AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Washegari tun karfe bakwai dai-dai Mu’azzam ya fito dining karyawa kamar yadda ya saba. Mummy kawai ya samu a dining din tana zaman jiransa, su suna can suna ta ramuwar barci wanda ba su samu sun yi ba a daren jiya. Ya yi shiri tsab cikin kayan sanyi bakake da jeans baki samfurin NEXT. Ya daure kafafunsa cikin bakin cambass. Cikin nutsuwa yake hada shayinsa wanda ya cikawa gahwah (coffe), amma kallo daya za ka yi masa ka fahimci cikin damuwa yake. Idan ya ce ba ya cikin damuwa kan auren nan da Daddy ya yi masa hakika ya yi karya. Ko ba komai wani nauyi ne aka dora masa wanda bai saba da shi ba.
Mummy ta yi gyaran murya ya dan daga manyan idanunsa farare kal! Ya dube ta, har wani sheki suke fitarwa na musamman da ba kowa yake lura da hakan ba sai wanda ya hada idanu da shi. Mu’azzam yana da kyau mai kayatar da idanu, mai sanyaya zuciya. Idan ka kalle shi za ka so ka maimaita ko don kyawun kwayan idanunsa. Sai dai kasaitar sa da jan ajinsa za su hana ka abokantake shi da sauri, idan ka samu ku ka gaisa ma ka gode. Bambancin sa da Aboulkhair kenan.
Wanda ya kasance mai faram-faram da son jama’a da yin haba-haba da su, balle makusantan sa. Matar sa tayi rantsuwa ta maya kan cewa babu mutum mai kirkinsa da saukin kansa a duniya.
Mummy har sau biyu tana gyara murya, amma ta rasa abin cewa, shi kuma hada shayinsa yake yi bayan gaisuwa bai ce mata komai ba. Ko yaya su Basma suka kwana bai tambaya ba, ta yi ta maza ganin cewa zai gama shan shayin ya tashi ne ya barta a wurin ba tare da sun tattauna akan zuwan bakin nasu ba, ta dube shi tace,
“Kana sane da zuwan su Basma?â€
A gajarce ya amsa “Eh’.
Duk suka yi shiru, yayin da shikuma yake sipping shayin a hankali.
Mummy ta sake cewa,
“Ashe aure Daddyn ku ya yi maka ni ba ni da labari?â€
Shiru Mu’azzam ya yi, kamar ba da shi ta ke magana ba. Ta ci gaba da cewa, “Shi kenan kuma don an sake ni ba ni da martabar da za a nemi shawarata kan al’amuranku? A kalla a ba ni hakkina na haihuwa ko?â€
Mu’azzam ya soma zama bored da maganganun Mummy, don bai ga wanda ya shafe shi a ciki ba. Tsakaninta da tsohon mijinta, shi me ye nasa a ciki saboda Allah? Karewa ma shi kansa ba a yi shawara da shi ba. Mikewa ya yi tare da aje kofin hannunsa ya yi baya da kujerarsa ya hau duba agogon swatch da ke daure a damtsen hannunsa.
“Mummy zan wuce office kuna bukatar wani abu?â€
Ta san in ta ce ta ji haushi ta wahalar da kanta a banza. Kewar Aboulkhairi ta zo ta lullube ta. Kawai sai ta soma hawaye, ta rufe fuska da tafukanta. Ta kifa kai akan teburin cin abincin ta na wani irin kuka mai ban tausayi.
Da yanzu yana nan yana lallashinta, da yanzu yana taya ta neman mafita ga damuwarta, da yanzu yana nan cikin damuwa da damuwarta… Da yanzu ya bata dukkan lokacinsa ya saurareta…. Sun tattauna lamarin yadda ya dace sun nemo mafita. Mu’azzam ya koma kujerar sa ya zauna ganin Mummy na wannan kuka. Wanda bai San musabbabinsa ba. Hankalinsa ya kai kololuwar tashi. Don shi har ga Allah bai ga cewa yayi wani abu wanda ba daidai ba. Ya kai hannunsa cikin sumar kansa yana cakudawa a hankali, ya ce,
“Mummy ki daina ganin laifina, ni ma ban san da zancen auren ba sai bayan da suka daura shi, Mummy I don’t want to talk too much…a kai, ba ni da masaniya a kan ala’amarin nan, me ki ke so in ce miki?â€
Mummy ta cire hannu daga fuskarta, yana ganin yadda hawaye ya wanke mata fuska. Hankalinsa ya kara dugunzuma ya tashi.
“Ba abin da nake so ka ce min, illa ka damu da damuwata Mu’azzam. Sau da yawa ina hadiye abubuwa sabida lafiyar ka, amma na lura bayan rashin lafiya cikin dabi’unka har da ‘hali’. Halinka ne Mu’azzam rashin damuwa da al’amarin kowa…!â€.
Zai yi magana ta katse shi, “Ni na san na yi rashin da ba zan mayar ba! Aboulkhairi, ban san muhimmancin ka ba sai da na rasa ka! Yadda ka damu da ni ni ban damu da kai haka ba! Ka taba cewa don Allah in so ka yadda nake son Mu’azzam. Yau ga ni ina kuka a dalilin rashin ka, Mu’azzam din da na kwallafawa rai ga shi a gabana, amma ban da bakin ciki ba abin da yake cusa mini.
Na hakura da aurena na shekaru sama da talatin saboda shi, amma ba ni da alfarmar tattauna matsala ta da shi…â€. Sai kuka ya kara kwace mata.
Ba abu kankani ke sa Mu’azzam kuka ba, amma dole yau Mummy ta sanya shi kuka. Ya ji yana mai kaico da yanayin halayensa lokaci na farko a rayuwar sa.
Abin da ba ta sani ba, rashin Aboulkhair ya kara taimakawa wajen cire masa walwala da yawan magana. Tun da ya fito daga asibiti walwala ta kara karanci agareshi. Da yana nan ko ba ya son yin magana in dai ya zo inda yake dole ya yi ta, ko ba ya son yin dariya sai ya yi. Zai so Mummy ta ci gaba da yi masa uzurin da ta ke yi masa kada ta gaza…. Zai so Mummy ta daina kwatanta shi da Aboulkhair ta kowacce fuska, domin Ubangiji da ya halicce mu sai Ya halicce mu da halaye mabanbanta, da kamanni daban-daban da personality iri-iri. Shi haka Ubangiji ya halicce shi.
7/6/21, 4:51 PM – Buhainat: 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

A wannan lokacin ba shi da abin yi ban da ya koma ya zauna, ya bata lokaci wajen lallashi da bata hakuri kawai, ba tare da ya yi mata bayanin cewa; shi ma in zai samu mai lallashinsa so yake yi. Ya fi ta damuwa a wannan lokacin, kuma ya fi-ta kewar Aboulkhair.
Koda ya je office yau a makare ya je, saida ya bada hakuri sosai. Yana shiga bayan yayi loosing tie din shi ya zauna a kujerarsa wayarsa ya fiddo ya sake tura wa Mummy text na ban hakuri sannan ya fuskanci ayyukan dake gabansa.

Bayan fitarsa Mummy ta dade zaune a wurin, har zuwa lokacin da text din Mu’az ya shigo mata, murmushi ya subuce a fatar bakinta sabida irin tausasan kalaman da yayi amfani da su duk da cewa ba masu tsayi bane, sai kuma tausayin sa ya lullube ta. Ta sani kwarai shima baya jin dadin yadda rayuwar shi ke tafiya, da gaske yana bukatar mace a gefen shi ba tare da ya san cewa rashin macen ne ya maida rayuwarshi incomplete ba. Ta samu kanta da yi musu addua Allah ya hada kansu shi da Aalimah tare da godewa Mansour cikin zuciyarta, don tana da kyakkyawan zaton wannan kokarin nashi ne ba na wani ba.
Ta share hawayenta ta koma daki. Basma ce kawai ido biyu tana shayar da ‘ya’yanta. Nan ta karbi mai sunanta daga hannunta ta zauna suka soma hira, hirar da ta tada Gumsu da Aalimah daga baccin gajiyar da suke yi. Aalimah ta mike ta nufi toilet don yin wanka. Mummy ta bi ta da kallo tana tausaya mata cikin ranta. Gaba daya ta rame, tayi zuru-zuru ta fita hayyacinta. Babu wata alama ta amarci a tare da ita. Kafarta ko lalle babu.

Kwanaki uku da Aalimah ta yi cikin gidan ba ta hadu da Mu’azzam ba ko sau daya. Yana riga kowa ficewa, kuma sanda zai dawo sun gudu daki sabida sanyi. Ba sa iya zaman falon duk da room-heater da ke aiki. Yana shigowa kuma da sassarfa yake hayewa upstairs din shi kada ma su samu damar ganin sa. Mummy da Gumsu ke musu girki, Aalimah ba ta umh ba ta umh-umh sai in sun sako ta cikin hirarrakinsu ta yi murmushi.
Idan a da tana kallon al’amarin matsayin almara ko mafarki, yanzu ta tabbatar reality ne. Cikin gidan Yayan su Mu’az ta ke, kuma wai a matsayin matarsa ta sunnah. Yayan nan nasu ita da Aboulkhair data ke matukar girmamawa da hidimar dafowa abinci da hadowa magunguna. Irin rayuwar da ta yi da Aboulkhair ake nufin ta maimaita da Mu’azzam! To ta ina? Ta ya ya? Da wacce fuska? Ta wace hanya? How could that be possible? Ko da a ce Mu’azzam zai ba da fuska (wanda ta tabbatar hakan impossible ne) ita wacce irin butulu ce ga Aboulkhair da za ta aikata hakan gare shi? Me yayi mata a rayuwa banda alkhairi da zata saka masa da auren Yayansa mafi soyuwa a gare shi?
Anya iyayensu na aiki da hankali da tunani a lokacin da suka yanke wannan shawarar suka kuma zartar da wannan hukuncin?
Irin tunaninnikan da Aalimah ke yawan yi kenan a duk lokacin da ta kadaice kanta cikin daki ko a toilet, don in tana tsakiyarsu ba sa bari ta yi tunanin komai, yanzun nan Basma za ta janye mata hankali da hira, duk dai don kada ta barta ta yi tunanin wanda ita ta san ya zame mata dole ta yi shi.
Satin su Gumsu biyu a LasVegas Daddy ya fahimci basu da niyyar komawa gida, sun je sun shantake abinsu Mu’azzam na jika su da jin dadi, kudi wannan atm guda ya basu suna sayen duk abinda ransu ke so, ita Gumsu sayayyar haihuwa take ta yi, Basma ‘ya’yanta da mijinta take yiwa sayayya da kannen mijinta ‘yan mata su Suhaima. A ranar da suka cika sati biyu Daddy ya kira ta yana ta fada kan su dawo haka, sati daya ya ce su yi amma sun je sun canza booking sun yi zamansu. Gumsu ta ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button