaban labarin nan ba da jimawa ba!!!
7/2/21, 8:24 AM – Buhainat: ADAMU DANKOLI

A bakin gate ta tadda Mu’azzam din don already Oncle Oussama yayi masa waya ya gaya masa ga Aalimah nan zata zo ta dauke shi zuwa airport, Mu’azzam cikin kokarin controlling damuwarsa da boye bacin ransa na wannan kumbiya-kumbiya da Iyayen nasu ke ta yi masa ya tambayi Oncle Oussama su Daddy din fa? Sun same su? Amma sai Oncle Oussama yace ai suna tare, da su zasu wuce Niamey gabadaya, sun dan samu hatsari ne ashe, amma da sauki sosai.
Ya kara da cewa sun dauko su daga asibiti Ambulance ta taho dasu filin jirgin shi kadai suke jira, har an sa su a jirgi karkashin kulawar likitoci. Hamoud da Oncle Eidrissa zasu biyo su daga baya sabida kada a bar su Aalimah babu babba tare da su.
Ba don ya gamsu da wannan bayanin ba sai don bai isa ya musawa Kawun nasu ba, ko ba komai ya san bazai gaya masa karya ba, kuma koma me suke boyewar daga karshe dole zai sani ai. Tunda yace suna raye kuma sun gansu suna tare dasu to alhamdulillah.
Sanda Aalimah ta iso get din gidan yana waya ne da Oncle Oussama, saida ta jira ya gama. Ta bude masa kofar gaban motar da nufin ya shiga amma sai yace ta fito ta koma gaban shi ya tuka motar, ya fadi hakan ne ba tareda ya kalli direction din da take ba, yace in ya so ta dinga nuna masa hanya. Bazai iya ganin mace da ciki tana tuki ba. Dazu ba karamin tashi hankalin sa yayi ba jin cewa ita zata tuka su Malam. Haka suka dauki hanyar airport babu mai magana a cikin su, babu mai kallon dan uwansa, sai zukatansu dake cike da zullumi iri daya; (tunanin halin da Aboulkhair da iyayensu ke ciki), sai nuna masa hanya data ke yi lokaci-lokaci har suka shiga cikin filin jirgin.
Ta nuna masa inda ya kamata yayi parking ya kashe motar Suka fito a lokaci daya.
Passengers har sun fara shiga jirgin wanda zai tashi dasu zuwa Birnin Tarayyah, don haka suna hango su su Malam dake zaune a reception suka mike suka tadda su. Malam ya kama hannun ta, ya kuma dafa kanta ya sanya mata albarka, tare da yi mata fatan sauka lafiya. Tana tsaye a inda suka barta suka wuce zuwa cikin jirgi. Mu’azzam shine karshen shiga jirgin bai san me yasa baya ko waiwaye ba.

Tana tsaye inda suka barta ta yi folding hannuwanta a saman kirjinta, tana kallon su suna shiga a hankali babu mai walwala a cikin su. A rashin sanin ta tare da farin cikin rayuwarta zasu tashi, wanda yau ya ke kwance a karkashin fukafukan jirgi. Instead of first class seats da ya saba hawa a duk lokacin da zai hau jirgi. Kullum yana gaya mata shi baya son economy class ko da zai tatike account din sa. Yau gashi a karkashin fukafukan jirgi. Da gaske rayuwa mai iya canzawa ce a kowanne lokaci ba tare da dan adam ya shirya ba. Shi yasa ake so a kowanne lokaci dan adam ya zamo cikin shirin haduwa da Ubangijin sa. Wannan shi zai sanya ya zamo koyaushe cikin aikata kyakkyawan aiki. Ta dade a tsaye don har sai da jirgin ya soma barin kasa sannan ta juya ta koma gida, tana mai jin duniyar bakidaya na yi mata wani irin kunci ta kowanne bangare wanda bata san dalilin sa ba.

A Abuja ne dai sai da aka bata musu lokaci wajen bincike da cike-ciken takardu kafin aka amince musu suka wuce da gawar zuwa Niamey.
Tun a cikin jirgin farko Mu’azzam ya soma shan jinin jikin sa, sabida bai ga majinyatan cikin jirgi tare da su kamar yadda Oncle Oussama yace ba. Daga Malam har Oncle din sun kasa hada ido da shi. Lokacin da sukayi transit a Abuja ya kara tabbatarwa ba tare suke da Aboulkhair da su Daddy ba.
A cikin jirgin da zai kai su Niamey hakurin sa da dauriyar sa ya gaza. Kallon su kawai yake yi cikin tsanaki. Malam ne a kusa da shi, yayin da Oncle Oussama yana daga kujerar bayan su. Dukkannin su tazbaha kawai suke ja, babu mai kallon shi, wani irin kallo yake yi musu idanuwansa na wani irin bubbudewa suna kankancewa duka a lokaci guda.
Duk yadda ya so su bude baki da kansu su bashi bayanin wani abu akasin abinda suka fada da farko amma sun ki cewa komai. Sai ya cigaba da zuba musu idon kamar yadda suke so. Amma bangare mafi rinjaye na zuciyarsa na tabbatar masa da cewa labarin da ke bakunan su ba mai dadin ji bane. Watakila dai su Aboulkhair sun bata. Ko kusa ransa mai yawan soyayya ga iyaye da tilon dan uwan nasa duk nisan zangon tunani da kintace da iyakar tsinkayen sa bai kawo masa mutuwar ko daya a cikinsu ba.
Yawan faduwar gaban da yake ta samu akai-akai na kara tabbatar masa da zargin sa na cewa su Daddy sun bata akan hanyarsu ta zuwa jamhuriyyar Nijar. Mu’azzam bai san cewa da gawar dan uwansa Aboulkhair suke tafe ba, sai da suka sanya kafa cikin family house din su na Raazii a unguwar plateaux. Shi dai Malam burinsa su isa Niamey da Mu’azzam lafiya. Ko ba komai uwarsa tana can, in ciwonsa ya tashi a bakon wuri inda babu kowa nasa ba su da yadda za su yi da shi, kuma Alhamdulillahi sun zo lafiya.

Gidan ya kacame da hidimar biki kamar jiya, saboda yau ne cocktail, dangi sun taru kamar su fasa gidan. Na birni dana kauye, Inna Kasisi na ta rabon abinci, Mummy Zulaiha ta tsame kanta tana daki da tazbaha a hannunta. Haka kawai ta ji duk bikin ya ishe ta tunda har yau babu labarin danta da mijinta.
Gumsu na yi wa amarya Khaleesat kwalliya suka ji maza na shigowa, Oncle Mainasara na fadin, “A kawo tabarmi. Ku matsa ku bada hanya. Sun dawo da gawar Aboulkhair, an ce shi kadai ne ya cika a cikin suâ€.
Mummy tana daga cikin daki ne amma tsaf kunnuwanta suna waje, komai da ake yi akan kunnen ta ne. Silalewa ta yi a zaunen data ke a sume yayin da Gumsu ta fito da gudu zaninta na kuncewa. Khaleesat ma haka.
A tsakar dakin Malam aka shimfide gawar Aboulkhair. Duka ‘ya’yan gidan maza sun shigo da makwabta da sauran al’ummar Annabi da suka samu labari a waje.
Malam ya ce a kira mahaifiyarsa ta zo su yi sallama, kafin a yi masa sallah. Sabida munin gawar ko wanka ba za a iya yi mata ba, sai ruwa aka yayyafa mata. Inna Kasisi ruwa take ta shafa wa Mummy, amma ko da ta farfado aka kai ta gaban gawar ta bude kyallen ta ga yadda Allah ya mayar da Aboulkhairinta da sauri ta rufe don fuskar duka ta zube. Baka iya shaida komai nasa. Sake silalewa ta yi ta suma a wurin. Gumsu ce da su Inna Bintou masu karfin gwiwar yi masa addu’a tare da sauran ‘yan uwa maza da mata. Amma Kasisi ma ta kasa duk irin taurin ranta kuwa. Kuka kawai take yi tana kiran sunan Aboulkhair. Khaleesat ma suma take ta yi kamar Mummy tana farfadowa. Yasmin na kururuwa ana hanata.
‘Ya’yan Malam gaba daya suna tsaye a kan gawar cikin dimuwa, kowanne rike da Alkur’ani mai tsarki suna karanta masa. Sabida yawansu nan da nan suka hattama sauka. Malam ya yi wa gawar Aboulkhair duk wani gata da addinin musulunci ya tanadar wa mamaci, suka hadu shi da ‘ya’yansa maza da jikoki da abokan arziki suka sallace shi, suka mika shi zuwa gidansa na gaskiya.
Mummy a karshe sai asibiti aka nufa da ita, don idan ta farfado ta tuno wai Aboulkhair ne babu, sai ta sake sumewa. Har aka yi addu’ar uku Mummy ba ta daina suma tana farfadowa ba. Likita ya tabbatar ta samu hawan jini farat daya. Khaleesat da Yesmin suna cikin wani yanayi wanda sai wanda ya taba rasa shakiki ne zai iya bayyana shi. Shakikin ma irin Monsieur Aboulkhair dinsu.
****

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button