AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Hailala suka saki da suka yi tozali da Dr. Mansour a gadon farko babu kafa guda, Daddy Ishaq na kwance cikin tsananin ciwo da karaya har biyar a kafa da hannu, bai san wanda ke kansa ba, sai Aboubacar wanda ke cikin wani irin hali na rai kwakwai-mutu-kwakwai.
Iyakar tashin hankali wadannan mutane sun shige shi irin wanda basu taba shiga a rayuwarsu ba. Duk abin nan da ake Aalimah ba ta sani ba, ta koma gida kamar yadda Oncle Oussama ya umarce ta yace in sun gama abinda suke za su kira ta ta zo ta dauke su. Ta kwantar da hankalinta an same su kuma babu wanda ya mutu amma sun ji rauni sosai kuma suna karbar kulawar gaggawa yadda ya kamata.
Da wannan dan kwarin gwiwar ta tuka motar a hankali kamar mai tafiya akan kwai ta koma gida, tana shiga ta wuce kitchen ta baiwa su Tabawa umarnin su dafa abinci za ta kai wa su mama asibiti, ga Hamoud da Mu’azzam can a falon Daddy su kai musu. Bata bi ta kan su Mu’azzam din ba, wadanda ke can falon Dr. Mansur sun yi zugum-zugum ko hira sun kasa yi a junansu tsakanin sa da kanin nasa Hamoud, Mu’azzam ya cure hannayensa wuri guda ya mikar dasu ya dora habarsa a kansu, banda sallah ba abinda ke tayar da su, ko ruwa basu iya sha ba tun shigowar su falon.
A lokacin ta samu ta rama sallolin da ke kanta, tayi wanka sama-sama, ta canza kayan jikinta. Suna gamawa Sabira tazo har daki ta sanar da ita, ta ba su umarnin su kai wa Mu’azzam da Hamoud falon Daddy, su kula dasu ko suna bukatar wani abu, ita kuma ta dauki na asibiti ta wuce gate ba tare da ta leka su Mu’azzam din ba, ta sanya a bayan mota ta tafi.
Malam Raazee da ‘ya’yansa sun yanke shawarar za su koma Niamey tare da Mu’azzam, don ya halarci jana’izar dan uwansa. Eidrissa da Hamoud su zauna tare da majinyatan kafin a gama jana’iza sai a san yadda za’a yi. In can za su koma da jinya to, in kuma Mu’azzam zai fita da su ne toh, duk da bai san halin da Mu’azzam din zai fada ba in ya fahimci ya rasa dan uwansa rabin-ransa, barin jikin sa, sanyin idaniyarsa, Aboulkhairi. Da haka suka bar asibitin suka bi motar ‘yan sanda tareda ambulance din zuwa filin jirgi. An yi sa’a akwai jirgi wanda zai tashi zuwa Abuja nan da awa daya don haka bazasu samu jinkiri sosai ba.
Kafin su isa airport, Aalimah Oncle Oussama ya kira a waya, yace ta dauko Mu’azzam daga gida ta kawo musu shi filin jirgi, zasu koma Niamey tare da shi, amma Kawu Eidrissa da Hamoud suna nan tare da majinyatan. Don haka ta fadawa Basma da Mama abinda Kawun nasu ya ce, ta tuko motar ta dawo gida don tafiya da Mu’azzam din kamar yadda Baffan nasu yayi mata umarni .
7/4/21, 10:50 AM – Buhainat: HARUNA TANKO
Da ATM card din Aalimah Mama ta biya duka hospital bill dinsu. Basma da ake jinya ita ta koma jinyar Aalimah. Ga danyen jego, ga jarirai sabuwar haihuwa har guda biyu. Abin duka babu dadi garesu ko ta ina. Abincin da masu aikin Mama ke kawowa babu mai iya cinshi. Duk kokari da kwarewar likitocin asibitin international sun kasa tsayar da cikin jikin Aalimah, dole aka yi mata tiyata aka cire shi babu rai, an gama masa halitta tsaf, don samun tata rayuwar. Abin gwanin ban tausayi.
In har kana da zuciyar imani dole ka kokawa iyalan RAAZEE a wannan hali na jarrabawar Ubangiji da suka tsinci kansu. Wanda basu taba tsintar kansu a kwatankwacin sa ba, Basma da jariranta da Mama sun warware, sune suke kula da jinyar Aalimah, yayin da Hamoud da Oncle Eidrissa ke kula da iyayensu da Aboubacar dake gadon asibiti. Duka daga ATM din Aalimah ake biyan duka asibitocin nan. Kafin sakon Mu’azzam ya cimmasu, na dauke marassa lafiyan daga Kano zuwa Amurka, tare da Hamoud.
Ranar da likitoci suka sallami Aalimah daga gadon asibiti, ranar ne Hamoud ya daga da su Daddy zuwa asibitin da Mu’azzam ya shirya musu jinya a garin Las Vegas, saukarsu a asibitin Southern Hills Hospital ke da wuya motar asibitin Southern Hills ta kwashe su karkashin kulawar likitoci zuwa asibitin. Dakuna na musamman Mu’azzam ya kama musu bakidayansu, kowanne dakinsa daban.
Tunda suka je ba su ga Mu’azzam ba, basu ji muryarsa koda a waya ba, asibitin ke ta dawainiya da su da bukatocin su tun daga airport, direban da ya dauko su ma na asibitin ne ba direban Mu’azzam ba. Ya kai majinyata asibiti, ya kai Hamoud gidan Mu’azzam ba tare da ya yi masa bayanin komai ba.
A gidan ne Hamoud ya tadda yaron Mu’azzam da direbansa Harrison inda yaron ya ce, zai dinga kawo masa abinci sau uku a kowacce rana bisa umarnin ubangidansa, direban kuma ya ce zai dinga kai shi asibiti wajen majinyatan duk sanda yake so, maigidansu an rike shi a asibiti tun jiya, shima ba shi da lafiya.
Duk kokarin Hamoud na su kai shi asibitin da Mu’azzam din yake sun ki. A cewar su ba’a yi musu wannan umarnin ba. Babu fuska ma daga gare su na a cika su da tambaya, they are very cautious akan aikinsu kowanne abin da ya kawo shi yake yi a gidan ya gama ya tafi.
Hamoud na takawa tsakiyar falon gidan ya ga gaba daya gilassan taga sun ragargazo kasa, duk wani abu na gilashi a fashe yake a gidan. Including talbijin dake manne jikin bango ta kwankwatse. Bai gama fita daga wanan mamakin ba sai da ya kutsa kai dakin barcin Mu’azzam.
Komai yayi raga-raga. Hatta kwan fitila bai tsira ba, da bed-side lamp, duk sun yi kwatsa-kwatsa ga jinin da ya tabbatar na Mu’azzam ne ya disa a wurare daban-daban.
Tsoro, mamaki, fargaba da tu’ajjibi suka cika Hamoud, rokon Allah yake cikin zuciyarsa ya sa ba Mu’azzam ne da kansa ya aikata hakan ba. To in ba shi bane wanene? Da sauri ya fito daga dakin ya rufe, ya nemi wanda zai iya kwana cikin dakunan dake kasa ya sauka a ciki.
Da safe da yaron Mu’azzam ya kawo masa karin kumallo ya tambaye shi dalilin da ya sa bai share gilassan dakin Mu’azzam ba, yaron ya ce, ba’a yi masa izinin shiga ba, amma ya share na falon kasa yanzu, jiya duhun dare bai barshi yayi aikin ba, amma shi zai iya shiga ya share na bed-room din tunda shi dan uwansa ne.
Hamoud ya karbi abin shara da mopper ya nade hannun riga ya shiga aiki, ya share dakin tas, ya goge ko’ina, ya feshe dakin da freshners, sannan ya yi wanka yaci abincin da aka kawo masa yayi shirin tafiya asibiti.
Ya samu su Daddy cikin kyakkyawar kama fiye da wadda suka zo a cikinta, an yi musu wanka, an sauya musu kaya, ga abinci mai rai da motsi suna ta ci, ya bi su daya bayan daya yana runguma yana hawayen farin-ciki. Sannan ya gaya wa Daddyn Mu’azzam abin da ya gani tun shigarsa gidan Mu’azzam.
Nan Daddyn ya ce da shi, kada ya damu, ya san likitoci suna kula da Mu’azzam yadda ya kamata yanzu haka, kuma sai ya dauki tsawon watanni zai fito daga hannunsu.
Cikin bayyanannen mamaki Hamoud ya tambayi Daddy Ishaq wanda ba ciwo ne kadai yake nukurkusar shi ba, ya maida shi ba umh ba uhum umh, ya fiddo tsufansa zahiri wanda jin dadi ke boyewa a baya, sai ido da dogon karan hancin su na iyalin Raazee kadai ya rage a fuskar ma’abociyar zati da kamala, illa rashin ‘Aboulkhair’ da Malam ya gaya masa. Koyaushe za ka same shi rike da carbi, rokon Allah kawai yake ya yi wa Aboulkhair rahama da gafara. Ya hada fuskokinsu da alkhairi. Yasa can ta fiye masa nan. Halin sa nagari ya bishi. Rayuwar duniyar bakidaya ta fice mai a ka.