AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Da gari ya yi haske bayan sun yi wanka sun shirya tare suka tafi gidan Daddy don yin sallama dashi da Mummy, bai fada musu tun jiya ba cewa yau zai koma kada su dakatar da shi, ba ya jin akwai abinda zai yarda ya hana shi tafiyar nan tareda ‘ya’yan sa a yau ba sai gobe ba, don ita ce kadai kwanciyar hankalinsa, kamar yadda Aalimah tace rabuwa dashi shine kwanciyar hankalin ta. Zai nesanta kansa da ita, nesantawa da babu ranar waiwaye don ta samu kwanciyar hankalin da ta ke hangowa.
Ya saya kwayan idanunsa cikin bakin PRADA mai duhu ainun. Shadda ce fara kal (getzner) a jikin sa dinkin tazarce. Kasancewar ba kasafai yake irin wannan dressing din ba sai ya fito kala daban a yau. Hakika kalar mamansa ‘yar asalin kasar Nigeria yau ta nuna sosai a jikin sa. Ko turare bai iya ya fesa ba sabida yadda yake sauri ya bar kasar Niger, amma kamshin sa ya riga ya kama komai nasa.
Sanda suka shigo Daddy da matan sa guda biyu da Yesmin tare da yaran Gumsu hudu Nurat da kannenta su Ikhram suna karin kumallo. Daddy ya bisu da kallo suna shigowa, wani farin cikin sake ganin su a tare ya tsirga masa. Yayi godiya ga mahaliccinsa mai yawan hikima da kyautayi ga bayin Sa. Murmushi yayi yana ja musu kujera akan dining din. Har kasa suka tsugunna suka gaida iyayensu sannan suka zauna a kujerar da Daddy yayi musu tayi aka cigaba da karin kumallon tare da su. Gumsu ta daina surutu, ta yarda yanzu babu muhallin yinsa. Sosai ta kame bakinta.
Suna gamawa Mu’azzam yake gaya musu sallama yazo musu zai wuce yanzu sabida ofis, kuma tare da su Basma zai tafi. Mummy ta zaro ido tace “ka bar min su mana Mu’azzam yaya zaka yi da kananan yara har biyu?†Babu kunya Mu’azzam yace ai babu matsala zai iya kula dasu. Tare zasu dinga fita ya saukesu makaranta ya wuce ofis, sanda yake tasowa suke tashi suma, kuma zai daukar musu dattijuwa mai raino musulma.
Mummy zata sake magana Daddy ya tare ta yace “Allah ya tsare, ya kiyaye ku, yayi muku albarkaâ€. Ya mikawa Aboulkhair mukullin motarsa yace ya kai su filin jirgi. Ya kara da duban Aboulkhair sosai wani abu ya fado masa, da sauri yace “drive with care. Fasten your belt. Da bismillah da ayatul kursiyyu kafa bakwai kafin tukin motaâ€. Aboulkhair ya amsa, tare da cewa “insha Allahuâ€.
Gumsu dakinta ta shige hawaye na zubo mata na tausayin Mu’azzam. Haushin Aalimah ya cika ta, har cewa tayi a ranta ba ita ba Aalimah insha Allahu. Tunda bata da tausayi ko kankani, kanta kawai ta sani da maslahar kanta. In bata tausayawa Mu’azzam ba, ai ta ji tausayin kananan yaranta.
Gidan Malam Razee suka koma, shine yaso batawa Mu’azzam lokaci don cewa yayi sam bai yarda ya tafi ba, ya zauna har Aalimah ta huce a maida aurensu su koma tare. Abinda Mu’azzam bai taba yi masa ba yau yayi masa wato gardama. Nan ya gane da gaske yake tafiyar yake so kuma ya yi fushi da Aalimah fushi mai tsanani. Aboulkhair shi ya ciwo kan Kakan nasu da kyar ya hakura ya yarjewa Mu’azzam tafiyar. Don ya gaya masa (a matsayin sa na likita) Mu’azzam is okay. He can handle himself.

Aalimah bata jima da tashi daga barci ba suna karyawa da yaranta a falon Inna Bintou ta tsinkayi sallamar Mu’azzam a tsakar kanta. Sallamar data ratsa har cikin kashi da bargon ta. Wuta ta dauke mata na lokaci mai tsawo domin sosai muryar ta ratsa cikin kunnuwa da jijiyoyinta. Su Basma suka dangwarar mata da kofin shayin ta har ya bare a jikinta, basu bi ta kanta ba suka kwasa da gudu sai wurin mahaifinsu. Rage tsaho yayi ya bude musu hannuwa suka shige ciki yana sumbatarsu daya bayan daya, ba tare da bata lokaci ba yace.
“Oya! Kowa ya dauko jakar kayansa tafiya zamuyiâ€.
Nan da nan suka hau tsalle suka runtuma daki da gudu sai ga kowanne rike da takalminsa a hannu, janye da trolley din kayansa. Basma tace “Mummy ki tashi ki dauko kayan ki†Mu’azzam yace “No Bassy, Mummy will stay at home, tana da abun yiâ€. Ya hau saka musu takalmansu. Tana zaune kamar an dasa ta tana kallon ikon Allah. Zuciyar ta na wani irin raurawa. Ya iso har gabanta ya ajiye mata passport dinta bisa cinyar ta. Ya kama hannun ‘ya’yansa yaja jakunkunan suka fice. Inna Bintou nata yi musu addu’a yana amsawa suka fice daga dakin.
Aalimah ta rasa abun da zata yi a wannan lokacin, kawai sai ta dora hannayenta biyu aka ta rushe da wani irin kakkarfan kuka, ta yaya zai zo har gabanta ya kwashe mata ‘ya’ya? Zuwa wata uwa duniyar da babu mai kula dasu???
Inna Bintou yi tayi kamar bata san da ita a dakin ba ta dau mayafi ta yafa ta fice don yiwa ‘yan biyu rakiya bakin mota.

Aalimah ta san ba mai kula ta ko kukan jini zata yi, haka ta tattara ta shige uwar daka, duniyar bakidaya tayi mata zafi. Ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji sanyi. ‘ya’yanta sanyin idaniyarta, ‘yan biyun ta abin farin cikin ta, wadanda bata iya barci batare da ta jisu cikin jikinta ba.
Haka ta ci kukan ta ta koshi, wanda ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani, ko sannu bata samu daga jama’ar gidan ba. Nasu mai sauki ne akan na Inna Kasisi, wadda ko gaisuwarta bata amsawa yanzu.
7/12/21, 4:49 PM – Buhainat: Inna Bintou ta zubowa jikanyar ta Hafsu shinkafa da miya ta shi go dakin da shi, Hafsu kai tsaye ta nufi Aalimah da abincin nan tana fadin ta sakko su ci. Warin miyar wadda taji tafarnuwa ya bigi hancin Aalimah. Wani bala’i ya ziyarceta kafin ta yunkura ta zauna ta kwararo wani uban amai wanda ya wanke Hafsu da shinkafar ta, ta cigaba da sheko shi kamar zata amayar da kayan cikin ta.
Da gudu Hafsu ta fita ta kira Inna Bintou. Wai Aunty Aalimah tana amai. Bintou da Kasisi dake madafi suka yi kasake! Suna kallon yarinyar tana digar amai kafin su juya su kalli juna. “Amai dai?†suka hada baki wurin tambayar ta. Daga bisani Bintou ta yunkura tabi bayan yarinyar zuwa dakin nata.
Ita ta taimaka mata ta wanke jikin ta, ta kuma gyara wajen ta kunna fanka da turaren wuta. Tun daga ranar Aalimah ta kwanta jinya, komai taci sai ya dawo, ta kuma ki yarda a kaita asibiti, kuka ma ta sakawa Inna Bintou ita Kano zata koma. Inna taje ta fadawa Malam halin da Aalimah ke ciki da Kano da take son komawa. Ta kuma ce tana zargin Aalimah karamin ciki gareta.
Malam yace zai turo Aboulkhair ya dubata, zai kuma sa shi ya saya mata tikitin tafiya Kanon.
Bayan fitar Bintou Malam Raazèe ya fada a tunani, wato hikimomin Ubangiji yawa gare su. Zuri’a tsakanin Aalimah da Mu’azzam ashe bata kare ba. Duk yadda Ubangiji ya shirya al’amarinsa dole bawa ya karba yayi imani. Idan Allah ya rubuta akwai sauran zama a tsakaninsu Aalimah bata da tsimi bata da dabara. Ga auren da kakar sa ke nema masa. Wanda shi sam hankalinsa bai kwanta da shi ba, don yana tsoron abinda ka je yazo, tunda Mu’azzam ba wai warkewa yayi daga lalurorinsa ba, su kadai suka san yadda suke zaune da junansu.
Aboulkhair Malam ya kira a waya yace yazo ya duba masa Aalimah bata da lafiya, ya sayo abinda yasan mara lafiya zai iya ci ya kawo mata kumallo take yi kullum. Abinci baya zama a cikin ta.
Shi da Yesmin suka zo gidan, Yesmin niki-niki da ledojin sayayyar da suka yo mata a supermarket. Dakin Inna Kasisi suka fara shiga suka gaisa, yace.
“Inna Aalimah muka zo dibawaâ€.
A take far’ar fuskarta ta canza tace.
“Kun bani ajiyarta ne?â€
Ko kadan Aboulkhair bai ji dadin abinda ya fahimta daga Kakar su akan Aalimah ba, ya san kuma abinda ya janyo hakan, zama yayi ya soma yiwa Inna nasiha yana gaya mata Aalimah bata isa ta tsarawa kanta rayuwa ba face abinda Ubangijin ta ya tsara mata, idan Allah yace iyakar zamanta da Mu’azzam kenan fushinta da ita bazai canza komai ba, da ita da Mu’azzam duka jikokinta ne, nunawa daya soyayya akan daya ko bin bayan daya ba nata bane. Yana rokonta ta zamo mai adalci a tsakanin su.
Inna Kasisi bata ce komai ba amma jikinta yayi sanyi ainun. Mamakin juriyar Aboulkhair ya kamata, kamar ba shine wannan da ada ake tunanin bazai iya rayuwa ba sai da Aalimah. Ta san kuma ba komai ya sa shi sadaukar da sayayyar ba sai kaunarsa ga Mu’azzam. Tana mai addu’ar Allah yasa wannan zumuncin nasu ya zame musu silar shiga aljannah.
Ta dubi Yesmin tace “to wadannan uban kayyayakin da kuka kwaso kuma na menene?†Yesmin tace “kayan dubiya ne†tace “to a sammin nawa†Yesmin tayi dariya tace “sai in zaki taso muje dubiyar tare†Inna tace “albarkacin kaza ai kadangare na shan ruwan kasko, muje mu ganta, koda dai ciwon nata ai ba mai warkewa bane sai ranar da ya bushi iskaâ€.
Aboulkhair ya fiddo ‘fresh milk’ mai sanyi daga cikin kayan ya dauki tambulan ya cika shi taf ya mikawa Inna yana murmushin jin abinda ta fada. Duk da bai gane hausar sosai ba. Ta karba tana sha tace “amman wannan madara da gardi take, gara ma ku bar min don bazata zauna a cikin ta baâ€. Saida Inna ta gama shan madara tana santi, Aboulkhair na kara cika mata kofi, duk don ya lallashe ta taje ta duba Aalimah.
Saida ta sha ta koshi, tana yi tana binkito masa tsofaffin laifuffukan Aalimah a gareta tun fara maganar auren ta da Mu’azzam da irin kiyayyar data nunawa auren, tace ta san dole aka yi mata zama da Mu’azzam, amma tunda ga zuri’a a tsakani shi kuma data kwallafawa rai yayi aurensa tun kan ya dawo don me bazata hakura ba? Ai ga aya nan Allah ya nuna mata haihuwa da Mu’azzam yanzu ta fara.
Da sauri Aboulkhair ya daga kai ya dubi Inna yana son gane me take nufi, amma bata kara cewa komai ba tace su wuce su je tana dakin Bintou.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button