AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

“I’m sorry my daughter, I failed to fulfill my responsibilities as a father. But that doesn’t mean negligence, it’s because I trust my wife so much on everything, (ki yi hakuri ‘ya ta, na gaza wajen cikasa hakkokina na Uba a gareki cikin gidana, saidai hakan baya nufin ‘sakaci’, a’ah, na yi ne sabida na yarda da mata ta akan komai. Ban taba zaton za ta iya yi min haka ba.
Na san ba ta son mutane, amma ban zaci har haka ba tunda ba yau muke tare ba. Kada ki kara zancen hostel din nan while I’m alive, living in America. In mutane ba su zage ni ba, Allah zai tambaye ni hakkin zumunci. Sai ka kyautata shi za ka shiga aljannah. Give me one last chance…(ki bani dama ta karshe)zan gyara komaiâ€.

3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM – Buhainat: 🌹 Aalimah 🌹
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
07030137870*

FREE PAGES 5

Tsakaninsa da Aunty Zulaiha babu mu’amala mai dadi, duk wannan soyayyar da ake masa an yi wurgi da ita. Yana tambayar kansa da ma haka ta ke? Ita shin meye matsalarta da zaman ‘yar dan uwansa ciki daya a gidan? Shi ya sha nono ya sakarwa ubanta! Inda hankali da tunani Zulaiha ba za ta yi masa abin da ta ke yi ba don ya kawo ‘yar Mansour gidansa. Wacce irin kulawa ce ba ya bawa nata dangin? Yana son Zulaiha matukar so ta yadda har ake ganin ta fi karfinsa. Amma wannan karon ya sha alwashin motsa kwanjinsa ba zai bari ta juya shi ba when it comes to Mansour. A kan komai ta yi ta yi, amma ban da wannan dan uwan.
Ita da kanta Aunty Zulaiha ta fara gajiya da irin zaman da ta ke yi da mijinta da ‘ya’yanta a kan wata banza Aalimah. Walwalar gidan completely reduced. Ga shi duk yadda ta so ya kwantar da kai ya lallashe ta ya soma ba ta excuses a kan zaman yarinyar tare da su ya ki yin hakan. Ta fahimci ma makarantar da zai kai Basma tare ya kai su wanda ke nuna babu ranar barin ‘yar Mansour gidan.
Dole ta sauke makaman yakinta ta nemi sulhu da shi, maimakon ya ba ta excuses ita ce ta dawo tana bayarwa. Tana gaya masa ita ba danginsa ne ba ta so ba, she don’t want the house to be bulky (bata so gidan ya cika) sannan yaranta za su matsu, dakin ya yi musu kadan, sannan a budget dinsu na abin da suke spendingmonthly babu karin komai, in karatu ta zo yi America ya maida ta hostel za ta fi maida hankali ta yi karatu sosai.
Wannan karon ma banza ya baiwa ajiyarta, yana tauna silly(wawayen) maganganunta a ransa, ko daya babu gamsasshe. Halinta ne dai da ya sani na rashin son mutane ba danginshi kadai ba har nata ma ba su ishe ta kallo ba, yadda shi yake zumunci da ‘yan gidansu da iyayenta ita ba ta yi.
Aunty Zulaiha dai ta ga babu mafita, wankin hula zai kai ta dare dole ta dawo ta lallaba abinta, ta ce ta yarda Aalimah ta zauna, amma a bude mata rufaffen dakin Mu’azzam da ke kasa ta koma, akalla dai su Basma ba su matsu ba.

Wannan karon ne ya dago manyan idanunsa na IYALAN RAAZEE da suka gigitata, ya dube ta da su da kakkausan kallo. Sun kada sun yi jazir. Sosai ta razana, don bai taba yi mata irin wannan kallon ba, in ba ta yi kuskure ba sai ta ce har tsana-tsana (hatred) ta hango a cikin kyawawan idanun da suka rudeta ta fada a makauniyar soyayyarsa.
Ya dade yana mata kallon har sai da ta ja baya don tsoron kada ya kai hannunsa gare ta.
“Da abin da na haifa, da wanda Mansour ya haifa daya ne a wajena, babu bambanci. You can book an apartment for rent in wannan ya muku kadan ke da ‘ya’yan nakiâ€.
Duk inda Aunty Zulaiha ta ke tsammanin Ishaq Razee a kan zaman Aalimah a gidansa, sai ta same shi ya wuce nan. He’s no longer the Ishaq she know, father of her children, apple of her eyes…! Mene ne abin yi a gare ta? Surrender! Zuciyarta ta ba ta amsa, wato sallamawa ga zaman ‘yar Mansour a tare da su. Ta yi amfani da wata hikimar daban ban da tursasawa.
A sati na biyu, kwana goma sha hudu da zuwan Aalimah America ta fahimci wani abu, Aunty Zulaiha ta canza mata sosai, tana janta a jiki in har Daddy na gida ko yana zaune a waje. In ba ya nan kuwa kashi ma ya fi ta daraja.
Maganar da ya gaya mata ta cewa;she can book a rent with her children (zata iya kama haya itada ‘ya’yanta idan gidan ya musu kadan) a kan Aalimah ta tsaya mata a zuciya, ta kuma sanya mata TSANARTA. A da, ba tsanarta ta yi ba, apparentlybako ne ba ta so a cikin gidanta. Amma reactions dinsa da amsoshinsa gare ta sun nuna yana son ‘yar dan uwansa kamar, ko ma fiye da yadda yake son ‘ya’yansa. Wani abu da zuciyarta ta gaza dauka, ba kuma za ta iya dauka din ba.
Duk kokarin Aalimah na kin sanya damuwa a rai don tana da masaniyar yadda ta illata kwakwalwar mahaifiyarta dole ta fara damuwa da halayen Mummy Zulaiha. Tana riga kowa fita a gidan saboda banki, amma duk suna riga ta dawowa. Duk walwalar da ta ke ciki da ta jiyo horn din motar Mummy, gabanta zai yanke ya fadi, ta soma neman inda za ta adana kanta.
Basma da Khaleesat suna da hankali, kuma zuwa yanzu sun lura Mummy is not happy any more da zaman Aalimah tare da su. Musamman suka same ta a daki suna lallashinta kan ta karbi Aalimah, she’s nice, she’ll come to like her too(tana da kirki, itama zata so ta) idan ta saki zuciyarta da ita. Ba tare da sanin Aalimah ba.
Ce musu ta yi su tashi su ba ta wuri, ita ina ruwanta da wata sister dinsu? Ko a kanta ta ke zaune?
Sosai ta saki rai da Aalimah, har da tsokana in Daddy na zaune. Rannan ta ce masa ma ya ba ta kudi za ta yo mata shopping ta lura akwai abubuwan da Aalimah bata da su. Dadi ya ji har ransa ganin ta fara son farin cikinsa.
A hankali yake nuna mata Aalimah yarinyar kirki ce ta ba ta dama ta fahimce ta, ba zai kawo wadda za ta cutar da su ba, above all jini ba wasa ba ne, jinin da ke yawo a jikin Aalimah, shi yake yawo a jikin ‘ya’yanta. Ta bude zuciyarta ta so mutane, mutum rahma ne, kuma falala gare shi. Duk da cewa zama da shi da wuya. Amma in kayi katari dana kirki rahma ne a gareka. Ya gaya mata irin canjin da yaransu ke samu tun zuwan Aalimah, yanzu har Yesmin ba ta bari sallah ta wuce ta.

Maimakon zuciyarta ta yi sanyi, sai ta kara zafafa ta fusata fiye da kima. Is she here to study, or to distort her children? (Ta zo karatu ne ko ta zo canza rayuwar ‘ya’yanta?) Amma ta hadiye ta kuma ba shi hakurin rashin fahimtar ta. Credit card dinsa ya bata ma gabadaya na bankin (Well Fargo) ya ce ta ciri duk abin da zai isa ta yi musu siyayyar dukkaninsu har ita.

A daren ranar bayan an yi dinner suka koma kan kujerun falon suka zazzauna. Mummyn aiki ta fara yi cikin system dinta ba ta kallonsu. Daddy news yake kallo a tashar Aljazeerah, ya canza ya mayar CNN. Basma na danne-danne cikin Ipad dinta, Khaleesat alqur’ani ne a hannunta tana manne da Aalimah wadda ita kuma text book ne a hannunta tana duba course din da suka yi yau, littafin introductory ne ga fanninta na harhada magunguna, in Khaleesat ta karanto aya cikin suratul Yasin, sai ta ci gyaranta ba tare da ta duba Qur’anin ba ita. Idonta na kan littafin hannunta.
Yesmin ta ce, “Aunty Aalimah, yaya ma ki ka ce addu’ar shiga toilet? Zanje nayi fitsariâ€.
Ta ce, “Allahumma inni a’uzu bika minal khubsi wal khaba’is. In an fito kuma a fito da kafar dama a ce, Gufranakallahummallazee azhab anniyal azaaâ€.
Yesmin ta maimaita, sannan ta nufi bandaki da gudu. Bayan ta dawo kowa ya ci gaba da abin da yake yi, kamar daga sama Yesmin ta sake cewa,
“Mummy ina dankwalinki? Ba kyau zama ba dankwali. Dubi yadda Shaitaan duk ya bi ya yi miki fitsari a kaâ€.
Ai kuwa kowa ya cira ido ya dubi Mummyn, har Daddy, sai a lokacin ya lura duk cikinsu babu wadda ba ta daure kanta ba sai Mummyn, kuma ya san da ba haka suke ba. Dariya ce ta kama shi, yadda Mummy ta yi wani kicin-kicin da fuska tana kallon Yesmin kamar ta kai mata mangara. Wai ita ce kanta da fitsarin Shaitaan? Tabbas a bakin Aalimah ta ji wannan nassin. This is not her words, beside(wadannan ba kalaman ta bane, tukunnama) yaushe ma dukkaninsu suka koyi daura kallabi? Oho! Ko silin gashinsu daya babu a waje, sun bi sun dukunkune abinsu cikin hula. Ba ta ce mata komai ba ta ci gaba da abin da ta ke yi, zuciyarta a cunkushe. So she want to change her chindren to total ‘yan kauye as she is ko me? Ba ta son shisshigi da katsalandan cikin al’amarin ‘ya’yanta, ina dalili? Aalimah must go! She cannot take it.
Tun zuwanta sau daya ta yi magana da gida, shi din ma da wayar Daddy. Ta nemi wayarta ta rasa sama ko kasa, ba ta sani ba can wani loko a cikin kayanta ta shige. Cike da kauna Daddy ke dubansu tana ma Khaleesat kari da ka, ba tare da ta duba Qur’an ba har suka gama. Khaleesat ta karanta Fatiha suka shafa. Cewa ta ke gobe za ta bai wa Shaikh (Malaminsu na islamiyya) mamaki, ta iya inda zai dora musu tun kafin kowa a ajin ya iya. Wata islamiyya Daddy ya kai su ta mutanen Libya in sun taso daga boko. Khaleesat ta haye sama tana fadin bacci ta ke ji, bayan ta sumbaci iyayen daya bayan daya.
Ya ce, “Aalimah kina kiran su Aboubacar kuwa kuna gaisawa? Dazu Mansour ya kira ni ina office ya ce in ba ki, ni kuma lokacin bana gida, na ce masa in na dawo I will check on you, me ya sa ba kya kiransu?â€
An tabo mata babbar damuwarta a dan tsukin. Ta sunkuyar da kanta, ta ce, “Daddy, tunda na zo ban ga waya ta baâ€.
Fada ya hau ta da shi, ya ce, he’s no longer her Dad kenan, tunda har ba ta da waya tsayin wannan lokacin ba ta bude baki ta gaya masa ba. Hakuri ta shiga ba shi tana fada masa ta san wayar ba bata ta yi ba, wani wajen ta jefa ta ta manta.
Ya dubi Aunty Zulaiha ya ce, “Yaushe za ku je shopping din ki sama mata waya?â€
Ta ce, babu damuwa za ta ba ta daya daga cikin nata kafin su je, sai weekend za su fita.
A gaban Daddy ta cire layin daya daga cikin kan wayoyinta guda uku, ta bai wa Aalimah. Hannu bibbiyu ta karba ta yi godiya.
Ya ce da Basma gobe kafin su fita ta kunna mata WiFi dinsu, ta kuma saya mata credit in sun fita gobe.
Sallama suka yi wa iyayen suka wuce dakinsu har Yesmin don su kwanta. Babu mai yin latti a cikinsu. Ta lura duk al’ummar kasar ma babu lateness cikin dictionary dinsu.
A washegari Basma ta sayi layin ta sanya mata, ta loda mata kudi. Yau ba su yi lecture da yawa ba suka koma gida. Ko abinci ba ta ci ba sai da ta kira kowa nata da sabon layinta. Duk ta haddace lambobinsu a kanta. A karshe ta kira Mahmoud, yana zaune a office dinsa cikin ma’aikatar hukumar zabe ta Katsina a lokacin, aiki ya dan ragu masa, ya dafe kai a kan tebirinsa. Ba tunanin komai yake ba sai na Aalimah. Tunda ta tsallaka Amurka bai kara jin duriyarta ba, she didn’t give him a call as she promised (bata kira shi ba kamar yadda tayi alkawari). Ko ta samu dadin duniya ne ta manta da shi? Ya sani tun tafiyar Aalimah, wata zuciyar na gaya masa ya yi wauta, babbar wauta kuwa da ya bari ta tafi ba tare da gamsasshiyar magana a tsakanin iyayensu ba.
Aalimah a Nigeria ma zubinta na ‘ya’yan manya ne, balle ta haura Amurka. Ko kadan ransa bai son wannan tafiyar, don dai ba yadda zai yi ne, tunda bai isa ya hana iyayenta iko da ita ba, tunda ba aurenta yake ba. Sai dai wani saqo can na zuciyarsa na gaya masa… this is the deadly mistake(kuskure mafi muni) da ya taba yi a rayuwarsa, babu wanda ya san da zancensa da Aalimah daga nasa iyayen har nata. A hakan kuma wai yana jira ta dawo ya aure ta. Yaushe? Ta wacce hanya?Kuma a ina? Sanda zata dawo ta kara shekaru da sanin ciwon kanta. Za ta iya haduwa da wani ya karkatar da zuciyarta daga gare shi… ‘NO!!!†Ya fada da karfi, tare da naushin tebirin da ke gabansa. Yana da kyakkyawan zato a kan, Aalimah, duniya ba ta gabanta. Za ta rike soyayyarsu da amana no matter what ya yarda da wannan!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button