AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Cikin dan lokaci Daddy Ishaq ya gama ginin kyakkyawan duplex dinsa a nan unguwarsu plateaux suka koma shi da Gumsu. Wannan ya kawo tabbataccen kwanciyar hankali a zukatan iyaye da ‘yan uwansa. Ranar litinin ya soma shiga sabon ofishinsa a Ministère des affaires ètrangères na kasar Niger.
Duk da ko kusa ba za’a hada sauki da sukunin rayuwar yanzu da wadda ya yi a baya ba, yafi jin dadin rayuwar yanzu, akan ta baya. Cike yake da godiyar Allah da ikhlasi a zuciyarsa, da albarkar iyaye baibaye da shi. Kullum sallolin su biyar cikin jam’i suke yin su shi da ‘yan uwansa da mahaifin su a masallacin dake like da (main house) dinsu. Babu wanda ya san ya saki Mummy, sai Malam da Inna.
Mummy ta dukufa neman aiki a yanar gizo don saving dinta ya fara yin kasa sosai. Kason data ke karba duk wata na shares dinta duk a cikin su da lalurorin yau da kullum yake tafiya. Rayuwar mai tsada ce sosai. Ta dukufa neman aiki ba ji ba gani amma kamar wadda uwa ta cewa jeki kya gani ko aptitude babu wanda ya kira ta duk da experience dinta. Ita ke dauke da nauyin karatun Yesmin, cinsu da shansu da maintenance din gidan, ga wanda ta ke turawa Mu’azzam duk da ba shi ya tambaya ba kuma ya hana ta amma ta ki ji, kullum gani take kamar albashinsa baya isar sa sabida tsadar magungunansa da rayuwar da yake yi mai tsada. Tana cikin wannan halin aka zo aka ce ta tashi daga cikin gidan masu shi za su shiga, aka nuna mata shaidar mallakar takardu da komai.
Ba da saninta ba Daddy ya dade da sayar da gidan ya karbe kudinsa ya tafi da su kasar haihuwarsa don ya gina gida acan, da kuma niyyar sa ta fara kasuwanci da su irin wanda ya taso ya ga Malam da manyan yayyunsa na yi, wato na shigo da kayan abinci daga kasar Faransa zuwa jihohin kasar Niger.
Bala’i goma da ashirin ga Mummy, Ishaq ya shammace ta, bata taba tsammanin zai sayar da gidan nan ba, daga karshe kan ba yadda zata yi ta tattara ta taho Las Vegas ita da Yesmin gidan Mu’azzam.
Mu’azzam sai dawowa office yayi ya gansu da iyayen kayansu tirim! Sun gyare dakin da Mummy ke sauka in tazo sun baje suna barcin gajiya. Ya tura Harrison yayo musu takeaway din abinci. Kwanansu uku kacal hayaniyar Yesmin ta fara hana Mu’azzam sakat, duk da kokarinsa na bin shawarar kawunsa Mansour na ya bude zuciyar sa ya kaunaci ‘yan uwansa, ya ba su kauna da kulawar da Aboulkhair ke ba su, yayi acting na mutum biyu a gare su, ya ga cewa abun kamar da wuya ba zai iya ba! Ya yi duk iya kokarin sa amma ya kasa. Mummy ta riga ta gama shagwaba Yesmin ta yadda bai isa ya tsawata mata ba yanzu zai ga bacin ran Mummy, kullum Yesmin sanyata take a gaba tana kuka wiwi kamar ‘yar goye kan wai su koma Boston bazata iya barin makarantun ta na can ba ko a maida ita cikin ‘yan uwanta. Ita bazata iya karatu a ko’ina ba sai a Boston. Mummyn kuma tayi ta aikin lallashi amma Yesmin ba ta fasa komai cikin shagwabar ta. Wannan ba karamin kular da Mu’az yake ba, yayi mata tsawa kuma cibi ya zama kari daga Mummy.
Zaman Mummy da Yesmin a gidan, su ba zuwan bakunta ba kamar yadda suka saba, a’ah, wannan karon zama suke nufin yi na har illa masha Allahu. Ba abunda yake so a rayuwarsa irin (kadaici) yadda zai samu damar ayyukan sa na office a nutse da zurfafa bincike akan aikin nasa. Amma shikenan yanzu bashi da hutu da nutsuwa a gidansa?
Kullum cikin ciwon kai yake kwana, muddin yana cikin gidan. Ga shi Mummy ta ce Daddy ya sayar da gidansu ne. Wato babu ranar da zasu bar shi ya sarara. Shi ba abun ya ce su tafi ba, ina za su je? Su dafa wannan su dafa wancan, duk gidansa ya dume da kamshin abinci kamar wani restaurant abin da shi kuma ba ya so tunda ba iyali ya aje ba. Mummy enjoys cooking in her life. Dabara ta fado masa, ba don ya gaji da mahaifiyarsa da kanwarsa ba sai don ya samu nutsuwa yadda ya saba. Ya kira Daddy ya hau rokonsa don Allah ya zo ya tafi da Mummy, ya gaya masa zamansu ya takura masa, basa barinsa yayi bacci da aiki a nutse. They are giving him headache. Yesmin is very noisy. Kuma Mummy bata son laifinta. Daddy ya yi ta dariya har da kyakyatawa har ya godewa Allah, a karshe ya ce da Mu’azzam.
“Shin mutum ya taba gajiya da uwarsa da kanwar sa?â€
Mu’azzam kamar zai yi kuka, ya ce, “Daddy ka fahimce ni, ni ba gajiya na yi da su ba, I love quietness, tunda suka zo na rasa samun sa, sannan suna mayar min da gida kamar gidan mata, alhalin ni ba aure ba. I want my house to be calm, cool, like before. Don Allah Daddy ka zo ka tafi da suâ€.
Damuwarsa ta bayyana karara cikin magiyarsa. Ga mamakinsa ko a jikin Daddyn sai cewa ya yi,
“Ku je ku yi ta cakudawa a haka, sonka ta ke, tunda har ta zabe ka a kaina. In ka ji ciwon kan ka sha paracetamol, in ka kasa zama da ita waye zai iya?
Gara ma ka sauya hali, ka fadada zuciyarka ka kaunaci kowa naka ka kuma koyi zama cikin mutanen da suka zame maka dole, don sauya maka akalar rayuwa zan yi bakidaya nan ba da jimawa ba, insha Allahuâ€.
Malam Raazee na cin tuwon dare Daddy Ishaq ya yi sallama, amsawa ya yi yana wanke hannunsa cikin bowl na silver. Daddy ya dauke kwanukan bayan ya gama wankewa ya yi gefe da su, ya zauna a muhallinsu.
Sake gaisawa suka yi irin gaisuwar su ta buzaye. Malam ya dube shi cike da kulawa yana tsane hannunsa da tawul. Ya ce,
“Ya ya Mu’azzam? Ya jikin nasa? Mun kwana biyu, ba mu yi waya baâ€.
“Mu’azzam yana lafiya, ko dazu ya kira ni…â€.
Nan ya ba shi labarin yadda suka yi dazu, suka yi ta dariya. Malam ya ce, “Ina ruwan Zulaiha, kaza uwar son ‘ya’ya, shi kuma dan gashi yana gudunta kamar kyanwa da beraâ€.
Daddy ya ce, “Abin da ta kasa ganewa kenan, shi Mu’azzam duk wata mu’amala in dai da shi za a yi ta, to a yi ta daga nesa-nesa, ko ya ya za ka zauna mai a gida, to fa zai ce ka takura masa. Zulaiha ta kasa ganewa, kodayake tausayinshi ta ke ji, shi kuma ba ya tausayin kanshiâ€.
Haka suka yi ta hirar Mu’azzam da Zulaiha suna cin dariya, Daddy Ishaq na fadin “Da kafarta za ka ganta ta dawo tunda masu gidan Boston suka bukaci abinsu, idan ita ba ta bar masa gidan ba na rantse shi zai bar mataâ€.
Aalimah ta yi sallama a dakin a hannunta karamar kwarya ce mai cike da nonon Rakumi mai dumi sabon tatsa, kai tsaye Malam ta nufa. Da murmushi a fuskarta ta russuna har kasa ta ce,
“Malam ga shi Inna Bintou ta ce a kawoâ€.
Hannu biyu ya sa ya karba ya ce, “Madalla da Bintou da jikanyar ta, an gaishe ku, madallahâ€.
Ta juya za ta fita, sai kuma ta dawo ta tsuguna.
“Malam Aunty Gumsu-Moiram ta yi min waya dazu tace in je in mata kwana biyu, na ce mata sai na tambaye ka tukunnaâ€.
Ya ce, “Ba yanzu ba Moiram ta yi hakkuri, bana so ki je ko’ina sai kin warware dukkanki, har yanzu ban ganki kamar yadda nasan ki ba, a bai wa Gumsu hakkuri inji niâ€.
Fuska a sake ta ce, “toh Malamâ€.
Ta juya ga Daddy ta gaishe shi cikin nutsuwa da sanyin muryarta.
Ya ce, “Anya Aalimah? Haka dan Adam zai rayu da damuwa bayan ba abin da za ta sa, ba abin da za ta hana? Dubi kasusuwan wuyanki, dubi idanunki yadda suka zuzzurma ciki. Don Allah don Annabi Aalimah ni Baban ABOULKHAIR ina mai cewa a karo na sau ba adadi, ki yi hakuri. Ki yi hakuri! Ki yi hakuri…â€.
Ko kafin ya kai karshe ya fahimci hawaye sun gangaro daga idanunta. Muryarta ba ta fita sosai. A sanda take cewa.
“Na yi hakuri Daddy, na dade da yin hakuri. Zuciyata ce ta ki daukar reality, ce min ta ke ba shi ne ya mutu ba, zai dawo. Don Allah Daddy da gaske ne??â€
Malam Raazee da Daddy Ishaq suka juyar da kai don share nasu hawayen.
Daddy ya ce, “Aalimah, wanda ya mutu ba ya dawowa. Ki yarda da ayar Ubangiji subhanahu wata’ala, kullu nafsin za’ikatul maut. Aboulkhair ba zai taba dawowa ba har abada. Ki bai wa rayuwarki da ke gaba kofa ko ya ya ne ta samu farin ciki kin ji Aalimah?â€
Daga kai kawai ta yi, don ba ta da abin da za ta yi bayan daga kan, ko ta yarda ko ba ta yarda ba, ya ce,
“Tashi je ki cikin ‘yan uwanki, Allah ya yi miki albarkaâ€.
Jiki babu lakka ta mike ta wuce cikin gida.
Bayan wucewarta da minti biyar daga Malam har dansa Ishaq babu wanda ya kara yin magana. Daga bisani Malam din yayi gyaran murya ya ce,
“Ni sai inyi ta wani tunani, a duk sanda Aalimah ta zo gabanaâ€.
Daddy ya ce,
“Tunanin mene ne Malam?â€
Malam ya girgiza kai, har da daga hannaye sama ya ce, “Uhum-um-umh-uhm, a bar kazar ‘yan boko cikin gashinta, yanzu in aka yi kokarin fige ta sai kun dawo da George Bush da Mungo Park gidan nan sabida kawo nassi na bijirewa da nuna kin amincewaâ€.
Murmushi Daddy ya yi, shi ma zuciyarsa ta yi nauyi. Babu mamaki idan ba irin tunaninsa Malam Raazee ke yi ba. Bai ja zancen da nisa ba ya yi wa Malam din sallama ya mike ya kwashi takalmansa ya fice don tafiya gidansa, wanda ba shi da nisa da gidan iyayensa trackable distance ne.
7/5/21, 8:20 AM – Buhainat: ADAMU DANKOLI