AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Aalimah ta yi sallama a shigifar kakansu. Daga shi sai Daddy 2 ta tarar a dakin, babu kowa. Ta samu gefen Malam ta zauna. Malam ya dube ta cikin kulawa, ya ce,
“Uwata me ya faru ne?â€
Ta saci kallon Daddy 2 wanda kallon fuskarsa kawai ta yi ta ji ya ba ta tausayi, da alama cikin damuwa mai tsanani yake. Ta ce, “Malam wai Daddy ne ya ce zai min aureâ€.
Yayi murmushi.
“Ke kuma ba kya so ko?â€
Ta ce, “Malam ba zan iya mantawa da Aboulkhair ba, balle in hada rayuwa da wani a bayansa, kullum ji nake a jikina zai dawo. Idan ya dawo ya same ni da aure, na ci amanarsaâ€.
Murmushi Malam ya yi kafin ya ce, “Ko da a ce MU’AZZAM ki ka aura ba za ki manta da shi ba?â€
Idanunta suka kara girma, at the same time suka kankance suka firfito waje, cikin sanyin murya tace.
“Malam, wanne Mu’azzam din?â€
“Mu’azzam Raazee Yayan Aboulkhairâ€.
Wannan karon Daddynta ne ya ba ta amsa, with every affirmation a cikin muryarsa.

Sai Aalimah ta gurfana a gaban mahaifinta a kan gwiwoyinta. Rokonsa ta ke idan wasa yake yi tana mai rokonsa da girman Allah da darajar zatinsa da ya bari, Mu’azzam tamkar uba yake a gare su daga ita har Aboulkhair. Gara ya aura mata mazan duniya bakidaya ta amince, a kan ya aikata wannan babban zunubin a gare ta.
Kamata ya yi ya tasar da ita daga durkuson da ta yi a gabansa kamar mai neman gafara. Idanunsa sun kada sun yi jajir da tausayin ta. Sai dai ko sama da kasa za ta hade ba ya jin akwai abin da zai sa shi fasa hada wannan aure, muddin yana raye ita ma Aalimah tana numfashi.
Ya ce, “Ki nutsu Aalimah ki fuskance ni, Mu’azzam shi na so tun farko ki aura Allah bai cika min wannan burin ba. Idan har da gaske kina kaunar Aboulkhair ba abin da za ki yi ki nuna masa wannan kaunar a lokacin da kasa ta rufe masa ido, banda tallafar rayuwar Mu’azzam. Kin sani Aboulkhair ba shi da wani buri da ya wuce Mu’azzam da lafiyarsa. Aalimah ba kya tausayin Yaya Ishaq? Mutumin da ya dauke ki babu bambanci da ‘ya’yan cikinsa ya karrama rayuwarki? Kina sane da cewa ba shi da buri a yanzu da ya wuce lafiyar Mu’azzam da cikar rayuwarsa. Ba za ki kasance mai rama alheri da sadaukarwa ba?â€
Aalimah cikin gunjin kuka ta ce, “Daddy, bana gudun Mu’azzam don rashin lafiyarsa. Ko kadan. Ina gudun aurensa ne kasancewar sa wanda ya fi kowa kusanci da Aboulkhair, ina matukar ganin girmansa, aurensa shi ne babban cin amanar da zan yi wa Aboulkhair a lokacin da babu shi…â€.
Wannan karon malam ne ya tare ta, “Uwata, shi ne babban farin cikin da za ki sanya shi. Shi ne babban gatan da za ki yi masa. Shi ne kauna ta hakika da za ki nuna masa. Hakkin ki ne mu ba ki dama wannan karon ki zabi mijin aure, shi ya sa har muka zaunar da ke a nan muna neman yardar ki da amincewar ki, ba don haka ba da ba za ma ki san an yi ba sai bayan an yi.
Ni na san uwata mai biyayya ce ga umarnin mu, mai farin ciki da farin cikin iyayenta. Kin zauna da Mu’azzam ko da ba gida daya ba a kalla za ki iya bada shaida a kan WANE NE SHI? Kuma kin ga yadda dan uwansa ke kula da shi, akalla muna da kyakkyawan zaton za ki iya taimakawa rayuwarsa a matsayinku na shakikan juna, ku taru ku rufa wa juna asiriâ€.
Aalimah ta rasa abin cewa, ta rasa hujjar kare kanta wajen Daddy da Malam, ban da ta zuba musu ido, sun riga sunyi nisa akan kudirinsu, kome zata ce bazasu gane ba, bazasu saurareta ba, tana mai jin abin da suke fadi kamar almara a cikin kanta. Tana mai kallon fuskokinsu na wulgawa kamar a majigi, tana ganin wasu abubuwa masu kama da taurari cikin idanunta suna ratsa fuskokinsu cikin idonta. Daga haka ba ta kara gane me suke cewa ba, kuma ba ta kara samun kalmar furta musu ba.

Ta farfado ne daga shidewarta ta ganta a cinyar Gumsu- Moiram, tana mata firfita da maficin kaba, Gumsu ta sa hannu ta debi ruwa tana shafa mata a kan farar fuskarta wadda ta cure ta yi jajir. Mikewa ta yi daga kwanciyar ta tashi zaune. Idanunta ta ke rarrabawa a dakin kafin ta fahimci a dakin Inna Kasisi suke. Ga Innar a gefe ta hada tagumi, bayan su babu kowa a dakin sai ita cikon ta uku.
Inna ta ce, “Gumsu, ki tafi da ita gabanki ta kwana biyu in ji Malam. Ki ci gaba da nuna mata gaskiya na tabbata za ta fahimci iyayenta, kuma za ta fahimci abin da suke so ta fahimtaâ€.
Zumbur Aalimah ta mike zaune, “Ba abin da zan fahimta in dai aure da Mu’azzam ne Inna, ba zai taba bani irin rayuwar da dan Uwansa ya ba ni ba, bayan ciwo da ke aiki a jikinsa har da hali. Halinsa ba irin na mutane ba ne. Na ce na yarda a aura min mazan duniya dukkansu, amma ban da Mu’azzam Inna…â€.
“Me ya sa ba ki gaya wa ubanki ba? Ni me ye nawa ne a ciki?â€
Inna kasisi ta katse ta cikin gatsali, kasan ranta cike da jin zafin kalaman Aalimah, duk wanda zai aibata Mu’azzam ko ba ta gaya masa ba, za ta ji zafinsa a kasan zuciyarta. Shi ne ya dauke su mutane masu daraja a lokacin da Zulaiha da Ishaq suka watsar da su. Shi ne ya fara kai ta dakin Allah kafin kowa ya kai ta. Shi ne ya dauki danginta da muhimmanci yake agaza musu fiye da kowa cikin ‘ya’ya da jikokinta. Shi ne ya dauke su mutane fiye da ubansa! Kaunar da ta ke masa ba ‘yar kadan ba ce, ba za ta juri ana aibata shi a kan idanunta ba.
“Gumsu na ba ki minti uku ki tattara Aalimah da kayanta ku tafi gidan ki. Zan iya hambare ta idan ta kai ni bangoâ€.
Gumsu ta kama hannun Aalimah suka mike, da ma tuni ta dibar mata kaya kala biyu ta zuba a babbar leda. Za su iya tafiya a kasa daga nan babban gida zuwa gidanta, amma a motar Daddy Gumsu ta jefa ledar kayan Aalimah, ta bude mata kofa ta shiga ta rufe, sannan ta zagaya mazaunin direba ita ma ta shiga ta ja su zuwa gidan, ga tsohon ciki a jikinta kusan watanni bakwai.
A gidan ma aiki daya Gumsu ta ke ta yi, wato lallashi, ban baki da jan hankali. Tana nuna mata illar ja da iyaye da yin fito na fito ga umarninsu. Ta ce,
“Aalimah, idan na fahimce ki Mu’azzam ne ba kya so, ba auren ne ba kya so ba?â€
Da sauri ta daga mata kai.
Gumsu ta yi murmushi, ta ce,
“In aka janye maganar Mu’azzam aka kawo wani za ki yarda ki yi aure ke nan?â€
Da sauri Aalimah ta gyada kai, ta kara da cewa, “Ko waye Aunty Moiram ku kawo, ban da Mu’azzamâ€.
Gumsu ta kama baki, ta ce, “Ko kunyar idona ba kya ji Aalimah? To kuwa sai dai bakin ciki ya kashe ki mu ci gumba! Mu kuma ba damuwa muka yi ki yi aure ba, ki auri Mu’azzam ki zauna da shi cikin rufa wa juna asiri shi ne abin da ya dame muâ€.

Kwana biyu kullum suna tirzawa, duk ta inda Gumsu ta billo sai Aalimah ta goce. Rashin kunya sosai take zubawa Gumsu son ranta. Gumsu bata taba sanin Aalimah nada baki ba sai a wannan lokacin. Itama bata raga mata, haushi take cusa mata ko ta ina, mai nuna soyayyar ta ga wannan hadin auren data fahimci lallashin bata lokacin ta take yi. Aalimah ta shirya ja da kowa don kubutar da kanta daga auren Mu’azzam. Daga baya ta je ta samu Inna Kasisi tace zata dawo da Aalimah gida, zuciyarta ta kasa jurewa, don kwarai Gumsu ke son Mu’azzam itama duk da ba wani sabo ne mai yawa a tsakanin su ba. Zuciyarta na matukar sonsa.
Ta kasa jure kiyayyar da Aalimah ke nunawa auren sa kiri-kiri bata shakkar kowa. Gata a cikin gidan ubansa. Amma duk abinda yazo bakinta shi take fada. Abubuwa da yawa akan kunnen Daddy take yin su. Ita kuma Inna Kasisi ta kwashe komai ta gayawa Dr. Mansour. Sai ya ga bari kawai ya kawo karshen komai, kowa ya huta, dama sun bata lokaci ne ko zata lallasu ta karbi auren da dadin rai. Amma tunda abin nata ba mai karewa bane bari ya karar da shi.
Ranar ta kama juma’a, bayan saukowa daga masallaci suka ga Daddy ya fito cikin shirin babbar shiga ta shadda Wagambari, babbar riga da hula sai kamshi yake yi.
Ya ce, “Gumsu, kira min Aalimahâ€.
A ladabce ta zo ta tsugunna a gabansa, ya kalleta cike da tausayin yadda ta rame ta fita hayyacin ta cikin sati guda kacal da yin maganar auren ta da Mu’azzam. Ya sassauta murya yace.
“Malam ne ya ce in tambaye ki, kin amince ki auri dan uwanki Mu’azzam?â€
Aalimah ta samu kanta cikin rudu. A rasa wanda za a turo ya tambaye ta sai UBAN MU’AZZAM? Wannan ma ai wayo ne da son cutar da mutum, tunda ko giya ta ke sha ba za ta iya duban tsabar idon Daddy Ishaq ta ce ba ta son Mu’azzam ba.
Ta shiga tunano tarin alhairorin Daddy Ishaq gareta a Boston…. Da lokacin da take auren dan sa Aboulkhair….hawaye suka wanke mata fuska.
Ya ce, “Ke nake sauraro Aalimah, mutane suna jira naâ€.
Ta samu kanta da cewa, “Na amince’’ (without a second thought). Tare da zubowar tawagar hawaye a kan kundukukinta.
Albarka Daddy ya shiga sanya mata, sannan ya kama hannayenta ya mikar da ita daga tsugunnon da ta yi, ya ce,
“Insha Allahu ba za ki yi nadamar auren dan uwanki ba, kuma rashin lafiyarsa ba zai zamo kalubale ga rayuwar aurenku baâ€.
Ya hada hannayenta da na Gumsu wuri guda, sannan ya fice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button