AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Duk abin da Ishaq Raazee da dansa Mu’azzam suka mallaka cikin asusunsu na bankunan kasar America ya kusa karewa a wannan doguwar kwanciya jinyar ba da sanin kowa ba daga shi sai matarsa. Bayan su Mummy sun koma Hamoud ya hadu da amaryarsa Khaleesat don shi da direban Mu’azzam suka je debo su daga filin jirgi, sai dai kowanensu zuciya ba dadi. A motar babu wanda ya yiwa dan uwansa magana.
Kai baka ce masoyannan bane masu neman cinye juna sabida soyayya gabanin faruwar wannan al’amari. Saidai ko yaya Khaleesat ta motsa sai ta hango idanun Hamoud akanta ta mudubin motar tana mai mamakin rama da jemewar da yayi cikin ranta. Ta ji zuciyar ta ta tabu. Amma kallon su take shi da aurensa dake kanta matsayin silar rugurgujewar farin cikin iyayenta da ‘yan uwanta.
Dukkansu a tankareren gidan Mu’azzam suka sauka bayan Mummy ta je Boston ta debo katinansu na banki kamar yadda Daddy yayi mata umarni.
Mummy na tausayin wadanda ke kwance a asibiti, amma hakika tana tausaya wa Hamoud da Khaleesat. Wadanda suka dauki alhakin faruwar komai suka dora a kan ‘AURENSU’. Dalili kenan da ya sa suka bi suka tsani auren bakidaya. Har basa son ganin juna. Ga su dai a gida daya, amma Mummy sai ta takura wa Khaleesat ta ke gaida mijinta Hamoud da safe. A cewarta ita bata son ganinsa. Wajen aikinsa nata bukatarsa amma ya kasa tafiya ya bar Kawunninsa a gadon asibiti. A satin da su Mummy suka zo aka ci gaba da ba su treatment domin kafin su zo an yi suspending medical treatment dinsu saboda karewar kudin da ke cikin duka account din Mu’azzam dake hannun Dr. Nebrass.

A kokarin Mummy na rage musu kashe kudi, ta dakatar da sayo wa Hamoud abinci a restaurant da yaron Mu’azzam ke yi sau uku a rana, maimakon hakan sai ta yo cefane mai dimbin yawa ta ke dafa musu bakidayansu, su dama majinyatan asibitinsu ne ke ba su. Wanda ya dace da lafiyar kowannensu.

Mummy na zaune ita da Hamoud a falo aka kira shi a waya. Tana gani ya share kiran, akayi-akayi ya ki dagawa, shi kuma bai kashe ba.
Ta cira kai daga abinda take yi tace, “Mahmoud ba kiranka ake ba ne?â€
Ya ce, “To ya zan yi Mummy? Su na gaya min ne hutun da aka deba min na aure ya kare in koma bakin aiki, ni kuma Mummy ba zan iya ba, har yanzu cikinsu babu wanda ya fara taka kafafunsa a kan kasaâ€.
Idanunsa suka kada suka yi jajir, ya ce,
“Mummy duk aurenmu ne ya jawo ko?â€. Ya fara kuka.
Mummy ta tashi ta koma kusa da shi, ta manta da surukuta tasa hannu ta dafa bayansa tana rarrashinsa, sai ga Khaleesat ta fito daga kitchen da faranti shake da abinci a hannunta. Tana ganinsa yana kuka wani abu kamar kibiya ya soki zuciyarta, ta saki farantin a kasa, ita ma ta yi kan Mummy tana kuka.
“Mummy da na san abin da zai faru ke nan, da ban ce ina son auren ba!â€.
Hamoud ya dago daga jikin Mummy jin abinda ta fada, yai mata wani irin kallo da saida Mummy ta rasa inda zata sa kanta don kunya, yace.
“Yanzu ne kika san hakan???â€
Tace “ko dama can ni ban shirya aure ba, takura min ka yi†yace “nikuma fa da aka takurawa in taimaka in aure ki da wuri ake son yi miki aure ana tsoron kada ki rasa miji?†Sosai Khaleesat ta kulu da jin gorin da yayi mata tace “Ni ce zan rasa mijin? Ai wallahi ka dai fada ne kawai amma nice nayi maka alfarmaâ€.
Mummy Zulaiha ta rasa yadda za ta yi da su Khaleesat, suna manne jikinta sai gori suke jefawa juna, amma kallo daya zaka yi musu ka fahimci fatar bakin su ce kadai ke magana amma cikin kwayar idanunsu kauna ce da soyayya zallah. Cece-kucen su da kukan Khalisat shi ya jawo Gumsu da ke kitchen.
Ta fito ta tsaya daga bakin kofar shigowa falon da ludayin miya a hannunta, hannunta daya ta sa ta kama kugunta, daya hannun ta nuna su da ludayin miyar hannunta, ta ce.

“Mummy, me nake gani haka? Wannan wace irin tabara ce? Kukan soyayya ne wannan ko mene ne???â€

Mummy ta ce, “Taya ni gani dai Gumsun Babansu. Sun bi sun daga min hankali. To wallahi ba zai yiwu ba, ba za ku kara min hawan jini da tashin hankali kan wanda nake fama da shi ba.
Ka yi muku booking ku tafi, in ji da majinyatan da ke gadon asibitiâ€.
Khaleesat da Hamoud suka hau hararar juna, tareda janyewa daga jikin Mummy a lokaci guda, kowanne kamar ya rufe dan uwansa da duka haka yake ji. Gumsu ta yi dariya tace,
“Karshen munafurci yau ina ganinsa a gidan nan. Don Allah ku soke juna da mashi sannan zan yarda kun daina son junaâ€.
Babu wanda ya kula ta a cikin su.
Hamoud ya tashi ya bar wajen, ita ma Khaleesat haka, amma yana shiga daki ya zauna a bakin gadonsa sai ya samu kansa da sakin murmushi, wani irin lallausar murmushi wanda rabon sa da yin irinsa har ya manta. Zai iya cewa tun faruwar al’amarinnan ga ahalinsa rabon da murmushi ya ziyarci fatar bakin sa. Kalaman Khaleesat da yanayin innocent fuskarta a sanda take fadar su yake tunawa daya bayan daya suna ta sanya shi murmushi. At last she’s mine. Ya fada a hankali, ya mallake ta ta zama tasa da dadi ba dadi. Sai kawai ya hau duba travel routine na kasar Japan kamar wanda ake yiwa umarni. Koda yake umarnin ne Mummy ta yi masa amma mai kama da taimako a gare shi. Ita kuma Khaleesat tana shiga daki kayanta ta soma hadawa. Tana yi tana waiwayen kofa kada Mummy ko Gumsu su shigo su ga abinda ta ke yi.

Alhamdulillah a washegari Daddy 1 da Daddy 2 suka soma taka kafafunsu akan kasa. Da taimakon likitoci da malaman jinya, Aboubacar yana iya zama da kansa, ya samu lahani ne mai matukar hatsari, karfe ne da gilashi suka shige cikin cikinsa, kusan aikin da aka yi masa ya fi na su Daddy cin kudi, su sun taka kasa, shi kuma ya zauna da taimakon (pillow).
Suka yi hira da Hamoud sosai a wannan ranar inda ya gaya masa jibi zai koma bakin aikinsa, amma kafin nan yana matuqar son a barshi ya ga Mu’azzam. Aboubacar ya ce “idan Nebrass ya zo ka roke shi na ga alama yana da kirki. A hannunsu Mu’azzam yake a private clinic dinsaâ€.
Da shawarar Aboubacar Hamoud ya yi aiki. Washegari da Dr. Nebrass ya zo har kasa ya durkusa yana rokonshi ya bar shi ya ga Mu’azzam, shi yana yi Aboubacar na yi har da hawayen su, ya rasa yadda zai yi da su, shi da ma Daddy Ishaq bai sa aka ba. Ba su san Mu’azzam ba ne, yanzu haka ya dade da samun sauki, ba ya son ganin kowa ne. He prefers to be alone a irin wannan yanayin. Nebrass ya ce su yi masa alfarma ya fara neman izinin Mu’az din tukunna, kada su mayar masa da aiki baya.

Aboubacar ya ce,
“Ka gaya masa karfe da gilashi sun huda min hanta, ya bar ni in ganshi kafin in cikaâ€.
Hamoud kuma ya ce,
“Ka gaya masa gobe zan koma Japan, kuma sai na yi shekaru uku ban zo gida ba, zan tafi tare da kanwarsa, muna neman albarkarsaâ€.
Dr. Mansour ya ce, “Kada ka gaya masa na rasa kafa, amma ka ce masa I want to shed my tears before him, sannan ne zan daina jin rashin Aboulkhair da na yi. Sai na ganshi zuciyata za ta rage ciwo!â€

Dr. Nebrass ya ce, sakonnin sun masa yawa, ba zai iya rikewa ba, kowa ya rubuta nasa a takarda. Duk haka suka rubuta jiki na rawa suka ba shi. Ya dubi Daddy 1 (Ishaq) yana murmushi ya ce,
“Kai ba ka da sako?â€
Murmushi ya yi mai fadi (broad smile) ya ce a gajarce,

“Babu!â€.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button