AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Tunda ta koma benen ba su taba haduwa da Mu’azzam ba. Ba wanda ya san da zaman dan uwansa, tana da toilet dinta cikin dakinta. Daga karfe shidda na yamma in ta yi wa Mummy gaisuwar yammaci ta dauki abinda zata ci a kitchen ta haye sama ba ta kara fitowa sai wayewar gari. Mummy kullum cikin observing dinta ta ke don ganin ko akwai wani sauyi a tare da ita? In ta zo mata gaisuwar safe ta dinga saka mata ido kenan, amma ga kwanciyar hankalinta ras ta ke ganin Aalimar kuma tana da tabbacin Mu’az bai dawowa sai Aalimah tayi barci, kuma sammako yake ya tafi office.
Sai kuma ta shiga damuwar ina yake zuwa haka after office hours? Kada dai shan giyar ya komama wa? Tunda bashi da lafiyar da zai nemi mata? Abincin safe kawai yake ci a gidan, wunin ranakun ba ta san ina yake samu ba, sai dai tana da tabbacin a WALDORF ASTORIA yake ci don baya cin wani abinci sai nasu kamar yadda ya saba a baya. Ba abinci ne damuwarta ba, inda yake zuwa sai dare ya nausa, shi ne damuwarta.
Mummy ba ta kara shiga cikin damuwa ba, sai da likitan Mu’az ya zo har gida ya same ta, cikin sirri yake gaya mata cewa, cikin satin nan jinin Mu’azzam ya hau, ko ta san me ye matsalolin sa na yanzu? Don hauhawar jini matsala ne babba ga mai matsaloli irin na Mu’azzam.
Mummy ta gaya masa iya abin da ta sani, cewa aure mahaifinsa ya yi masa ba da saninsa ba, kuma matar Aboulkhairi mai rasuwa. Har ma tana gidan ta tare. Nebrass ya yi rubuce-rubucensa, sannan ya tambaye ta ba’a yi masa wani abun da ba ya so? Ma’ana ba’a takura shi yin abinda zuciyar sa bata so? Mummy ta yi shiru, ko zamansu tare da shi itada Yesmin sarkin rikici ai ba ya so. Biyayya kawai yake mata ya takura kansa matsayinta na uwarsa ya danne ransa yake zaune da ita amma a kasan ransa baya so. Ya fi son kadaici. To amma in ta bar gidansa ina za ta?
A yanzu kam ba ta da karfin kama gida a U.S tunda ba ta aiki, sannan ba ta son yin nisa da shi, tana matukar tsoron abin da zai faru duk ranar da Mu’azzam ya kusanci Aalimah. Ita zaman gadi ta ke yi, idan Aalimah ta ki Mu’azzam wace mace ce za ta yarda ta zauna da shi a karo na uku? Kwarai tana tsoron zuwan wannan ranar. Amma Gumsu da kilbibinta ta raba musu daki ita da Aalimah.
Hawaye ta share, ta ce da likita Nebrass,
“Ni kaina ai damuwa ce ga Mu’azzam, amma likita ba ni da inda zan jeâ€.
Cikin mamaki Nebrass ya ce, “Ina mijinta? Yana nufin Baban su Mu’azzam?â€
A sanyaye ta ce, “Mun rabuâ€.
Kamar ya ce da ita, “Kuma aka ce dole sai kin zauna a kasar da ba taki ba?†Sai kuma ya yi shiru, ya soma ja mata kunne a fakaice.
“Mu’azzam dai yana son nutsuwa, yana bukatar sarari daga hayaniya inda hali. Ita kanta matarsa ta yi nesa-nesa da shi, in ba shi ya neme ta ba, Madame, lafiyar dan ki ita ce first, ya kamata ki duba wannanâ€.
Ya yi musu sallama ya tafi.
7/7/21, 8:09 AM – Buhainat: Damuwar Mummy ta nunku. Ta ga cewa komawa Nigeria ko Nijar ya zame mata dole kada wani abu ya faru da Mu’azzam da kyakkyawan treatment din da yake samu Ubansa ya ce ita ce sila.
Kuma a ranar Daddy Ishaq ya kira Aalimah a waya, ya ce ta kai wa Zulaiha wayar yana son magana da ita. A sautinsa ta ji fushi mai tsanani don Nebrass ya kira shi ya gaya masa komai.
Daddy ya soma fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ya ce, in ta kashe Mu’azzam sai ya yi shari’a da ita. Mummy na kuka ta shiga ba shi hakuri, kuma ta gaya masa ba ta da kudin tikiti, sai karshen shekara take karbar kamashonta na banki, sannan tsoro ta ke ji kada wani abu ya faru da Aalimah, Mu’azzam zai rasa mata ta uku… ita kuma burinta shi ne ya zauna da aure ko da babu abin da zai shiga tsakaninsa da matar.
Murmushi Daddy ya yi, ya kuma fahimce ta. Ya ce,
“In dai tikiti ne zai saya musu ita da Yesmin, wannan maganar da ta ke yi kuma ba huruminta ba ne, tunda ko likitansa bai ce don me aka yi auren ba. Ta bar wa Allah komai kamar yadda kowa ya bar masa.
Da wannan nasihar da Daddy ya yi mata Mummy Zulaiha ta soma hada kayanta don barin Las Vegas. Yesmin ta fi kowa farin ciki, ko ba komai ta san Daddynta ba zai barta babu karatu babu aure ba. Kuma zata kasance cikin ‘yan uwanta, ita kuma dama damuwarta kenan.
Har karfe goma sha daya na dare suna zaman dakon jiran dawowar Mu’azzam don yin sallama da shi, wanda yau yayi nisan kiwo fiye da koyaushe, bayan Daddy ya aiko musu da ticket mai zuwa Nigeria ba Nijar ba. Wannan ya dan taba ran Mummy, amma da ta tuna babu aure a tsakaninsu sai ba ta ga laifinsa ba. Kamar tuni yake mata da hakan.
Mu’azzam bai tashi shigowa gidan ba sai karfe goma sha biyu na dare. Zai haye benen shi kamar yadda ya saba ya gansu a zazzaune kamar masu neman gafara.
“Lafiya Mummy ba ku kwanta ba?â€
Mummy ta harareshi kafin tace. “Abinda yakamata da magidanci kenan ya dawo gidansa lokaci irin wannan Mu’azzam? Ina kake zuwa sabida Allah? To ba wani abu ya hanamu kwanciyar ba, jiranka muke mu yi sallamaâ€.
Mummy ta fada idanuwanta sun yi rau-rau suna son zubar da hawaye. Jikinsa a sanyaye ya ciro kafarsa daga steps din daya soma takawa ya dawo ya samu waje a gefenta ya zauna.
Maimakon ya bata amsar waccan tambayar sai ya jefa mata tambaya shima.
“Mummy an yi muku wani abu ne wanda ya bata muku rai?â€
Girgiza kai ta yi, “Ko daya Mu’azzam, kana kula da ci da sha na, suttura da lafiyata daidai karfinka. Ko da samun ka ya ragu ba ka gaza da ni ba ta kowanne fanni. Na sani ba ka son a zauna kusa da kai, amma ko a fuska ba ka taba nuna min hakan ba duk da na sani. Zan koma cikin iyaye da dangi, ina rokonka in na bata maka a tsayin zamanmu ka yafe miniâ€.
Ta kai gefen mayafinta tana share idon ta, “Ka rike Aalimah da mutunci da amana, don Allah Mu’azzam ko don alfarmar mahaifinta…â€.
Sauraron Mummy yake yi attentively har ta yi shiru. Kafin ya ce,
“Ni Mummy zamanki bai takura ni ba, ni da ba zaman gidan nake ba? Ku ci gaba da zamanku har Allah ya huci zuciyar Daddy ya maida ke dakinkiâ€.
Girgiza kai ta yi, “Gara in tafi Mu’az, ya dau zafi da yawa, tafiyar tawa ce kadai za ta sa ya sauko har yayi tunanin maida ni dakin nawa. Na dinga zuwa muku ziyara insha Allah lokaci zuwa lokaci. Kayi min alfarmar bazaka sake yin dare irin wannan a waje ba. Saduwar alkhairi don tashin asuba za mu yi. Je ka turo min Aalimahâ€.
Ya yi dan jimm! Kamar bai ji abin da ta ce ba. Tana da tabbacin ya ji din, duk da haka ta sake maimaitawa,
“Je ka turo min Aalimah mu yi sallamaâ€.
Kamar ya ce, “Ba ga Yesmin nan ba?â€
Ya tuna cewa, sallama yake yi da mahaifiyar tasa, gara ya yi mata duk abin da ta ke so su rabu lafiya, don haka ya mike ya nufi kafar benen cikin takunsa kamar na saraki. Zuciyarsa na tsukewa da wannan umarni na mahaifiyarsa, wanda babu yadda zai yi da shi ta ko’ina, domin kamar da gayya ta yi shi, don ta sa su ga juna shi da Aalimahr da yake gudarwa kwana da kwanaki.
Kayan barci ne a jikinta masu sulbi ruwan shanshanbale. Kanta cikin hular sanyi fara sol wadda ba ta rufe ko rabin gashin kanta ba. Ta hadashi ta nannade kamar gammo a tsakiyar kanta, ta rufe rabin jikinta da bargo mai tsananin laushi da santsi. Barci ta ke sadidan a lokacin da Mu’azzam ya murda kofar, bakinsa dauke da sallama kamar ta rowa. Ba ta amsa ba, don haka ya idasa shigowa dakin yana mai cije lebensa na kasa. Kamshin wani sassanyan turaren wuta dana mata ya bugi hancin sa. Saida ya tsaya ya shaqa sosai yayi ajiyar zuciya. Da alama mai nauyin barci ce, ya lura in zai kwana yana sallama ba za ta ji shi ba. Karasawa ya yi har gaban ta ya dan janye bargon kadan daga jikinta.
Maimakon ya tashe ta, sai ya tsaya kawai yana kallonta. Bai taba yi mata wani kyakkyawan kallo ba sai yau. Mace har mace, wadda ko cikin abzinawa sai an tona, mai tarin nutsuwa, kamala, kunya, kawaici da ilmi. Yana iya tuno kyakkyawar rayuwar da ta yi da mijinta abin kaunarsa Aboulkhair. Don me iyayensu suka yi wannan bahagon hadin?
Aalimah na matukar ganin girmansa, shi ma haka, yana bata respect har guda biyu; na kasancewarta matar kaninsa da yake matukar so, da kuma wanda halayenta ababen yabo suka sayo mata a idanunsa. Bai shirya wannan zubar da kimar ba (rayuwar aure da ita) daga nan har zuwa inda Allah ya nufa da rayuwar kowannensu.