AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Kasuwanci iri-iri ya gwada a kasuwar Nouhou market, inda daga karshe na hatsi wato kayan abinci shi ya fi karbarsa. Ya je garin Zinder duk kan sana’arsa ya ga Kasisi ya aure ta, ya tafi da ita Yamai. Sai da Kasisi ta yi haihuwa biyar ya auri Bintou, ita kuma daga Arlit. A lokacin mahaifinsa ya jima da rasuwa, lokaci-lokaci yana zuwa gida ya ga ‘yan uwansa da mahaifiyarsu, wadanda duka sun yi aure sun hayayyafa a can su ma, Yahayya shi ne ya gaji mahaifinsu wajen bada karatun buzu, shi ne kuma yake rike da ragamar gidan da sana’arsa ta kiwo. Duk da a lokacin Ibrahim bai yi wani karfi ba a hakan yana taimaka wa ‘yan uwansa sosai.
Wani zuwa da ya yi da iyalinsa bayan auren Bintou da haihuwarta ta fari, ya tarar da rasuwar mahaifiyarsa.
Wannan karon tunda ya bar gida ya dukufa neman na kai, ya mallaki karamin gida a unguwar (Liberte), unguwar talakawa ce a Yamai. Zamani na kara habaka, masu sana’ar kayan abinci suka gane wa sabuwar hanyar shigo da shinkafa da sauran kayan abinci na alkama irin su macaroni, taliya daga kasar Faransa zuwa manyan biranen Nijar ba Niamey kadai ba. Sai dai ita din ta zame musu cibiyar kasuwancin. Wannan shi ne silar arzikin Malam Ibrahim Sarhamu Razee da tarihin zamansa a babban birni (Niamey), kuma asalin su Aalimah, iyaye da kakanninsu.
*

A Yamai Zulaiha ta haifi danta na fari, wanda Ishaq ya radawa sunan mahaifinsa ‘IBRAHEEM MU’AZZAM’, shekarar Mu’azzam daya Ishaq ya samu aikin da ya kai shi kasar Amurka a Niger Consulate America. Suka tattara suka koma kasar Amurka shi da iyalinsa.
Ya jima yana aiki a consulate na kasarsu kafin hanyoyi su bude masa sosai, ya koma karkashin siyasar gwamnatin kasar mai tabbataccen aikin gwamnati a hannunsa, ya ajiye aikin consulate a gefe ya zama dan kasa mai zaune da cikakken lasisi. A can ya haife sauran yaransa hudu daya bayan daya; Abulkhairi, Basma, Khalisat da Yasmin. In ka hada harYayansu haifaffen Yamaisun zama su biyar kenan.
Bayan dawowarsu Amurka Mummy Zulaiha ta ci gaba da karatu, inda ta yi digirinta a fannin tsimi da tanadi (Economics). Yanzu haka MummyZulaiha Raazee ma’aikaciyar banki ce da (JPMorgan Chase). Girman kai da fadin raisai abin da ya karu cikin halayenta. Al’adunta duk sun juye sun zama na al’ummar da ta ke zaune da su.
A hakan kuma ta raini ‘ya’yanta mata guda uku, mazan kam Babansu na matukar kokari a kansu, a halin yanzu yana jan su a jikinsa yadda ya kamata.He’sspending most of his leisure time with them yana dora su a kan tafarki mai kyau tun bayan mummunar kaddarar data shigo rayuwarsu. Da ma an ce ‘ya mace ta Uwarta, Da namiji na Ubansa.

Suna daukar lokaci ba su je Yamai ba, amma in suka je din suna jimawa. Suna kuma zuwa Kano wajen dangin Mummy, saboda mugun hali irin na Zulaiha ko nata dangin ba ta ja a jikinta, ba ta taba daukar wani nata ta kai inda ta ke ba. A haihuwar Basma ne shi Ishaq ya biya wa mahaifiyarta da Yayarta da Inna Bintou suka je, Inna Kasisi ta ki zuwa, don ba ta son duk wani sha’ani da zai hada ta inuwa daya da Zulaiha, zuciyarta ba za ta dauka ba.
*

3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM – Buhainat: 🌹 *Aalimah🌹 *SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

07030137870

FREE PAGES 3

MANSOUR RAAZEE
Sanda Yayansa Ishaq ya koma gida Yamai, shi kuma jami’ar ta rike shi don ya yi mata aiki bayan kammala hidimar kasarshi. Ya je ya ga iyayensa, ya kuma gaya musu samun aikinsa a inda ya yi karatu, atafau Inna Kasisi ta ce ita ba ta yarda ba, tunda babu Ishaq ya dawo gida ya nemi aikin ya yi aure. A nan yake gaya musu ya samu mata a Zaria abokiyar karatunsa. Nan ma Inna Kasisi ta yi tsalle ta dire ta ce ba ta yarda su kara yo mata wannan auren ba, ga Zulaiha nan da aka auro ba dadinta suke ji ba.

Mansour, ba shi da abin da zai ce da mahaiafinsu a duniya sai Allah ya ji kansa, ba don ya mutu ba. Yadda yake din bai yi karatun zamani ba, amma wayewarsa da rayuwa da yadda yake tafiyar da tsarin rayuwarsa babu matsi babu takura ga ‘ya’yansa, in har ba addini suka kauce wa ba, wane wani Farfesan. He is very soft on them (shi mai tausasawa ne a garesu). Shi ya tsaya masa ya auri ‘Aseeya’ diya ga shugaban jami’ar na wancan lokacin.
Aseeya ‘yar ajinsu e wadda ta fi duk ‘yan ajin kankantar shekaru. Babanta V.C, uwarta Dr. duk a jami’ar Ahmadu Bello. Asalinsu ‘yan Maiduguri ne daga kabilar Margi, aiki ya kawo mahaifinta A.B.U Zaria inda mamanta ta yi doctorate dinta a Microbiology, ta fara lecturing a nan itama, shi kuma yana matsayin V.C.
A nan cikin A.B.U aka haife su ita da Yayanta Suraj, ajinsu daya ita da Mansour Raazee a tsangayar aikin jarida.
Da fari haduwar jini ce tsakaninsu da aron note da yin tutorial in jarrabawa ta matso wanda ya rikide ya koma soyayya tsantsa. Tun abin bai yi nisa ba iyayenta suka so su dakatar kasancewar Mansour bakon haure. Suna tunanin watarana zai dauke musu ‘ya, ya mayar kasarsu.
Amma da Malam Ibrahim Sarhamu Razee ya tako da kansa tun daga Niamey shi da manyan ‘ya’yansa Oussama da Edrissa suka zo har Maiduguri nema wa dansu auren Aseeya, Prof. Kashim, kasa badawawannan farin ba’abzinen dattijon mai kama da Larabawan Hijaz kasa a ido ya yi, sabida haiba da kamalarsa. Ya kuma yi duk iya binciken da zai yi a kan Mansour, inda ya tarar asali kam sai dai ya gaya wa Aseeya, tun kafin zuwan Malam Ibrahim.
Ba da jimawa ba aka yi auren Aseeya da Mansour, suka tare a gidansa da jami’ar ta bashi, shekara na zagayowa ta haifi Da namiji, ya sa masa suna Aboubacar.
Sai da Aboubacar ya shekara bakwai aka haifi ‘AALIMAH’, ita ma sai da ta shekara biyar aka fara yi mata kanne; Sultana, Suhaima da Sabrina.
Har inda yau ke motsi Baban Aalimah Malamin jami’a ne mai matsayin Dr., Amma sun bar Zaria sun koma jami’ar Bayerota Kano bayan rasuwar mahaifin Aseeya, wato Prof. Kashim, mahaifiyarta ta koma Maiduguri cikin danginta.
Wannan ya tayar da hankalin Aseeya ta ce ba za ta iya ci gaba da zama cikin A.B.U ba, tana kallon kofar gidan da iyayenta suka rayu, hakan yana dawo mata da memories na rayuwarta tare da su. Har sai da ta samu matsala a kwakwalwarta (anxiety). Duk son da Mansour ke wa A.B.U haka ya barta ya koma Bayero don kwanciyar hankalin maidakinsa.
A sannan ne suka fahimci wani babban jigo nasu a Nigeria ya fadi (Prof. Kashim), ta ajiye aikinta da ta ke yi a gidan talbijin, sai abin da Mansour ya kawo, kusan komai da ta saba na rayuwarta dainawa ta yi. Da aka raba musu gado ta yi wa nata adani sosai a banki da wani kuduri a zuciyarta.
Yana kai ta Maiduguri akai-akai wajen mahaifiyarta da danginta, kuma suna zuwa Yamaiwajen nashi iyayen a duk sanda suka samu hutu.
A sannu Inna Kasisi ta fahimci Aseeya ba halinta daya da Zulaiha ba, they are totally opposite in every aspect.
Sonsu ta ke da zuciya daya, tare da girmama ko da kare ne in dai daga Nijar ya fito, sabida son da ta ke wa mijinta,. Yayanta Suraj ya bar kasar tun mahaifinsu na raye, tun daga zuwa karatu a kasar Canada ya yi zamansa a can musamman da mahaifinsu ya rasu, mahaifiyarsu ta koma Maiduguri, bai kara sha’awar dawowa Nigeria ba.
*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button