AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Cikin kwana bakwai Aalimah ta samu karfin jikinta, sabida kulawar data ke samu daga Aboulkhair da Yesmin. Ya hadata da magunguna masu kyau wadanda suka taimaka wajen rage mata yawan aman data ke fama da shi, ga kayan dadi iri-iri kullum yana baiwa Yesmin ta kawo mata leda-leda, tuni ta barwa su Inna abincinsu sai kayan kara jini dana kara kuzari da yake aikowa. Mummy Zulaiha kuma kullum sai tayi mata waya ta tambayeta abinda take son ci, tun tana jin nauyi har ta daina. Don haka kwanon abincin ta na musamman ya koma gidan Daddy wanda Mummy da kanta ke shiga kitchen ta girka mata, kullum Yesmin da Nurat ke kawo mata.
Saida ta warware sosai ta maida jikin ta Malam yayi mata iznin tafiya Kanon kamar yadda ta bukata.
A daren ranar ta hada kayanta tsab tana cike da doki. Washegari Aboulkhair ya saya mata tikiti ta tafi Nigeria. A Abuja tayi transit kafin ta taso ta sanya layin ta na Nigeria ta kira Yaya Aboubacar ta gaya masa lokacin da zata sauka. Kafin aje Kano ta jigata sosai. Amma tarbar data samu a gidan su tasa ta mance da duk gajiyar data kwaso.
Ta samu gidan nasu da albarkar baki na musamman, Dr. Suraj Kashim wan Mama da matarsa Ilham da biyu daga cikin yaransu Mustapha da Maryam sun zo ganin gida daga kasar Canada. Maryam zata yi sa’ar Sultana itace ta biyu a ‘ya’yan aunty Ilham. Mustapha zaiyi sa’an autarsu Suhaima. Don haka tuni ta ware a cikin ‘yan uwanta data dade bata gani ba anata harkar arziki, tana ta taka-tsan-tsan kada wani cikin su ya fahimci cikin nan da bata so a sani. Sai fama take da zumbulelen hijab tun zuwanta har aunty Ilham na tsokanar ta ko Mu’azzam ne yasa ta yawo da hijabi, anan Mama take gayawa Ilham ai babu auren, ta gaya mata duk abinda ya faru.
7/13/21, 5:59 PM – Buhainat: Aunty Ilham ta taimaka mata ta sanya lallausar leshin data kawo mata, ta zaunar ta gefen gadon ta tana yi mata sassanyan make-up. Sai gyaran muryar Uncle suka ji a bakin kofa yana fadin “Ilham ina ‘yar taki ne? Ta zo suje ko tausa ta yiwa mijinta ya rage gajiyar zirga-zirgar nan da ya shaâ€. Ilham tayi dariya Aalimah ta sadda kai kamar tace kasar ta tsage ta shige. Yace “maza fito ki same shi a mota driver zai kai ku masaukin shi. Daga yau har kwana uku na sallame ku, in zaku wuce U.S kuzo muyi sallamaâ€.
Aalimah kamar tayi kuka bayan wucewar Daddy, bata ankara ba kuwa ta ji hawaye sun sauko mata data ji cewa da gaske zata bar Ilham da iyalin ta bada jimawa ba. Aunty na cewa ta yi hakuri ta bi umarnin babanta, ta bar Mu’azzam ya fanshe watannin da ya yi ba tare da ita ba cikin kwanaki ukun nan. Ta armasa masa su su shiga cikin kundin tarihin rayuwar su. Sakamakon haka Allah zai iya bata Aljannah. Ga bin iyaye ga bin mijiâ€. Dariya tayi don ta san aunty Ilham wayo take mata.
Ita ta tsitstsintar mata duk abinda tasan zata yi amfani dashi ta jefa mata a jaka. Ta dauko mata jakar suka fito tare. Mu’azzam da Uncle na bakin motar Uncle suna magana direban yana daga cikin motar. Fitowarsu yasa suka yi sallama, aunty ta bude mata kofa shi kuma Dr. Suraj ya bude masa, suka shiga suka rufe musu tare da daga musu hannu.
Har suka iso hotel din da Mu’azzam ya sauka basu yi magana a junansu ba, shi Mu’azzam waya yake da Aboulkhair yana gaya masa gashi a Canada ya zo biko, Aboulkhair yace “Canada kuma?†Murmushi yayi yace “can ta yi kaura, tunda zaman gidan Malam Raazee ya gagara, kasan mace in ta wuce zaman gida tace kuma sai ta zauna to akwai matsala, don bazata taba jin dadin sa ba, musamman a cikin dattijai†Aalimah ta harare shi ta gefen ido. Aboulkhair yace “gidan Dr. Suraj ta koma kenan?†yace “eh, in dama ta ki ba sai a koma hagu ba?†Murmushi Aboulkhair yayi yace “kuma Inna Kasisin tana can tana cigiyar ta, ta dade da saukowa, auren data ke nema maka ma da bakinta tace ta fasa, ba za’a samu macen da zata zauna da Mu’azzam tsakani da Allah cikin kowanne hali irin Aalimah ba.
Tana fadi da bakin ta “Aalimah ce ta zauna dashi a halin rashin lafiya, don lafiya ta samu bazata amince wata ta more ta ba Aalimahr baâ€. Duk zancennan da suke yi akan kunnen Aalimah sabida a hands free Mu’azzam ya sanya wayar.
Ta tsurawa Mu’azzam ido jin abinda Aboulkhair ke fada. Mu’azzam ya samu lafiya as in how? Dama lalurarsa mai warkewa ce? A take kuma kwakwalwarta ta tafi tunano mata wani zance makamancin wannan da suka taba yi da Daddynta farkon aurenta da Mu’azzam. Cewa Mu’azzam zai iya warkewa bayan samun accurate treatment na akalla shekaru goma. Kuma ya dade da cika wannan ka’idar. Yadda yake romancing dinta dazu passionately kuma cikin nutsuwa ba yadda ya saba ba. Idanunta suka cigaba da budewa akan Mu’azzam yana ta hira da Dan uwansa yana ta murmushi kamar ya manta da ita cikin motar. Irin murmushin da ba kasafai yake yi ba sai yana cikin matsanancin farin ciki. Sassalkan sajensa ya kwanta lufff akan fuskarsa ya kara masa ilhama da cikar zati. Fararen hakoransa a waje, kamar wanda aka yi wa bushara da Aljannah.
Lumshe Idanunta tayi, a lokacin data ji sanyin hannun Mu’azzam a cikin nata. Ta kuma ji motar ta daina motsi wato sun iso masaukin nasu. Direban ya daukar mata jakarta da Ilham tasa mata daga bayan mota, ya rakasu da ita har kofar dakinsu ta cikin lifter. Sannan ya sake biyo lifter ya dawo kasa ya dauki motar don kaiwa ubangidansa.
Tun daga shigarsu dakin da Mu’azzam ya sanya mukullin shi ya bude, abubuwa basu kara daidaituwa ga Aalimah ba, duniyar ta bata kara zama cikin seti ba, haka shima Mu’azzam. Duk yadda ta zaci kewar data ke jin ta yi ta Mu’azzam mai dumbin yawa ce, ashe na fatar baki kawai ta sani. Ba da sanin ta ba kowacce gaba ta jikinta tayi kewar tasa ba zuciyarta kadai ba. Da farko akwai dari-darin abin da ‘yar fargaba a tare da ita. Kafin wani dan lokaci kuma ta tsinci kanta da mika wuya bakidayan ta. Sakamakon ganewa data yi cewa Mu’azzam din da ba shine yanzu ba. Gabadaya Mu’azzam din data sani a baya ya canza mata, things are going very soft and gentle from him. Ta yarda bayan lafiya da nutsuwa harda kwas (course) a soyayya ya samu wanda a baya bashi da kamarsa.
A can baya ta haqqaqe abinda ya sani shine ya biya bukatar sa anyhow; disregarding her own emotions. Kuma akai-akai kamar cin abinci. A hakan kuma take son abinta, take kula da dukkannin bukatun sa, domin tana gamsuwa ta kowannne bangare. Amma yanzu it goes along with her own pleasure and contentment. Tare da kula da rashin jigatar da ita a matsayin ta na mai tsohon ciki. Hawaye ta soma yi na farin ciki da godiya ga Allah. Ta yarda Mu’az ya samu lafiya. Komai ya koma dai-dai yadda ya kamata ya koma. It tastes good…. It tastes romantic. Wata rayuwa ce da bata taba mafarkin samu a Mu’azzam ba.
Daga nan kuma sai barci, barcin da suka dade basu yi mai nutsuwar sa ba a kafatanin rayuwarsu. Ba su suka farka ba sai karfe biyar na asubahi, tare suka yi jam’in sallar asubah. Sun dade suna addu’a batare da kowanne ya san abinda dan uwansa yake roka akan dan uwansa ba. Aalimah rokon Allah take ya dorar da lafiyar Mu’azzam, bata taba samun nutsuwa a rayuwar aure irin ta yau ba. Tana rokon Allah ya dorar da wannan rayuwar ya dawwamar dasu cikin alherinsa.
Ga Mu’azzam, rokon Allah yake ya sauki Aalimah lafiya, ya raya musu ‘ya’yansu rayuwa ta addinin muslunci. Abubuwan da bai taba ji akan Aalimah ba, su suke kara overwhelming dinsa yanzu. Ashe wannan sune feelings…..sune emotions. ….. sune affection… sune so da kauna wadanda a baya bai san su ba? Idan kuwa har sune dan uwansa Aboulkhair yayi kokari, kokarin da a yau ya jinjina masa, yayi masa sadaukarwar da shi ba zai iya ba! Don abu na karshe da bazai iya ba a yanzu shine rabuwa da Aalimah!!!
Suna kwance kalmashe cikin jikin juna, lullube cikin lallausar duvet, sanyin Ontario na yau kamar har yafi na kullum ratsa kashi da bargo. Mu’azzam yace “umh Aalimah, gaya min yaya bayan rabo? Na same ki cikin yanayi na kwanciyar hankali da jin dadin rayuwar da ta same ki, sabanin ni da darare suka yi ta wucewa da yawansu idona biyu har ketowar alfijir. Bana komai sai zubawa ‘ya’yanki ido suna nasu baccin ina kallon fuskar ki cikin fuskokin su. Me yasa ki kayi tunanin cewa rabuwar mu ita ce mafi alkhairi?â€
Aalimah ta kwantar da kai bisa kirjin Mu’azzam tana mai jin komai na rayuwa yanzu yayi mata daidai, daidai da yadda take kwana tana addu’ar Allah ya mayar mata da shi, daga lokacin data yanke musu hukuncin da ta ke ganin shine abinda ya dace dasu bakidaya, tace.
“Ya Mu’az nima bansan dalilin da yasa na yanke hukuncin dana yanke ba, abinda na sani a lokacin shine I’m desperate, hopeless. Amma daga ranar da hakan ta faru ni kuma ban kara rayuwar farin ciki da jin dadi ba, ji nake kamar na yanke bangaren daya kunshi dukkan farin cikin na yar. It was regrettable, though, ko kai ne a matsayi na a lokacin abinda zaka yi kenan. Dawowar Monsieur Aboulkhair abin farin ciki ce a garemu amma hakika ta ruda ni sosai. Wani al’amari sai Ubangiji.
Zawarcin bashi da dadi ko kadan, bana son tunawa, kowa bai min ta dadi ba sai Daddy da Mummy, su kadai suka karbi uzrina, kai dan gata ne Ya Mu’az ban ga wanda ake so a zuri’ar mu kamar ka baâ€.
Dariya Mu’azzam ya saki yayi cuddling dinta sosai, dan kankanin bakin ta yayi kissing kafin yace.
“Kina jin dadin yimin wannan gorin Aalimah; ba wanda ake so a gidan RAZEE kama na, na yarda basu yi miki ta dadi ba amma kisa a ranki duk a cikin son da suke miki ne. Fatan su da burinsu shine mu kasance tare, mu raini ‘ya’yan mu tare.
Me nake da shi a duniya da zan sakawa Aboulkhair wannan sacrifice din da yayi min? Wallahi babu. I love him to an extent. Ji nake idan zan yi ta haihuwar ‘ya’ya maza ina saka musu Aboulkhair yayi kadan ya nuna godiyata a gare shiâ€.
Haka suka karar da wunin yau bakidaya a gadon barcinsu, sallah kadai ke tada su. Abinci daga hotel din ake shigo musu dashi, Ilham ta ce zata aiko Mu’azzam ya ce ta bar shi. Baya son ko kuda ya gitta a tsakanin su. A shekaru bakwai da suka yi tare a baya, basu taba samun shaquwar da suka samu a kwanaki ukun nan da sukayi a Ontario ba. Soyayyar ta ninku, ta karu, ta rubanya. Basa ganin kowa a gabansu sai junansu.
Mu’azzam ya kira Madame Ruqayya mai rainon su Basma yace ta bashi Aboulkhair da Basma. Basma na karba ya mikawa Aalimah, sallama kawai Aalimah tayi Basma ta shaida ta, soyayyar uwa da Da sai Allah. Maimakon Basma tayi murna da jin mamarta kuka ta saki, tana fadin Mummy kin guje mu, kin barmu mu kadai a wajen Madame da Daddy, kin ki dawowa saboda kin daina sonmu…..â€.
“Basma uwa tana daina son dan ta? Wannan impossible ne. Baki San uzrina ba Bassy, I’ve a green great giant surprise gift for you. Tare da sabon Baby zan dawo, mace ko namiji wanne kika fi so?†Nan da nan Basma ta share hawaye ta saki dariya tana fadin “Allah Mummy? In dai da gaske kike to na daina fushi, dama duk ‘yan ajin mu suna da baby a gidan su banda ni, yaushe zaki dawo?â€
Aboulkhair ya kwace wayar daga hannun Basma, “Daddy your boy is missing you, yaushe zaka dawo?†Aalimah ta lumshe idon ta, soyayyar uwa da Da na ratsa ta. “Yaron na Daddy ne kadai ko? Ya manta da Mamansa?†Aboulkhair ya zabura, ya sake kankame wayar a hannunsa. “Mummy ke ce?†Nice Monsieur Aboulkhair, ina fatan ba ka yiwa Madame Ruqayyah rikici?†Shima sai yasa kuka yana fadin “mummy me muka yi miki kika tafi kika bar mu mu kadai? Ko a waya bakya kiran mu? Daddy kullum baya bacci sabida kin ki dawowa, don Allah Mummy ki dawo bana son zama da Madame Ruqayya ke da Daddy nake so….â€.
Ta kasa tsayar da hawayen da suka shimfido mata, ta kai yatsunta ta share su, tace “Aboulkhair it’s a promise nan da kwana biyu zaka ganni a Vegas tare da Daddy. Amma sai ka daina cewa baka son zama da Madame Ruqayyah, kaga bazata ji dadi ba tana iya kokarinta a kan kuâ€. Ya juya ya dubi matar ya yi mata murmushi ya ce “Madame sorry. My Mummy is coming back soonâ€.
Yau dai wayar ta uwar da ‘ya’yanta ce ko uban basu nema ba har suka kare hirar, wadda ake yin ta ana sharar hawaye da koke-koke. Mu’azzam yana daga gefe Aalimah ta yi matashi da gadon bayan sa duk yana jin su yana murmushi.
Ya karbi wayar daga hannunta ya kira Malam Razee, ita kuma ta shiga toilet don yin alwala. Tana jin su suna hira yana gaya masa ai yazo yayi biko gashi a hotel tare da Aalimah. Daga bayin Aalimah ta saki salati tana fadin “haba haba Ya Mu’az? Haba don Allah†Malam Razee yace “hotel kuma? A wane gari kuma?†Yace “wani kayataccen hotel ne a birnin Ontario, ita Ontario din cikin kasar Canada take, nan Aalimah tayi hijira gidan Baffanta na wajen uwa, a cewar ta tunda bakwa son taâ€.
Murmushi Malam Raazee yayi yana hamdala a fili da boye saida ya baiwa Mu’azzam tausayi. Ya tabbata har hawaye yake yi duk da baya ganinsa. Malam yace “ko yau mutuwa ta zo, burika sun gama cikka. Kowa dake cikin ‘ya’ya da jikoki na ya samu rayuwar da hankalina ya kwanta da ita. Ka rike ‘yar uwar ka amana Mu’azzam ku rufa asirin juna. Allah yayi muku albarka, ya albarkaci zuri’ar kuâ€.
7/13/21, 6:00 PM – Buhainat: Kafin kace meye wannan zance ya tadda su Inna Kasisi, Inna Bintou, gidan su kawu Oussama da gidan Daddy1. Aalimah da Mu’azzam sun koma har sun tafi yawon amarci. Zancen ya baiwa Gumsu dariya tace da wanda ya zo ya gaya musu “wane amarci da zungureren cikin?†Amma zuciyar ta kal kamar takarda.
Gumsu ta dau waya ta hau doka kira Nigeria, Basmah ta kira tace “kin ji wai yar tawayen can ta gaji da zaman gida ta koma gidan ta har an tafi honeymoon wata kasa, nace wane yawon amarci da zungureren ciki?†Basmah tace “kayyasa! Dadi na da gidan Malam Raazee karawa miya gishiri, wani lokacin har da onga, ba wani yawon amarci da suka tafi dama tana can shine ya bita†Gumsu tace “wai ba tana gidansu ba?†Basmah tace “tunda son kai ya rufe maku ido yaushe zaku damu da inda take? To masu sonta sun dauketa zuwa Canada ko wata daya bata rufa anan Kano baâ€. Gumsu ta ji duk kunya ta kama ta, tunda Aalimah ta bar Niamey bata kara neman ta ba balle ta tambayi lafiyar cikin jikin ta tace “don Allah ki bani lambar taâ€. Basmah tace “wallahi banni badawa, in da kunya ai baza ki nemeta ba yanzu data dawo gidan Dan ki. Watanni sama da hudu baki kirata ba ko don jin lafiyar abinda ke cikinta sai yanzu data yarda ta koma gidan dan ki? Wannan son kai a fili da me yayi kama!â€.
Gumsu tace “ki yarda dani Basmah ba son kai bane ba, tausayin Mu’azzam da yaran nake ji. Yanzu data yarda ta koma baki ji dadin dana ji ba, ba shikenan komai ya wuce ba?†Basmah tace “to shi da kike jin tausayi baya tausayin kansa, da yana tausayin kansa da ya dade da neman sulhuâ€. Sai da Gumsu ta kafa naci sannan Basmah ta hakura ta bata lamabar Aalimah ta Ontario.
Sanda Gumsu ta kirata Mu’azzam take wa cumbing kanshi ya fito daga wanka. Don haka bata daga ba sai da ta gama, ta kuma taimaka masa ya gama shiryawa, Mus’ab ne zai zo ya daukesu zuwa gidan Uncle suyi sallama ta hada kayanta don gobe jirgin asubah zasu bi zuwa U.S. Gumsu bata fasa kira akai-akai ba har Mu’azzam ya gaji yace ta daga wayar nan. Tana dagawa taji Gumsu. Ajiyar zuciya tayi tace “ko dai wrong number ne?†Gumsu da borin kunyar ta tayi ta bata hakuri tana gaya mata abinda take hange na barinta gaban ‘ya’yanta tunda in ta ki Mu’azzam ta ki Aboulkhair karshenta dole wani daban zata aura ta bar yaran cikin maraici ita abinda bata so kenan tayi hakuri ta fahimceta ta daina kullatar kowa akan haka, soyayyar da suke yi mata ne ya janyo hakanâ€. Mu’azzam ya gaji da jiran Aalimah su fita yace da hannu wacece ne? A hankali ta motsa labbanta tace masa “Gumsu-Moiram†murmushi yayi ya karbi wayar yace “inason fita da iyali na, ko za’a bar wayar sai mun dawo?â€
Gumsu ta shaqa tace “ina can ina maka kamfen, har gaba na kulla sabida kai, kana nan kana min kora da hali ko?â€
Yace “to ai ni ban sa ki ba, dadi na dake sa-kai a uku babu gaira babu daliliâ€. Aalimah bata san sanda ta saki dariya ba, in Mu’azzam ya san yadda Gumsu ta damu da al’amarinsa da bai yi mata haka ba. Ta karbi wayar tace mata ta hakura, sannan ta barsu suka fita.
Sunyi kwalliya ta alfarma cikin shigar mutanen Nijar dukkansu. Mus’ab na tuki suna baya. Ya dan juyo ya dubi Aalimah yace “we’re gonna miss you so much Adda, kwana ukun nan da baki gidan baki ji yadda gidan ya koma boring ba kowa baya walwala musamman Maryamâ€. Murmushi tayi tace “nima zanyi kewar ku, yadda halshe bazai iya bayyanawa ba, duka gidan I enjoyed your company so muchâ€. Mu’azzam yana jin su bai ce musu komai ba.
Daidai lokacin da suka iso gidan, duk mutanen gidan suka tarar a falo. Kowa yayi jigum kamar wadanda aka yiwa mutuwa. Aalimah na shigowa Maryam ta nufe ta ta rungume tana kuka tana rokonta kada ta tafi. Daddy yace “yau naji ikon Allah in da za’a ce kada mace ta je gidan miji, kema kwana nawa zakiyi a gidan da zaki hanata zuwa nata? Kuma wai don rashin kunya a gaban mijin ta?†Su Taufeeqah suka hau dariyar Maryam, Mu’azzam yace “Maryam duk sanda kike son ganin Adda zan miki visa kije Las Vegas. I promisedâ€. Ai nan da nan Maryam ta saki Aalimah ta hau tsalle.
Anan suka ci abincin dare suka nitsa hira har saida yaran suka yi barci, Anty da kanta ta hadawa Aalimah kayanta tsab, Mus’ab ya sanya a mota. Anan suka karar da rabin daren, sai da zasu tafi Anty ta fiddo sayayyar data yi mata na kayan jarirai unisex cikin katuwar jakka, dana su Basmah suma kowa ya samu jaka guda. Daddy kuwa kudi ya zuba mata cikin account din da ya dade da bude mata tun zuwanta kamar sauran ‘ya’yansa, duk wata yana saka musu kudi don bukatocinsu, yace in tana so ta kwashe ta mayar U.S account din ta ta rufe account din in kuma zata bar shi to, Aalimah sai hawaye, ta rasa bakin godiya, tace bayan dawainiyar da suka sha da ita wata da watanni, kuma har da karin wannan dawainiyar. Uncle Suraj Kashim yace “akul! Ta sake kira masa dawainiya, dole ne yayiwa Asseya da ‘ya’yan ta dawainiyar don bata da kowa sai shiâ€. Da haka suka yi sallama Aalimah na ta kuka. Don ji take kamar wannan shine lokaci na farko da zata je gidan miji.
Basu samu sunyi barci ba don suna shigowa lokacin sallar asubah na yi. Sallah suka yi daga nan suka kimtsa. Chauffeur na hotel din shi ya kaisu filin jirgi tare da kayan su.
A cikin jirgi Aalimah ta kwantar da kai a kafadun Mu’azzam, rayuwarta bakidaya ta dinga gilma mata tamkar a majigi. Ta faro ne daga zuwanta Boston, inda daga nan tarihin rayuwar ta ya fara, rayuwarta gidansu Mu’azazam, haduwar ta da Aboulkhair, aurensu har zuwa rabuwar su. Aurenta da Mu’azazam da irin kalubalen data fuskanta a cikin auren, haihuwarsu zuwa rabuwarsu da kuma kalubalen data fuskanta a cikin rabuwar. Har kuma zuwa yau da Ubangiji ya sake binding dinsu together. Hakan kadai ya ishi bawa ya yarda Ubangiji Subhana mai yawan hikima ne, komai yayi kada bawa yasanya ayar tambaya. Duk abinda ya tsara ya san dalilin yinsa. Data yi hakuri da kaddarar auren Mu’azzam yau gashi ta ci ribar hakurin ta. Ubangiji ya san cewa Mu’azzam shine mafi alkhairi gareta akan Aboulkhair shiyasa ya canza rayuwar su ta fuskar da ya ga dama. Hakurin data yi a zama da Mu’azzam bai tashi a banza ba. Hakika kowa ya bi iyayensa ya kuma fawwala al’amarinsa ga Allah zai iya masa.
The fact that ana son juna kamar a hadiye juna baya hana rabuwa a wa’adin da Allah ya tsara, ko ba’a mutu ba rayuwa tafe take da kaddarori kala-kala masu sabbaba rabuwar. Kuma karfin soyayya baya hana karewar aure a wa’adin da Ubangiji ya nufa. Wannan shine ya faru tsakanin ta da Aboulkhair wanda har abada bazata manta ba a karkashin zuciyar ta. Abu guda take da tabbacinsa; daga ranar da ta soma son Mu’azzam a matsayinsa na mijinta, daga ranar da ta zama sirrin Mu’azzam ya zama sirrinta, gabadaya rayuwar data yi da Aboulkhair ta zama shudadden al’amarin da bata sake tunawa da wani feeling ba. Aboulkhair ya rikide ya juye ya koma kamar Yaya Aboubacar a idanunta.