AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Tayi kwalliya cikin atamfa Ghana wax koriya shar, daidai lokacin da ta fuskanci yana fitowa cin abinci sai ta fito ‘dining’ ta zauna, ta gaji da buyan tana so ta ganshi ko daga nesa ne in ba haka ba bata jin zata kai daren yau a raye, ta zuba abincin amma ta kasa ci sai juyi take da cokali a cikin tangaran. Dai-dai nan Mu’azzam ya fito daga dakinsa yana waya. Kallo daya tayi mashi ta ambaci “Ya Allah†cikin zuciyarta, sannan kuma tayi gaggawar kawar da kanta kada kwarjini da haibarsa su yi mata lahani a idanunta.
Ya shirya cikin ‘American suit’ bakake wuluk kamar kullum, neck-tie din wuyansa na yau red ne, amma sai ta ga kamar yau yafi kowacce rana yin kyau. Kamar yau ya fara sanya suit a jikinsa. Kamar yau ta fara ganinsa. Yayi fes! Yayi fresh! Kuruciyarsa ta fito sarari. Har ya zo kusa da ita ya ja kujera ya zauna bata sauke ido a kan shi ba.
Yayin da shi kuma ya ja ‘food warmer’ gabansa ya bude, ya dauki plate zai zuba sai ta mike ta karbe shi ta zuba masa daidai yadda ta san yana bukata, ta koma ta zauna tayi shiru tana satar kallon shi daga karshen idanunta tana cigaba da juya cokali a cikin abinci. Zuciyarta tayi haske, ko ba komai a ce Mu’azzam mijinta ne kadai ta gama morewa. Tunanin matsalar da ke kwance cikin auren nasu ta sanya jikinta yin matukar sanyi.
Mu’azzam yana cin abincin nashi amma hankalinshi na kanta. Ta koma ‘cool Aalimah’ din ta. Dama an ce ‘kayan aro baya rufe katara’. Murmushi yayi ya girgiza kai ya cigaba da cin abincinsa.
Da ace tuntuni ya san common hug da kiss zai ladabtar masa da ita ai da bai zauna tana bashi wahalar data bashi a baya ba. Da tuni an dade da wuce wurin. Ta dube shi da alamar tambayar ko me ya sanya shi yin murmushi? Ture plate din gaban shi ya yi, ya sunkuya a gabanta dai-dai fuskarta kasa-kasa ya ce da ita,
“Da za ki zauna a haka yadda ki ke, ai da na ji dadiâ€.
Murmushi ta yi, don sarai ta gane abin da yake nufi. Ya sarke hannayensa biyu, ya kuma dora habarshi a kansu ya yi magana cikin sanyin murya.
“Aalimah, why do you want to change me (Aalimah, me ya sa ki ke son ki canza ni?)â€.
Da sauri ta cira kai ta dube shi, amma ta kasa magana, ashe ya ramfo ta tuntuni ita kadai ta ke shirmen ta?
Ya ce, “Answer me Aalimah, why? Me ya sa ba za ki barni a yadda ki ka same ni ba?â€
Hawaye suka ciko idanunta, ba jimawa suka garzayo kan kuncinta, hanky dinsa ya ciro daga aljihunsa ya mika mata. Da sauri ta karba ta share, sannan ta furta masa abin da ke cinta a zuci.
“Because I want another Aboulkhair in youâ€.
Da sauri ya girgiza mata kai cikin gamsuwa da amsar da ta ba shi.
“Aalimah!â€.
Ya kira sunanta cikin sanyin murya,
“Kama da wane ba ta wane! The fact that we belong to the same parents ba zai taba zama cewa za mu zama daya ni da shi a komai ba. Ki yi hakuri ki karbe ni a yadda nake, ni ma na fi son ki a yadda ki ke. Mai kunya mai kawaici mara hayaniya. Na kuma yi miki alkawarin zanyi miki duk abinda kike so gwargwadon ikona, amma ki daina aro personality din da ba naki ba kawai don kina so in canja daga yadda nake, zan kyautata miki iyakar iyawata insha Allahu but please accept me the way I was.
Na san ya fi ni kirki, ya fi ni dadin mu’amala, ya fi ni nuna miki soyayya. Aalima ki sani, ni ba ni da lafiya. Ina mai kokawa ne da kaddarar da ta same ni. Amma tabbas rayuwarmu tare na yarda cutuwa ce a gare ki. Aalimah na yanke shawarar in sauwake miki auren nan ko babu amincewar iyayenmu don ki samu farin ciki irin na kowanne ma’aurata. Iyayenmu su yi hakuri, na yarda ina cutar da ke a cikin gangar jikin ki da zuciyar ki.
Ni ma ba son raina ba ne zamowata a haka, I’m fighting with my destiny. Na san yadda zan bai wa su Daddy hakuri, in kuma nuna musu ba ki da laifi…â€.
Girgiza kai ta ke yi da sauri, hawaye na bin kuncinta. Hankalin ta yayi mugun tashi.
“Na zabi zama da kai Yaya Mu’azzam a cikin kowanne hali a yadda na same ka. Babu saki tsakaninmu har abada. Ina son ganin iyayena da malam cikin farin ciki kamar yadda nake son rayuwa taâ€.
“Ki sanya su farin ciki ki nakasa kuruciyarki Aalimah? I can’t give you sexâ€.
Da dukkan affirmation na zuciyarta ta daga masa kai, mai nufin, eh ta amince, zata zauna da shi haka. Mu’azzam bai san lokacin da ya bude mata dukkan hannuwansa ita kuma ta tafi a hankali ta shige, suka rungume juna suna hawaye da runguma mai tsananin karfi (tight-hug). Rungumar data bude shafin sabuwar rayuwa a gare su.
A haka suka ci gaba da rayuwar, sai dai su yi dan romancing a tsakaninsu. Wanda ke matukar wahalar da Aalimah a karshe. Ta rasa inda za ta sanya kanta a matsayinta na mace mai cikakkiyar lafiya. Rannan ta ce, bari ta kwaso magungunan Aunty Gumsu, watakila za su taimaka wa Mu’azzam ya ba ta farin cikin da gangar jikinta ke bukata.
Amma a karshe, matukar azaba suka sanya ta, wanda sai da Mu’azzam ya tausaya mata, ya kuma soma tunanin dole ne ya yi wani abu don inganta rayuwar aurensa.
A washegari ta ce da Mu’azzam za ta fita shopping ya ce ta bari ya dawo office sai ya kai ta, ta ce, a’ah ya sa Harrison ya kai ta da wuri ta ke bukatar shopping din. A yadda yake tattalinta ba ya son duk abin da zai bata mata rai, dole ya amince da tsarinta.
Ba ta ce da Harrison ya kai ta ko ina ba, sai asibitin Mu’azzam, tana son ganin Dr. Nebrass.
Da karramawa tsohon baturen ya karbe ta, a lokacin da ta gaya masa ita ce maidakin Engnr. Mu’azzam Raazee.
Ya ba ta wajen zama, ya kuma ba ta abin sha, amma ba ta sha ba, ya kuma ba ta dukkan hankalinsa don ya fahimci muhimmiyar magana ce ta kawota.
“Doctor I want my husband to live without the help of Anti-Androgensâ€.
Ta kifa kai a kan teburinsa ta saka masa kuka mai cin rai, wanda dole duk wanda ya ji ya fahimci tana cikin tsananin damuwa, ya tausaya mata a kan hakan, don ya san da ma hakan za ta faru.
Ba ta fito ta yi masa bayani baro-baro ba, saboda kunya ta diyan musulmi, amma ya gane dalilinta na zabar Mu’azzam ya zauna da lalurarsa yadda Allah ya bar masa ita, ba tare da sun daddaure shi da magungunan kashe tasirin androgens (sex hormones) a cikin jikinsa ba.
“It’s o.k Mrs. Raazee, its ok stop crying. Tunda kin zabi hakan shikenan. Daman maslahar taki ce, amma tunda kina ganin zaki iya jurewa it’s quite okayâ€.
Shi ne amsar da likita Nebrass ya ba ta. Ba haka taso al’amarin ya kasance ba babu yadda zata yi ne. Ta yi hakuri har na tsawon shekara guda da rabi, amma wutar son Mu’azzam da ke ruruwa a zuciyarta sannu a hankali, da kuma yawan physical relationship dake faruwa tsakanin su yanzu, da kwana da suke yi bisa gado guda kalmashe cikin juna, ya sanya ta kasa cigaba zuba masa ido kamar watannin baya.
*******
Dr. Nebrass, ya gaya wa Mu’azzam zai rage karfin anti androgens a jikinsa tunda yanzu yana da aure. Ba tare da ya gaya masa matarsa ta zo ta same shi ba. Mu’azzam ya yarda nan da nan, don shi kanshi al’amarin ya fara damunsa. Ba soyayyar Aalimah ce ta yi masa katutu ba, a’a, tausayinta ne. In don ta shi ne, yana jin dadin rayuwarsa a haka. Amma ya sani Aalimah tana cutuwa matukar cutuwa ba dan kadan ba, kawaicinta da alkunyar ta ke sa tana danne komai bata nuna masa gazawarta, tunda ya ba ta option na zama da shi ko a’ah, kuma ta zabi cigaba da zaman anyhow.