AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Basma ta kama haba, tunda suke tare ba ta san Aalimah da tsiwa da rashin kunya ga na gaba da ita ba. Lallai da gaske ta ke kin Mu’azzam din. Tunda har ya sauyata rana daya. Gumsu ta ce,
“Gara da ki ka gani da idanunki, in wani na bai wa labarin rashin kunyar da Aalimah ta ke min ba zai taba yarda ba, ni kuma kamar dole sai na shiga sha’aninta. Babanku ke ba ni hakuri wallahi da tuni ta tsufa a Las Vegas, don ta soma kawo ni bangoâ€.
Basma ta sako kafa tana shigowa falon ta ce, “I can relate. Amma ni lallashi ne nawa tunda ba zan so Yayana ya same ta duk kasusuwa ba, kada ta soke min shi. Na fi son ya ganta bul-bul, ko’ina ya taba ya ji tubus. Don haka don Allah don Annabi ‘Aal’ ki karbi abinci ki ci…â€.
Kawai sai Aalimah ta sunkuya a kan stool ta fashe da kuka, maganganun Basma kamar sabon Ubangiji ta ji su a kwanyarta. Shigowar Daddy kenan har zai wuce dakinsa ya jiyo kukanta, har zai kyale ya rabu da su don ya san maganar daya ce dai, sai kuma ya dawo sabida tausayin da Aalimah ke ba shi. Dakin ya shigo yana fadin, “Gumsu! Gumsu! Sabida Allah ba za ki lallashe ta ba sai dai ki dinga tunzura ta ko?â€
Sai kuma ya ga Basma, ya ce, “Ke kuma saukar yaushe? Me ku ka yi mata haka?â€
Cikin kuka ta ce,
“Daddy, Basma ta zage niâ€.
Basma ta hau gaishe shi da kokarin kare kanta, ya ki amsawa, ya hau ta da fada.
“Ku da za ku lallaba ta sai ku dinga kunnata, bayan kun san a kan tsini ta ke?â€
“Ka yi hakuri Daddy, ba za mu sake baâ€. Basma ta fada cikin ladabi.
Ya wuce cikin fushi. Basma da Gumsu suka kama abin da ke gabansu don yanzu tsoron sharrin Aalimah suke ji. Ka ce ‘allura’ ta ce ka ce ‘garma’, don ta ga Daddy yana biye mata.
Kwana biyu bayan nan Daddy ya umarci Gumsu da ta kai ta cikin gida ta yi sallama da kowa, wurin Malam ya zama daki na karshe da za su je. Tun Aalimah na kallon al’amarin a matsayin almara har ta yarda gaskiya ne. A lokacin da Malam Ibrahim Raazee ya dora mata sadakinta a tafin hannunta ya kuma bude kofofin nasiha, ban hakuri, ban baki da neman afuwa daga gare ta, kan cewa sun yi exercising power dinsu ta iyaye a kanta kan ba yadda za su yi ne su ma, su samu nutsuwa da kwanciyar hankali in ba hakan ba.
Wannan ne gata na karshe da suke jin za su yi wa rayuwarsu ita da Mu’azzam. Babu mijin da suke ganin zai rike ta da daraja da kima bayan Aboulkhair sai shi Mu’azzam, su ma kuma babu matar da za ta rike musu Mu’azzam da lalurorinsa tsakani da Allah sai ita. Wannan ne hujjarsu ta hada su aure, ta fi kowa sanin yanayin rayuwarsa bayan Aboulkhair tunda sun zauna tare, ta kuma zauna da Aboulkhair ta ga yadda yake kula da shi. Don haka suke da kyakkyawan fata a kanta. Ta yi hakuri kada ta bada musu kasa a ido. Ta manta da kusancin dake tsakanin shi da Aboulkhair ta gina sabuwar rayuwa mai inganci. Aboulkhair ya riga ya yi tafiyar da bazai taba dawowa ba, kuma shima hakan ne gata na karshe da zata yi masa wato tallafar rayuwar Mu’azzam a sanda babu shi.
Aalimah ta ji hawaye masu dumi sun zubo mata, a lokacin da kakansu ya gama yi mata wannan nasihar. Shima yana share nasa hawayen a karshe. Sosai yake tausaya musu dukkansu ita da Mu’azzam din yadda zasu fara fuskantar sabuwar rayuwar da babu Aboulkhair a cikin ta. Ta samu hannayenta da rike kudin sadaqin kam-kam ba tare da sun yi shawara da ita ba. Wanda ke nufin; sun karbi auren Mu’azzam da hannu bibbiyu, ba tare da sun ba ta damar yanke hukunci tsakaninta da zuciyarta ba.
Ana tsaka da zub da kankara (snow) suka sauka a Las Vegas. Don haka ba karamin shiri suka yi wa ‘ya’yan Basma ba, suka kuma sanya su a bayansu ita da Gumsu suka goye da zani. Aalimah ko taya su hidimar yaran ta ki yi sai cin fushi ta ke. Daga lokacin tashinsu da lokacin saukarsu Daddy ya gaya wa Mu’azzam. Wanda har zuwa lokacin yake cikin halin rudu da kidimewa, ya yi kokarin ya fahimtar da Daddy ba zai iya wannan auren ba Daddy ya ki sauraronshi, ya ce,
“Auran nan Mu’azzam an riga an daura shi, ka yi hakuri kawai kamar yadda ta yi hakuri. Ka karbi kaddara kamar yadda ta karba. Ita ma ba ta so, amma ta nuna muna da ikon sanya ta ta yi, ta yi ko da babu son ranta. Haka nake so kai ma ka karba.
Ya kare zancensa da cewa “Mu’azzam ba ka san ta ya ya aka kulla auren nan ba, ba da son ran wasu a cikin gida ba. Burin su ka dawwama a haka babu aure saidai ka ga ‘ya’yan su na yi. A hakan da kake ka tsolewa wasu da dama ido suna kullin ka ba tare da sanin ka ba.
Ina so ka sani duk duniya bayan ni da mahaifiyarka sai Mansour a masu kaunarka. Ka fidda ni kunyar dan uwana mai kaunata da zuri’ata mai kuma kaunarka tsakani da Allah, ka rike Aalimah amana tsakaninka da Mahaliccin ka, in ka yi min haka ka gama min komai Mu’azzam, albarka ta gare ka ba za ta taba yankewa ba!â€.
Wadannan maganganu na Daddy sun firgita shi, sun sanyayar masa da jiki ba dan kadan ba.
Don haka Mu’azzam ya tattara damuwarsa ya hadiye. Babban jin dadinsa da ya kasance su Mummy suna cikin gidan. Ta samu abokan hira da taya ta zaman gidan. Don shi kam ba za a fara abin da ba za’a wanye lafiya tare da shi ba. Yana matukar jin dadin rayuwarsa a yadda yake yin ta, baya maraba da kowanne canji.
Ko Mummy bai gayawa su Basma na tafe ba, kamar yadda bai yi mata bayanin komai ba cikin abubuwan da suke tattaunawa da mahaifinsa. A ganinsa abin da aka dauka da muhimmanci shi ake tsayawa yi wa mutane bayaninsa, yadda suka ajiye ‘yarsu idan zaman ya ishe ta ya tabbata za ta yi musu waya su zo su dauke ta. Tunda shi an yi masa kandagarki da rabuwa da ita har abada.
Harrison ya tura ya dauko su a filin jirgi. Bai san da wanne ido zai kalli Aalimahn Aboulkhair wai a matsayin matar sa ba. Kasancewar Harrison ya san Aalimah bai sha wahalar gane su ba, ya shigar da kayansu booth yana ta yi wa Aalimah fara’a, shi a dole ya nuna ya santa, amma yadda ya ga fuskarta kamar hadarin da ya hadu ya nausa yayi gabas, dole ya hadiye sanayyarsa cikin cikinsa.
Mummy da Yesmin na barci a dakinsu da ke kasa suka ji tashin sautin su Basma. Da farko sun dauka cikin mafarki ne, amma da suka ji ‘ya’yan Basma na canyara kuka sun rasa inda za su sa kansu da wannan weather mai tsananin sanyi wadda ba su taba riskar kansu cikinta ba, dole suka yarda ba mafarki ba ne. Fitowa suka yi da azama sai kuma suka kwasa da gudu suka rungume juna.
Sun dade ba sa tare, sun dade ba su ga juna ba. Soyayyar Mummy da ‘ya’yanta ta motsa. Kwana suka yi a zaune. Duk da Mummy na sanyo Aalimah cikin hirarsu sai ta ga Aalimah din ta ki sakin jiki. Sai sunkuyar da kai ta ke ta kasa kallon fuskar Mummy. Sosai ta ke cikin rudu da damuwa, ita kuma haka za ta kare rayuwarta cikin auren ‘ya’yan mutum daya?
Gumsu ce ta fadi wa Mummy ko me kenan bayan sun sallaci asubahi. Mummy sai ta fashe da kuka wanda dukkaninsu ba su san ko na mene ne ba. Har sai lokacin da ta mike ta shige daki. Kukan damuwa ta ke dana farin ciki duka a lokaci daya, damuwarta shi ne ta san Mu’azzam ba shi da lafiya wannan ba karya ba ne. Ta san yadda aka wanye a aurensa na farko, tsoro ta ke ji kada a maimaita a kan Aalimah. Farin cikinta shine yau Allah ya cika mata burinta Mu’azzam yayi aure, ya zama cikakken mutum mai cikakkiyar rayuwa kamar kowanne dan adam. Babban farin cikinta kuma shine dawowar Aalimah cikin iyalinta. Don ta tabbata in ta kubuce musu sun yi asarar da ba zasu mayar ba.
Ta dade cikin tararradin sake yin aurenta tun bayan gama iddarta. Tana ganin kimar yarinyar domin a tsawon zamanta da Aboulkhair ba ta taba ganin wani hali na ashsha a tare da ita ba. Har gobe kuma tana jin kunyarta na mugun halin data nuna mata a baya, lokacin da Allah ya hada su zama tare a Boston.
Hakika tana son Mu’azzam ya yi aure amma ta wani fannin ba ta so Ishaq ya hada da Aalimah ba. Tunda ba su san me auren zai haifar ba. Ta so su ci gaba da zumuncinsu a haka, Aalimah ta samu miji mai lafiya kamarta ta aura, don tserar da zumunci da ganin mutuncin juna.
Ga shi sun ce an riga an yi auren, ba ta da wata kima gare su a yanzu balle har su yi shawara da ita kafin ayi. Za ta ci gaba da zama tare da Mu’azzam da Aalimah don ganin ba su kusanci juna ba, balle shakuwa ta shiga tsakaninsu. Har akai ga abinda zai bata komai. A ganin ta hakan kawai zata yi ta tserar da auren nasu.