AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Wanan kauna ta zahiri da badini da dan uwansa da ‘ya’yan ‘yan uwansa suka gwada wa Mu’azzam a kan idonsa, ta wadatar da shi da zuciyarsa, ya fahimci Mu’azzam din mutum ne abin so, mai matukar kima da daraja a gare su!!!.
****
Lokacin da Dr. Nebrass ya kai wa Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee sakon ‘yan uwansa da Baffansa, yana zaune gefen gadonsa na asibiti yana shan hot coffee. Coffee ne mai zafi da kauri wanda yayi daidai da yanayin da ake ciki na tsananin sanyi a birnin LasVegas a yammacin ranar wata Asabar. Yana sanye da thick coat ruwan toka a sama da karamar riga short-sleeved daga ciki da dogon bakin wando (Armani code). Suma ta taru a kansa sosai tasu ta buzayen usli duk da kasancewarsa ba ma’abocin tara ta ba. Amman zaman asibiti yasa yanzu ta taru sosai ta mummurde ta zama wani irin curl.
Takardun ya bi daya bayan daya cikin nutsuwa yana karantawa, Dr. Nebrass na tsaye a kansa yana son ganin reaction dinsa. A matsayinsa na likitansa komai na Mu’azzam din sai ya rubuta musamman ci gaba irin wannan ga lafiyarsa. Ana so Mu’az din ya dinga socializing da mutane na jikin sa musamman masoyansa irin haka, zasu taimaka kwarai wajen restoring farin-cikin da ya rasa.
Gani ya yi Mu’azzam ya yi dan murmushi abin da tun zuwansa gadon asibitin bai yi ba. Ya daga kai yana kallon likitan, murya a sanyaye cakude da damuwa ya ce,
“Haka Aboubacar ya ji ciwo???â€
Nebrass ya ce,
“Duk ya fi su jin mummunan rauniâ€.
Har zai gaya masa Dr. Mansour babu kafa, ya tuna ya ce kada ya gaya masa. Cikin lallashi da siyasa ya ce,
“In zuciyarka ba ta amince wa ganinsu ba zan ba su hakuri. Amma hakika sun damu sosai da son ganinka, musamman mai rauni a cikin, har hawaye yake min. Shikuma dayan dana ji sun kira, Hamoud, daga yanayin sa zai iya bada komai da ya mallaka don ya samu ganin ka ko sau daya ne kafin ya wuceâ€.
Mu’azzam ya runtse idonsa, da sauri kuma ya bude su akan likitan ya ce,
“Let them in, please…â€.
Dr. Nebrass ya bude kofar, Hamoud ya turo Aboubacar a hankali kan kujerar marasa lafiya na musamman, wadda ke hade da na’urori a jikinta, Mummy ta turo Mansour Raazee kan kujerar guragu, Mu’azzam sai ya saki kofin coffee da ke hannunsa ya zube a kasa, kofin ya fashe, ya sanya fuska a tsakanin cinyoyinsa ya sanya kuka mai tsuma rai.
“Wace irin kaddara ce ta fado wa rayuwarmu haka?â€
Gumsu ce ta karshen shigowa, ta turo Daddy Ishaq a tashi kujerar, bai rasa kafa ko hannu ba, amma raunikan jikinsa da suka sha plasta Allah ya yi yawa da su. Har gaban Mu’azzam Mummy ta kai Daddy Mansour.
Matsawa yayi kusa da Mu’azzam din sosai ya runguma shi a jikinsa, ya kai hannu bayansa yana shafawa a hankali, yana mai magana cikin taushin lafazi, yana tunasar da shi ya godewa Allah cikin kowanne hali. Ni’imominsa gare mu sun fi jarrabawarSa yawa.
“Mu’azzam ka ce Alhamdulillah! Ka yi wa dan uwanka addu’ar samun rahma da gafarar Ubangijiâ€.
Wato duk inda Gumsu ta ke, sai an san tana wuri, yanzu ma cewa ta yi cikin kulawa,
“Doctor me Mu’azzam ke son ci in dafa masa gobe?â€
A hankali Mu’azzam ya cira kai yana son ganin wace ce wannan ana ta rai da lafiya tana ta abinci?
Ganin kallon haushin da yake mata ta ce, “Kalle ni da kyau, ni ce Gumsun Daddynku. Mu’azzam komai ya yi zafi maganinsa Allah, ka daina kuka ka kama hailala. Na fi ka jin rashin dan uwanka, ni abokiyarsa ce, abokiyar shawararsa. Amma na san soyayyata da shi shi ne in ta yi masa addu’a ba zubda masa hawaye ba, ka ji Mu’azzam?â€
Cikin ransa yake tambaya, ita kuma wannan wace ce a cikin dangi??
Dr. Nebrass surutun Gumsu ya fara hawa masa kai. To balle kuma Mu’azzam ya sani, don haka ya ce su koma su bar Mu’azzam ya huta, tunda sun ganshi.
Da ma motar asibitin da suke ce ta kawo su da taimakon Nebrass, aka maida kowa inda yake.
Mu’azzam ya jingina da taga yana kallonsu, ana sanya majinyatan a mota with care, iyayensa masu tarin koshin lafiya da kuzari. Wato rayuwa gaba dayanta ba ta da tabbas! Kuma dan adam har ya mutu ba’a gama mai halitta ba; yau Baba Mansur ne ya zama gurgu. Wasu zafafan hawaye suka kwararo masa. Fata yake ya bude ido ya ga cewa duka wannan mafarki yake yi, fata yake ya juya bayansa ya ga shigowar Aboulkhair rike da magungunan da zai sha wunin yau maimakon Nebrass. Fata yake ya juya ya ga shigowarsa da jarida ya zo masa da labari. Fata yake ya juya ya ji ya ce ya sauko kasa su ci abinci Aalimarsa ta dafa musu! Fata yake ya juya ya ji shi yana hawowa upstairs din gidan sa da takun nan nashi gudu-gudu, sauri-sauri irin na zaratan matasa masu cike da koshin lafiya da kuzari.
Hakika dan adan bai hada sani da Ubangiji ba; Da ya san rayuwarsa a Las Vegas gajeriya ce da ya bar shi sun zauna tare a gidansa kamar yadda Aboulkhair din ke matukar so. Da ya san rayuwarsa gajeriya ce a Las Vegas da ko kusa bai bari sun zauna a muhalli daban-daban ba. Da ya jure wa kowacce irin hayaniya ta Aboulkhair ya zauna tare da shi har karshen rayuwarsa…..!
Inama ana maida hannun agogo baya!!!
Ina ma… Ina ma… Da na sani… Duka abubuwa ne wadanda dan Adam ba shi da maganinsu! Wadanda ba sa wanke zuciya a lokacin da suka riga suka yi wa zuciyar kawanya… Azabtar da zuciya suke don sun san cewa sun riga sun yi mata illa ta ko’ina. Kalmomi ne da ya tabbatar ba za su daina yi wa kunnuwansa azaba da amsa-kuwwa ba, daga yau har zuwa karshen rayuwarsa.
7/4/21, 10:50 AM – Buhainat: ADAMA DAUDA
“Daure ki sha, ko kurba uku ne kin ji?â€
Juyar da kai ta yi cikin son fashewa da kuka. Mama ta sake komawa barin da ta juyar da kan cike da damuwa da kofin mug na tangaran a hannunta mai cike da kunun kanwa.
“Kin san jikinki jikin jego ne Aalimah, ki dinga shan kunun nan ko da ba za ki ci komai ba bayan shi. A ce magana daya kullum sai an yi ta nanata ta kamar cin kwan makauniya?â€
Fuska ta sanya cikin tafukanta biyu ta fara wani irin kuka. Wanda ke tasowa tun daga karkashin zuciyar ta. Sautin sa na mai bayyana halin kunci da ragaita da zuciyarta ke ciki.
“Ni Mama ki rabu da ni, don Allah ki kyaleniâ€. Ta furta cikin wata murya mai ban tausayi.
Daidai lokacin da likitar da ke kula da ita ta bude kofa ta shigo da Nurse biye da ita. Cikin sakin fuska ta isa gaban gadon da Aalimahn ta ke, inda sabo sun saba da wannan kukan na Aalimah tun kwantar da ita a asibitin. Gata bata jin lallashi. Tausayi dattijuwar take bata sabida yadda ta damu da ‘yar tata. Ta karbi kofin daga hannun Mama, ta cire hannun Aalimah daga fuskarta, wanda tuni ya jike sharab da hawaye.
“Mrs. Aboulkhair ba sai na sake maimaitawa ba, jikinki yana bukatar sinadarin abinci mai gina jiki, kada ki manta ‘Da’ aka cire a jikinki ba karamin ciki ba. Ki rage wa Maman ki da ‘yar uwarki damuwa ki dinga cin abinci kin ji?
Allah ba ya dora wa rai abin da Ya san ba za ta iya dauka baâ€.
Ta kai kofin kunun bakinta. Aalimah ba ta da zabi ban da kurbar kunun. Tamkar koyaushe dandanon abinci ya fi dacin madaci daci a bakinta. Amma saboda wannan taron dangin da suka yi mata, Dr. Rayhanah na yi, Mama na yi, dole ta shanye kofin kunun nan tsaf. Nurse da Doctor na kara lallashi, Mama ma na yi da tattausan lafazi, yayin da Basma ke zaune daidai kafafun Aalimah tana shayar da jaririyarta, Hussainar na goye bayan Mama.