AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Aalimah na kwance bisa doguwar kujerar falon Inna Bintou, duk ta dashe tayi fari fat. Ta rame ta fita hayyacinta, idonta na fuskantar kofa sanda Aboulkhair ya sawo kai, Yesmin biye da shi da katuwar leda, sai Inna Kasisi karshen shigowa. Mamakin ganin Inna ya kasa boyuwa a idanunta. Kallo daya Inna Kasisi tayi mata ta tabbatar da zargin da suke mata. Aboulkhair tsintsiyar hannunta ya kama na wasu ‘yan mintuna ya kuma gwale idonta sannan ya taba temperature na wuyanta. Yace “tun yaushe ne kika fara vomiting din?†Ta rufe idanunta a hankali tace “last week†yace “banda aman sai me kuma?†Ta dan cuno baki tana kunkuni ita an dame ta. Haushi ya kama Inna tace “zaki bude baki kiyi magana ko ya tafi ya barki da ciwon ki?†Ta zumburo baki kafin tace “ciwon kai da zazzabin dareâ€. Aboulkhair ya dan kura mata ido kafin yace “when last kika ga period dinki?â€.
Zaro ido tayi tana masa kallon tsoro da razana. Ita ta san rabonta da period tun a Las Vegas, bata taba damuwa ba sabida dama ta kanyi tsallaken wata, amma yanzu daya yi mata wannan tambayar sai taji damuwar duniya ta rufto mata. Shiru tayi ta kasa cewa komai. Sai zuciyarta dake ta kai kawo a allon kirjinta tana son fitowa ta bakinta sabida tsabar kidima. Ta zazzaro ido kawai tana kallonsa.
Murmushi yayi mata ya zauna sosai a gaban ta. Kayan da suka kawo mata ya janyo gabansa, ya fiddo kwalin boost (locozade) karami ya bude ya saka straw a ciki ya mika mata tunda Inna tace madara zata sanyata amai. Saida ta harare shi sannan ta yunkura ta tashi zaune. Har yanzu murmushin bai bar fatar bakin shi ba yace “karbi ki sha wannan Maman Aboulkhair. It will boost your energy ki daina wannan kwanciyar kamar ruwaâ€.
Ta mika hannu ta karba jikinta har rawa yake yi sabida yunwa, duk abinda ake dafawa a gidan babu wanda zuciyar ta ke sha’awa. Wadannan masu ruwa-ruwan su take so. Nan da nan ta shanye ta bashi kwalin, zai bude wani ta nuna fresh milk din tace shi take so. Ya bude ya zuba mata. Ta kafa kai kamar Allah ya aikota ta shanye gorar madarar nan bakidayanta. Tayi wata irin ajiyar zuciya mai nauyi. Kafin ta sunkuya ta fashe da wani kakkarfan kuka.
Tace ita tun kafin su zo Niger rabon ta da period dinta. Amma ta saba tana tsallaken wata shi yasa bata damu ba. Idan ciki ne ita ina zata tsoma rayuwar ta?
Aboulkhair yayi mata wani irin kallo, yace “shi uban Dan yace baya so? Koko bashi da yadda zai yi da shi in an haife shi?†Tace “ni bazan haifi Da bana gidan ubansa ba†yace “to da kyau, kisa a ranki kin haife Dan nan lafiya kin gama, ko kwarzane kika yi mishi muma mun san hanyar kotu. Taimaka min da fitsarin ki Yesmin ta kawo min yanzuâ€. Wata uwar harara ta zabga masa ga idanun kaca-kaca da hawaye tace “bani badawa din†mikewa yayi daga zaman da yayi a gabanta yana wani makalallen murmushi. Allah-Allah yake ya bar wajen ya kira Mu’az don yi masa wannan kyakkyawan albishir, yace.
“Rike abunki. Shi ciki ai dan duma ne da sannu zai bayyana kansa. Bansan me zai zama tukuicina na wannan albishir din ba. Oh me!â€.
Inna Kasisi ta dade da barin dakin tun sanda Aalimah ta soma kukan nan nata mai ban haushi. Yesmin dai na jinsu bata tofa ba amma zuciyarta ta cika fal da farin ciki. Tana addu’ar Allah yasa albarkacin wannan cikin Aalimah ta hakura ta komawa Mu’azzam.
Yace “zan dawo na kawo miki magungunan da zasu taimaka aman ya tsaya dana karin lafiya, saura ki ki sha, wallahi zaki ga abinda baki soâ€.
A wannan rana Aalimah yadda taga rana haka taga dare. Ta rasa inda zata tsoma ranta. Wannan ciki shi ake kira unwanted pregnancy. Tun tafiyar Mu’azzam da ‘ya’yansa bata ware lokaci tayi tunaninsu ba sai yau, kullum makomar rayuwarta kawai take tunani.
Ta tuno ranar da aka yiwa Mu’azzam albishir din tana da ciki, riritawar da ya dinga yi mata lokacin rainon cikin ta, bautar da ya dinga yi mata don ta haife masa ‘ya’yansa lafiya, yadda ya hanata girki daga samun cikin ta zuwa haihuwarta. Duka rabin rainon ‘ya’yansa shi yayi abinsa. Duk abunda ya mallaka nata ne da ‘ya’yanta. Kulawar Mu’azzam a gareta unexpressable ce. A cikin maza samun mijin da ke muhimmanta matarsa da daga girman darajarta kamar sa, abu ne mai matukar wuya.
Yau gata zata yi rainon ciki a dakin kakarta, ba wanda ya damu da ta ci ko bata ci ba sabida son zuciyar ta. Yo son zuciya mana! Laifin me Mu’azzam yayi mata data yanke wa rayuwar su wannan tsatstsauran hukuncin? Wanda ta tabbata cutuwa ne ga dukkannin su. Ba don Allah ya jefo su Aboulkhair ba, da haka zata kwana da yunwa. Ba abinda ya damu su Inna Kasisi, dan gara-gara Inna Bintou tana sassauta mata.
Aboulkhair din da ta ke fadin bazata iya kalla alhalin tana auren Mu’azzam ba, shi gashi yana rayuwa da wata macen a kan idanunta. Har da albarkar zuri’a a tsakani.
Me Mu’azzam yayi mata a rayuwarsu banda alkhairi? Abinda ya faru dasu Ubangiji ne ya rubuta shi bata isa ta kankare faruwarsa ba. Yanzu gashi sakamakon rashin tawakkalinta ta janyowa kanta kiyayya a zukatan mafi yawan ‘uwan ta. Ta janyowa kan ta rainon ciki a dakin kakarta, ta yi missing duk wannan gatan na Mu’azzam! Ta tabbata Mu’az yayi mummunan fushi da ita, tunda har ya kai tsayin wannan lokacin bai taba nemanta ba, bai taba hada ta da ‘ya’yanta sun gaisa ba, anya bata yi kuskure ba? The deadly mistake din da ba zata iya gyarawa ba?
Gashi da Ubangiji ya tashi nuna mata bata isa ta kashe auren da kwanansa bai kare ba, ya kaddareta da boyayyen ciki, wanda ke tabbatar da har yanzu tana cikin zummar mijin ta har sai ta haihu. Ko yaya yake rayuwa da yaran shi kadai? Koda yake ko tana nan abubuwa da yawa shi yake musu, a wannan fannin bata jin sa, sai ko ta bangaren lafiyarsa.
Anan din ma tana da tabbacin he is doing well, in dai da Dr. Nebrass a raye, to kowacce irin matsala zata zo masa da sauki. Yawan ibadarsa kuma zai zamo kariya a gare shi.
Abu daya take da yaqini dashi akan Mu’azzam, duk fushinnan da yake yi da ita, bazai shafi abinda ke cikin ta ba. Zai so shi tamkar sauran ‘yan uwansa.
Zata yi masa rainon abunsa, ko albarkacin sa ya dubi nadamar ta ya yafe mata kuncin data jefa shi a ciki, koda bazai yi mata alfarmar komawa dakinta gaban ‘ya’yanta ba.
A washegari kowa dake gidan ya ji batun cikin Aalimah. Anas murna ta koma ciki, domin kuwa a baya yana kirge da watannin cikar iddarta. Yanzu kuwa ya fara fidda rai duk da ance faduwar gaba asarar namiji.
A daren ranar da suka baro Aalimah, Aboulkhair ya kulle kansa a daki ya kira Mu’azzam. Yana cike da wani irin doki da farin ciki.
A can Las Vegas, adaidai lokacin Mu’azzam na yiwa yaransa shirin kwanciya barci zasu kwanta, sabida gobe litinin don haka da wuri suke kwanciya.
Ya amsa wayar Aboulkhair da hannu guda, daya hannun yana shafa kan Basma, wadda ke dan rikici irin na mai jin barci.
“Mu’az…. kunnenka nawa? Menene goron albishir dina? Aalimah dai ciki gare ta, kuma a yadda na kintata yayi watanni ukuâ€.
Gaba-gadi ya fadi sakonsa, ba tare da jan rai ba .
Wani irin shiru Mu’azzam yayi, tamkar ruwa ya cinye shi.
“Mu’az…. Mu’az kana kan layi?â€
Aboulkhair ya tambaya jin shirun nasa yayi yawa.
“I’m on the call†ya fada a matukar gajarce.
“Ba zaka yi hakuri ba ku daidaita haka ko sabida shi? I didn’t expect it to be that longer, ban zaci fushin naku zai kai har zuwa wannan lokacin baâ€
Murmushi yayi, yace “Aalimah ba zata taba sona ba Aboulkhair, I’m sure she is not happy with it. A da ne ban damu data so ni ko ta ki ni ba, abinda nafi baiwa muhimmanci shine kasancewar mu tare.
A yanzu kuwa na san how it feels to be loved by the one you love. Ciki kuma nayi farin ciki da shi Allah ya raba su lafiya in karbi Da na. Ka barta tayi rayuwarta yadda ta zabe ta. Yanzu haka aure zan yi niâ€.
Aboulkhair ya kaskantar da murya yace “na roke ka kada kayi wannan kuskuren, ka bata lokaci. Auren huce haushi kake so kayi, kuma bazai haifar mana da alheri baâ€.
Murmushi Mu’azzam yayi, har ransa ya san Aboulkhair gaskiya ya fada, auren da ya amsawa Inna zai yi na huce takaicin Aalimah ne, amma ba zai iya rayuwa da wata diya mace bayan Aalimah ba, amma wani bangare na zuciyarsa yana insisting da ya yi auren don ya huce haushin tozarcin da Aalimah tayi masa. Ta rasa inda zata ce ya sake ta sai a gaban Alkali. In ta bukata cikin sirri ita da shi ai shi me iya sadaukar da komai ne don farin cikinta da kwanciyar hankalin ta.
Har suka yi sallama bai ce da Aboulkhair ya fasa ko bai fasa ba.