AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Aalimah ta yi wani dan juyi cike da jin dadin barcinta jin sanyi na shigarta tun daga tafin kafa, sakamakon dan janye bargon da Mu’azzam yayi daga jikin ta. Jikinta ne ya ba ta akwai mutum tsaye a kanta. Da sauri ta bude ido, wadanda suka kada suka yi jajir sabida nauyin barci, sai suka rikide suka bada wani irin yanayi mai motsa zuciya, bata yi aune ba sai samun idanun ta tayi kane-kane cikin na Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee, wanda ke tsaye saitin kanta ya zuba mata ido. Da mugun sauri ta yayibi zanin gadon ta rufe jikinta gaba daya. Juyawa ya yi yana mai sakin tsaki ya bar dakin yana mai ce da ita da murya ciki-ciki,
“Ki zo Mummy na kiranki a kasaâ€.
Dakinsa ya karasa cikin takunsa na nutsuwa da kasaita, lokar jikin gadonsa ya bude. Lokacin shan maganin sa har ya wuce yana can yana yawo a titi duk don kar ya hadu da Aalimah, gashi ya tashi a banza tunda Mummy sai da ta san yadda tayi ta hada su. Magunguna ne ga su nan birjik! Wadanda aka rubuta mood stabilizers su ya cira ya dauko gorar ruwa cikin karamin firjin da ke gefen gadonsa, ya watsa su cikin bakinsa, ya bi su da ruwa. A hankali ya kwanta bisa gadonsa yana maida numfashi a sannu. Saukowar da bai kara yi ba kenan sai asubahin wayewar gari. Shi da kansa ya tuka Mummy zuwa airport bai hada ta da Harrison ba.
Har da Aalimah aka tafi kai Mummy airport, don haka a hanyarsu ta dawowa daga shi sai Aalimah cikin motar an rasa mai yin ko motsin kirki a tsakaninsu. Aalimah ko numfashi za ta fitar sai ta tabbatar ta sake shi a hankali, yadda ba zai zama takura ga Mu’azzam ba. Ta san halinsa sarai, ba yau ta sanshi ba.
Suna isowa gida ta bude motar a hankali ta fita, haka nan a hankali ta rufe ta silently. Ta juya cikin takun nutsuwa ta shige cikin gida, ko kofa za ta bude a hankali ta ke yi, don sanin cewa Mu’azzam ya biyo bayanta.
******
Tafiyar su Mummy sai ya mayarwa da Aalimah gidan kamar maqabarta. Har zuwa washegarin ranar bata kara sanya Mu’azzam a idanunta ba. Ko motsinsa bata ji ba duk da cewa dakunansu na daura dana juna. A washegari Mu’azzam sammako yayi ya fice office ko karyawa bai yi ba, tana iya jiyo fitar motarsa daga gidan. Tana daga kwance a gadonta tayi ajiyar zuciya. A lokacin zuciyarta tayi zurfi cikin tunani mai dimbin yawa. Shikenan rayuwarta da Aboulkhair ta zama tarihi? Mu’azzam ne zai maye duk wani gurbi da Aboulkhair ke kai a baya? Ta yaya hakan zai kasance?
Bata taba yiwa Mu’azzam wani kallo bayan na Yayan su ba, ko ta ce Yayan mijinta. Rayuwar shi da tata ba iri daya bace; ratar dake a tsakani mai tsananin fadi da girma ce. Ga matsalar da yake ciki wadda bata san ranar warkewar ta ba. Saidai tana da tabbacin aggressiveness dinsa bazai shafe ta da komai ba. Zata iya yin nisa da shi a duk lokacin da taga alamun yana kokarin shiga cikin sa. Tunda Aboulkhair ya gaya mata yadda yake. Wanda ana daukan shekaru ma hakan bai faru ba. To amma babbar lalurar fa?
Aalimah ta nisa, ta aje gwauron numfashi.
Ko lokacin da take tare da Aboulkhair ita ba mai son yawan auratayya bace, wancan ma kenan da ya kasance soyayya ce mai tsanani a tsakani balle wannan da ya zamo hadin iyaye, ba da son ran ko dayansu ba.
Tana matukar ganin girman Mu’azzam da ganin kimar sa cikin idanunta, bata fatan zuwan ranar da zama irin na auratayya zai kasance tsakanin su. Koma dai yaya ne, tasa a ranta zaman iyayensu zata yi a gidan nan ba zaman Mu’azzam ba, wanda take da tabbacin shima ba son auren yake yi ba koda ace bai bude baki ya furta ba. Alamu duk sun gama bayyana kansu.
Data gaji da tunanin wanda ta amince bazai kawo mata mafita ba cikin tarin kalubalen dake gabanta, sai ta tattara komai ta mikawa Ubangiji. Ta tashi ta dauro alwala ta shiga gabatar da nafilfili.
Lokacin gari yayi haske, ta yunkura ta mike daga kwanciyar bayan ta ture bargon rufarta. Kai tsaye toilet ta fada tayi wanka tayi brushing bakinta ta dauro towell ta fito. Ta bude closet dinta ta soma ruwan idon kayan sanyawa. Ba Mu’azzam take da niyyar yiwa kwalliya ba kawai ta samu kanta yau cikin sukunin zuciya irin wanda bata taba samu ba tun rasuwar Aboulkhair. Lallai ne da ake ce aure rahma ne, kuma gidan miji ‘yanci ne ga diya mace koda wane iri ne kuwa.
Ruwan idonta ya tsaya akan wata doguwar riga ‘dark blue’ wadda nauyin duwatsun jikinta yafi yadin rigar nauyi, ta cirota ta zura a jikinta sannan ta zauna kan stool gaban dressing mirrow tana gyara dogon sassalkan gashin kanta wanda saida dabara take iya tazarsa.
Wayarta dake kan bed-side tayi kara da kiran sallah wanda shine ringing tone dinta. Mikewa tayi ta isa ga wayar ta dauka. Ganin sunan mai kiran sai ta zauna a gefen gadonta cike da farinciki tana amsawa.
Mama ce.
Bayan sun gaisa cike da shauki irin na Da da mahaifi ta tambayi lafiyar kowa na gida, Mama ta tabbatar mata kowa lafiya, ashe Daddy na kusa, don Mama mikawa Daddy wayar tayi tace shi ke son magana da ita. Aalimah ta gaisheshi shi kuma ya dinga zuba mata albarka akan biyayyar data yi masa, ko daga sautin muryarta ya fahimci ta kwantar da hankalinta yanzu ta kuma rungumi kaddararta da hannu bibbiyu.
Dr. Mansur yace “Aalimah kinsan dai ni na haifeki ko?†Ta gyada kai cikin tabbatarwa kamar yana ganin ta. Yace “to ki yarda bazan taba yin abinda zai cutar da ke ba. Kada rashin lafiyar Mu’azzam yasa kiyi tunanin don bazai samu matar aure bane yasa muka aurar dake gareshi, ko kadan, Ko ‘yar wa Mu’azzam yake so a fadin kasar Nijar zai aura mun dai ga bashi da niyya ne. Bari in gaya miki wani abu wanda ko uban Mu’azzam da ya haifeshi bai sani ba.
Rana ta karshe dana gana da Aboulkhair a dakina, munyi maganganu masu yawa akan Mu’azzam, kin san dai fannin rashin lafiyar Mu’azzam ya karanta har matakin consultant, kuma yake kan cigaba da zurfafa ilmi akai a jami’ar Johns Hopkins, ya gaya min bincike na karshe da suke kan yi of recent research ya nuna Mu’azzam zai iya warkewa gabadaya, zai koma normal sexual life bayan shekaru kamar goma in dai an kula da bashi treatment. Ya gaya min yana so ya gayawa Mu’azzam amma ya fasa don kada yace sai ya warke zai yi aure, amma ko likitansa Nebrass yasan Mu’azzam zai iya warkewa daga yanzu zuwa kowanne lokaci in aka kidaya yawan shekarun da ya kwashe cikin lalurar karkashin kyakkyawar kulawa kuma zai iya rayuwar aure yanzu haka (under treatment).
Shine dai yake tsaurarawa kansa damuwa da ganin cewa rayuwar sa ta gama amfani. Amma babu cutar da Allah ya saukar a duniya ba tare da ya saukar da ita tare da maganin ta ba. Ki yi tawakkali ki tattara komai ki barwa Allah. Kiyi addu’a kan Allah ya hada kanku da kuma zukatanku wuri guda, ki zubawa sarautarsa ido.
Ni Mansur Sarhamu Raazee na tabbatar miki sai kinyi alfahari da wannan auren watarana kuma sai kin zo kin gode mini. Soyayyata gareki ce tasa nayi miki wannan zabin. Zabin da duk cikin family din RAAZEE babu mai kamar naki. Ki kwantar da hankalinki a gidanki kinji Aalimah? Ki kuma yi hakuri da halin Mu’azzam mutum ne mai wuyar sha’ani. A matsayin ki na mace, zaki iya canza shi zuwa duk irin yadda kikeso ya koma. Mu’azzam is a nice person kuma idan kinyi hakuri zaki ci riba wataranaâ€.
Aalimah hawaye take yi tana sharewa da bayan hannunta. Ta san Daddy na sonta amma zata iya bayar da shaidar son da yake yiwa Mu’azzam ya nunka nata sau goma. Zuciyarta na mai amanna da kowacce kalma dake fita daga bakinsa.
Cikin rishin kuka Aalimah take fadin.
“Don Allah Daddy ka yafe mun gardamar dana yi maka a baya. Na rasa nutsuwa ta ne a lokacin. Ba kiyayya nake yiwa Mu’azzam ba, sannan ba rashin lafiyar sa ke damuna ba, ina dai duba kusancinsa da Aboulkhair ne. Amma daga yau na yi maka alkawarin cire komai daga raina insha Allahu, na yarda haka Allah ya rubuto mana bakidayan mu. Na san aure a tsakaninmu halastacce ne. Na yarda da duk abinda ka fada, ko Mu’azzam ba zai warke ba zan zauna dashi insha Allahu har karshen rayuwata. Ka taya ni addu’a Allah yasa nima ya so ni irin yadda Aboulkhair ke so na……!â€.
Sai kukan ya kwace mata bakidaya.
7/9/21, 7:20 PM – Buhainat: Aalimah