AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

              ******

Kada kaso kallon soyayyar data afku tsakanin Aalimah da Mu’azzam da yaransu a filin sauka da tashin jirage na garin Nevada (Las Vegas) a wannan rana, wadanda Harrison ya debo ya taho dasu don su tarbi iyayen nasu. It was so emotional da har ya fiddo hawaye daga idanun Aalimah. Kwannaki suka cigaba da juyewa zuwa satittika har Aalimah ta shiga watan haihuwar ta.
A wadannan satittikan numfashi ne kawai Mu’azzam baya yiwa Aalimah sabida tattali da soyayya. Idan ofis ya tafi hankalinsa yana kansu, Allah-Allah yake ya dawo gida ya tadda su, idan yana gida lokutansa nata ne. Har Allah ya nufi Aalimah da haihuwa lafiya ta haifi da namiji tamkar Mu’azzam yayi kakhi ya tofar.
Wannan karon rigima ta barke tsakanin matar da mijin kan sunan da za’a sanyawa yaron, Mu’azzam yace wancan lokacin ya bata dama ta sa Basmah wannan karon ta bar masa Malam Raazee zai sa, ita kuma ta dage Daddy 1 (Ishaq) za’a sanya, bazata taba manta gudummuwar sa da soyayyar sa cikin rayuwarta ba, cikin halin dadi ko sauyin rayuwar da suka samu kansu. Rigima kafin ranar suna tsakaninsu ta ki karewa har kunnen Daddy 2. Ba da wata-wata ba ya bi bayan Mu’azzam yace ta bari asa tsohonsu, shekara mai zuwa war haka tasa himma ta sake haifowa sai asa mata Ishaq din. Tsohon mu mai ran karfe ki bari mu samu magajinsa. Aalimah tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka tace “Daddy, abinda yasa nace asa Daddy 1 sabida Khaleesat ta saka Malam recently ko wata biyu ba’a yi ba†Daddy yace “Malam Raazee ai baya isar mu, ya kamata a ce dukkan ku ya kasance cikin ‘ya’yan ku da Malam Raazee, na Khaleesat daban naki dabanâ€. Aalimah ta sakar masu don sun fita gaskiya.

Ranar suna Mu’azzam ya yiwa jaririnsa khutbah da suna Ibrahim (Sarham). Lokacin da ya kira Malam Raazee ya gaya masa baya jin dadi, jikin girma ya motsa masa, a kwance yake amma don farin ciki cewa yayi wannan karon sai ya taka kafafunsa gidan Mu’azzam har kasar Amurka.
Shi da Oncle Oussama da Eidrissa Mu’azzam ya yi wa visa zuwa U.S. Duk da tsufa da karancin koshin lafiya yace sai yaje gidan Mu’azzam koda sau daya ne a rayuwar sa. Mu’azzam din kuma ya kudurce a ransa zai yi amfani da damar a duba masa lafiyar Malam din sosai. Mummy, Gumsu, Daddy 1 da Daddy 2, Mama Aseeya, Hamoud da matarsa Khaleesat, Aboubacar da matarsa Basmah duk haka suka dunguma zuwa birnin Las Vegas. In da suka tarar da Dr. Aboulkhair da iyalin sa (Sa’eedah da danta Abu Turab) suma sun zo daga Boston don halartar sunan Sarham.

Aalimah ta kasa tsaye ta kasa zaune da shirin tarbar iyaye da ‘yan uwansu, wadanda za su zo takanas don taya su murnar alherin da ya same su na karin girman da Mu’azzam ya samu a CHEVRON da kuma haihuwar magajin Malam wato Sarham. Ita da Aunty Sa’eedah ke ta wannan shirye-shiryen tun gabanin zuwan bakin nasu da kwanaki uku. Kafin bakin su iso hatta cokalin da za su ci abinci sun tanada. Sun yi time-table na girke-girken da zasu ke musu a kullum a tsayin kwana bakwai da za su yi tare da su. Sun tsara za su rike matan a nan gidan Mu’azzam tunda yana da girma, Malam Raazee ma a gidan zai zauna, sun gyare masa daki a downstairs kada ya sha wahalar hawa bene, maza kuma tuni Mu’azzam ya kama musu hotel din da za su sauka.
A ranar da za su iso, bakidaya iyalin Mu’azzam dana Aboulkhair suka dunguma filin jirgin saman (John F. Kennedy) suka tarbo su zuwa gida.
Mummy Zulaiha don farin ciki tana arba da Mu’azzam da Aboulkhair tsaye a tare, sun juya baya suna magana da junansu, ta tuno lokutan data kwashe cikin kukan zuci dana fili, na tunanin Aboulkhair ya bar su kenan har abada, da lalurar Mu’azzam da bata taba barin ta kwanciyar hankali ba tsayin shekaru masu yawa, hakan kadai ya ishi bawa ya kara imani, ya tsoraci Allah, mutuwa ba karya bace, tana iya zuwa a kowanne lokaci babu notice, bazamu taba guje mata ba, sai in lokaci bai yi ba, haka rashin lafiya duk arzikin ka da gatan ka sai idan Ubangiji ya ga damar yaye maka a lokacin da ya so. Ji kawai suka yi Mummy ta rungume su ta baya su duka biyun ta saki kuka mai sauti tana hamdala a fili. Dukkan su sai suka sanyata a tsakiyar su suka rungumeta suna lallashin ta.
Ko da suka iso gida hira ce ta yaushe gamo ta tsinke a tsakanin wannan family don daga Aboulkhair har Mu’azzam da iyalinsu sun kwashi lokaci ba su je gida ba. Gumsu nata aikin nata na bada dariya, ba ruwanta da surukai ko Kakanni, komai ya zo bakin ta fade take.
Aalimah da Sa’eedah suka hade da su Basma da Khaleesat, Yesmin da karamarsu Nurat suka yi ta dawainiya da iyayensu da Kakansu. Kowaccen su ta aje iyali abin gwanin ban sha’awa. Yau Basma da Aalimah da Khaleesat har rayuwar Boston sai da aka tabo aka dara cikin nishadi.

Masha Allahu laquwwata illa billah.
Karshen littafin AALIMAH kenan.
Kuskuren da ke ciki ku taya ni rokon Allah ya yafe mini. Alherin da ke ciki, Allah ya raba mana ladarsa ni da ku bakidaya.
Taku har abada; Sumayyah Abdulkadir.
TAKORI

           Karin Bayani 

Na samu fatawar malamai mabanbanta akan makomar auren Aalimah da Mu’azzam, bayan bayyanar Aboulkhair, fahimta fuska, wasu malaman sun ce miji na farko shi ke da mata amma wannan fatawar ta tsaya ne akan shekaru hudu da bacewar mijin bai bayyana ba, kuma babu iddar mutuwa, Abulkhair sai bayan shekaru bakwai ya bayyana, sannan da iddar mutuwa, don haka nayi amfani da mafi rinjayen fatawar malamai wadda tace miji na biyu keda mata, ko a bata zabi ita matar, ta zabi wanda take son cigaba da zama da shi a tsakanin su biyun in bayan shekaru hudu ne kuma bata yi khul’iy ba. Allah shine mafi sani. Wallahu a’alam Allah shine mafi sani. Idan nayi kuskure ina rokon Allah ya yafe mini.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button