AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Wai kuma sai ya ji kamar kalamanta sun masa tsauri da yawa. Kamar ta dan zuba masa ruwan zafi….. Ta zo gabansa tana fadin tun ranar data rasa mijin ta kaza-kaza…….tsaki ya ja mai sauti. Da kyar ya fizgo sauti daga makogaronsa. Ya ce.
“Did I ask you how you are feeling when lost your husband?†Ta wani murguda baki ta juyo masa keya, yana hango lallusar gashin baki sidik data kalmashe a cikin bind. “Toh, Na ga ka yi min wata fassara ne daga yi maka tausaâ€. Murmushi yayi cikin takaici. “Friendship ki ke so?†Ya sake tambayar ta. Bayan ya kauda idonsa da sauri.
Ta ce, “Ehâ€.
Ya ce, “To na amince miki ki shiga makwabta ki cigita ki nemi sa’anninki watakila za ki dace da samun abokinâ€.
Rausayar da kai ta yi abin tausayi.
“Yaya Mu’azzam ka manta a inda muke ne? Ai ba ruwan kowa da kowa, ta yaya zan shiga gidan mutanen da basu sanni ba ban sansu ba, ba addini da yaren mu daya ba?â€.
A dan harzuke ya ce, “Na ji, zan miki komai ki ke so, but don’t touch me like this again, pleaseâ€.
Ta ce, “ba wani abu ne mai yawa nake so ba, hira nake so mu dinga yi tare, zuwa yawon cikin gari ni da kai da daddare, beaches, shopping malls da kasuwanni duk mu dinga zuwa tare a duk lokacin da zanyi cefane ko sayayya, ka kuma daina bani sako ta hannun Harrison ba na so, ka bani da kanka ba muharramina bane, duk wani sako tsakanina da shi daga yau ka yanke shi, zan kuma din ga shigowa dakin nan duk sanda na ga dama..…Na daina tsayawa a bakin kofa ina neman izni kamar wata almajira…..â€.
Da sauri ya katseta,
“….Ban yarda da wannan ba. Ki shigo min daki duk sanda kika ga dama in kuma ba a shirye nake ba fa. You are just creating a problem, ….you and your problems…â€.
Dariya ya bata sosai, da ganin fuskarsa ka san ta hada masa zafi. Ta hadiye dariyar ta ta ce “ba su kenan ba ai issues din nawa, sai kuma hada maka ruwan wanka kullum da aje maka towel, sai kuma zabo maka kayan da zaka dinga sanyawa, I also want be choosing neck ties for you. Tied it by your neck…. That’s all I want from youâ€.
Ajiyar zuciya ya yi, ya kura mata ido kamar ya maketa, me yarinyar nan ta ke so ta zama ne? Ya tambayi kansa.
“Close to your lifeâ€.
Abin da ta ke nufi kadai kenan, zuciyarshi ta bashi amsa, shi kuma wannan wani gurbi ne da ba zai iya bai wa kowa ba. Intimacy din zai yi yawa. Aalimar da ya sani da kunya da kawaici a lokacin Aboulkhair, wadda ko ido bata iya hadawa da shi, yau rana daya ta zo masa da wasu bakin halaye tamkar mai multi personality disorder! Ba ya tantama zama da matar Daddy ne ya maida ita haka. Tunda bata da kawar data fi ta.
“Ki yiwa Allah ki kyaleni Aalimah, kin ga inada ayyuka da yawa, in dai system ce zan saya maki gobe ki dinga yin karatu da ita insha Allahuâ€.
Turo baki tayi kamar kankanuwar yarinya “Yaya Mu’azzam ni ban ce ka saya min computer ba, inada ipad. I mean nothing, I only need a friend in you. Tunda an rabo ni da kowa nawa an kawo ni nan, inda ba ni da kowa sai kaiâ€.
Ta soma jan hanci alamun kuka zata soma daga kowanne lokaci daga yanzu.
Mu’azzam ya shafo sumar kansa cikin damuwa, da sauri ya ce, “to shikenan na yarda, amma kar ki sake taba ni, don Allahâ€.
Aalimah ta sake cuno baki, ta mike tana kunkuni har da bubbuga kafa a kasa.
“Ai Allah bai ce kada in taba ka ba!â€.
Abin ya ba shi dariya a karo na farko, amma ya gintse.
“To kuwa kada ki sake shigo min daki in ba ni na neme ki ba. Abincin a bar min a dining in na bukata zan zo da kaina in ciâ€.
Juyowa tayi cikin far’a mai yawa tace masa.
“Nan fa daya! Mun riga mun wuce wurin nan, ka riga ka amsa. I will be in my husband’s bedroom whenever I wish. Magana biyu ba taka bace Yaya Mu’azzamâ€.
Girgiza kai yayi ya bita da ido a sanda ta kama hanyar ficewa.
Har ta kai bakin kofa ta juyo ta marairaice. “To don Allah in zo ka kai ni shopping? Wallahi ko man shafawa ba ni da shi, ni ko kayan lefe babu wanda ya yi min just because an fi son ka a kainaâ€.
Bai san sanda ya ce “Je ki ki shirya†ba.
Har da dan tsallenta ta fice kamar wata kankanuwar yarinya.
Mu’azzam ya dafe kansa dake sarawa saboda rigimar Aalimah, ya dade bai yi magana mai tsayi irin wannan ba, ta sa shi magana mai yawa. Ita a dole sai ta koyar da shi sakin jiki da ita. Bayan da farko ta nuna masa ba ta da hayaniya, ashe shigo-shigo ba zurfi ta yi masa? Murmushi ya yi tare da lumshe idanunsa. Ashe hayaniyar ga wanda ya iya ta nishadi take sanyawa? Kwarai ya samu kansa cikin nishadi wanda rabonsa da irinsa har ya manta. Ya koma ya jingina da jikin gadonsa, yana mai hasashen inda karshen wannan tafiya za ta kai su???.
Suna tafe cikin motar Mu’azzam (Acura) fara sol, Mu’azzam ne ke tukin motar. Tunda suka taho kira’ar Sheikh Abdurrahman Sudaith ke tashi a motar cikin (Suratul Ali’Imran). A fili Mu’azzam ke bin karatun wanda ya sanya wa Aalima nutsuwa sosai. Ta nutsu, ta kwantar da kanta a masangalin kujerar da ta ke zaune tana sauraronsa. Ba ta yi mamakin iya karatun Mu’azzam ba, kasancewar Aboulkhair ya gaya mata komai na rayuwarsa har a Madinah.
Shagon da yake nasa shopping din ya kai ta, ya ce ta je ta yi siyayyarta zai jira ta a mota, idan ta gama ta yi masa flashing ya je ya biya su tafi. Ta fahimci abin da yake nufi (ba zai jera da ita ba) to ita kuturwa ce ko ko me yake nufi? Duk da haka ta gode, domin sauyuka ne da ba ta tsammata a nan kusa ba daga gare shi.
Ta shige cikin shagon kai tsaye wajen kayan kwalliya ta dosa. A sannu za ta canza komai da yardar Allah. Ashe dai duk laifinta ne wannan mugun zaman da suka shekara cikin sa. Mu’azzam yana da saukin kai matuka idan kayi hakuri da shi kuma a sannu zaka fahimce shi. Yadda ka bayyana kanka da haka yake biyar da kai. Tana rokon Allah ya ba ta kwarin gwiwar mayar da Mu’azzam ma’abocin walwala da farin ciki kamar sauran mutane koda ba entirely ba.
Mu’azzam bai san me Aalimah ta sayo ba, sai da suka dawo gida, ta ware nata siyayyar a dakinta ta dauki wata katuwar leda ta bi shi da ita. Yana kokarin canza kayan jikinsa zuwa pajamas ta yi sallama tare da tura kofar ta shiga gaba-gadi tana mai kawar da kai daga gare shi ba tare da ta bari yayi mata iznin shiga ba. Tsaki ya yi mai sauti ya juya mata baya, ya ci gaba da zarga igiyar pajamas dinshi. Yarinyar nan tana son shiga rayuwarsa da yawa, abinda ba zai dauka ba. A dan fusace ya juyo yana kallonta, ta ce shopping ya kai ta, an dawo kuma ba za ta barshi ya huta ba? He want to be alone ko ya samu ya sha maganinsa ya kwanta.
“Oh please Aalimah mene ne kuma?â€
Ya tambaya, rabi a fusace, rabi cikin boye fushi.
Zama ta yi gefen gadonsa ta soma fiddo kayan da ke cikin ledar, shampoo ne na maza (Arganavita), shavers da after shaves kala-kala turaren wanka (bath robbs), handkerchiefs, vest, boxers da duk wasu tarkace na maza irin wadanda ta ga yana amfani da su. Ta marairaice tare da karyar da kai, ta ce,
“Da ma sayo maka na yiâ€.
“Na ce ina bukata?â€
Ta yi kasa da murya,
“Don na san kana bukatar neâ€.
Ta tattara su ta yi toilet din shi da su. Bin bayanta ya yi da kallo, ko’ina a jikinta rausaya yake kamar mai yi da gangan. Bai dauke idonsa ba sai da ta kule cikin toilet din. Ya yi ajiyar zuciya ya bar kallonta. Bai san me ta ke so da shi ba kuma, duk abinda take so yayi mata, amma bazata barshi ya huta ba, ta fara takura masa. Ba ya son damu, gara zaman su Mummy sau dubu da wannan Aalimar ta yau, ba sa gigin shigar masa daki. Amma Aalimah… Aalimah… ta fara shigar masa hanci, in ta yi wasa zai bar mata gidan gaba daya.
Cikin kwanaki bakwai da suka biyo baya Aalimah tayi nasara mai yawa akan Mu’azzam, ko baya son magana sai ta bashi dramar da zai yi dariya. Ta like masa ta nace masa kamar kaska. In zai tafi ofis sai ta bata masa lokaci. Har stool din mudubin dakinta ta dauka ta mayar nasa dakin saboda ta taka ta kamo tsahon Mu’azzam ta daura masa necktie, yana baya so ta bari amma sai tayi, bata damuwa da gwasalensa ko kadan, ba dama ya zabi kayan sanyawa sai tace ita basuyi mata ba, dole da wanda ta dauko zai yi amfani, undies dinsa ita ke wankewa kal duk bayan kwana uku wadanda duk farare ne.
In tana son sa shi dariya to tace a baki zata bashi abinci. Rannan data dage sai ta bashi ta ciko fork da dankalin turawa ta nufo bakinsa, abin yayi amusing dinsa sosai yace “Aalimah mai yasa bakya ji ne wai? Ni kuma gotai-gotai dani zan tsaya ki bani abinci a baki? Ki jira ki haifi dan ki tukunna sai ki yi ta bashiâ€. Sai ta rangwadar da kai tana masa wani irin kallo da ita kanta bata san tayi ba tace.
“Allah zai bani ne!â€.