AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Dan guntun scene din da ya faru a dakin Mu’azzam ta ke ta tunawa da ta koma nata dakin, wani ta yi murmushi, wani ta yi ajiyar zuciya. Ta kai gwauro ta kai mari a tsakiyar dakinta, tana mai naushin hannunta cikin tafin hannunta. Aalimah, ta samu kanta da son yin kyakkyawan bincike na ilmi bayan wanda Aboulkhair ya gaya mata a kan lalurar maigidanta Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee. Ta hakan ne zata san irin matakin da zata dauka akan zaman su da yadda zata bullowa rayuwar auren su, tunda kuwa abu ne wanda ba su da damar gujewa dukkanninsu. Auren su is inevitable. Don haka maganar wahalar da zukatansu ba shine mafita ba, mafitar itace ta nemi hanyoyin da zasu dorar da zaman nasu. Ciki kuwa har sai ta fahimci lalurorin sa bakidaya a ilmance, a likitance, a rubuce, a mu’amalance sannan in theory and practice.
Ta fara da shiga manhajar google inda ta binciki cikakken bayani a kan what the problem is all about? Sannan ta ke shiga library din Mu’azzam idan ya fita office, tana masa bincike, yana da manyan littattafai da suka shafi compulsive sexual disorder. Cikin manyan littattafan da ta debo daga library dinsa zuwa dakinta akwai ‘A Psychometric Investigation of the Hypersexual Disorder Screening Inventory’ (By J. Engel. 2019). ‘The Danger of Hypersexual Disorder’ (Dr. Martin Kafka), sai kuma ‘Compulsive Sexual Behaviour’ (A Review of the Literature) NCBI (By KL Derbyshire, 2015).
In takaice miki Aalimah sai da ta zama kamar wata ‘yar karamar Farfesa (Professor) a kan lalurar Mu’azzam sabida karatu da bincike, inda ta fahinci komai ta gane kan komai, ba tare da Mu’azzam din ya san tana yi ba.
Abu na gaba da ta ke son yi shi ne, ganawa da Dr. Nebrass Sheldon, ta kuma rasa hanyar yin hakan, tunda ba ta ganshi yana zuwa gidan su ba, ba ta kuma san a ina suke haduwa ba shi da Mu’azzam din. A lokacin da ta fahimci behaviour din, sai ta ga ba maraba da yadda Aboulkhair ya labarta mata. Ta dai samu faffadan bayani ne da cikakken ilmi akan lalurar.
Aalimah ta manta da wani abu wai shi ‘AURE’ dake tsakaninta da Mu’azzam, sai motive na ‘yan uwantaka. Sosai ta ke jin son ta tallafi rayuwar shi a haka, a hakan da yake da wannan lalurar, yadda Halima ta kasa. Ta ke ji a ranta cikin kowanne hali, za ta iya jimirin zama da Mu’azzam sabida biyayyar iyaye da kauna ta jini.
Ba abin da Uncle Ishaq bai yi mata a rayuwa ba! Ta tuno dauki ba dadin da ya dinga yi da matarsa a kanta. Ranar da ya gane Mummy ta hanata zuwa makaranta har na tsawon sati biyu ta maida ita boyi-boyin gidanta. In bata manta ba a ranar har hawaye yayi a kanta. Ya rungumeta a jikinsa kamar shi ya haife ta ya bata hakuri kamar zai ciro zuciyar sa ya bata don tayi hakuri ta cigaba da zama da su. Ya yi mata komai a rayuwa daga zamanta a gidansa har zuwa yau data auri Mu’azzam. Da yardar Allah jininsa bazai tozarta a hannunta ba.
Ta ji tana son shiga cikin rayuwar Mu’azzam ta kowanne bangare, ta fahimce shi yadda Aboulkhair ya fahimce shi, ta taimaka wa lafiyarsa yadda Aboulkhair ke taimakawa, ta kawo murmushi akan fatar bakinsa, ta kawo sauyin rayuwa mai tattare da nishadi. Duk da ba ta da shaidar ilimin da ya danganci wannan lalurar a yanzu, tana da fahimta a kai daidai gwargwado. Tana so ta shiga rayuwarsa ta ko ina yadda Aboulkhair ya shiga. Ta taimaka ta ko’ina, yadda Aboulkhair ke taimakawa. Har ake ganin murmushi a fatar bakinsa idan har suna tare, tana yiwa kanta kwadayin samun irin wannan matsayin a wurin Mu’azzam idan har zata samu dama! Tana rokon Allah Ubangiji ya dafa mata, ya agaza mata a bisa wannan niyya tata ta alkhairi akan mijinta.
******
Misalin karfe biyar na yamma Mu’azzam ya dawo office. Bai tsaya a ko’ina ba, kai tsaye cikin yanayin tafiyarsa mai kama data jinin sarauta ya soma taka matattakala ya haye upstairs don isa ga dakin barcinsa.
Bai dade da shiga ba ya ji Aalimah tana kwankwasawa. Wani abu da ba ta cika yi ba a tsayin watannin da suka kwashe tare, wato shigo masa daki in ba da kwakkwaran dalili ba, sai dai ta girka masa delicious ya ci ya more, in ba ta da lafiya ya kan kai ta asibiti, wanda sau biyu ne ma kawai tayi ciwon mara, ta fada masa abubuwan da ta ke bukata na cefane ya sa Harrison ya kawo mata. Ya lura bata komai yanzu sai karatu a library wanda bai san na menene ba. Ta dauki hankalinta da lokacinta kacokam ta mallakawa library, ko dakinta ya shiga zai ganta da glass tana karatu a ipad dinta, abinda ke gudana a tsakaninsu kenan a tsayin watannin su masu dan dama tare.
A tunaninsa tun wancan zuwan nata dakinsa da ya gaya mata maganar da ba ta taba zato ba, sanda tace ya maida ta makaranta ko aikin ta na pharmacy ba ta kara gigin zuwa dakin shi ba, don ta fahimci kamar ya gama karbar auren nasu, tana kuma tsoron abinda zai biyo bayan hakan, don haka tun daga lokacin ta janye jiki ta koma rufe jikinta a cikin hijabi yayin zirga-zirgar ta a gabansa, a falo ne ko a madafi. Duk wannan kwalliyar da ake cancadawa an daina. A wurin sa hakan ba karamin taimako ya zamo a gare shi ba, sabida ganin da yake yawan yi mata da dan kusancin da ya soma ginuwa a tsakaninsu ya soma birkita shi, ya gaya wa Nebrass yana so ya kara dose din magungunansa, kamar fa sun daina aiki a jikinsa kwanakin nan, don ya gaya masa yana kasa barci a yawancin lokuta da tunanin matar sa kuma ba ya son ya rabe ta. He is afraid of his new mood and the consequences.
Sun zauna sun yi magana heart-to-heart shi da likitocinsa, sun tabbatar masa zai iya rayuwar aure fa ya daina zancen a kara dose, amma ba lallai matar ta samu yadda ta ke so daga gare shi ba muddin yana cigaba da shan anti-androgens kamar yadda ya saba, bi ma’ana, ba lallai ya gamsar da ita a shimfida ba sabida karfin magungunan da suke bashi. Wadanda aikinsu shine kashe tasirin sex hormones a cikin jikinsa. Idan kuma aka dauke shansu shi ma matsala ne babba ga lafiyarsa, career dinsa da zaman lafiyarsa, don al’amarin zai zamo out of control. He will need nothing but sex. Mu’azzam ya gaya musu ya zabi ya zauna da ‘yar uwarsa a haka, cikin zabin da suka bayar duka babu mai sauki, babu wanda za’a ce gara shi. Tun dai ita ba ta nuna kosawa da zaman nasu a haka ba. Kuma da ma ba soyayya ce tsakaninsu ba.
Yana da tabbacin ta san lalurarsa, duk da ba su taba yin zance makamancin wannan da ita ba. Amma ai ta zauna da ABOULKHAIR.
Shi ya lura ma yanzu hankalinta ba ya kansa. Yana ga karance -karancen ta da rubuce-rubucen ta kamar mai rubutun thesis. A ganinsa zata fi kyau da zama malamar makaranta ba mai harhada magunguna ba.
To sai kuma yau da ya ji ta tana kwankwasa kofar sa. Bayan shigarsa dakin da mintuna biyu, ko zama bai kai ga yi ba, don haka daga inda yake tsaye ya bude kofar. Aalimah rike da zazzafan coffee cikin kofi mai zurfi ta dora akan karamin faranti na tangaran ta mika masa. Karba ya yi ya koma cikin lallausar kujerar dakin kwaya daya tal ya zauna. Itama ta zauna a gefensa dab da shi. A zuciyarsa gode mata yake yi sau ba adadi. Ta yi matukar sanin abin da yake bukata ta fannin ci da sha. Ta kuma san abin da ya kamata ta bai wa mutum ya ci ko ya sha a yanayi da lokacin da ya dace.
Ko da ya zauna coffee din ya hau sipping duk da zafinsa ba tare da ya cire takalman kafafunsa ba.
A yadda Aalimah ta sa a ranta daga yau ne za ta canza akalar rayuwar ta da Mu’azzam tunda ta gama research dinta. Ta gaji da wannan rayuwar da suke yi mara focus. Hijabi ne a jikinta dogo daga sama har kasa. Hannu tasa ta cire shi gabadaya ta ajiye a hannun kujerar da suke zaune. Saukowa ta yi ta gurfana a gabansa, ta debi kafafunsa ta hau cire masa takalman, ta gama ta hau zare masa safa (socks) ta debe su ta kai shoe rack, wato ma’adanar takalmansa. Ta jefa safar cikin kwandon kayan wanki.
Har ransa ya ji dadin wannan taimako data yi masa amma ko akan fuskarsa bazaka gane ba. Ba ta tsaya a nan ba, toilet dinsa ta wuce kai tsaye ta hada masa ruwan wanka mai dumi daidai da yanayin da garin ke ciki. Ta zuba turaren wankansa na desire dunhill ta aje masa towell a kusa, sannan ta fito.
A inda ta barshi ta same shi ko motsi bai yi ba yana mamakin ta da karfin halinta. Tunda yake a rayuwarshi ba wanda ya taba shigar mishi toilet including Aboulkhair. Tana fitowa tsugunnawa ta yi a gabansa hannunta akan kafafunsa cikin sanyin murya da kaskantar da kai ta ce,
“Yaya Mu’azzam na hada maka ruwan wankaâ€.
Cikin idanunta ya dube ta yana dan zaro ido na mamakin wannan canji da yake ta gani yau a tare da ita, bai ga komai ba cikin idanun ta sai tsantsar kulawa gare shi. Ko da ya mike don rage kayan jikin sa sai ta fita. Duk karfin halin ta da kankanbar ta ta kasa tsayawa. Murmushi yayi shi kadai sannan ya sunce ya shiga. Kafin ya fito daga wankan ya yi sallah, ta hada lafiyayyen lunch ta kawo masa.
Ta sanshi da son lemon Sangria Mocktail, ta san shi ne abin da ya tare ta da shi a zuwanta na farko gidansa tare da Aboulkhair. Bazata taba maanar ba. Ranar da ta fara ganin c a rayuwarta. Don haka tun safe ta duba procedure din yadda ake yi a yanar gizo, ta zage ta hada masa shi da kyau da ban sha’awa.
Sanda ya fito tawul ne mai fadi daure a jikinsa iya kugunsa, da wani a hannun sa yana goge jiki da shi, sosai ta sadda kai kasa kamar tace kasar ta tsage ta shige, ba ta iya ta dago ba ko yin wani kwakkwaran motsi har ya hangota ta mudubi ya ga halin takurar data ke ciki, da sauri ya lalubo kayan da zai sa ya saka. T. Shirt ce ruwan goro (Tommy Hilfiger) da shudin wandon chinose. Yana satar kallonta ta karshen idanunsa ita ma tana satar kallonshi. Bata da niyyar barin dakin, tayi zamanta a gefen gadonsa sai kace dakin ta. Yau yarinyar nan tana son shigar masa hanci da yawa, har kaya yasa a gabanta amma bata fita ba. Wanda bai ga dalili ba.
“I want to be alone, pleaseâ€. Ya fada yana mai zama a gefen gadonsa.
Ko ta ji haushin kalamansa to ta shanye ba ta nuna ba, ta ce, “Abincinka zai yi sanyiâ€.
Bai yi musu ba wannan karon, don sosai yake jin yunwa, ya sauka kan karamin rug-carpet, dake gaban gadonsa, ya janyo tray din da ta aje ya soma cin abincin. Da ya kammala ya cika tambulan da lemon Sangria Mocktail yana dubanta da mamaki. Exactly wanda yake hadawa da kansa, ta kashe shi da murmushi, kafin ta ce “nayi kokari ko Yaya Mu’azzam?â€
Shi kuma ya amsa da sauri, “Yes, and I appreciate, you really tried!â€.
Murmushi ta yi, tana kallonsa yana shan lemon, komai da yake yi gently yana matukar burgeta.
7/9/21, 7:20 PM – Buhainat: Aboulkhair ya ce……… “He cannot develop emotion…â€. Ita kuma so ta ke ta koya masa jin emotion ko ta halin kaka. Ya ji ta a ransa ko da bazai mata so irin na soyayya ba. Ba don tana jin soyayyarsa mai yawa a ranta ba, sai don tana so ta canza musu tsarin rayuwa, tayi enhancing yanayin rayuwar sa gabadaya. Ta kawo sauyi a cikin rayuwar sa ko yaya ne.
Yana gama cin abincin ta kwashe komai ta kai kitchen ta dawo, samunsa ta yi ya bude system dinsa ya kwanta rigingine tsakiyar gadonsa da system din a kan ruwan cikinsa. Cikin kokawa da abin da zuciyarta ke umartarta ta saci kallonsa. Ba abin da zai bukata a yanzu sai mutstsikar kafa da jan yatsu don warware gajiya. Wani bangare na zuciyarta na hana ta, wani na angiza ta. Idan ta biyewa Mu’azzam zasu shekara goma cikin mugun zaman da suke yi. Ita kuma ta gaji, don ita ke cutuwa, tana so ta kawo karshen komai. Idan bazai yi zaman aure da ita irin na sauran mutane ba, gara ya maida ita gaban iyayenta.
Daga lokacin da ta taso zuwa sanda ta zauna daga saitin kafafun sa Mu’azzam bai ankara ba. Sai kamshin jikinta da ya riga ya haddace mai birkita masa lissafi daya bakunci kofofin hancinsa na turaren NUDE by Rihanna.
Tafin kafarsa ya gani cikin hannayenta akan cinyoyinta tana tausarsu tana mutstsikarsu a hankali daya bayan daya cikin nutsuwa kamar wadda ta yi mastering a Physiotheraphy bayan ta zauna a gefen kafafun nasa.
Yana so ya hana ta, yana so ya dakatar da ita, amma pleasure din da yake samu daga hakan unabandonable ne. Kuma bai taba tsintar kansa a kwatankwacinsa ba. Aikin da yake yi mai muhimmanci ne amma sai ya kasa gane me yake yi. Aalimah ta ci gaba da yin abin da ta ke yin ba tare da tunanin komai a ranta ba, sai kawai ta ji muryar Mu’azzam ta soma canzawa har bata fahimtar abinda yake fadi sosai, a lokacin da yake rokonta da ta bari. “….Stop it Aalimah….. please stop it……!â€. Ya taso ya zauna ya jefar da system din gefe, kama hannuwanta biyu yayi ya rirrike jikinsa yana wani irin kyarma. In ita ta shirya wa hakan a tsakaninsu shi bai shirya ba, har gobe a matar ABOULKHAIR yake kallonta.
Ta ce, “Yaya Mu’azzam, nifa tausa kawai nake maka don na ga ka gaji ba da wata manufa ba, sai ka barni ni kadai a daki alhalin bani da abin yi. Akalla mu dinga hira ni da kai, mu abokanci juna ko ya ya ne, mu dinga jin damuwar junanmu, mu debe wa juna kewar iyaye da ‘yan uwa tunda ba mu da kowa a nan sai junanmu.
In kai kana da aiki a system din da za ta taya ka hira, ni ba ni da shi. I just want us to be friends, abin da ka ke tunanin ina bukata ba shi ba ne Yaya Mu’azzam, na dade da cire wannan section din daga gangar jikina tun ranar da na rasa Aboulkhair, ban kara tunawa ni mace ba ce, balle in yi tunanin neman wani abu daga garekaâ€.