AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

“Mummy ce ta ce mu kara sati don Aalimah ta sake sosaiâ€.

Cikin mamaki Daddy ya ce, “What? Da ma har yanzu tana gidan Mu’azzam? Na dauka tuntuni ta koma Kano? Ashe Zulaiha ba za ta taba yin hankali ba?â€
Ita dai Gumsu ta yi shiru, ta kuma shiga dana sanin ambatar Mummy da ta yi, ba ta san cewa bai sani ba, da ba za’a ji a bakinta ba. Ko da ta ke da surutu na barkwanci ta ke yi amma ban da na tsegumi da munafurci. Daddy ko sallama bai yi mata ba ya kashe wayarsa.
Sun yi booking za su tashi a washegarin lahadi, don haka suka zauna a falo suka ki yin barci suka kuma ki shiga daki suna jiran Mu’azzam ya dawo, don su yi sallama da shi. Mu’azzam, wanda gidansa ya zame masa kurkuku a yanzu, ba shi ya shigo ba sai karfe goma na dare.
Hannayensa biyu cikin aljihun bakar kwat din jikinsa, kafarsa daure cikin fararen cambass samfurin (NIKE), da dan gudu-gudunsa ya shigo zai haye upstairs din sa kamar yadda ya saba. Bai yi tsammanin ganin ko mutum daya a falon ba kamar yadda suka saba, amma sai ya gansu dukkanin su suna zaune zaman jiran shigowar sa ban da Aalimah kadai. Ga dukkan alamu kuma zaman ba na komai bane dakonsa suke. Dole ya dawo ya zauna a kujerar da ke fuskantar Mummy yana tambaya ko lafiya ba su kwanta ba? Basma ta ce,
“jiran ka muke yi mu yi sallama, gobe za mu koma gida insha Allahuâ€.
Kada kai ya yi irin na ‘to ni me ye nawa a ciki?’ Kafin ya dawo ya samu kujera kusa da Basma ya zauna, ya sanya hannu cikin aljihun kwat dinsa ya fiddo kudi ko kirgawa bai yi ba ya bai wa Basman, ta sa hannu ta karba tayi godiya, ya dauko wasu ya bai wa Gumsu. Gumsu ta harare shi shida kudin nasa, ta ce,
“Ni ba kudi nake so ba, kawai Malam ka kular min da ‘ya ta. Na ba ka amanar ta, ka tausaya mata, ba ta da kowa a garin nan sai kai. Ba zaman Mummy ta ke yi ba, zamanka ta ke yi, don haka ba zan tafi ba sai an ba ta dakin ta da Daddy ya ce a ba ta, ba dakin Mummy ya ce min ta zauna baâ€.
Mummy ta harare ta ta gefen ido, Gumsu kan ba ta haushi wani lokacin, ta fiye wuce gona da iri, tana nufin ta fi-ta sanin abin da ya kamata ne? Ta ce,
“In kin tafi zan raka ta dakin nata aiâ€.
Gumsu tayi tsalle ta dire ta ce atafau sai ta kai Aalimah dakin da ya zam mallakinta za ta bar gidan. Mu’azzam mikewa ya yi zai wuce ba tare da ya ce komai ba. Kansa ya dau zafi sosai, ba ya son hayaniya, komai kankantar ta. Ita kuma Gumsu ya gama fahimtarta ‘yar hayaniya ce ba tun yau ba. Ba shi da zabi ban da ya lallabata ta bar masa gidansa. Ya ce ta biyo shi ya nuna mata dakin da aka yi furnishig din da sunan ‘yar tata. Da karfin gwiwarta ta bi bayansa.
Kwarai ta yaba da bedroom din, sosai furnitures din suka burge ta. Ga dakin kusa da dakin barcinsa. Duk wani motsi da daya yayi dayan zai ji shi. Hakan ya yi mata sosai. Ta je ta takura Aalima ta yi wanka a gabanta cikin ruwan turare na musamman, ta fiddo mata kayan da za ta sanya sababbi kar! A ledarsu, ta feshe su da turare, ta gyara mata dogon gashin kanta. Sannan ta rufe ta cikin lullubi ta kai ta har dakinta gefen gadonta.
Ta gama karance Mummy Zulaiha tsaf! So ta ke ta hana kusanci tsakanin Aalimah da Mu’azzam, amma ba ta san dalilinta ba, shiyasa ta dage sai ta kawo Aalimah dakin ta da kanta, cikin zuciyarta ta ce, “Allah ya fi kiâ€.
Ta zauna a gefen Aalimah ta soma yi mata huduba, ta ce, duk runtsi ta zauna a dakinta, ba ta yarda ta koma dakin Mummy ba, ta shiga rayuwar Mu’azzam ko ba ya so. Ta cire kunya ta kutsa kanta cikin rayuwarsa kota yaya, don in ta biyewa Mu’azzam zata shekara cikin gidan sa basu gaisa da juna ba, wanda wannan ba shine kudurin iyayen su a kan su ba; so suke ta canza Mu’azzam ya dinga walwala da farin-ciki kamar kowa. Duk abin da ta ke so ta dafa da kanta kada ta dogara da girkin Mummy, gidanta ne ba gidan Mummy ba, ta kasa zaman nata auren kada ta sake ta hana ta nata zaman auren.
A hankali Aalimah ta ce, “Aunty Gumsu ni wace ce da zan yi fito-na-fito da ita a gidan danta? Dan ma da ba son shi nake yi ba dole aka yi mun?†Sai kuka.
Gumsu ta ce, “Zauna nan wawuya ki yi ta dakon rashin so, tunda kin ga shi zai fishshe ki. Ki dubi Mu’azzam daga sama har kasa za ki tabbatar ba karamar kyauta ce Allah ya zabo ki cikin dubban mata ya yi miki ba. Ruwan ne ki karbi wannan kyautar da hannu bibbiyu, ruwanki ne ki yi wasarere da ita ki yi wa kanki asaraâ€.
Ta mike za ta fita, sai kuma ta juyo, ta dan rungumeta a jikinta ganin tanata hawaye ba kakkautawa.
“Take it easy my daughter. Insha Allahu sai kinyi alfahari da wannan aure. Mu’azzam is a genius you will soon come to love your husband fiye da son da ki kai wa kaninsa. Na zuba miki duka magungunan da na tanadar miki a lokar gadon ki, Enjoy yourself my daughterâ€. Ta yi murmushi sannan ta sumbaci goshin ta ta fita.

Ita ba karamar yarinya ba ce, ba kuma yau ta fara aure ba, sarai ta fahimci magungunan da Gumsu ke nufi. Wani siririn murmushi tayi mai kama dana tausayin kai. A ranta ta ce,
“Kin dai ajiye min sinadaran da zasu taimaka min wajen tafiya ta lahira duk ranar da ya waiwaye ni. Don ba ki san lalurarsa ba neâ€.

                    *****

Gida ya zama daga ita sai Mummy da Yesmin. Tunda maigidan ba zama yake a cikinsa ba sai lokacin barci. Haka kawai shi da gidansa an haramta masa zaman cikinsa. Wannan abu na ci masa tuwo a kwarya. A da, ba abin da yake so irin ya bude ido ya ganshi a falonsa ko a balcony din gidansa, hakan na sanya shi nishadi matuka. The unbelievably beautiful building of his house wanda mutanen Las Vegas suka kira fierfield terrace and the scent of his tidy green grasses na sanya shi nishadi. Amma yanzu ya zama daga gida sai office sai kan titi.
Wani lokacin zuciyarshi kan shawarce shi to ya dinga zuwa BAR mana don rage lokaci kadai ko ba don ya sha ba? Wata zuciyar sai ta ce, kai yanzu in aka ce ka doshi inda giya ta ke da sadaka sai ka je? Bayan ita ce silar mutuwarka a tsaye ba don ka mutu ba? Ka dai nemo wurin zuwa, amma ban da matattarar shan giya. Kowa ya debo da zafi bakin sa.

Aalimah na kokarin amfani da hudubobin Gumsu a zamanta da Mummy cikin gidan. Ta amince Gumsu mai kaunarta ce da zuciya daya. Sosai take girmama Mummy kamar uwar data haife ta. Bata saukowa kasa sam sai za ta nemi abin da za ta ci. In Mummy ta dafa nasu tana aje mata a food warmer in tanaso ta dauka. In bai yi mata ba ta dafa abinda take so. Tsakaninta da Mummy gaisuwar safe da yamma, tana shiga ta gaishe ta. Ta kuma zauna suna hira da Yesmin. Ita ma ta lura da abin da Gumsu ta gane Mummy ba ta son zamanta upstairs, ta fi son ta dawo nan dakinta su zauna tare don dai ba yadda zata yi ta gaya mata hakan ne. Dalilinta na hakan ne ba ta sani ba. Yesmin kan haura saman wajenta su yi hira. Tana nuna mata damuwarta kan karatunta da aka katse mata a Boston. A bakin Yesmin ta ji cewa Daddy ya sayar da gidansu na Boston dalilin dawowar su nan kenan.
Aalimah ta dade tana mamaki, a baya in wani ya ce mata Daddy zai taba barin rayuwar Turai ba za ta taba yarda ba, sabida yadda Turan ta ratsa jikinsu shi da ‘ya’yansa. Ta san Mummy dole ta zauna don ba za ta iya karbar rayuwa a Nijar da sauki ba. Don ma Yesmin ta sakaya ba ta ce an saki Mummy ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button