AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

“Daddy, Mu’azzam yana da disorder ne?â€
Ya tsinkayo muryar Hamoud can saman kansa yana tambayar sa. Cikin murya mai ban tausayi da bayyanar da kauna.
Daga masa kai kawai ya yi, hawaye na bin fuskarsa na tausayin Mu’azzam. Ya san tabbas Mu’azzam ya yi dauriya, ya yi dauriya, ya yi dauriya har an zo gejin da kwakwalwarsa ta kasa jurewa, ciwonsa ya tashi, da taimakon rashin magani da baya sha. Shine ya yiwa gidan sa wannan aika-aikar. Wadda rabon da ciwon ya sake tashi yayi irin haka anyi shekaru tara.
Hamoud gefe ya koma ya sharbi kukansa mai isarsa, tausayin Mu’az da kewar Aboulkhair ya lullube masa zuciya, yana sharar hawaye da hankicin sa yake fadin.
“Ubangiji ka saukaka muna! Idan laifi muka yi gare Ka Ya ubangiji Ka gafarta mana!â€.
Ya durkushe a wurin yana ta kuka. Daddy Ishaq ma na yi wiwi. Tunda aka fada masa rasuwar Aboulkhair bai yi kuka ba sai fa yanzu. Da Hamoud ya gaya masa halin da Mu’az ke ciki. Ga gabban jikinsa na zogi ta ko’ina, kashi yana hadewa da dan uwansa.
A fili yake fadin,
“Ya Arrahmanurrahim ka saukaka muna! Mun tuba Yaa Ubangiji mun tuba! Hamoud da gaske ne na rasa ABOULKHAIRI???â€
Hamoud babu baki sai kuka, da istigfari a fili da yake ta yi.
Likita ne ya bude kofa ya shigo jin koke-kokensu, ganin halin da suke ciki ya ce da Hamoud zai hana shi zuwa asibitin kwata-kwata idan raunata majinyatan zai dinga yi, maimakon ya karfafe su sai ya zo ya raunana su?. Da hannu biyu Hamoud yake rokonsa kada ya hana shi shigowa wajen Kawunninsa. Yana ta kuka a fili kamar ba namijin soja ba, sojan ma na sama. Likitan ya ce, to ya daina kuka a gabansu. Rantsuwa ya shiga yi masa kan ba zai sake ba, amma kar ya hana shi ganinsu. Tausayi ya sa likitan ficewa daga dakin. Ya sayo musu kofa a hankali.
******
Sauki na samuwa gare su a hankali a cikin gangar jiki, amma ban da a zuciyoyin su. Sun gaya wa Hamoud za’a sanya wa Daddyn Aalimah kafar plastic leg da zarar ya samu lafiya. Mu’azzam ya sakar musu katunan bankinsa na bankuna guda biyu; WellFargo da JPMorgan Chase ya ce komai a cira a yi musu, komai ake bukata a cira kawai. Wannan nauyin ya dora shi ne a wuyan tsohon likitansa kuma wanda za’a iya kira amintaccen sa a Las Vegas bakidaya duk da a haife ya haife shi wato Dr. Nebrass Sheldon, wanda ya yi retire shekarun baya, daga baya kuma ya bude private clinic nasa na kansa. Shi ne amintaccen Mu’azzam sabida dadewar da yayi karkashin kulawarsa tun farkon lalurarsa, shi ya daurawa alhakin kula masa da iyayensa da ya kawo asibiti kafin gushewar nasa hayyacin. Yana karkashin kulawar manyan likitocin kwakwalwa yanzu haka abokan aikin Aboulkhair, karkashin jagorancin Dr. Nebrass din wanda yayi gaggawar nema bayan dawowarsa kamar yadda Malam Raazee yayi masa umarni.
A baya Nebrass ya damkawa Aboulkhair file din Mu’az, kulawar sa da komai da ya danganci lafiyarsa ya koma hannunsa, amma bayan dawowarsa daga tafiyar da yayi zuwa gida Niger da rasuwar Aboulkhair zaune cikin kwakwalwarsa, dole ya nemo Nebrass da ya fahimci yana cikin risk na tashin ciwon sa a kowanne lokaci daga yanzu, da kuma rokon da Malam Raazee ya yi masa na ya kai kansa ga likitocin sa, in ba haka ba bazai bar su Daddy a hannunsa ba.
Ko kafin Nebrass ya iso gidansa don ya duba shi, kasancewar baya gari yayi ‘yar tafiya zuwa Orlando Mu’azzam ya riga yayiwa gidansa mummunar illah, ya ji wa hannayensa ciwo, yayi asarar dukiya mai yawa, ya shiga black episode na aggressive tendency sabida ya dade baya shan magani kuma ya kasa karbar reality na rashin Aboulkhairi na har abada a tare dashi….
Nebrass da Daddy sun san juna tsayin shekaru goma sha a baya, tun Mu’azzam na Boston yake dubashi kafin ya shiga jami’a a nan Nevada (Las Vegas). Wato tun dawowarsu Massachusetts sakamakon lalurar Mu’azzam, aka hada shi da Nebrass a matsayin mashahurin neuropsychiatrist din da babu kamar sa a U.S. Tsayin lokacin da Mu’azzam ya dauka yana karbar treatment a hannunsa ne ya haifar da aminci da girmama juna a tsakaninsu, Nebrass ya zama kamar Babansa sabida ya manyanta. A wani bangaren abokin sa. Sannan Mu’azzam na yi masa alheri sosai.
Daddy na kan gadon asibiti, ga dori a ko’ina a kafafu da hannayensa, amma sosai yake magana, yana kuma gane komai da kowa da ke kansa sabanin su Aboubacar. Nebrass ya sameshi a wannan ranar da daddare, ya gaya wa Daddy kudin account din Mu’azzam sun yi kasa sosai, jinyarsu da tasa (wadda ta fi tasu cin kudi) ya lamushe komai, jinya a turai ba wasa bace har ta rayuka uku ban da shi uban gayyar mai karbar (special psychiatric care), ya kara da cewa ya yi reporting din rashin lafiyar Mu’azzam a kamfanin su a matsayin sa na likitansa don haka sun bashi isashshen hutu har zuwa ya samu ingantacciyar lafiyar da yake ganin zai iya komawa bakin aikinsa.
Kamfanin man petir na Chevron na ji da Engnr. Mu’azzam Ishaq Razee sabida hazaqarsa da zurfin ilminsa, don haka yana daga cikin ‘yan gaba-gaban goshin da ake ji dasu a Chevron Corporation. Ya gayawa Daddy salary account din Mu’azzam baya hannun sa, Mu’azzam bai bashi ba, kuma a halin da yake ciki bazai iya tambayar sa ba, don haka kudi tafiya suke ba sa shigowa.
Daddy ya ce ya zo masa da waya ya kira Mummy Zulaiha.
Mummy, wadda ke can Niamey cikin sabuwar rayuwa ta dayanta Allah da jin tsoronsa hadi da jingine farin ciki baki daya a muhallinsa, ta amsa wayar mijin nata a can kuryar dakin Inna Bintou. Gaba daya Mummy Zulaiha ta zama kashi da rai don rama, idanunta kyawawannan sun zama abin tsoro sabida yadda suka zurma cikin kwarmin idanunta. Fatar bakinta ta bushe rayas, alamun babu isasshen ruwa da jini a jikinta. Sakamakon rashin cin wadataccen abinci na lokaci mai tsawo. Tsufan ta da gayu ke boyewa a yanzu ya fito sarari bakidaya kowa na ganinsa.
Daddy Ishaq yace.
“Ku yi shiri ke da Gumsu ku dawo, ku taho da Khaleesat da Yesmin tunda mijinta yana nan tare da mu. Ki nemo (credit cards) dina a suitcase dina ku zo da su Las Vegasâ€.
Muryar Mummy Zulaiha gaba daya ta dushe sabida yawan kuka, wanda ya zama babban abin yinta tun ranar da aka ce da ita babu Aboulkhair, tun ranar da ta bude kyallen da aka rufe shi ko fatar fuskar sa ba ta yi saura ba, ta zagwanye kamar konewa ta wuta a sakamakon munin hadarin mota, al’amarin da ya jefa ta a wani hali na kaka-ni-kayi, har yau kuma ba ta fita daga cikinsa ba, da tashin hankalin da faruwar hakan ya jefa ta a ciki.
“Daddy Aalimah fa?â€
Mummy ta tambaye shi, wasu sababbin hawaye na tsinke mata. Jin cewa zasu koma rayuwa a Boston, babu Aboulkhairi babu mai dakinsa Aalimah.
Shi ma hawayen yake yi, ya ce, “Zulaiha babu magana a kanta yanzu sai ta haihu. Ki barta kusa da mahaifiyarta zata fi sakewa. Kuna tare ne?â€
Mummy ta rushe da kuka wurjanjan.
“Daddy cikin ma babu shi, ya tafi tare da Babansa. Na rasa laifin da mu kai wa Ubangiji Daddy, ya yi mana wannan talalar a lokaci daya…â€.
“A’uzubillah! Kul Zulaihatu! Maza ki yi istigfari ga wannan sabon. Shi Ya ba mu, ba tareda mun san zai bamun ba, kuma Ya ga damar karbe abinsa a lokacin da ya ga dama sabida ya fi mu bukatarsa. Maza ki yi tuba ga sabonki Zulaiha, ki gode maSa da kyautar rayayyun ‘ya’ya har guda hudu da ya bar maki. Ki roka musu rayuwa mai tsayi da albarka tareda ke.
Hakika rashinsa ba karamin rashi ba ne gare mu baki daya, amma tunda Mu’azzam ya jure ke ma za ki iya jurewa. Ki yi hakuri Zulaiha kin ji, ki yi hakuri, ki yi hakuri ki fauwalawa Ubangijiâ€.
Mummy na ci gaba da kuka da hawaye da majina, ta ce,
“Na yi hakuri Daddy, na yi hakuri. Ya ya jikinku?â€
“Muna kara samun sauki kullum cikin rahamar Allah, har an sayo kafar da za a sanya wa Mansour. Ki gaya wa Aalimah ya ce yana gaishe ta, amma ba yanzu zan hada su su yi waya ba, ina so duka su kara samun sauki a zukatansu tukunnaâ€.
Mummy ta ce,
“Daddy ko kudin tikiti babu a hannuna, namu duk sun yi expire, dole in shiga cikin tsohuwar ajiya ta. Allah sarki Mu’azzam, yau shares (hannun jari) din da ya saya min da kudina zasu yi mana ranaâ€.
Ya ce, “Amfanin neman naki kenan ai, ki rufa min asiri a sanda na gaza, ni ma yanzu aljihuna zan shiga mun cinye na Mu’azzam tas! Rayuwa kenanâ€.
7/4/21, 10:50 AM – Buhainat: KWATARKWASHI