AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Wuta ta dauke wa Mu’azzam na lokaci mai tsawo. Numfashinsa ya nemi daukewa. Ya rasa a duniyar da yake. Shidewar wucin-gadi ce ta same shi a lokaci guda.

“Daddy, ka san abin da ka ke cewa kuwa?â€
Ya tambayi mahaifin nasa in subdued (cikin karayar murya). Bayan ya tabbatar cikin zahiri ne abinda yake ji din daga bakin mahaifinsa ba mafarkin ido biyu ba. Kuma ta bakin sa yake son ya ji.

“Ni kuwa na san abin da nake cewaâ€.
Ya bashi amsa.

“Daddy, likitoci sun ce maka na samu waraka ne?â€
Girgiza kai yayi kamar Mu’azzam din yana ganinsa. “Ko kadan Mu’azzam, kawai na mika komai hannun Ubangiji neâ€.
Mu’azzam ya yi shiru cikin harhada kalmomin da zai jefa wa mahaifinsa, amma kunyar abin da zai ce din ta hana shi magana. So yake ya ce da shi cikin biyun wanne ya zaba masa? Za su zauna da matar ne ya zuba mata ido har abada a matsayin ta na matar auren sa, yana ci gaba da taking kwayoyin anti-androgens, ko kuwa zai daina shansu ne ya rayu da ita cikin compulsive-sexual behaviour? Da aggressiveness mai iya tashi a kowanne lokaci?
Kamar Daddy ya san abin da yake sakawa da warwarewa a zuciyarsa, sai ya sanyaya murya ya soma magana cikin yanayin rashin nuna karaya,
“Ni dai Ishaq Sarhamu, ban tanadar wa rayuwar ku komai ba, ban zabi daya ba cikin abin da ka ke tunani. Babu kuma likitan da yace min ka warke. Da Allah na dogara. Shi na damka wa rayuwarka Mu’azzam, Ya yi yadda Ya ga dama da ita, na amince (wa man yatawakkal alal-lahi fa huwa hazbuhu). Amma ba zan juri ganinka cikin wannan rayuwar da ka ke yi ba mara future, mara ma’ana, mara focus, mara aspiration. A matsayina na Uba dole in yi wani motsi a kai ko da kuwa motsin nawa ba zai zamo solution ba, ko da motsin nawa ba shi ne daidai ba. A kalla dai na samu sanyi a zuciyata na cewa na sauke nauyin da ke kaina, wanda Ubangiji ya rataya min
Likitoci basu ce bazaka iya aure ba, kaine ka zabi hakan Mu’az sabida bacin ran abinda Halima tayi maka da bakin cikin rasa ita waccan ‘yar Ethiopia. Amma zasu iya taimaka maka kayi normal rayuwar aure kamar kowa based on treatment. Please accept my decision and submit everything to Allahâ€.
Mu’azzam bai san lokacin da ya ce, “Daddy, ita kuma matar fa? Ba ka tunanin me zai faru da tata rayuwar? Me hakan ke nufi ga tata rayuwar? Ba ni da soyayyar da zan ba ta! Ba ni da kaunar da zan raba da ita. I have no feelings a kan diya mace. Daddy wannan zai zama zalunci ne a gareta….…â€.
“Mu’azzam!!!â€
Mahaifin ya kira sunansa da karfi.
‘‘Da kai da Aalimah duka ‘ya’yana ne, ba zan zalunci kowannenku ba, ina da kyakkyawan hope na cewa ban cutar da kowa a cikinku ba. Gata na yi wa dukkanninku.
Ba wanda zata samu da zai yi replacing Aboulkhair a gareta in ba kai ba. Ba wadda zaka samu ta rungume ka tsakani da Allah sama da ita. Ya rage naku ku karbi wannan gatan ko ku hambare shi ku bada mana kasa a ido. Suna nan tafe karshen satin nan, a kara gyara ko’ina na gidan kamar yadda na yi umarniâ€.
Daga haka ya kashe wayar sa. Ba tare da ya bashi damar cewa komai ba.

Ya dade rike da wayar a hannunsa, ya dade yana tauna kalaman mahaifinsa a bisa ma’auni na hankali da tunani. Da ya ji tunanin na son janyo masa ciwon kai, kuma babu wata hanyar kubuta a cikinsa dole ya hakura ya kwanta bayan ya kashe wayar sa. Amma duk yadda ya so ya runtsa hakan bai samu ba. Wani suna da Daddy ya ambata yake son tuno a inda ya san sunan.

“Aalimah!!!â€

Ya fadi sunan a kan harshensa duk dai a kokarinsa na tuno mamallakiyar sa. Wa ya sani da wannan sunan a duniya bakidaya ban da matar rabin ransa ABOULKHAIR???

Mu’azzam ji ya yi duniyar na yin katantanwa da shi kafin ta dire shi a kan tsakiyar gadonsa. Tambayar kansa ya shiga yi; tsakanin shi da su Daddy wane ne mai cutar kwakwalwa? Wa ya fi dacewa da karbar rehabilitation? In har Aalimar da ya sa ni suke nufin sun karba masa auranta, tabbas lokacin da zai yi gammo ya bar gari ya zo kafin su zo su tadda shi. Abu na karshe da ba zai iya ba ko duk duniya za ta taru a kansa!!!

                 ******

Gumsu ce tsaye a kan Aalimah tana fama da ita a kan ta yi wanka, yayin da ita kuma ta ce ko da a ce za ta fi kowa wari a duniya ta daina wanka.
Gumsu ta yi dariya wadda ke kara qular da Aalimmah, ta ce, “To ni da ki ke yi wa tambotsai mene ne nawa a ciki? Inji dai ba ni na kar zomon ba balle a bani ratayar sa? In ba tsoro ba ki yi a gaban Inna Kasisi mana? Sai a bayan idonsu ki ishe ni da rashin mutunci kala-kala, kada Allah ya sa ki yi wankan, Basma na hanya, ta zo ta ga abin da ki ke yi, wai don ba ki son dan uwantaâ€.
Wata irin harara Aalimah ta zuba wa Gumsu.
“Idan ita Basman uwata ce ta sanya ni karbar sadakin nanâ€.
Gumsu ta ce, “I can relate. Ni wallahi kin fara sa min ciwon kai, wajen Inna zan maida ki. Don in zan shekara ina fada musu rashin kunyar da ki ke min ba yarda za su yi baâ€.
Ta jefa mata bath kit dinta ta bar wajen.

Waya ce ta iso wa Gumsu cewa Basma ta iso, tana dakin Inna Bintou, tana tambayar inda Aalimah ta ke. Basma ba ta san da sabon gidan da mahaifinta ya gina a nan Yamai ba, kamar yadda ba ta san da sakin da ya shiga tsakaninsa da mahaifiyarta ba. Ta dade da sanin Mummy na son zaman U.S kamar me. Ta gaya mata ita ta zabi zaman can, shi da Gumsunsa sun zabi dawowa don haka kowa ya kama hanyarsa.
Ba irin rarrashin da Basma ba ta yi wa Mummy ba kan ta bi sawun mijinta, ta ce sai ranar da Mu’azzam ya warke, bayan tana da masaniyar babu maganin da zai yi maganin lalurar Mu’azzam a dare daya, sai dai a bi alternative a gode wa Allah.
A ganin Basma, Mummy ta yi amfani da lalurar Mu’azzam ne kawai don ta ci gaba da zama a U.S, in ban da haka mutumin da ba gari daya suke ba, me za ta kulla wa rayuwarsa?
Hatta sayar da lodge dinsu na Boston da Daddy yayi Basma ba ta sani ba. Don haka bata san cewa Mummy a gidan Mu’azzam take zaune ba.
Isowar su Niamey kenan ita da tagwayen ‘ya’yanta, Daddy ne ya kira ta musamman don ta taya Gumsu lallashin Aalimah kasancewar ta wadda tafi kowa shaquwa da Aalimah din, su kuma raka ta dakin ta su biyu. Basma jin ta ta ke kamar a gajimare don farin ciki da kulla wannan aure da iyayensu suka yi. Koda Mu’azzam ba ya shiga rayuwarsu Allah ya sani tana matukar son dan uwanta. Kuma ta dade tana fargabar ranar da Aalimah zata yi aure a wani gidan daban ta bar hannun su, don haka ko ta’ina ita wannan hadin ya yi mata daidai.
Akwai wata magana da suka taba yi da Aboulkhair ta sirri gabanin rasuwarsa, wadda ta goge duk wani bacin rai da kullaci da ta ke da shi akan yayan nata Mu’azzam;

Ya gaya mata Mu’az ba shi da lafiya.
Ya gaya mata aggressive patient ne.
Alakar su ta nesa-nesa na da alaka da mental state dinsa.

Bayan haka bai gaya mata kowanne irin disorder yake fama da shi ba.

Basma a dakin Inna Kasisi, bayan sun gaisa ta karbi twins tana fadin,
“Masha Allah da ‘yan lukutaye, kun zo don ku amshe min miji, to kwalelenku duk jar fatarkuâ€.
Dariya Basma ta yi tana fadin, “Kai Inna akwai kishi, ta ga ‘yammata masu lafiyayyar fata duk ta gigiceâ€.
Inna ta ce, “Ke kuwa ai dole. Muna zaune da mijina lafiya, yana nan-nan da ni ya ga wadannan larabawan naki ai sunana ma mantawa zai yiâ€.
Basma ta sake kwashewa da dariya da ma gwanar dariya ce tun yarintar ta. Abin dariya bai da wuya a wajenta. Kullum fararen hakoranta a waje suke. Very jovial kamar Yayanta Aboulkhair Ta ce,
“Inna ina amaryar tamu ne? Na leka dakin Inna Bintou ba ta nanâ€.
Inna Kasisi wadda ke jin haushin Aalimah har iya wuya ta kyabe baki, ta ce,
“Tana gidan Gumsu, kafaffiyar yarinya mai zuciyar banza. Ni da Aalimah ai mun dade da raba jiha. Wanda duk ba ya son Mu’azzam ni ce ba ya so wallahiâ€.
Murmushi Basma ta yi ta ciro nono tana bai wa ‘yarta, ta ce, “Inna ku bi ta a sannu, ba son shi ne ba ta yi ba. Monsieur Aboulkhair ta ke tunawa da kusancin da ke tsakaninsu, it’s not easy to endure (jure hakan abu ne mai wuya)â€.
Inna ta mike don zancen ba ya mata dadi ko ta ina, a ganinta Aalimah kiyayya ta ke yi wa Mu’azzam kawai don ba shi da lafiya.
Ta ce, “In dai lalura ce babu wanda ya wuce ta, uwarta ma yau shekaru goma sha biyar tana fama, haka ubanta ke hakuri da ita da kalar tata lalurar, ita ma ta je ta yi hakuri da lalurar dan uwanta, waraka a hannun Allah take, cewa nake kun ce bada magani ta karanta? Ba sai ta yi ta ba shi maganin ba su zauna lafiya?â€.
Zancen ya so ya bai wa Basma dariya, da ta karanta bada magani ai ba likitar kwakwalwa ba ce. Likitancin ma sai neuro-psychiatry. Rokon Inna ta ke yi ta sa a raka ta gidan Gumsun (gidan mahaifinta), tana cijewa tana fadin,
“Kada ki wani je ki lallashe ta, bar ta da halinta na tsiya. Aure don Mu’azzam bai sa kansa ba ne, da tuni ya auri hudunta a rana dayaâ€.
Basma ta tabbatar Inna Kasisi ba za ta sa a raka ta inda Aalimah ta ke ba, ta dau zafi da ita sosai, sai ta koma wurin Bintou, ita ce ta sa autanta Bello ya raka ta.
Daga bakin kofa Basma ta tsaya, tana kallon diramar da ake tsakanin Aalimah da Antinta Gumsu a kan cin abinci, Gumsun na fadin;
“Ki ci kada mu kai ki da komada, haka kawai ki sossoke min Da, rama ba ta kyau da amarya’.
Ta ce, “Anti Gumsu ina girmamaki, ina ganin girman ki, amma in ki ka kai ni bango zan yaye hijabin girman nan da nake ba ki. Na ce ba zan ci ba, ki yi min dura in ya zama doleâ€.
7/6/21, 4:51 PM – Buhainat: BASMA

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button