AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Mu’azzam ya mike daga kan abin sallarshi ya samu kujerar zaman mutum guda kusa da Kawun nasa wanda ke zaune cikin kujera ya zauna. Ya yi zurfi a tunanin da yake yi, har bai san sanda Mu’azzam ya zauna kusa da shi ba. Ajiyar zuciya ya saki lokacin da ya ji muryar nan ta Mu’azzam mai taushi da gardi a kunnuwan mai saurare na tambayarsa ko shi kadai ne?
Ya ce, “Eh, Harrison ya kawo niâ€.
“Ina Daddy da Mummy da wannan matar Daddyn mai surutu?â€
Daddy 1 yayi murmushi.
“Suna can gidanka, ga abinci ma na musamman mai surutun ta bani in kawo maka, amma su ma suna parking za su koma Boston, ashe ka damu da su ba ka nemansu?†Ya fada yana dan harararsa.
Murmushi ya yi, ya ce,
“Su ma ba sa nemana Oncle, especially Daddyâ€.
Da sauri ya katse shi, “Don sun san halinka ne, a zo dubaka ka ce an dame ka. Anya Mu’azzam ba za ka sauya hali ba? Ko kowa zai dame ka ai ban da iyaye! Zulaiha tausayi ta ke ba ni wallahi, ta damu da kai sosai, tana so ku dinga hira kuna tattauna al’amura amma ka ki ka ba ta dama, ina amfanin kadaici? Wane jin dadi ka ke samu a cikinsa?
Mai share musu wannan hawayen yau babu shi a doron kasa! Ina sake gaya maka Mu’azzam dole ka canza, ba aggressive tendency ba ko kai ka fi kowa zafin zuciya a duniya dole ka bude zuciyarka yanzu ka kaunaci mutanen dake zagaye da kai, ka rungume kannenka da iyayenka, ka ba su kulawa da farin cikin da mutum biyu za su ba su, in ba haka ba ka shirya gamonka da Allah ka ji na gaya maka.
In ma da lalura to da hali! Halin ka ne Mu’azzam rashin son mutane. Kai yanzu matsayin uba ka ke ga kannenka bakidaya, ba su Basma kadai ba har da su Aalimah. Don ba su da wanda ya fi ka.
Wanda ke sa su farin cikin yana mantar da su kai da wanzuwarka Allah ya yi ikonSa a kanshi, sabida kai din da baka son su kai yake so ka rayu tare dasu. Kuma dole mu karbi hukuncinsa da kyakkyawar zuciya. Ni na tafi, ka yi tunani a kan maganganu na da kyau. Allah ya kara maka lafiyaâ€.
Ya mike ya fita, bayan ya sunkuya ya sumbaci Mu’azzam din a goshinsa. Bin bayansa ya yi da kallo yana dan dingisawa akan kafar robarsa kamar mai son tashi ya bishi, yana mai tauna kowacce kalma da ke fitowa daga bakinsa, yana mai yarda da ita cikin aminci da gaskatawa. He must be a changed man, amma ta yaya? Shi kansa bai sani ba.
Kawu Mansur na nufin ya dauki dukkan halayen Aboulkhair ya yafa yanzu, wanda ba abu ne mai sauki a gare shi ba. Aboulkhair is what he is kawai, charming, jovial, cheerful and passionate. Yana bukatar wanda zai taimaka masa hakan ta kasance da shi shima. Gashi kuma bazai iya rayuwa da kowa cikin gidan sa bayan Aboulkhair ba. Kenan wannan canjin da Kawu Mansur ke masa fata ba abu ne mai sauki a gare shi ba.
Shi kam abin tausayi ne, shi kadai aka yiwa mutuwa haqiqa. With Aboulkhair aside things are always easy for him. Ba tare da shi ba bai san yaya rayuwa zata koma masa ba. Yanzu in ya bar asibiti bai san ta yaya zai fuskanci sabuwar rayuwar ba. Rayuwar da babu Aboulkhair a cikin ta. Yana rokon Allah ya bashi juriya da karfin gwiwar karbar rayuwa a duk yadda ta zo masa.


Daddy Mansour ya koma Niamey ya tadda iyalinsa da sabuwar kafarsa ta roba cike da ikhlasi, kada ku so ku tona farin cikin da iyalin Raazee suka kasance a ciki. Kwana daya, biyu, uku ya huta ya ce zai koma Nigeria don komawa bakin aikinsa, kafar ta zauna masa sosai wadda ba za ka taba zaton ba ta gaske ba ce, ban da dan dingisawa da yake yi in yana tafiya.
Aboubacar da Basma tuni sun wuce. Malam Raazee da Inna Kasisi suka ce su yi ta tafiya tunda sun ga cewa zama a kasashen da ba su da kowa shi ya fi musu, amma su bar musu Aalimah.
Ita ma Aalimah ko da Mama ta tuntube ta da zancen ta fi son zaman Yamai din a kan komawa Nigerian. A cewarta za ta kasance cikin kadaici in ta koma wanda shi ne babban abin da ke jefa ta cikin kewa da tunanin mijinta Aboulkhairi.
Daddy 1, Mama Asi da ‘yammatansu uku; Sultana, Suhaima da Sabrina suka taho gida cike da alhinin halin da suka baro Aalimah a ciki.
Aalimah idan ta yi wanka da safe shi ke nan ko vaseline ba ya ganin fatar jikinta, balle kuma kwalli abin adon mata a idanunta. Hakika mutuwar Aboulkhair ta zo mata unexpectedly, a lokacin da ta ke at the zenith na jin dadin rayuwar auratayya. Ya lullube ta da dukkan so da kauna, ya maida ita sarauniya a cikin mata ‘yan uwanta. Don haka har zuwa yanzu da ake neman watanni shidda da rasuwarsa ta kasa karbar reality na rashin sa da sauki. Kullum mutuwarsa da kewarsa fresh suke dawo mata.
Har yanzu ji ta ke a jikinta kamar Aboulkhair ba mutuwa ya yi ba, ya je Boston ne bada jimawa ba zai dawo ya tadda ita, ya dauke ta su koma Las Vegas, su cigaba da rayuwar nan tasu mai ban sha’awa. Amma da ta ga watanni na shurawa da gasken-gaske babu ko waiwaye har an kwashi watanni kwarara guda tara, dole ta fara karbar reality na fara sabawa da rashin sa.
A kullum Inna Kasisi da Inna Bintou cikin tattashinta suke da nuna kulawa da kyautatawa. Abinci sai wanda ta zaba za’a dafa a gidan. ‘Yan uwanta kannenta su Balkissa dasu Rumana kullum kafafunsu na dakin Inna Bintou inda Aalimah ta ke, su kwaso labarai suyi ta bata na abubuwan da ke faruwa a gari, tamkar su goya ta don lallashi da son debe mata kewa. Dole ta fara sakin ranta, amma ba don ta yarda cewa za ta kara wata rayuwar farin ciki a gaba ba. Sai don ‘yan uwa, iyaye da kakanninta su yarda ba aikin banza suke yi ba, tana karbar rarrashinsu, kaunarsu da soyayyarsu.


A yadda Daddy ya so a karshen wannan watan za su yo hijira daga Boston din Massachusetts su koma kasarshi ta haihuwa Niger Republic shi da matanshi da sauran ‘ya’yan shi biyu, amma a yau komai ya canza, sakamakon Mummy Zulaiha data juyawa al’amarin baya. Mummy kuka ta ke yi tana karawa tun daren jiya kan cewa ba za ta iya barin kasar ta bar Mu’azzam shi kadai alhalin ta san ba shi da kowa a cikinta ba. Ta yarda Daddy da Gumsu su tafi, amma ita da Yesmin a barsu. Ya kada ya raya Mummy ta ce sai dai ya sake ta, wannan karon ta zabi Mu’azzam a kan aurenta.
Jikin Ishaq Raazee ya yi mugun sanyi, shi ma ya dade yana wannan tunanin, yadda za su tafi su bar Mu’azzam shi kadai babu kowa nasa. Ga lalura mai iya motsawa a kowanne lokaci. To abu ne in aka hada da iyayensa yanzu baya jin shakkar yin sa komai tsaurin sa don fatan gamawa da su lafiya.
Duk da ba gida daya suke zaune da shi ba, ba kuma gari daya ba, kowanne lokaci suke so suna zuwa ganinsa, uwarsa na kula da shi ta hanyar ziyartarsa akai-akai. A hakan da yake yana taka muhimmiyar rawa wajen gyara rayuwar mahaifiyarsa, yana da tabbacin shi ne ya canza ta ta koma mutuniyar kwarai. Yana amfanar da su da ‘yan uwansu na birni da na kauye, idan ya raba shi da aikinsa ya raba shi ne da madogarar rayuwarsa dungurungum. Balle aiki da ‘Chevron’, wanda sai mutum mai sa’a a cikin masu sa’a.
Ga shi ya riga ya gaya wa kowa zai dawo gida a wannan shekarar, har babban aiki ya samu a Yamai. Wanda ya tabbata zai rike shi shida iyalinsa a zamansa cikin kasarsa ta haihuwa har zuwa karshen rayuwarsa. Ta ya ya zai dawo ya ce da iyayensa wadanda burin su kenan ya dawo gida yace ya fasa saboda farin cikin matarsa?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button