AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Dan uwansa Mansour ya kira, don su yi shawara kan wannan al’amari.

To al’amari kowa ya san in dai akan Mu’azzam ne to fa Mansour Raazee baya wasa da shi, kuma bazai bi bayan kowa ba sai in da Mu’azzam zai amfana.
Budan bakinsa sai cewa yayi.
“Ai kowa ya san abinda ya faru, kuma kowa ya san Mu’azzam yana da lalurar da bai kamata a yi nisa da shi irin haka ba. Uwa wasa ce? Ko an san wahalar data ke sha akan dan ta da lafiyarsa? Ko kana tunanin hankalin ta zai taba kwanciya tana can yana nan? Wannan karon ina bayan Zulaihatu!â€.

Wannan ita ce amsar kawu Mansour.

To shi an sa shi a kwana. Bayan wa zai bi? Mummy tana nan akan bakanta haka Malam da Inna Kasisi.
Da ya kira mahaifinsu cikin ladabi da tsanaki ya yi masa bayanin fasa dawowarsa yadda zai fahimceshi, da dalilin da ya janyo hakan. Da ikirarin Mummy Zulaiha na saidai ya sake ta. Shiru ya yi masa, shirun da ke nufin yana da ja a kan hukuncin da suka yanke shi da dan uwansa da mai dakinsa.
Malam Raazee ya yi gyaran murya ya ce, “A kan Mu’azzam ne ko?â€
Ya ce, “Eh Malamâ€.
Malam ya ce, “A kan sa ne ka fasa dawowa cikin asalinka da tushenka?â€
Daddy Ishaq ya yi shiru, Malam ya ce, “To ku ci gaba da shirinku na dawowa tunda dai ka samu aiki, wanda zai rike ka a nan din, duk wadda ta ce ba za ta dawo ba a cikinsu na yi maka umarni da ka sake ta din!
Mu’azzam yana hannun Allah! Shi din jarumi ne kuma sadauki a cikin mazaje. Na tabbatar maka cikin kowane hali zai iya kula da kansa. Ya riga ya tsaya da dugadugansa baya bukatar tallafin ku sai addu’arku. Rashin cikar lafiyar sa bai rage shi da komai a rayuwa ba. Cewa nake ko da ku ke kasa daya ba garinku daya ba? To ta ina ku ke sanin halin da yake ciki din?
Gashi ni kuma bani da buri a yanzu fiye da ya kasance duk sanda nake son ganin ka in budi ido in ganka a gefe na cikin ‘yan uwanka, ko in yi tattaki akan kafafuna zuwa gidanka. Shekara da shekaru kana yimin wannan alkawarin a-sha-ruwan-tsuntsayen. In kunyi hakuri kwana nawa ya rage min in baku fili kowa yayi rayuwar da ya zabawa kansa? Sai dai in dama can ba ku da niyyar dawowaâ€.
Jikin Daddy Ishaq har rawa yake. Ko’ina a jikinsa tsuma yake yana baiwa malam hakuri. Ya kira Mummy da karfin sauti ya ce,
“Zulaiha!â€. Sai da gidan bakidaya ya amsa.
Ta ce, “Na’am!†Tana mai saukowa daga saman bene a nutse cikin takun gayuntan nan. Saida ya bari ta gama saukowa tsaf suna masu fuskantar juna, ya dube ta cikin tsakiyar idanun ta yace.
“Ki hada kayanki mu koma Niamey tareâ€.
Gyara zama Mummy ta yi cikin karamar kujerar falon, ko kadan muzuran da yake yi mata bai girgiza ta ba, ta ce,
“Na gaya maka ba sau daya ba ba sau biyu ba, ba zan koma in bar Da na baâ€.
“To sai ki zabi daya, aurenki ko komawa Niameyâ€.
Kai tsaye (without a second thought) Mummy ta ce,
“Na zabi sakin, Allah ya sa shi ne mafi alkhairi a gare niâ€.
Daddy ya rubuta saki daya cikin zafin rai ya ajiyewa Mummy akan cinyarta ya fice ya bar gidan.
Mummy ta tadda Gumsu a dakinta tana ta hada kaya. Ta ce,
“To Gumsun Babansu, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi, idan na taba bata miki a tsayin zaman mu ina mai rokon ki ki yafe mini. An ce zo mu zauna zo mu saba, hakika ni naji dadin zama da ke. Ni na karbi red card tunda na zabi zama kusa da Mu’azzamâ€.
Gumsu ta saki crystal din da ke hannunta zata saka shi cikin kwali, ji ka ke tush! Ya tarwatse a kasa. Salati ta shiga yi tana maimaita kalmar innalillahi… Mummy ba ta bi ta kanta ba ta juya ta fita daga dakin. Sai a lokacin hawaye suka zubo mata.

Karshen tashin hankali Gumsu-Moiram ta shige shi, ta yi kokarin rarrashin Daddy tana kuka kada a ce don ya aure ta ya rabu da uwar ‘ya’yansa, ya taimake ta kada duniya ta zage ta. Da wane ido zata sake kallon su Basma? Da kyar Daddy ya samu ya lallashe ta inda ya tabbatar mata rabuwarshi da Mummy Zulaiha ba ta da alaka da nata auren. Ya gaya mata zabin da Malam Raazee ya bayar ita kuma ta zabi sakin. Ko ita Gumsun ta zabi zaman Malam Raazee ya yi izinin a sake ta.
Jikin Gumsu ya yi mugun yin sanyi, ta rasa wanene mai gaskiya tsakanin Mummy da Daddy? Shi yana so ya yiwa mahaifinsa biyayya don ya gama da shi lafiya ita kuma Uwa ce mai jin qan abinda ta haifa mara cikakkar lafiya!
7/5/21, 8:20 AM – Buhainat: HABUBAKAR ADO

#

Cikin satin suka biyo jirgi da komai nasu suka baro kasar Amurka. Bari na din-din-din. Ishak Raazee na mai jin wata irin kewa wadda sabo ke haddasawa na mamayar zuciyarsa. Mummy na mai jin kamar ita daya ta rage a fadin duniya sabida kewar mijinta da ‘ya’yanta. Saidai ko kadan bata yi nadamar hukuncin da ta zartas ba. Yesmin na kuka kamar ranta zai fita a kan rabuwar iyayenta, suka taho shi da Moiram da diyarta Nurat, ya baro mata Yesmin ne don rage mata bacin rai.
Haka Mummy ta yi kokarin shanye damuwarta wannan karon ba tare da ta raba ta tare da Mu’azzam ba, ganin cewa bai jima da barin gadon asibiti ba. Kuma in ba za ta manta ba Aboulkhair ya hane ta dora wa Mu’azzam damuwa, ko dai ta shanye kayar ta ita kadai, ko ta raba ta tare da shi (Aboulkhair) din, amma sharing dinta da Mu’azzam babbar illa ce ga kyakkyawan treatment din da yake samu.
Ko da ta koma office a washegari da niyyar bada hakuri a maida ita bakin aikinta wani ta tarar a mazauninta (JP MORGAN CHASE) ba su daukar wasa da aiki, ko da kuwa da excuse. Balle ita nata babu excuse din ma. Rana daya aka nemeta a kasar aka rasa. Tsabar rudanin rayuwar data samu kanta ya mantar da ita cewa ita din ma’aikaciya ce, ma’aikaciyar ma ta babban bankin Amurka irin JP Morgan. Haka ta dawo kafafu a sage, ta soma neman wani aikin ta yanar gizo, amma har watanni uku suka shafe bata dace ba. Sakamakon matsin lambar da musulmin kasar ke fuskanta a lokacin daga sabuwar gwamnatin Amurka karkashin mulkin sabon shugaban kasa Donald Trump. Da yawa sai komawa suke kasashen su na asali. Ba don Yesmin da ke zuwa makaranta ba Las Vegas za ta tattara ta koma bakidaya, in Mu’azzam ba zai rike ta ba ita da autarta, ya san yadda zai yi da su. Shine kadai dolenta a yanzu.


     FLASHBACK

An sallami Mu’azzam ranar wata lahadi, sati guda kacal ya kara a gida, sannan ya koma aikinsa. Ya hada wayoyinsa, ya kira duk wanda ya dace ya gaisar. Ciki har da Mummy, ta gaya masa tana Boston amma ba ta gaya masa cewa Daddy ya sake ta a kansa ba. Sosai ta koyi hadiye damuwa, in ta tuna da Aboulkhair.
Ta san da yana raye ransa zai yi matukar baci, za ta kiyaye abin da ba ya so a bayan ransa. Ta kasance mai bata masa rai da hakan a sanda yake raye. Zata kasance mai kiyayewa a sanda babu shi. Ta ce masa Daddy yana Niamey, kuma ta turo masa kudi cikin account dinsa kafin ya samu albashi ya soma shigo masa ta san zai bukace su sosai.
Sosai ya yi godiya, yana mai jinjina soyayyar uwa ga abin da ta haifa, ta Mummy is special. Ita dai ‘ya’yan ta kawai. Su samu jin dadi shine burin ta. Kada su nemi wani abu su rasa a rayuwar su. Bazata taba canzawa daga hakan ba.
Ya kira Daddy suka yi hira sosai, inda ya gaya masa ya koma Yamai, ya samu aiki a can da hukumar hulda da kasashen wajen su, yanzu kuma ya samu wani makeken fili kusa da gida ya saya ya fara gini. Gini yake so ya yi one in town wanda dukkansu zasu sake a cikin sa.
Ya cigaba da gaya masa amon muryarsa dauke da kauna irin ta uba ga dansa, irin tsarin duplex din da yake so a yi masa. Yace sai yafi gidansu na Boston kyau nesa ba kusa ba, zai masa part din sa guda wanda zasu ke sauka in sun zo shi da iyalinsa. Sosai ya baiwa Mu’azzam dariya. Ya canza position din rikon wayar daga dama zuwa hagu ya cigaba da sauraron almarar Daddy. Koko ya ce mafarkin Daddy. Ba tare da Daddyn ya kula da karbar da yake yiwa zancen nasa ba ya cigaba da labarta masa cewa har dakin yaran su za’ayi a cikin bangaren nasu, a zuba duk wani nau’I na kayan wasan yara. Mu’azzam tausayin mahaifin nasa yayi matukar kama shi, su iyaye wato har kullum fatan su nagari ne ga ‘ya’yan su ba ruwansu da reality din da rayuwar ‘ya’yan ke fuskanta.
Ji yayi idanunsa na son kawo ruwa, don haka ya matsu su yi sallama da Daddy. Ko kusa bai yi masa zancen mahaifiyarsa ba har suka yi sallama, hausawa suka ce wai ido da kunya. Ba zai iya kallon tsabar idanun sa ya gaya masa ya saki uwarsa ba sabida ta zabi zama a kusa da shi ta bashi kulawa. Sai Mu’azzam ya dauka za ta bi su ne daga baya in ta gama kintsawa, tunda ita ma’aikaciya ce. Bincike-bincike da zakule-zakulen halin da wani ke ciki da ma tun fil azal ba halinsa ba ne shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button