AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Aalimah, ta ja dogon numfashi a yayin da tunaninta ya zo nan, tana kallon su Basma na shigowa falon, babu kamannin ‘ya’yan Auzinawa ko na Malam Bahaushe ko kadan a tare da su, sun fi kama da ‘ya’yan kasar Somalia. Fatar Babansu da ta mamansu bahaushiya ta cakude ta ba su wata irin colour da complexion mai ban sha’awa. Ga su da tsayi da mulmulallen jiki tubarkallah. Sunshades a idanun Basma da Khaleesat, dogayen wandunan jeans na mata da rigunan Armani collection a jikin kowaccensu. Khaleesa ta kusa kamo Basma a tsayi, babu dankwali a kansu gashin Abzin din ya kwanta a kafadunsu.
Basma a gaba, sai Yesmin biye da ita, sannan Khaleesa, Aunty Zulaiha da Daddy suka biyo bayansu.
Tsayawa ta yi a kofar kicin din ta harde hannayenta a kirjinta tana kallonsu da murmushi irin na ‘yan uwantaka. Khaleesat ce ta fara ganinta, ta zare sun shade dinta ta mutstsika idanunta ta ce,
“Daddy, am I dreaming? She looks so much like Aalimahâ€. (Daddy Mafarki nake yi? Ta yi kama sosai da Aalimah). Sannan ne hankalin kowa ya kai gare ta.
Aunty Zulaiha kam shaf! Ta manta da zuwanta, sai yanzu ta tuna. Take fuskarta ta sauya, ta wuce upstairs kai tsaye.
Basma ta yi cilli da jakarta ta yi kanta da dan banzan gudu, saura kadan su sha kasa su duka biyun, tana kakabin murna. Daddy ya wuce kujerun falon ya ajiye suitcasedinshi, yana rike da falmaran din suit din jikinshi. Gogaggen dan boko wanda ya ga jiya a Amurka yake kuma ganin yau, ga furfura nan tsilli-tsilli a kanshi, amma tsammani za ka yi Balarabe ne ba ba’abzine ba. Dogon hancin nan zur! Kamar na Babanta.
Kujera ya samu ya zauna a gajiye yana kallon Aalimah da ke tahowa, Basma da Khaleesa sun sako ta a tsakiya har gabansa, sun bi sun rirrike hannunta, bakinsu kamar zai tsage don farin ciki, kan kujerar suke kokarin zaunar da ita kusa da Daddyn, amma sai ta zame ta zauna a kasa daura da kafafunsa ta soma gaishe shi cikin harshen Hausa.
Cewa yake, “Tashi-tashi ‘yata ki zauna a kujera, kin sha hanya. Ki yi hakuri I couldn’t make it taking you from airport, I went to California for a meeting, dawowata kenan. Ina fatan kin ci abinci kin huta?â€
Murmushi ta yi, ta ce,
“Babu damuwa Daddy, kuma na ci abinciâ€.
Ya kalli Basma ya ce, “ Basma bani jakar canâ€.
Ta dauko jakar ta kawo masa babu ko russunawa kamar ta mikawa sa’anta, Aalimah ta ji wani iri a ranta. Budewa ya yi ya fiddo wasu takardu ya mika wa Basma, ya kuma mika wa Aalimahn wasu irinsu. Ya bawa kowaccensu biro ya ce ta sanya hannu karkashin dokokin jami’ar da za su je. Sai a lokacin ne Aalimah ta ga admission letter dinta da kwas din da Babanta ya zaba mata.
Zukar numfashi ta yi ta fesar, tana rokon Allah ya fidda ita kunyar iyayen ta, ta sha ji a bakin Yayanta Aboubacar how complicated pharmacy is (tsaurin kwas din harhada magunguna) lokacin da Daddy ya ce ya karanta shi don shine abinda Kakansa Prof. Kashim ya karanta ya kuma zauna akan (proffessorial chair) dinsa har mutuwar sa, ko don ya farantawa Mama, Aboubacar ya fitittike ya ce shi ba zai iya ba, Accounting yake so.
Nasiha sosai Daddyn ya yi musu a kan su tsare mutuncinsu, su maida hankali kan abin da ya kai su. Bai yarda da yin saurayi ko friendship da maza ba, duk kuma ranar da ya ga hakan zai cire kowaccensu ne ya yi mata aure. A karshe ya yi musu addu’a, ya gaya musu jibi za su fara registration.
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM – Buhainat: 🌹 Aalimah 🌹
*
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
FREE PAGES 6
Ta jima a jikinsa tana ba shi hakuri, sannan ya ce ya hakura, amma in tana son zaman lafiya ta daina kawo masa wadannan sababbin halayen da ta billo da su, kuma ta zauna lafiya da Aalimah don zamanta daram a gidansa, tunda ba tare suka hada kudi suka sayi gidan ba. Duk ta ce ta yarda, sannan suka yi dan gajeren romancing dinsu suka fito, suka tadda yaran duk sun sha wanka sun shirya gwanin sha’awa. Daga Basma har Khaleesat kayan Aalimah ne a jikinsu. Sun dan matse su sabida duk sun fita garin jiki. Don ma dai manyan riguna ne dinkin Nijar. Ta hadiye wani abu da ya tokare ta a wuya, ta kama hannun Yesmin suka fita. Ta dauka motarsa zai nufa ya shiga ya tafi inda za shi, sai ta ga ya ce duk su shigo tashi motar.
Mummy kamar ta yi kuka don ya rushe duk wani plan da ta shirya. Ta shirya a ranta ba wani traditional wears da za ta saya musu, kuma ba za ta sai wa Aalimah wani abin kirki ba, kwancen su Basma za ta dawo ta tattara mata. Ta san ba shi da sanya ido, ba abin da zai fahimta. Amma yanzu ta san ya ruguza komai.
Chevrolet din Daddy suka shige dukkansu. Ya zauna a mazauninsa ya sanya belt, sannan ya tsaya yana dan duba abu a wayarsa,da alama adireshin inda zai je yake dubawa a yanar gizo. Sannan a tsanake ya dauki hanya. Aalimah sakin ido da baki da hanci ta yi sosai tana shan kallon birnin Boston, don tunda ta zo ban da makaranta, babu inda ta ke zuwa.
Su Khaleesa na ta hira a tsakaninsu ba ta sa musu baki ba, wani lokacin ma ba sosai ta ke fahimtar maganganunsu ba, sabida yanayin accent dinsu. Sun iya Hausa, amma ba sa janta da nisa, wato jefi-jefi suke yinta. Ta lura Mummy ba ta da walwala sosai tunda suka taho duk da Daddy na yi mata hira. Tafiya suke sosai kamar za su bar cikin gari, kafin Aalimah ta ga sun hau wani titi da aka rubuta Newbury street Boston. Sun yi tafiya sosai a cikinsa kafin su karkata ya yi parking a kofar wani katafaren shago a samansa an rubuta Riccardi. Tunda Mummy ta fahimci shagon African Germents ne na maza da mata ta sake gyara zamanta cikin motar tana duba Ipad dinta.
Daddy ya dan dube ta ya ga ba ta da alamar fita sai ya mika mata hannu ya ce,
“Give me the credit cardâ€.
Ba musu ta dauko a jakarta ta ba shi abinsa.
“Ba kya bukatar komai?†Ya sake tambaya cikin kwantar da murya.
Ba tare da ta dube shi ba, ta ce,
“A nan dai babu, su shiga su fitoâ€.
Ya kada kai ya bi bayan yaransa wadanda har sun shige shagon sun hau elavator. Abubuwa kadan suka tsitstsinta a Riccardi don kayan maza na Africa sun fi yawa. Basma ta ce, Daddy ya kai su wani shagon again. A cikin mota ya zauna ya kira waya ya yi magana da wani abokinsa dan Nigeria, mutumin ya hada shi da matarsa suka yi magana, sai ya ja motar. Wannan karon kan titin Harrison Ave Daddy ya shiga.
Tun daga nesa Aalimah ta hango dogon ginin da ya tabbatar mata wannan karon su Basma za su samu har ma fiye da irin kayan da suke so. Daddy ya yi parking a parking lot suka firfito, wannan karon ma banda Mummy, Aalimah, ta daga kai tana karanta sunan shagon, ‘ZAINAB SUMU PRIMITIVE MODERN’. A cikin shagon nan su Basma sun yi siyayyar kaya da jewelleries har da na banza. Da ta ga Aalimah ta ki daukan komai ita da kanta ta dinga daukar mata duk abin da ta daukar wa kanta. Sai dai tana bambanta colour. Ta fahimci Aalimah na son ‘dark colours’ sabida kalar fatarta don haka komai ta daukar wa Aalimah mai turuwa ne sosai, sai ta daukar wa kanta lighter one. Hatta Yesmin sun gwangwajeta da kayayyaki daidai jikinta, sun samu kaya iri-iri, na Nijar, na Najeriya, na Senegal, na Arab da na D’jbouti. Daddy shi yake nuna musu wasu ma ya ce su kara. Sai da Khaleesat ta ji tausayin creditcard dinsa, ta ce su barshi haka, amma shi ko a jikinsa. Ya basu suka zare kudin komai, za su fito kenan wani Bature ya biyo su da gudu ya ba su wani littafi yana tallata musu malldin The Germent District, ya tabbatar musu za su samu shagon beyond their expection, za su ji shi kamar suna cikin Africa in dai batun tufafi ne. Basma ta ce a je, Khaleesat ta ce, sai dai wani lokacin, Aalimah ta ce su tausaya wa Daddy su barshi haka. Hannu ya dora a kan kafadunta ya bubbuga.
“If you like atamfa, lets go Aalimah, kada ki ji tausayin wannan Daddyn he loves you more than his moneyâ€.
Dariya suka yi suka shiga mota suka tafi. Aalimah dai ta kafe a barshi haka sai wani lokacin. Ganin ta dage suka yarda.
Sai da suka yi nisa Mummy Zulaiha ta yi gyaran murya, su kam har sun manta Mamansu na cikin motar saboda rashin motsinta. Daddy ya dan dube ta ya maida idonsa kan titi. Duk kokarinsa na fahimtar matarsa ya kasa. Ta zame masa ‘alqibla-less’. Ta dan motsa dan kyakkyawan bakinta tana magana, “Mu shiga kasuwa daBURLINGTON MALL zan yi cefane da tawa siyayyarâ€.
Bai ce komai ba ya karkata kan motar ya nufi kasuwar da ta fada, su suka taya Mummy da tura sayayyar da ta ke yi a shopping bag, har ta gama cefanen kayan abinci kala-kala nau’i-nau’i suka sa a bayan mota. Daga nan sai suka wuce Burlington Mall din ta yi ta sayayyar kayan gayunta, su ma ba a barsu a baya ba duk wani abin amfani na mata na tsaftar jiki da kayan shafa da kamshi sun saya, Daddy na ta biya, sannan suka taho gida.
Kafin su iso gida Mummy ta saki rai sosai tana ta jan mijinta da hira, su ma yaran tana kula su har Aalimah. Shi dai kallonta yake yana mamakinta. Ta zame masa kamar wata mai ‘Multi personality disorder’ yanzu ta ke daidai anjima za ta koma wata majanuniya. He loves his wife as such! Wato yana son matarsa a duk yadda ta ke. Take-away suka yi na KFC kafin su shiga gida don already dare ya yi, kuma duk yunwa suke ji mai girkawar ma Mummy ta gaji tibis. Tun a lokacin ta soma regrettingkorar Easther da yanzu kafin su dawo sun tadda komai yana jiransu a kan dining. To wai ma da ta yi gaggawar korar Easther how sure is she (wane tabbaci ta ke da shi na cewa) Aalimah ta iya girkin da za su iya ci har mijinta? Damuwa karara ta bayyana a kan fuskarta har suka shiga gida.
Kafin su kwanta, suna zaune a falo tare da yaran, Daddy ya ce, “Zulaiha ina tunanin daukar wa yaran nan driver, Basma ba ta kai shekaru sha takwas baballe ta dinga tuka su. Duk da Aboulkhair is coming for his holiday next month bana jin zai juri jigilar kai su da dauko su da wannan baccin safen nasa. Hanya ta da tasu are parallel (sun baude) ina makara most often (sau-tari)â€.
Da sauri Mummy ta ce, “Ka san bana son strangers Daddy, ka bar zancen daukar driver din nan don Allah. Ni zan dauki nauyin kai su da dauko su dukkaninsu. Na gama course din da office suka sanya ni yi a Worcesterkarfe hudu zan dinga dawowa, kuma zan zauna wata guda a gida kafin na koma office so I will take care of their transportationâ€.
Cike da gamsuwa ya gyada kai sannan ya dago ya dube ta yana murmushi.
“Promotion in progress… Ummu Mu’az, wannan karon ya kamata a cire min parcentage, kudi sun yi miki yawa matar nan kuma ba mai ci, ke kanki ban ga kina ci baâ€.
Dariya ta yi cikin nishadi ta kada masa kyawawan idanunta,
“Kai ma ka san wa nake tarawa.
I want him to own a lodge in one of the America’s most expensive luxury condos. Be it in San Francisco, Miami, Los Angels, Dallas, Seattle, New York, Oahu, Ohio, Chicago, nan Massachusetts, or wherever he like. A penthouse; irin wanda ko a garuruwan nan dana ambata sai dan gata zai iya mallaka. Ka san Allah Daddy ba don kaina nake wahalar aikin nan ba. I’m doing it for “MU’AZZAM†da lafiyarsa, tunda na lura shi in don ta shi bai damu ya tara komai ba.
Abin da ya sani kawai shi ne, ya yi ta bautawa wannan aikin nasa, yana karar da kudin a gidan haya, bayan wannan ban san me Mu’azzam ke yi da kudin da yake samu ba. I’m sometimes wondering he belongs to CHEVRON (wani lokacin ina tababar kasancewarsa ma’aikacin CHEVRON)â€.
Murmushi sosai Daddy yake yi yana sauraronta da mamaki. Ba tun yau ba ya sani, Mu’azzam is her favourite childcikin ‘ya’yanta, amma bai taba sanin abin ya kai haka ba. Ta ci buri mai girma a kansa.
Wato duk tsayin shekaru goman nan da ta dauka tana aiki da JP Morgan Chase yana mamakin me ta ke yi da kudinta, tunda duk bukatunta babu wanda ta taba dauke mishi, sannan ya san ba iyayenta ta ke kaiwa ba, don shi ne ya gaji da ganinsu cikin tsohon gidan da suke ciki ya sauya musu, hatta petir din da za ta zuba a mota yana wuyansa, ashe this is her dream! Gyara zama ya yi sosai ya fuskance ta, ya kira ta da sunanta na yanka,
“Zulaihatu!â€
Wannan ya tabbatar mata maganar da zai yin is highly sensitive. Bai damu da amsawarta ba, ya ce, “Ki fidda ZAKKAH, ki yi sadaka, ki kai iyayenki Hajj da duk wanda ya kamata cikin ‘yan uwanki. Sannan ki ninka kyautatawarki gare su.
Ba’a san gawar fari ba, amma use your opportunity when it is in your hands (wani lokaci na zuwa da za ki so ganinsu ko sau daya, amma zai zamo ba sa raye, ki yi amfani da damarki a lokacin da ta ke hannunki). Mu’azzam baya neman agajin ki a halin yanzu, domin ya riga ya tsaya a kan duga-dugansa. Abinda yake bukata daga gareki shine kawai ADDU’A da sanya albarka. And thank Allah the exalted for making you two alive together,which is his foremost success in life(kuma ki godewa Ubangiji Mabuwayi da ya raya ku tare, wannan shine babbar nasarar sa a rayuwa). Wannanita ce shawara ta gare ki a matsayina na mijinki, uban ‘ya’yanki,wanda ya fi kowa kaunarki in an cire iyayenki. Besides, this boy is making a lot of money beyond your expection (ta wani gefen, wannan yaron yana samun kudi fiye da tsammaninki). Yarage naki ki dauka ko kada ki dauka. Ina kara maimaita miki cewa(Mu’azzam ba ya bukatar kudinki don ya tsaya da kafafunsa, abin da yake bukata shi ne, KE din kanki a raye, da addu’o’inki.
Yana gama fadin hakan ya tashi ya hau sama ya barta a nan tana ta karanta wasikar jiki. Tana analysing kalamansa filla-filla.
*