AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Daidai lokacin da Hamoud da Mu’az din suka isko su. Har kasa suka tsugunna cikin ladabi suna gaya musu an samu jirgi mai zuwa Abuja, wanda zai tashi nan da awanni biyu. Kuma duk Mu’azzam ya saya musu tikitin bakidayansu, ya ce shi ma zai je, bai yarda ya zauna a Niger bai san halin da suke ciki ba.
Babu yadda suka iya, suka yi shahadar kuda dukkansu suka taho Abuja, inda daganan suka hawo jirgi mai zuwa Kano. Mata ba su san wainar da ake toyawa ba. ‘Yammata na can suna shirya wa angwaye roti, manya na girke-girke, an boye amarya Khaleesat a daki. Gumsu da Zulaiha kadai ke cikin damuwar da ba ta hana su shiga mutane ba, saboda yadda kowa ya zo gidan su yake nema, don yi musu Allah ya sanya alkhairi.

                *****

Da jirgi ya sauke su a Kanon-Dabo taxi biyu suka yi shata zuwa gidan Dr. Mansour, duk da Mu’azzam ya ce su bari ya yi waya gidan kakanninsa na wajen uwa a zo a dauke su, amma cikinsu ba wanda yake jin zai iya minti goma cikin filin jirgin bai san halin da wadannan rabin jikin nasa ke ciki ba. Shi ma Mu’azzam dalilin da ya sa ya fi su kwanciyar hankali shi ne, bai san komai game da wayar da Aalimah ta bugo ba. Hamoud ma bai sani ba, manyan kadai suka yi maganar a tsakaninsu. Edrissa cewa ya yi da Mu’azzam sun biyo baya ne don su bincika abin da ya hana su tasowa tunda an kasa samun wayoyin kowa a cikinsu, har na Aseeya.
Tun kafin su karasa gidan Uncle Oussama ya fiddo waya ya kira Aalimah. Ta ce ga ta nan zuwa za ta dauke su zuwa asibitin da suke.
A kofar gidan suka sassauka, sai dai sun kasa shiga duk da Bilyaminu ya ce su shigo din. Har Aalimah ta iso wajen a motar Aboubacar duk ta yi wani wujiga-wujiga ta fita hayyacinta kwana daya rak! Dabara ta zo wa Uncle Oussama yadda za su hana Mu’azzam zuwa police station, sai sun fara zuwa sun tabbatar da abinda ya faru, ya ce shi da Hamoud su shiga gidan su jira su, tunda motar ba za ta kwashesu su duka ba. Mu’azzam ya soma shiga rudu, ko daga ganin yanayin Aalimah, bai taba ganinta cikin wannan yanayin ba, yarinya ce ‘yar kwalisa ta kin karawa mai tarin nutsuwa a iya sanin da yayi mata.
Damuwarsa ta soma bayyana karara akan fuskar sa, sannan ya za’a ce ita mace mai ciki ta tuka mota su tafi wani wuri su samari masu jini a jika a ce su koma gida su zauna? Amma bai furta tunaninsa ba, don a fuskokinsu basu bashi damar yayi musu tambaya ba, don haka ya zuba musu ido ya ga iya gudun ruwan su, sai Aalimahr ya daga idonsa dake a rine ya jefa wa tambaya.
“Ina Aboulkhair? Ina Daddy da Baba Mansour?â€
Aalimah ta juyar da kai cikin wani yanayi mara fassaruwa, ba tareda ta dube shi ba kanta na kallon kasa tace.
“Ni ma ban sani ba!â€
Sai hawaye suka zubo batare da ta ankare ba. Wadanda suka kara dugunzuma zuciyar Mu’azzam.
“To yanzu ina za ki kai su?â€
Wannan karon kamar cikin fusata ya tambaye ta. Don ya kasa gane dalilin wannan kumbiya-kumbiya da ake masa.
Da sauri Uncle Ossama ya ce, “Mu’azzam, in na isa in fada ka bi, to ku je ciki ku jira mu kai da Hamoud, za ta raka mu mu yi bincike a kansu ne a ofishin ‘yan sandaâ€.

“I will drive youâ€.

Mu’azzam ya fada cikin soma jin wani abu mai kama da mugun tsoro da matsananciyar fargaba na shigar sa. Wace irin magana ce wannan, ba a san inda suke ba? Bata suka yi ko sace su aka yi? Sai ka ce wasu kananan yara?
“Ita ta san garin, kai kuwa baka san ko’ina ba, shi ya sa za ta tuka muâ€. In ji Malam, yana mai dafa kafadunsa wannan karon cikin sautin lallashi, ganin cewa jan ido da nuna karfin iko bazai yi tasiri ba gare shi a wannan lokacin.
Bai ce komai ba ganin cewa sun fishi hujja, ya dan ja da baya ya bi su da ido suna shiga motar daya bayan daya. Da Hamoud ya sanya hannunsa cikin nasa ya sarke, ya ja shi a hankali zuwa ciki, sai bai yi masa musu ba.

Kai tsaye ofishin ‘yan sanda na Bompai Aalimah ta nufa kamar yadda ‘yan sandan suka gaya mata. Da tambaya da komai har suka samu ofishin da ya kamata su nema.
Da ta dan soma bayani, tun kafin ta gama aka yi musu jagora zuwa ofishin kwamishina. Kamar dama jiran su ake yi. Malam yace da Aalimah ta koma mota ta zauna ta jira su. Kuma bata yi musun bin umarninsa ba.
Mikewa kwamishinan ya yi ya ba su hannu dukkansu cikin mutuntawa. Ganinsu manyan mutane farare tas-tas dasu kamar larabawa, ga tsohon ya sha rawanin da ya sanar da shi malamin buzu ne. Sannan suka samu kujerun dake fuskantarsa suka zazzuna. Daga inda suke suna iya karanto sunan kwamishinan dake like jikin wani dan karfe ruwan gold akan teburinsa; Commissioner of Police Isma’ila Dauda Kataki.

Sai da kwamishina ya ga sun nutsu, sun bashi dukkan hankalin su. Sannan ya soma da yi musu tunasarwa a matsayinsu na musulmi da ya rataya a wuyan dukkanin mu da mu karbi kaddara mai kyau ko mara kyau, mai dadi ko mara dadi, domin samun cikar imanin mu. Dukkansu sun gama mika wuya ga karbar koma me zasu ji a wannan lokacin, wanda ba irin hasashen da basu yi ba kafin kwamishina ya gama zagaye-zagayen sa, zukatansu kamar su fito daga kirazansu a lokacin da Kwamishinan yake gaya musu mummunan hatsarin motar da ya afku kafin a shiga boarder din dake tsakanin Najeriya da Nijar, tsakanin motocin guda biyu babbar (Jeep) da karamar mota (toyota Camry), wanda a take ya yi sanadiyyar rayuka uku. Sauran suka jikkata, mummunar jikkata, kuma su ba su san wadanne ne na wannan motar ba, wadanne ne na waccan motar ba. Gabadaya sun cakude ta yadda sai wadanda suka san su ne kadai zasu gane su. An dai kai gawarwakin guda uku matuary kafin zuwan ‘yan uwansu don su tantance su. Wadanda suka ji ciwo kuma suna karkashin kyakkyawar kulawa.
Sun samu wadannan I.D cards dinne guda biyu na shaidar gida da wajen aiki a aljihun motar Jeep da ta ragargaje na wani Aboubacar da wani mai suna Mansour. Shiyasa aka taho dasu Kano.

A take Malam Raazee da ‘ya’yansa suka soma ambatar, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’unâ€. Yi suke suna maimaitawa, wani ba ya jin na wani.
Kwamishina ya ci gaba da kwantar musu da hankali da tausasan kalamai. Ya fada musu su zo a je su tantance gawarwakin su kuma ga wadanda suka tsira a emergency unit na asibitin Malam Aminu Kano.
Ba su bata lokaci ba suka fito, a cikin mota suka tadda Aalimah ta kifa kai akan sitiyarin mota abin tausayi. Idanunta sun yi ja sun kankance. Fargabar halin da za’a ce mata su Daddy na ciki ya gama karar da dukkan kuzarin ta. Kafin ta dago har sun shigo motar jikin su yanata rawa. Suna masu kauda kai daga gareta. Ba wanda ya iya ya hada ido da ita. Motar ‘yan sandan da za ta yi musu jagora na gabansu, suka ce da Aalimah ta bi bayansu ba tare da sun yi mata bayanin komai ba.

A mutuary na asibitin Malam, ba su bi ta kan wadanda aka ce sun tsira ba, sai wadanda aka ce sun mutu!!!

Allah sarki! Kada ku so ku ga fuskar tsoho Ibrahim Sarhamu Raazee da manyan ‘ya’yansa a wannan lokacin. Shekarun su sun kara bayyana akan jajayen fuskokinsu. Azabtuwa suke a zuci da ruhi. Sun kasa shaida gawar kowa cikin ukun da aka nuna musu sabida yadda halittarsu ta jikkata. Wasu daga ciki hannu da kafa suka fita.
Eidrissa ne ya nuna daya daga ciki, ya ce ko mutuwa ya yi ya dawo wannan Aboulkhairi ne ba zai kasa shaida shi ba. sauran ba su da zabi ban da su amince a fitar musu da shi.
Da taimakon ambulance da kwamishinan ‘yan sanda aka tafi da gawar filin jirgi don yin cuku-cukun tafiya da ita Niamey. Malam ya ce a nuna musu rayayyun, inda likitocin suka kai su ga masu hatsarin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button