AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Halin da suke ciki kenan tun bayan rasuwar Aboulkhair da tafiyar Daddy 1 da Daddy 2 da Aboubacar kasar Amurka. Ba su da kowa da suke gani su ji dadi sai junansu. Wata irin kewa ke rarake zukatansu da ciwo mai tsanani. As a husband, ya kasance miji abin kwatance, kasaitacce a zuciyar matarsa wanda babu wanda zai iya tona zuciyarta ya ga halin da ta ke ciki, sai ita kanta. As a brother, shi dan uwa ne like a diamond a wajen kannensa, babu mai iya tona zuciyar Basma don hango zurfi da fadin wannan rashin da ta yi sai ita kanta. Amma sosai ta fi Aalimah juriya, domin ba a fada da ita a kan cin abinci ko don jariranta su samu nasu abincin da Allah ya halitta a jikinta. Sosai ta ke cin abinci, sai in abin ya ciyo ta ne ta ke dangwarawa Mama su ta kulle kanta a toilet ta yi ta kuka.
Yau likita ta ba su sallama, ba don zukata sun warke daga zogin da suke ba a’ah, sai don dukkaninsu suna da lafiya ta gangar jiki. Suka tattara suka koma gida, mama na ci gaba da gasa wa Aalimah da Basma jikinsu da tawul. Sun samu wayar Mummy da Aunty Gumsu inda suka yi musu sallama suka ce za su koma su ma don jinyar su Daddy, saboda Hamoud zai koma bakin aikinsa. Lokacin da suka bai wa Khaleesat wayar don ta yi sallama da su, domin tare da mijinta za ta wuce daga can ba su tsinana komai ba su duka ukun a handsfree sai kuka.
Mama ce ta kwace wayar. Tun daga ranar ba su kara ji daga su Mummy ba, suka ci gaba da jego karkashin kulawar Mama.
Ranar da Basma ta yada wanka aka yi arba’in din Aboulkhair a Yamai, sakon Malam Raazee ya isko su cewa, dukkansu su yi shiri su koma Niamey, zuwa har su Aboubacar su dawo gida. Mama ta soma yi musu shirin tafiya, an yi sa’a su Sabrina suna cikin hutun makaranta.
Basma ce ta saya musu tikiti, daga na Abuja har na Niamey. A washegarin ranar suka daga bakidayansu bayan Mama ta sallami masu aikinta Tabawa da Sabira da cewa inta dawo za ta neme su su dawo bakin aiki. Bilyaminu ya yi musu fatan alkhairi bayan Aalimah ta biya shi kudin aikinsa na gadi, har na wata uku masu zuwa a gaba.

A dakin inna Bintou suka sauka, Mama na dakin Inna Kasisi. Tunda suka zo Basma ba ta san kukan jariranta ba, kullum suna goye a bayan Bintou da Kasisi, idan Malam ya dawo zai ce a kai masa su su taya shi hira. Inna Bintou ba ta barinsu su zauna zugum-zugum din da suke zama, yanzu za ta dauke musu hankali da hira ko da ba za ta samu su tofa albarkacin bakinsu ba sukan yi murmushi. Ta ce Basma ce mai sa wa a yi kuka, don haka ta koma dakin ‘yammata ta bar mata Aalimah mai maida komai ga mahaliccinta.
Abin da ba ta sani ba har gara Basma na yin kuka ta ji dadi a zuciyarta, ita al’amarin da ta ke ji a tata zuciyar yanzu bayan dawowarsu Yamai ya fi karfin ta zubda hawaye. Baza ta gaji da cewa mutuwar Aboulkhair ta shammace ta ba; muguwar shammata. A daidai lokacin da take ganin babu diya macen data kaita sa’ar samun farin cikin dake cikin rayuwar aure. Rokon Allah ta ke yi ya dau ranta ta bi Aboulkhair a ko’ina yake, kuma cikin kowanne hali, a ganinta hakan shi ne kawai kwanciyar hankalinta da samun farin cikinta.
Ba ta son tuno komai na rayuwar da suka shimfida tare. Idan ta kai hannu ta shafa cikinta ta ji shi ma babu, zuciyarta neman fitowa ta ke daga allon kirjinta. Hakika an jarabci rayuwarta da mafi tsananin jarrabawa, tana rokon Allah cikin sujjadar kowacce sallar farillarta, ya kawo sanadin da za ta cinye wannan jarrabawa idan mai cinyuwa ce. Domin ta shafa a ko’ina ba ta ga ranar da za ta haye ta ba. Idan dawowar farin ciki cikin rayuwarta shi ne tsallake wannan siradin, tana da tabbacin har abada ba za ta tsallake shi ba. Ba mutane irin Aboulkhair ke shigowa cikin rayuwar dan Adam su fita da sauki ba. Ba mutane irinsa ke ajiye memories irin wadanda da za’a iya daina tunawa cikin rayuwar auratayya ba.
****

        A LAS VEGAS

Watanni hudu kenan da faruwar wannan al’amari ga iyalan Raazee. Cikin wadannan watanni al’amura da yawa sun faru, majinyatan suna ta samun sauki cikin yardar Ubangiji. Dorin Daddy 1 da Daddy 2 na kafafu da hannaye duka ya yi kyau, an kuma kunce. Daddy 1 na tafiya da taimakon croches karafa guda biyu, yayin da Daddy 2 ana jiran raunin kafarsa ya karasa warkewa a makala masa plastic leg, wadda Mu’azzam ya saya masa. Aboubacar ya warware bakidaya sai dan sauran abin da ba’a rasa ba, don haka aka soma yi masa shirin tahowa gida don komawa cikin iyalinsa.
Duk tsawon zaman jinyar nan da Aboubacar ya yi ba su yi waya ba shi da Basma, asibitin ba sa barin majinyatansu rike waya don samun cikakkiyar nutsuwarsu. Haka Hamoud da ya wuce Japan shi da Khaleesat bai hada su sun gaisa ba ko sau daya. Mummy da Gumsu da ke yawan zuwa ganinsu, sai dai su fada masa lafiyar Basma data jikokinsu twins Don haka a yau da likitoci suka tabbatar masa da samun lafiyarsa suka kuma ba shi sallama, cike ya ke da dokin ganin iyalinsa.

Ba yadda Mummy Zulaiha ba ta yi da Aboubacar ba a kan ya kara sati daya ko ya kara murmurewa ya kara samun karfin jikinsa, amma Aboubacar ya ki. Yace Basma ta karasa jinyarsa. A daddafe ya kara kwana uku a gidan Mu’azzam bayan sallamarsa daga asibiti. Mummy ta saya masa tikiti mai zuwa Niamey kai tsaye daga Las Vegas babu transit.

Mummy Zulaiha a wannan dan lokacin ta yarda kishiya ‘yar uwa ce (idan ka yi katari da mai kyakykyawar zuciya kuma ta kirki). Gumsu ta zama kamar kanwarta ta jini, tare suke gudanar da dukkan al’amuransu na yau da kullum a gidan Mu’azzam, kama daga girki yau wannan ta yi, gobe wannan ta karba, jinyar mijinsu da dan uwansa da taimakekeniya a tsakaninsu. Gumsu-Moiram, ba ta da matsala ko kadan, ke dai barta da wauta, ban dariya da barkwancinta wadanda ke sayo mata soyayyar jama’a, inda duk ta zauna sai an san da ita a wurin saboda ban dariyarta. Mummy ta samu kanta da jin kunyar kanta in ta tuno haukan data rika yiwa mijinta da ‘ya’yanta akan auren Gumsu. Ita kam in haka kishiya take, to tana alfahari da tata, da zuciya daya take son ‘ya’yan ta. Sai ka rantse da Allah kwanciyar mijinsu jinya ba ta dame ta ba, harkan gabanta kawai ta ke, shi ma kansa Daddyn gaya masa ta ke a gaban kowa.
“Gara ma ka mike daga jinyar nan haka Daddy, Allah ya gani na yi hakuri. Gumsu ba ta da wani mijin bayan kai, ya ya ka ke so ta yi da ranta?â€
Ko a gaban likitoci Gumsu kan fadi wannan magana idan ta bushi iska, sai dai Daddyn da Mummy su ji mata kunyar ita babu ruwanta.
Bayan tahowar Aboubacar, ya zama daga Daddy 1 sai Daddy 2 a gadon asibiti. Ba dakinsu daya ba, kowa da dakinsa daban, amma suna yawan haduwa, in an fito da su shan iska a garden din asibitin ko an fito da su motsa jiki a gym. A nan ne su kan yi hirarrakinsu da suka shafe su ko ‘ya’yansu, da kuma iyayensu da ke gida Niger.
A yau ma kamar kullum, an fito da su ‘garden’ domin shan iska. Daddy 1 ( Ishaq) ya dubi kaninsa Daddy 2 (Mansur) ya ce,
“Ina lissafe da watanni, Aalimah ta dade da gama takaba, me ka shiryawa rayuwar ta a bangarenka?â€
Daddy 2 yayi saurin girgiza kai, a sanyaye ya ce,
“Me kuwa na shirya mata ban da abin da Ubangijinta ya shirya mata?
Muna namu Allah na nashi, kuma nashin shi ne gaskiya, dukkanmu lalube muke yi a cikin duhu.
A da ne nake wannan wautar (future planning) ga ‘ya’yana, amma yanzu kullum cikin istigfari nake a bisa hakan. Duk abinda Allah ya shiryawa rayuwarsu dai-dai neâ€.
Daddy 2 ya yi murmushi, shi shaida ne a kan cewa Mansour ya fi shi shiga tashin hankali da rashin Aboulkhair, ya dade yana sambatu har a cikin baccinsa. Ko lokacin da ake masa gyaran karaya akwai Aboulkhairi cikin sambatunsa irin na radadin ciwo. Wani tunani ne mai nauyi ke yawo a zuciyarsa daga jiya zuwa yau, wanda ya ke tsoron furtawa gare shi, ko ko ya ce, ba shi da ikon furta shi ga kowa ko ta ina aka je aka dawo. Don haka ya ja bakinsa ya yi shiru, yana sauraron bugun da zuciyarsa ke yi, wanda ke tafe da sake da jaddada masa muhimmancin maganar da ba ya son yi din da kowa banda zuciyarsa a kowanne bugu guda daya na zuciyarsa, tunanin ya hana shi sakat, shi kuma yana bi yana danne shi da fin karfin zuciya da karfafa imani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button