AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4
AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Kamar kullum washegari suka yi wanka suka shisshirya. Mummy Zulaiha ta zo har dakinsu ta yi kiran Aalimah. Tare suka fita ta nuna mata duk yadda ake amfani da injinan cleaning din gidan, da yadda ake tsaftace shi. Sannan ta tambaye ta ko ta iya girki? Ta ce ba abin da ba ta iya girkawa ba. Sai ta ce, har English meals? Ta ce, ta iya wasu a wurin Mamanta. Sai ta ce, to shi kenan daga yau ita za ta dinga girki da cleaning, mai aikinta ta yi tafiya. Tana kuma son kullum ta gama abincin dare kafin dawowar Daddy. Tana kuma son wannan zancen ya tsaya a tsakaninsu. Incase su Basma za su tambaye ta wani abu a kan hakan, ta ce, ita ta sa kanta.
Aalimah ta yi motsi da bakinta tana so ta tambaye ta makarantarta kuma fa? Amma ganin ba fuska dole ta hadiye. Tun a lokacin ta fara girkin rana bayan MummyZulaiha din ta nuna mata yadda ake amfani da komai.
Ta yi cleaning, ta yi girkin rana, ta yi na dare. Ko na minti biyu ba ta huta ba. Da suka tambaye ta ko me ta ke yi haka tun safe? Ta gaya musu yadda uwarsu ta gaya mata. Ta kara da cewa, Easther ta yi tafiya shi ya sa ta ke taimaka wa Mummyn. Allah ya so tun farko Mamansu ta hore su da komai, ba ta da son jiki ko kankani.
Ranar litinin, wato washegarin ranar,Mummy Zulaiha ta kwashe ‘ya’yanta ta kai makaranta, ta bar Aalimah a kitchen. Mamaki ya kama su har hada baki suke wajen tambayarta,
“Aal, will not go to school Mum?â€
Ta lailayo ashariyar da ba su san ta iya ba ta antaya musu, ta kuma ce duk wanda ya kara yi mata zancen wata “Aal†ubansa za ta ci ciki da waje. Ta cire ta daga makarantar don ubansu, su je su gaya wa ubansu su ga yadda za ta ci mutuncinsu. Duk suka yi lakwas. Zaginta da balbalin bala’inta ya fi karfi a kan Basma, ta ce ta san ta fi kowa firirita a kan wata Aal, to in ta isa ta je ta gaya wa ubanta RAAZEE ISHAQ ta cire Aalimah daga makaranta.
Hatta abokan karatun Basma sun fahimci yau ba ta cikin walwala. Wadanda suka damu har tambayarta suke yi, me ke damunta? A gajarce ta ke cewa, “Headacheâ€.
Da yamma motar makaranta ta bi ta koma gida, Mummy ta ce su Khaleesat kawai za ta dinga maidawa gida, she’s old enough ta kula da kanta (Basman).
Ko da suka dawo a kitchen suka tadda Aalimah ko wanka ba ta samu ta yi ba saboda aiki. Har wanki Mummy ta jibga mata don ma dai da inji ne. A ranta ta ce, in kin ji wuya za ki koma inda ki ka fito.
Idanu narai-narai da hawaye Basma da ke tsaye a bakin kofa ta ke kallon Aalimah, wadda duk ta yi gumi ta yi maiko, ta takarkare sai kankarar tukunya ta ke da cokali tana ci, abinci cokali daya wannan Mummy ba ta bata ba, duk da ita ta yi girkin. Tazo ta kwashe shi tsaf ta kai ‘dining’ kuma ta kasa-ta-tsare a falon tana ta ayyukan ta cikin system dinta, bata bari Aalimah ta ganta ba ta bar wurin da sauri ta yi sama da gudu, ta fada gadonta tana hawaye. Me za ta iya a kai banda fada wa Daddy? Babu!
Haka suka wuni dukkansu sukuku da su cikin damuwa da mamakin Mummy. Su dai sun san ko a cikin iyaye tasu uwar is exceptional wajen kyautata wa ‘ya’yanta. Yaushe ta canzazuwa maketaciya?
Rayuwar da suka yi ta yi kenan har tsayin wata guda, sai Daddy zai dawo ta ke cewa ta je ta yi wanka, sai za a zauna cin abincin dare za ta samu ta ci. Amma ba ta da breakfast ba ta da lunch. Sai karshen mako kuma, shi ma don Daddy na gida tana da freedom duk da haka komai ita ta ke yi, bai taba lura ba. Yanayin abincin gidan ne kawai ya lura ya canza, kuma ya fi jin dadinshi a kan na baya. Kuma da yake Allah ya yi shi mutum mara sa ido ko bin kwakkwafi, bai taba tankawa ba. Sakin ciki yake ya ci iyakar cinsa.
Karatu fal! Ya yi wa Aalimah fintinkau, ya wuce ta, an bada assingments har ba adadi ba ta yi ko daya ba. Absentness dinta da ya yi yawa shi ya sa coordinator dinsu da wasu daga cikin course tutors suka ankara. Makarantar ta yi tracingguardian phone number dinta a file dinta suka yi mishi phone call officially.
Ina kwalin digiri da masters din Mummy Zulaiha ya je ta manta da hakan zai faru? Oho! She’s blindly chasing a way to push poor Aalimah from her house. Ta manta an ce rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya.
Karfe biyu na rana Aalimah tana kwashe abincin da ta gama girkawa a warmers, Mummy Zulaiha tana sama bedroom dinta tana barci abinta hankali a kwance. Kuka ta ke yi mara sauti tana share hawaye da hanci da gefen mayafin da ke kanta. Ba tana kuka ne don aikin da Mummy ke jibga mata ba wanda ko makaho ya shafa ya san ya fi karfinta ita kadai, ko kukan yadda ta kasa treating dinta kamar ‘ya’yan da ta haifa ba, tana kuka ne na tausayin kanta da iyayenta. Sun hana idonsu barci, sun yi fafutuka sun kawo ta don ta yi karatu an raba ta da shi a banza a daidai lokacin da ta fara fahimtarsa, kwakwalwarta ta bude ya soma shiga kanta, an maida ta boyi-boyin gida on no reason. Ba ta son zama sanadin kawo commution tsakanin ma’auratan, amma da ta ce da kawunta ya maida ita hostel tunda ita ta fahimci Mummy Zulaiha zamanta a gidan ne kawai ba ta so.
Ba zato ba tsammani sai ganin Daddy ta yi a tsaye a bakin kofa, ya dogara hannunsa na dama da kofar kicin din. Ta yi nisa a kukanta, shi ya sa ko motsin motarsa ba ta ji ba.
Daddy ya jima a tsaye a bakin kofa yana kallon Aalimah ba tare da saninta ba, ba kuma tare da sanin shi kansa mintuna nawa ya ba ta a wurin yana nazarin abubuwan ba. An ce four weeks rabonta da school, ya zo ya same ta tana girki a kitchen. Wannan na nufin duk abincin da suke ci tsawon sati hudun da ya fahimci canzawarsa ita ce ke girka shi? Wannan ne dalilin Zulaiha na korar mai aikinta, ta kuma hana shi daukar driver da ya ce zai daukar musu? Ba ya so ya yardar wa zuciyarsa Zulaiha ta aikata hakan da gan-gan, kuma za ta iya cin amanarsa har haka.
Ba zai yi saurin yanke hukunci ba sai ya ji daga bakin kowaccensu. Shigowa kicin din ya yi ya kama hannunta ya ja ta suka fice daga gidan, kafarta ko takalmi babu. Da fari ta tsorata, amma da ta ga Daddy ne sai ta yi shiru. Kukan ma bakidaya ya dauke. Ta san yau dubun Mummy ce ta cika tunda yanzun ba lokacin dawowarsa ba ne. Za ta yi amfani da wannan damar ta roke shi ya maida ita hostelno matter what. Yau da a ce zama ne ya kawo ta gidan ba karatu ba, she’s willing to do beyond what Mummy wants from her… ita ma uwa ce a gare ta kuma uwarta ma tana sa ta aiki, amma ba ta hora ta da yunwa. Daddy murfin chevrolet dinsa ya bude ya sanya ta a gaban motar, ya zagayo ya shiga mazauninsa a nitse ya fita daga compound din gidan nasa suka hau titi.
Sun yi tafiya mai nisa ba tare da ya ce komai ba, ita kuma ta yi kokari ta daina kukan da ta ke yi ta tsane hawayen idanunta tsaf! Amma kallo daya za ka yi mata ka fahimci ta ci kuka ta koshi, abinka da farar mace, fuskar nan ta yi jazur kamar jini zai fito. Sai daya yi nisa da unguwar su ‘Martha’s Vineyard Real Estate’ sosai sannan ya gangara ya sauka a gefen titi.
Yadda fuskarta ta yi jajawur saboda kuka haka tashi ma ta yi, duk da shi ba kukan ya yi ba. Tsananin bacin rai ne ya maida shi hakan. Ba Zulaiha kadai ya ji matukar haushi ba, har ita Aalimahn. Cikin fada ya soma yi mata magana cikin harshen su Temachek. Ga abinda yake cewa.
“Me yasa baki gaya min ba ta kai ki makaranta ba?â€
Shiru ta yi, don ba ta san amsar da za ta ba shi ba. Mummy ba ta bata damar hakan ba, ‘ya’yanta ma sun kasa gaya masa balle ita? Idan ya dawo Mummy kasawa ta ke ta tsare har sai ta tabbatar ya shiga dakin barcinsa ya kwanta. Ko ba don wannan ba baza ta iya hada shi fada da matarshi da ta zo ta same su suna zaune happily da ‘ya’yansu, sannan tun washegarin ranar da Mummy ta ce zata dinga driving dinsu ta karbe wayarta data bata daga cewa za ta debi wasu muhimman contacts dinta da ke ciki, ba ta dawo mata da ita ba, and she lacks the courage to ask her again (bata da karfin gwiwar sake tambayar ta) tunda ta san wayarta ce.
Ko iyayenta da Yaya Aboubacar ba ta kira ba a tsayin kwanakin nan kusan talatin. He trust his wifeso much(ya yarda da matarsa sosai) ta yadda har ya daura mata alhakin kai su da dauko su.Howcould she told him that his wife is a green snake? (Ta yaya zata iya gaya masa cewa matar tasa macijin sari-ka-noke ce?â€.
Jin ta yi shiru,sai ajiyar zuciya kawai take yi, sai kuma ya sassauta daga fadan da ya ke yi mata.
“Gaya min kin ji ‘yata Aalimah, me ke faruwa a gidan da ban sani ba? Ya ya aka yi kowa yana zuwa makaranta banda ke? Kada ki ji tsoro ki gaya min ba abin da zai same ki. Sai na ji gaskiya daga bakinki ne zan san matakin da zan daukaâ€.
Sosai ya ke lallashinta, yadda Daddynta ke yi in yana so ya ji cikinta. Kuka ne ya kufce mata, ta soma yinsa sosai.
“Na roke ka da Allah Daddy ka maida ni hostel, Daddy da Mama zuciyarsu za ta karye, in na kasa yin karatun nan. I’m not here to stay at home. I’m here to study, don Allah Daddy â€.
Shiru ya yi zuciyarsa har barbawa ta ke yi sabida bacin rai. Daga bisani ya ce,
“Ina wayarki? Me ya sa ko text ne ba ki yi min ba in kin kasa kira na?â€
Cike da fargabata ce,
“Ta karbi wayartaâ€.
Wuta ta dauke masa na dan lokaci, kafin ya ce cikin sanyin murya.