AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Aalimah tun suna kanana suka taso da fahimtar cewa, mamansu is a mental patient, sannan suka fahimci Babansu na tsananin sonta. Tana daukar lokaci lafiya kalau don tana kan shan magani, amma in abin ya tashi ba Babansu kadai ba su kansu suna jin jiki. Babu duka babu zagi sai kuka. Za ta kwana ta wuni tana kuka kamar ranta zai fita babu gaira babu dalili. Ta bar shiga komai nasu, ta bar yi musu girki. A irin wannan lokacin Babansu ke yi musu komai; wanka, girki, shirin makaranta, wankin uniform da dukkan hidimar da uwa ke yi wa ‘ya’yanta.
Da Aboubacar ya soma hankali shi yake kula da Maman. Baban ya kula da su ita da su Sultana. A haka suka taso da wata irin shakuwa matsananciya tsakaninsu da Babansu, Mamansu tana da tsauri a kan tarbiyyarsu, hakan ba ya nufin ba ta sonsu, amma tana da zafi. Ba su nemi komai sun rasa ba, amma ba su da wadatar da sauran ‘yan uwansu na Yamai ke da shi.
Babansu bai dogara da komai ba sai albashinsa, sannan ba shi da halin rokon ‘yan uwa wai don sun fi shi wadata. Ya dogara da kansa ya tsare wa iyalinsa komai na bukatun rayuwa daidai misali, irin na kowanne cikakken dan boko. A halin yanzu Dr. ne shi a jami’ar Bayero a tsangayar kimiyyar sadarwa.
Aalimah na matukar son zuwa Yamai, ta iya harshen mahaifinta sosai don kusan duk wani hutu mai tsawo a can ta ke yinsa. Inda za ta hadu da ‘yammatan family sa’anninta su Balkissa ‘ya’yan Kawu Oussama su yi ta dabdalarsu tun suna yara. Ko a cikin jikoki Aalimah ta daban ce a wajen Kakansu. Sakamakon ita kadai ya sanyawa sunan mahaifiyarsa.
Yana sonta son da ba ya iya boyewa, kowa ya kwana da sanin hakan a familyn, Aalimah ce ta gaban goshin Mallam. Kuma shi ya zaba mata wannan suna na Innarsa (Aalimah) wato mai ilmi.

‘Margi’ da ‘Abzin’su suka hadu suka haife Aalimah, don haka na bar wa mai karatu ya siffanta kamannin Aalimah Mansour yadda yake so. Babu wanda ya damu da yin wani abu wai shi auren zumunci a wannan family kowa yana kawo wanda yake so ne ya aura, don haka babu rikici babu rashin fahimta, kansu a hade yake kamar tsintsiya. Sai dan abin da ba a rasa ba, wanda ba ka rasa shi a kowanne extended family, shi ma ya fi yawa a tsakanin faccaloli (matan ‘ya’yansu), amma jikokin gidan da ‘ya’yan gidan kam kaf dinsu kansu a hade yake.

Haduwar Aalimah da Mahmoud ta faru ne tana ajin karshe a sakandire ta staff school inda ta yi sakandire. Mahmoud abokin Yaya Aboubacar ne, tare suka yi karatu a nan B.U.K. Mahmoud bakatsine ne, wanda ya fito daga karamar hukumar Kaita ta jihar Katsina.Da suka zo yin hidimar kasa aka kai shi wata makaranta da ke daura da sabuwar jami’ar Bayero.
Daddyn su Aalimah ya san irin abotar da ke tsakanin Aboubacar da Mahmoud, don haka da Aboubacar ya zo yana nemawa Mahmoud alfarmar zama tare da shi a nan boys quartersdinsu wajen mahaifinsu, Daddyn ya amince, amma kuma ya ce masa ya gaya wa Mahmoud dokarsa ita ce; karfe tara na dare yake rufe gida, in ya amince ya zo ya zauna babu laifi.

Zaman Mahmoud Kaita a gidan Dr. Mansur Razee zama ne na aminci. Ya samu iyalin Dr. mutane masu karamci, tarbiyya, tsantsar ilmi da son junansu. Dole duk wanda ke gaba da kai a haihuwa ka ce masa ‘Yaaya’, ka dinga respecting dinsa. Wannan ne babba abinda ya ja hankalin Mahmud ga son hada jini da iyalin Dr. Mansour Raazi. Tsakanin Daddy da yaransa auzinanci suke yi ko yaren Temachekwato harshen Inna Kasisi, Mama ce kadai ke musu Hausa da Turanci. Wani lokacin ma tana musu Margiduka ba wanda ba sa ji. Duka yaran gidan sun saba da shi, suna kula shi kamar Yayansu Aboubacar, banda Yayarsu Aalimah.

Wata mutum guda daya a gidan Dr. Mansur Razee mai wani irin halina seriousness irin na Babanta. Ba ta da hayaniya, ba ta da sakin jiki da mutane. She’s very authoritative ga kannenta, kuma sosai suke jin tsoronta. Shi kansa Yaya Aboubacar wani lokacin sai ya ji tana commanding dinsa. Abin yana ba shi dariya sosai. Kafin ya ankara, ya zama infatuateda kan Aalimah,so much so that, in ya wuni bai ga giftawarta ba, sai ya yi ta zarya kamar zararre a cikin gidan ko ya tambayi Sultana cikin hikima. Sau tari yarinyar kan ce masa, ‘karatu ta ke yi’, kuma ‘ba’a yi mata magana in tana karatu’. Ta hakan ya gano cewa; karatu is the best hobby for Aalimah, kuma da shi zai yi amfani ya jawo hankalinta gare shi.
Aka yi sa’a Aboubacar ya tafi Yamai a safiyar wata litinin zai halarci daurin auren daya daga cikin cousins dinsa dan Kawu Saddam wato jikan Inna Bintou. A ka’ida kuma Aboubacar ke yi musu extra lesson kullum bayan sun dawo daga islamiyya wadda ita ma a nan cikin New Site ta ke, don haka Daddy ya dora alhakin koyarwar a wuyan Mahmoud kafin dawowar Aboubacar.
Wannan shi ne mafari, mafarin soyayyar Aalimah da Mahmoud Sulaiman Kaita.
Ta samu Mahmoud irin mazan da ta ke burin aura, wato yaro dan boko mai kwakwalwa da nunawa macen da suke so soyayyah a fili kamar duk duniya ba wata macen sai ita. Kafin dawowar Aboubacar sun shaku fiye da zato, sai daga baya ya fahimci ko me suke ciki.
A zuciyarsa ya yi musu fatan alkhairi, amma a fili ya dora wa mu’amalarsu ido, har ya fahimci tsaftacciyar soyayya ce suke yi wa juna, Mahmoud ba yaudarar kanwarsa yake da niyyar yi ba, har ya gama hidimar kasarshi ya koma garinsu Katsina, shi da Aalimah remains in contact ta wayar Yaya Aboubacar ba tare da sanin Mama da Daddy ba wadanda ya san ba za su taba amincewa aurar da Aalimah a daidai wannan lokacin da ko sakandire ba ta gama ba, shi kuma yana son abokinsa da Aalimah don ya san in har ta aure shi to ta yi miji, wanda zai rike masa ita da daraja da mutunci har karshen rayuwarta.
Dalilinsa kenan na kyale su suka ci gaba da contacting juna ta wayarsa. Don Aalimah a lokacin Iyayensu basu bata damar mallakar waya ba. Bayan komawar Mahmoud garinsu, ba da jimawa ba ya samu aiki da hukumar zabe ta kasa a can Katsina, ita kuma Aalimah ta gama jarrabawar fita sakandire a shekarar. Ba jimawa sakamakonsu ya fito, tana daga cikin zakarun gwajin dafin da (BUK staff school) ta yaye a shekara ta 2015.
A wannan lokacin ne Maman su Aalimah wato Aseeya ta samu mijinta da takardun banki,mai dauke da sunanta na fixed deposit account da ta bude da gadon mahaifinta. Kudi ne zunzurutu da a iyakacin rayuwarsa bai taba mallakar ko da rabinsu ba. Ta gaya masa kudurin da ta ke da shi, wato tana son kai Aboubacar karatu jami’ar da mahaifinta marigayi V.C ya yi a kasar America. Tana so Aboubacar ya gaji Babanta. Watarana ya zama kamarsa….as the only male child she have (a matsayin sa na Da namiji daya kwal data mallaka).
Murmushi Daddy ya yi ya dube ta sosai cikin idanunta, sannan ya soma magana.
“Aboubacar bai da sha’awar hakan, bai da sha’awar ilmi mai zurfi,abinda yake mafarki kawai(is to become a banker), amma kina da wani dan, da zai iya cika miki wannan burin. Amma fa in za ki kauda kowanne irin tunani ki bada kwarin gwiwaâ€.
Da mamaki ta ke kallonsa,
“Duk ‘ya’yana mata ne Daddy, he’s the only male one….â€.
“… Mace ma mutum ce!â€
Ya yi hanzarin katse ta.
“…Amma me rauniâ€. Ta ba shi amsa.
“Idan za a yi ta kallon rauninta ba za’a ba ta damar bada gudunmawarta ga al’umma ba. Musamman in aka fahimci cewa tana da motive a kan neman ilmin. Don haka in har amincewa ta da shawara ta ki ke nema, to Aalimah ce za ta tafi karatu ba Aboubacar ba. Shi ya ci karfin duk wani karatu da zai yi a gaba, tunda yana da kwalin degree. Duk wani abu da zai kara karantawa a gaba ado ne kawai ga na bayaâ€.
Mama ta yi shiru tana tunani, kafin cikin sanyin jiki ta ce,
“Daddy ka fahimce ni, ba kasancewar Aalimah mace wajen karatu ne abin dubawa ba. Yadda tafiyar mace wani waje bata halatta ba tare da muharrami ba. Aalimah ba mu yi mata aure ba, mu dauke ta mu kai ta kasa irin America mu ajiye mu ce ta yi karatu babu idon kowa a kanta babban kuskure ne duk irin tarbiyyarta.
Ubangiji ma sai ya tambaye mu. Na sani bokonka mai zurfi ne, irin wanda ke hana ku daukar hakan da muhimmanci, amma hakan zai zama mana damuwa a gaba, kada garin neman gira a rasa idoâ€.
Ta karasa cikin karyewar murya.
Murmushi Dr. Mansur ya yi ya ce,
“Na fahimce ki, na kuma fahimci abinda kike so na fahimta, ni ma ba zan amince ta zauna a hostel ba, hannun Yaya Ishaq zan damka ta. Ta zauna cikin iyalinsa.
Fadamiki ne ban taba yi ba, ya sha cewa in ba shi ita ya hada da yaransa su Basma ya rike ina cewa, sai ta gama makaranta. Ni ma kuma akwai nawa tanadin da na dade ina yi don haka kudin nan naki ki yi tunanin business din da za ki fara da su, ni zan dauki nauyin makarantar Aalimahâ€.
Nan Mama ta nuna ba ta yarda ba, ta san ba shi da wannan halin, amma ya ce ta kyale shi.
Abinda Mama bata sani ba shine;Federal Scholarship ne ya samo mata ta hanyar wani abokinsa shugaban scholarship board na kasa, tare suka yi karatu, wato Dr. Obi Olayinka. Da mama ta dage tana so ta bada tata gudummawar sai ya ce, to ta saya mata ticket, amma duk sauran shirye-shiryen Babanta ne ya yi mata.
Sai da komai ya kammala, admission da komai, sannan ya kira dan uwan nasa ya sanar da shi komai. Ishaq din ya ce da bai yi wahalar neman scholarship din ba ma ya yanke shawarar sanya su ita da Basma daga aljihunsa a wannan shekarar, amma tunda ta riga ta samu shi kenan ya sako ta a jirgi ta taho.
Ranar da Aalimah za ta taso kuma tafiya ta kama shi daga office dinsu zuwa California zai kwana daya, don haka ya tura wa Dr. Mansour adireshin gidan nasa, ya ce ta dauki drop har gida.
Zulaiha tana wajen aiki sanda za ta iso, yaransa maza kuma duk ba sa gari. Wannan shi ne tarihin su Aalimah da asalin tahowarta kasar America. Kafin ta taho ta je Maiduguri da Yamai ta yi sallama da kakanninta da ‘yan uwanta. Inna Kasisi kam abin bai yi mata dadi ba ko kusa, yadda ba ta son rabar Zulaiha, haka ba ta son kowa nata ya rabe ta, balle Aalimah wadda ko a cikin jikokinsu ita ta daban ce, mai kyakkyawar tarbiyyah da sanin ya-kamata. Suna ji da ita fiyeda sauran jikokinsu. Tsoronta Allah tsoronta kada ta koyo dabi’un ‘ya’yan Zulaiha da kullum ke sanya ta cikin takaicin wai cikin zuri’arta suke.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button