AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Ina Mu’azzam???

Mu’azzam ya bai wa kowa matukar mamaki, don kuwa abin da aka zata ba shi aka tarar daga gare shi ba. Shi ya sanya dan uwansa a kabarinsa, babu ko digon hawaye a fuskarsa, da hannunsa ya debi kasa sau uku da hannu bibbiyu ya rufe shi. Abin da Oncle Oussama ya lura da shi kawai shi ne; daga ranar bai kara sanya komai a bakinsa ba! Har maganinsa kuwa. Bai zubda hawaye ba, bai sake cewa kala ba. Wannan ya daga hankalin Malam wanda ke kwana daki daya da shi don kula da duk wani motsinsa yana kuma yi masa addu’o’i. Ba ya bari ya matsa ko nan da can. Ko bandaki ya shiga sai ya bishi ya tsaya a kofa.
Ranar da aka yi sadakar uku, ya ce da malam zai koma America zai nemi asibitin da ya dace ya kai su Daddy, ya kuma nema wa Dr. Mansour da Aboubacar medical visa suma a ci gaba da kula da su a can.
Babu wanda ya hana shi, don sun san cewa, hakan shi ne daidai, musamman da yake ya daina shan maganinsa, suna tsoron abin da hakan zai haifar, gara ya koma inda za a kula da shi shima.

Bayan tafiyar Mu’azzam ci gaba aka yi da karbar gaisuwa a gidan na Malam Raazee. Mummy na shan drip a asibiti har ta soma karbar reality.
Khaleesat ta kasance cikin tashin hankalin da ya fi na kowa a gidan, don a cewarta sanadin aurenta ne Monsieur Aboulkhair ya rasa kyakkyawar rayuwarsa. Tana mai kaico da wannan aure! Gumsu na kwabarta a koyaushe da cewa; mutum ba ya tsallake ajalinsa! Fadin halin da wannan family suke ciki ya yi kadan biro ya rubuta shi.
Mu’azzam ya kira malam Raazee ya sanar da shi ya yi processing visa din Daddyn Aalimah da Aboubacar, za su taso sati mai zuwa dukkansu, kuma ya hada da Hamoud don ya taya shi kula da su a can.
Malam ya ce,
“In ce ko kana shan naka maganin takwara?â€
Mu’azzam ya yi shiru.
Malam ya kwantar da murya, ya ce, “Takwara tafiyar wani tashin wani ce, rashin Aboulkhair ba yana nufin karewar taka rayuwar ba ne, tunda har yanzu kana numfashi. Na gane abin da ka ke yi, kana so ne kai ma ka illata kanka; ta hanyar kin shan magani. Takwara, mutuwar dan uwa na sani da ciwo, ciwo ba dan kadan ba, dan uwan ma irin Aboulkhairi mai tarin alkhairi, wanda samun kamarsa sai an tona.
To amma a matsayinmu na musulmi, dole ne mu yarda da kaddara komai dacinta. Mu kuma yarda cewa kulli nafsin za’ikatul maut. Ka yi hakuri Mu’azzam ka ji? Don Allah ka kula da lafiyarka…..â€.

Sai a wannan lokacin ne Mu’azzam ya fara wani irin kuka… Ya yi kuka ya yi kuka kamar ransa zai fita, Kakan nasa bai hana shi ba, hasali ma shi ma taya shi ya shiga yi suka yi ta yi a waya. A karshe Malam Raazee ya ce,
“Ba zan bari ka dauki kowa cikin majinyatan nan ba sai ka sha magani, ka kai kanka ga likitocinka sun kula da kai, in ba haka ba su zauna a nan kusa da ni, duk zan iya jinyar su. Gobe da ma zan kwaso su duka daga Kanon bakidayansuâ€.

Bai bari Mu’azzam ya ba shi amsa ba ya kashe wayar sa.

        KANO, NIGERIA

Aalimah ba ta san wainar da ake toyawa ba sai a daren ranar dasu Mu’azzam suka wuce Niamey. Oncle Eidrissa ne ya kira ta a waya, ya ce suna tare da su Daddy an gansu. Cike da farin ciki ta ce,
“Ouncle Oussama ya gaya mini, har na gayawa su mama, sune a Aminu Kano da muka je dazu ko? Yaya jikin nasu? Oncle ina fata basu ji ciwo sosai ba?â€
Ya ce, “Eh, muna can, amma sun ji rauni sosai wallahiâ€.
Ya kara da cewa. Ta kawo musu dardumar sallah da ruwan sha.
Ta ce, “Oncle abinci fa?â€
Sai dai kuma ta karaya, da amsar da ya bata, da yadda take jin yana magana babu karsashi ko kankani a amon muryar sa, karfinta kuma ya kare dama da dawainiyar jinyar data ke sha a kwanaki ukun nan, she’s very exhausted, idanuwan ta har zafi suke yi na rashin barci, amma don karfin hali ba ta fasa kula da majinyatan ta ba. Ko dama can ita mai karfin zuciya ce akan komai. Duk da zuciyarta cike take taf, da kewa da tunanin mijinta. Taraddadin halin da yake ciki ya hana ta mallakar kanta. Tana jin salama ne in ta tuna an gansu kuma suna cikin gari daya itada Aboulkhair sannan suna samun kulawa daga likitoci yadda ya kamata kamar yadda su malam suka gaya mata, ta dan yi hakuri za’a barta ta gansu ba da jimawa ba.
Hawaye ya zubo wa Eidrissa, tausayin yarinyar yake ji sosai har cikin ransa. Takabar dake gabanta yake hango mata, da yadda zata haifi da ya rayu bai san Ubansa ba, ya ce,
“Bar maganar abincin nan Aalimah, wa zai iya cin shi? Ba ni Aseeyah idan tana kusa, kuma zata iya karba wayaâ€.
A lokacin mama ta soma warwarewa sosai, ta mika mata wayar, mama ta karba tayi masa sallama, ya ce,
“Aseeyah!â€
Ta ce, “Na’am Kawunsuâ€.
Ya ce, “Mu musulmi ne ko?â€
Ta ce, “Kwarai da gaskeâ€.
Ya ce, “Wadanda suka yarda Allah ke rayawa kuma shi ke kashewa?â€
A kwance ta ke a gado, amma jin inda zancen sa ya nufa sai ta mike zaune, Aalimah ta sanya mata pillow a bayanta ta ta jingina, sake manna wayar tayi a kunnenta. Ga Aalimah ta kafe ta da idanu kamar mai son a fadi komai akan kunnen ta, don haka ta mike daga gadon ta nufi bakin taga don kaucewa wadannan kaifafan idanu na Aalimah.
“Tafi kai tsaye Kawunsuâ€.
Ya rufe ido ya gaya mata komai. Ya ce, “Na rasa yadda zan yi in gaya wa Aalimah ta rasa mijinta, na ganta da ciki, wanda da alama bai gama girma baâ€.
Mama ta shiga salati, hawaye na zuba mata tarara! Ta ma manta Aalimahr na dakin. Jikinta ya hau tsuma da karkarwa.
Aalimah da Basmah da ke dakin duk suka yo kanta. Basma ta dauki wayar da ta yasar a kasa ta bi kira na karshe, Oncle Eidrissa ta gani, don haka ta bi bayan kiran.
“Oncle Basma ceâ€.
“Ku yi hakuri Basma kun ji, da kaddarar da Ubangiji ya dora mana. Kulli nafsin za’ikatul maut, Aboulkhairi bai yi gaggawa ba, mu ma duk lokaci muke jira!â€.
Basma ta shaki wani azababben numfashi, tana mai kokarin fizgo sauti daga makogaronta.
“Oncle Daddy? Hubby? Suna ina?â€
Ya share hawaye, muryar yarinyar kadai za ka ji ka fahimci ta gama mika wuya da jin ko ma me za ta ji. Tana da dauriya sosai kamar ko fiye da Aalimah.
Ya ce, “Basma ki dayanta Allah, ki yarda da kaddara sai ki samu cikar imani. Dan uwanki Aboulkhair Allah ya yi masa rasuwa. Har sun wuce da gawar Niamey don a suturta ta. Ga iyayenku da mijinki a nan tare da mu a gadon asibiti, sun jikkata. Mummunar jikkata. Mu gode wa Allah a cikin kowanne haliâ€.
Basma sai juyawa ta yi ta ga Aalimah a kasa, tana shure-shure, ta manta tsabar rudewa a handsfree ta sanya wayar. Allah ya taimaka a cikin asibiti suke, nan da nan ta danna kararrawar kiran likitoci, likitoci biyu da nurses biyu suka shigo suka dauke ta suka aza bisa gado suka soma kokarin ceto numfashinta da ceton abin da ke cikinta. Sakamakon jini da ya tsinke mata duka a lokaci guda.
7/2/21, 8:24 AM – Buhainat: KWATARKWASHI
A daidai wannan lokacin rashin lafiyar Mu’azzam ya fado masa a rai. Da sauri ya juya kafin ya karaso inda suke ya dubi babban dan sa Oussama da ke gefensa na dama a tsaye.
“Oussama yaya za mu yi da Mu’azzam? Ba’a gaya masa tashin hankali, idan ciwonsa ya tashi anan ya ya za mu yi da shi? Gashi babu Aboulkhairi tare da shi, babu shaidar komai na rashin lafiyarsa ko asibitinsa tare da muâ€.
Duk dauriyar Uncle Oussama da taurin ransa yau kallo daya zaka yi masa ka ga ya baka tausayi, murya a raunane ya ce.
“Yanzu ya za’a yi Malam? Dole ya je shima, za mu dauki Hamoud ne mu barshi? Tun jiya cikin damuwa yake, yana gaya min ya kasa samun nutsuwa saboda rashin samun wayar kanin nasa, da rashin isowarsu tun lokacin da ya kamata a ce sun iso dinâ€.
Suka yi zugum-zugum a tsaye, idanuwansu sun kada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button