AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

A yau ne aka sallame su bakidaya daga asibitin Southern Hills, direban Mu’azzam ne ya kwaso su dukkansu zuwa gidan Mu’azzam, Mummy ta ce ya lissafa mata albashinsu daga ranar da Mu’azzam ya shiga asibiti zuwa yau ta biya su. Budan bakin Harrison sai cewa ya yi, albashin shekara Mu’azzam yake kullawa a lokaci guda ya basu, kuma ko ba don haka ba shi mai hidimtawa iyayensa ne ko babu ko sisi sabida kyautayinsa, jin kansa da kyautatawarsa gare shi. Harrison ya kare zancensa da cewa;

“I wish him a quick recoveryâ€.

Ya fita ya bar falon. Fuskarsa dauke da alhinin rashin sanin halin da Ubangidan nasa ke ciki. Wanda yake jin kamar ya dauka ya mayar a kansa.

Falon ya saura Daddy 1, Daddy 2 da matansa guda biyu, Yesmin da Nurat sun fita da Harrison zai kai su saloon, Daddy 2 ya ce,
“To alhamdulillahi, ni ma lokacin komawata gida ya yi, wannan gari naku sai ku, sanyin cikinsa mai takurawa da matsantawa ne. Yaya Ishaq, Zulaiha, Gumsu-Moiram na gode da dawainiyar ku, Allah ya rubuta a mizanin Hassanaat na zumunci, ya sa ya zame mana silar shiga aljanna baki daya, Ya jikan Aboulkhair, halinsa na gari ya bi shi. I have missed a darling son but I’m sure Ubangiji Rahmanur-rahimu ya fi ni son shi….â€.
Bai rufe baki ba ya lura sun soma yin sana’ar tasu (sharbe) Zulaiha da Gumsu, babu yadda za’a yi a ambato Aboulkhair a waje ko a yi masa addu’a suna wajen ba su zubda hawaye ba. Don haka ya yi maza ya sauya zancen sa da tambayar Daddy 1 yaushe Mu’azzam zai fito daga asibiti?
Zai so ya ganshi kafin ya koma. Akwai zantuka masu muhimmanci da yake son yi da shi. A take Daddy 1 ya karbi wayar Mummy. Dr. Nebrass ya kira, suka yi magana ya maida wayarsa aljihu.
Ya dubi kanin nasa ya ce, sai sabon wata za su kyale Mu’azzam ya shiga harkokinsa, they are very cautious a kan aikinsu ba kamar kasashenmu na Africa ba, sai sun tabbatar ba shi da damuwar da za ta dami kwakwalwarsa, kuma zai iya aikinsa normally, sannan zai iya daukan al’amuran rayuwa a zahirin yadda suke ba tare da sun shafi matsalarsa ba, amma shi zai iya ganinsa idan Mu’azzam din ya amince.
Ko da Nebrass ya gaya wa Mu’azzam Kawunsa na son yin sallama da shi zai koma Nigeria, bai ki ba. Hasalima sosai yake son ganinsa shima, ko yana kin jama’a ban da kawu Mansour da Aboulkhair shi kansa bai san dalili ba. Watakila don sun fi kowa iya tafiyar da shi ne da odd behaviours dinsa (baudaddun halayensa). Tare suka shiga dakin Mu’azzam da yammacin ranar, inda suka same shi yana sallah, Dr. Nebrass ya fita, Daddy 1 ya zauna zaman jiransa ya idar yana jan tazbahar hannunsa.
Bayan ya yi sallama ya dade yana addu’a, ko ba’a tambaya ba Daddy 1 ya san me Mu’azzam yake roka. A yanzu ya sani ba shi da wata bukata mafi muhimmanci wadda ta wuce ta samun rahmar Aboulkhair a wajen Allah. A sanda yake raye, ba su da bukata mai muhimmanci sai junansu. Aalimah ta taba gaya masa sabida Mu’azzam Aboulkhair ya dage ya tsaya tsayin daka ya karanci neuropsychiatry.
Al’amarin da ya dade yana burge shi hadi da kayatar da shi a zuci. Ya dade bai ga ‘yan uwan da ke son juna fisabilillah irin Mu’azzam da Aboulkhairi ba ko a labaran hikaya. Ta kuma gaya masa irin takaddamar da suka sha da Mu’azzam kan su zauna gida daya amma ya ki amincewa. Ba ya karantar zuciya, amma ya san Mu’azzam na nan yana regretting. In ya ce regretting yana nufin nadama mai sa zuciya ciwo da hanata jin dadin rayuwa ko ta yaya. Allah kenan.
7/4/21, 9:48 PM – Buhainat: HABUBAKAR ADO

#

Cikin satin suka biyo jirgi da komai nasu suka baro kasar Amurka. Bari na din-din-din. Ishak Raazee na mai jin wata irin kewa wadda sabo ke haddasawa na mamayar zuciyarsa. Mummy na mai jin kamar ita daya ta rage a fadin duniya sabida kewar mijinta da ‘ya’yanta. Saidai ko kadan bata yi nadamar hukuncin da ta zartas ba. Yesmin na kuka kamar ranta zai fita a kan rabuwar iyayenta, suka taho shi da Moiram da diyarta Nurat, ya baro mata Yesmin ne don rage mata bacin rai.
Haka Mummy ta yi kokarin shanye damuwarta wannan karon ba tare da ta raba ta tare da Mu’azzam ba, ganin cewa bai jima da barin gadon asibiti ba. Kuma in ba za ta manta ba Aboulkhair ya hane ta dora wa Mu’azzam damuwa, ko dai ta shanye kayar ta ita kadai, ko ta raba ta tare da shi (Aboulkhair) din, amma sharing dinta da Mu’azzam babbar illa ce ga kyakkyawan treatment din da yake samu.
Ko da ta koma office a washegari da niyyar bada hakuri a maida ita bakin aikinta wani ta tarar a mazauninta (JP MORGAN CHASE) ba su daukar wasa da aiki, ko da kuwa da excuse. Balle ita nata babu excuse din ma. Rana daya aka nemeta a kasar aka rasa. Tsabar rudanin rayuwar data samu kanta ya mantar da ita cewa ita din ma’aikaciya ce, ma’aikaciyar ma ta babban bankin Amurka irin JP Morgan. Haka ta dawo kafafu a sage, ta soma neman wani aikin ta yanar gizo, amma har watanni uku suka shafe bata dace ba. Sakamakon matsin lambar da musulmin kasar ke fuskanta a lokacin daga sabuwar gwamnatin Amurka karkashin mulkin sabon shugaban kasa Donald Trump. Da yawa sai komawa suke kasashen su na asali. Ba don Yesmin da ke zuwa makaranta ba Las Vegas za ta tattara ta koma bakidaya, in Mu’azzam ba zai rike ta ba ita da autarta, ya san yadda zai yi da su. Shine kadai dolenta a yanzu.


     FLASHBACK

An sallami Mu’azzam ranar wata lahadi, sati guda kacal ya kara a gida, sannan ya koma aikinsa. Ya hada wayoyinsa, ya kira duk wanda ya dace ya gaisar. Ciki har da Mummy, ta gaya masa tana Boston amma ba ta gaya masa cewa Daddy ya sake ta a kansa ba. Sosai ta koyi hadiye damuwa, in ta tuna da Aboulkhair.
Ta san da yana raye ransa zai yi matukar baci, za ta kiyaye abin da ba ya so a bayan ransa. Ta kasance mai bata masa rai da hakan a sanda yake raye. Zata kasance mai kiyayewa a sanda babu shi. Ta ce masa Daddy yana Niamey, kuma ta turo masa kudi cikin account dinsa kafin ya samu albashi ya soma shigo masa ta san zai bukace su sosai.
Sosai ya yi godiya, yana mai jinjina soyayyar uwa ga abin da ta haifa, ta Mummy is special. Ita dai ‘ya’yan ta kawai. Su samu jin dadi shine burin ta. Kada su nemi wani abu su rasa a rayuwar su. Bazata taba canzawa daga hakan ba.
Ya kira Daddy suka yi hira sosai, inda ya gaya masa ya koma Yamai, ya samu aiki a can da hukumar hulda da kasashen wajen su, yanzu kuma ya samu wani makeken fili kusa da gida ya saya ya fara gini. Gini yake so ya yi one in town wanda dukkansu zasu sake a cikin sa.
Ya cigaba da gaya masa amon muryarsa dauke da kauna irin ta uba ga dansa, irin tsarin duplex din da yake so a yi masa. Yace sai yafi gidansu na Boston kyau nesa ba kusa ba, zai masa part din sa guda wanda zasu ke sauka in sun zo shi da iyalinsa. Sosai ya baiwa Mu’azzam dariya. Ya canza position din rikon wayar daga dama zuwa hagu ya cigaba da sauraron almarar Daddy. Koko ya ce mafarkin Daddy. Ba tare da Daddyn ya kula da karbar da yake yiwa zancen nasa ba ya cigaba da labarta masa cewa har dakin yaran su za’ayi a cikin bangaren nasu, a zuba duk wani nau’I na kayan wasan yara. Mu’azzam tausayin mahaifin nasa yayi matukar kama shi, su iyaye wato har kullum fatan su nagari ne ga ‘ya’yan su ba ruwansu da reality din da rayuwar ‘ya’yan ke fuskanta.
Ji yayi idanunsa na son kawo ruwa, don haka ya matsu su yi sallama da Daddy. Ko kusa bai yi masa zancen mahaifiyarsa ba har suka yi sallama, hausawa suka ce wai ido da kunya. Ba zai iya kallon tsabar idanun sa ya gaya masa ya saki uwarsa ba sabida ta zabi zama a kusa da shi ta bashi kulawa. Sai Mu’azzam ya dauka za ta bi su ne daga baya in ta gama kintsawa, tunda ita ma’aikaciya ce. Bincike-bincike da zakule-zakulen halin da wani ke ciki da ma tun fil azal ba halinsa ba ne shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button