AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Mu’azzam sai ya samu kansa da amsa fatan Aalimah a cikin ransa na Allah ya bata Da. Sai dai method din samun dan har gobe bai san ta ina zai zo ba. Amma kwarai shima yake fata da addu’ar ganin dan kansa a duniya. Bai san irin soyayyar da wannan dan zai gani daga gare shi ba.

Abin da ta sa a gaba yanzu shi ne, neman Dr. Nebrass, kwarai ta ke son ganawa da shi. Amma ta rasa hanyar kai wa gare shi. Itama ta san wasa ta ke ta taba wayar Mu’azzam, yadda yake kaffa-kaffa da abarsa kamar munafukin miji mai mata hudu. Dabara ta zo mata, tunda dai ba ya shiga bayan gida da waya.
A wani marece ta yi sallama ta shiga dakin, asabar ce ba ya zuwa aiki, kuma gab ake da shiga lokacin sallar azahar.
Ko kallonta bai yi ba, yana bisa keken motsa jiki da ke can gefe a dakin. Waje ta samu ta zauna, in ta ce ba ta jin ciwon shakulatin bangaron da Mu’azzam ke yi da ita a wasu lokutan ta yi karya, sabida ba haka mijinta mai sonta ya sabar mata ba. Sai dai ta sa a ranta zamanta da Mu’azzam zaman jihadi ta ke yi. Zaman son maida shi mutum kamar kowa, mai cikakkiyar rayuwa kamar kowanne dan Adam. Albarkacin mahaifinsa da nata, wadanda ba su rage ta da komai ba a rayuwa. Kuma alhamdulillah ta san cikin kashi arba’in cikin dari (40%) tayi nasarar sauyawa Mu’azzam halayensa da dama.

Tunda an ce babu magani na farat daya a kan lalurorinsa, a ganinta dabarunta za su yi aiki wajen ba shi ingantacciyar rayuwa. Sannan fisabilillahi ta fara shiga halin ha’u’la’i mai tsanani da gangar jikinta, wanda har ya soma shafar lafiyar barcinta da sukuninta, bukata irin ta kowanne dan Adam mai lafiya a cikin gangar jikinsa, musamman wanda ya san cewa yana da aure. Kuma ga mijin yana tare da shi ko yaushe.
Dadin dadawa yawan shigewa Mu’azzam da ta ke yi duk da ya nuna ba ya so a yanzu yana tasiri sosai a zuciya da gangagar jikinta. Ita kuma a wannan dan tsukin ta zama infatuated akansa. In fact, bata taba jin son kusantar wani da namiji a duniya irin yadda take ji akan Mu’azzam ba. Amma shi ko a jikinsa.
Barin keken motsa jikin ya yi ba tare da ya ce da ita ci kanki ba don ya san wata matsalar ta zo masa da ita, wadda yau hutawa yake son yi, bashi da lokacin sauraronta, “you…. and your problems†(kamar yadda yake kiranta), ya shige toilet don dauro alwala. Aalimah ta yi wuf! Ta dauki wayarsa, ta lalubo lambar Nebrass ta shigar cikin tata, ta ajiye masa.
Fitowa ya yi daure da alwala, a lokacin da ita ta ke shirin barin dakin. Ciki-ciki ya ce da ita, “Ki zo mu yi jam’iâ€.
Ba tare da ta juyo ba ta ce da shi,
“bani da tsarkiâ€.
Ta fice ta ja masa kofar.
7/9/21, 7:20 PM – Buhainat: RAAZEE’S

Bayan ya idar, ya zauna bisa darduma yana tunani. A tun sanin da ya yi wa Aalimah bayan aurenta da Aboulkhair yarinya ce mai kunya da kawaici, ko kwayar idanun shi ba ta iya kallo, wani irin respect ta ke ba shi irin wanda ta ga Aboulkhair na ba shi. Haka farkon zuwanta gidansa wannan halin bai canza ba ko kadan. Me ya sa ta sauya halin ta rana daya? Ta ke so shi ma sai ya sauya ko ta wanne hali? Haushinta da yake ji yau na wadannan sababbin halayen ne da ta aro ta yafa rana daya, ta cika masa gida da su. Wanda ke nufin tana da mission a kansa da ta ke son cikawa, amma ba halinta bane. Aalimah ba son shi ta ke yi ba in ya yi la’akari da tsayin lokacin nan ba ta taba neman shi da ya ba ta hakkinta na aure ba. Wata zuciyar ta yi saurin kare ta da cewa “ita za ta nema ko kai?
A al’adarta ta iyaye da kakanni, miji ke kai kansa ga matarsa ba matar ke kai kanta ga mijin ba. Ko babu soyayya mata basa jurewa wannan. Kuma ta san kana da lalura, tsoron hakan ma na iya cire mata sha’awar komaiâ€.
Yana wannan tunanin ya ji motsinta tana shigowa. Daga kai ya yi ya dube ta a hankali, doguwar riga ce a jikinta (milk colour) samfurin Oman, yadin kamar na roba, don haka ya fiddo surar jikinta shapely, ta daure kanta da dankwalin rigar, gashin kanta ya kwanto ta baya. Ya samu kansa da kasa dauke ido a kanta. Wani magnet na jan idanunsa zuwa gareta. Ya kasa dauke ido a kanta.
Ba tare da ta ankara da irin kallon da yake mata ba a yau take ce da shi.

“Nan zan kawo maka lunch, ko in bar shi a dining?â€
Zuba mata idanu ya yi kamar wani maganadisu na fizgar zuciyarsa zuwa gare ta. Kamar wanda aka yi wa wahayi; ji ya yi duk wani nauyinta da shakkarta da yake ji, a yau ya kau daga idanunsa. Hannunsa ya mika ya kamo nata a hankali, tare da ambaton sunanta da sassanyan sauti daga can karshen makogaronsa. Sai jinta ta yi gaba daya a jikin Mu’azzam ba tare da ta shiryawa hakan ba, ya soma wani irin sunsuna ta tun daga wuyanta har cikin jikinta. Turaren da ya dade yana ji daga nesa nesa yana dimautar dashi yau ya samu completely a jikinsa.
Aalimar da ya dade yana kallo daga nesa nesa yana kintata laushin fatar jikinta da sulbin bakinta, yau ya samu kwance a jikinsa.
And the skin is softer than he imagined.
Samun kansa yayi da rungumeta sosai tare da manna ta a kowacce kusurwa ta jikinsa.
Ajiyar zuciya yake saukewa a jejjere kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa. Is that the feeling of being with a woman???
Idan kuwa shine it’s the most pleasurable, and most intoxicating feeling in the history of man ever.
A hankali ya shiga kurdawa ta wuyanta har ya samu ya kai bakinsa zuwa ga nata.
It is a kind of gentle kiss wanda ya hautsinasu cikin dan lokaci bakidayansu.
Jikinta rawa ya soma yi tare da tasowar dadadden al’amarin da ta jima tana kokawa da shi da karfin hali da karfin addu’a. Kamshin jikin Mu’az da wanda ke fita daga bakinsa na mouthwash din da yayi amfani da shi shi ne babban abin da ya ribace ta. A lokacin da ya soma kissing din tsakiyar bakinta sai komai ya kwace mata. Ta manta cewa, wannan Mu’azzam ne ba Aboulkhair ba. Yanayin yadda yake sumbatar tata ba ta taba jin irinsa a duniya ba. Ya zamanto cewa ta gama mika wuya ga duniyar Mu’azzam…
Yayin da tafiya ta yi tafiya sai Mu’azzam ya rasa kuzarinsa bakidaya. Duk kokarinsa ya kasa komai bayan kissing din, cikin sanyin jiki ya koma gefen gadon ya zauna yana mai dafe kansa… Ita kuma Aalimah barin dakin ta yi tana mai jin har abada ba za ta sake iya hada ido da Mu’azzam ba.
Kwana uku suna buyar wa juna, sai dai ya samu abincinsa a ‘dining’, ta daina shiga dakinsa, duk wannan karambanin ta daina, ta zama calm, cool kamar farkon zuwanta, ta san ba karamin tsallake rijiya da baya ta yi ba, kunyarta ya ke ji, yana ganin ya zama raggon namiji, wanda bai iya biyawa matarsa bukata, tana ganin ta zama mara aji da tayi saurin bada kanta ga Mu’az haka. Gashi babu biyan bukata, ta san ba komai bane tasirin magungunansa ne. Ita dama bata da tsarki so bata cikin irin damuwar da Mu’azzam ke ciki. Ta kasa zaune ta kasa tsaye a daren yau da sabon al’amarin dake sakadar zuciyarta a hankali a hankali a kwanakin nan, yana rarake ruhinta kusufa-kusufa tun ranar da wannan dan physical relationship din ya shiga tsakaninsu, ba komai bane sai yawan tunanin MU’AZZAM da son ganin shi. Da kasancewa cikin wani irin shauki a duk lokacin da ta ji muryarsa yana magana a waya koda Harrison ko motsin sa zai shiga daki. Ba abinda take son ji sai muryarsa, ba abinda take son gani sai fuskar sa, ba abinda take so sai kasancewa tare da shi muddin rayuwar ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button