AALIMAH HAUSA NOVELNOVELS

AALIMAH HAUSA NOVEL BOOK 1, 2,3, & 4

AALIMAH HAUSA NOVEL BY SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI

Wayar da ke gefensa ce ta hau ruri, ta yi har ta katse, ta sake ci gaba kafin ya dauka. Lambobi ne rututu irin na kasar waje. Wani sanyi ne ya tsirga a zuciyarsa, ya amsa da sauri.
“Aalimah!â€
Ya fada in exclamation.
Bai ba ta damar cewa komai ba ya dora, “You keep me anxiously waiting(kin barni inata jira cike da taraddadi) kwana ashirin da daya, Na dauka ma kin manta da niâ€. Ya fada da karyewar sauti.
Sosai ta ji tausayinsa ya kama ta, ta san yadda Mahmoud ya damu da ita, yake kuma sonta ita ko rabin hakan ba ta masa. Tunda ta zo ba za ta ce ga lokacin da ta ware ta zauna don ta yi tunaninsa ba. She justadmires him, she likes him,because he has brain.(Kawai tana son shi sabida hazakarshi). Haka nan tana jinsa a ranta sakamakon shakuwar da suka yi da shi na shekara guda a gidansu. He is good and well-mannered (yanada kyawawan dabi’u).
Sanda za ta taho a waya suka yi sallama, ya tada hankalinsa sosai, kiris ya rage ya yi mata kuka. Ya ce, tsoro yake ji, tsoron rasa ta. He’s afraid, and he don’t know WHY?.
Murmushi ta yi, murmushin nan nata mai nutsar da zuciya, duk da Mahmoud ba ya ganinta ya ji sautin murmushinta. Shekarunta goma sha shidda, amma ma’abociyar tsinkaye ce, amma tsinkayenta bai taba tsinkayo mata akwai abin da zai sa ta ki Mahmoud ba, ko ta juya masa baya. Cewa ta yi da shi,
“We cannot run-away from our destinies, but I’m hoping that destiny tied us togetherâ€.
(Bazamu iya gujewa kaddarorin mu ba, amma ina fatan kaddarar ta bar mu tare).

Wadannan sune kalaman Aalimah da yake kwana ya tashi da su tun tafiyarta, zuciyarsa na yi musu fassara kala daban-daban, mai dadi da mara dadi. Wannan ne yanayin da yake ciki har zuwa yau da ya samu kiran Aalimah. Ya lumshe ido ita kuma ta yi ajiyar zuciya. A hankali ta shiga warware masa dalilin da ya sa ba ta kira shi ba tun zuwanta, she lost her phone, she has been busy with school, (ta rasa wayar ta, tana cikin hidimar makaranta) ko su Mama ba ta kira ba sai yau.
Ajiyar zuciya ya yi, ransa ya yi masa dadi. At least Aalimah ba ta manta shi ba bayan shigarta USA. Suka shiga hira ya gaya mata har Aboubacar ya kira don ya samu lambarta ya gaya masa su ma da lambar kawunta suke magana da ita, ya san in ta nutsu za ta kira shi. Ya kara da yi mata nasiha kan ta kama kanta a kan wanda ya santa da shi, shi in son samu ne ma ta dinga sa hijabi da niqabi he’s always afraid bai san dalili ba.
Dariya Aalimah ta yi a ranta tana tunanin ta ya ya wani zai ce yana sonta a nan? Duk abin da yake hange ba haka yake ba, ga ‘yammata nan birjik masu mugun kyau da ya dame nata ya shanye, abin da ta lura ma kowa is busy with himself a nan ba ruwan wani da harkar wani in ba wani naka ba. Hijab kuma ai ba sai ya sa ta ba tana sa abinta (a lokuta da dama) duk da kanana ne, amma ta san shigarta is fully Islamic.
Sai da Khaleesat ta shigo tana kiranta, sannan suka yi sallama da Mahmoud ta kashe wayar gabadaya. Ba ta da ra’ayin shiga kowanne‘social media’ don yanayin karatunta, sannan kuma, ba ta son hayaniya, ba ta da ra’ayinta.
Ranar asabar da safe Aunty zulaiha ta gaya musu su shirya za su je shopping da yamma kuma za su shiga kasuwa. Daddy na gefe yana ta ‘making calls’, amma ya ji ta. Bayan ya gama ya dube ta da murmushi ya ce,
“Umm Mu’az, ki kai su inda za a samu ready-madeAfrican wears ki saya wa kowa yadda ta ke so, sun gaya min sun daina saka wando, sai ki hada musu da Arabian gownsâ€.
Cikin mamaki Mummy Zulaiha ta dago ta dubi Khaleesat, sannan Basma da Yesmin ta ce, “Dalili? Are we in Africa or what?â€
Duk suka yi shiru suka sunkuyar da kai ganin yadda ta fusata ainun. Gab ta ke da ta kai musu duka. A nitse Daddy ya bi ta da ido yana son karanto matsalar matarsa a dan tsukin nan,she becomes pepper-tempared. Shin ita wace irin uwa ce da ba za ta iya bambance abu mai kyau da mara kyau ga ‘ya’yanta ba? Al’amarin Mu’azzam bai isa ya zama iznah a gareta ba? Me suka yi abin bacin rai a nan?She’sgetting angry easily a dan tsukin nan duk da yadda yake kokarin kyautata mata don ta kara sakin ranta da Aalimah.
A nutse ya ce da ita“I think you are supposed to be happy, they are trying to adopt their native culture (Na yi tsammanin farin ciki zakiyi, suna kokarin daukar al’adun su na gado) su ajiye wannan mara tushen?â€
Tashi ta yi fuuu! Ta bar falon ba tare da ta ce da shi komai ba ganin yadda yaran gabadaya suka zuba mata ido har Aalimah.
Safah da marwah Mummy ta shiga yi a dakinta. Tunanin hanyoyin da za ta bi ta kori Aalimah daga gidanta ta ke yi from every direction ta rasa. A karshe ta samu guda daya, duk da ba ta da tabbacin dorewarta da sahihancinta..
Kafin yamma ta yi kokari ta saki ranta. Yau ita da kanta ta shirya musu abincin rana. Aalimah ta zo tana so ta taimaka mata don ta aiki Easther ta ce ta wuce ta ba ta guri, ba ta son karambani. Su Basma da ma ba abin da suka tsana irin aiki, don haka ko kusa ba sa dosar kichin in ba wani abu za su dauka ba.
Easther na dawowa ta kira ta gefe, ta sallame ta da kudi masu yawa, ta ce da ita daga yau ba ta bukatarta, ta je ta nemi wani aikin, amma duk sanda ta ke bukatarta za ta yi mata waya ta dawo. Easther har da kukanta, domin ba karamin sabawa ta yi da gidan aikinta ba da iyalin gidan bakidaya. Su din masu karamci da kyautatawa ne a gare ta. Amma tunda Mummy ta ce za ta dawo da ita wani lokaci she will go home, and wait. Amma ba za ta iya neman wani aikin ba. Kudin da Mummy ta ba ta za su iya rike ta da mahaifiyarta har tsawon shekara daya.
Asabar da lahadi Daddy ba ya zuwa ko’ina. Haka kawai ya yideciding ya bi su kasuwar kan a barshi shi kadai a gida. Ba tare da ya gaya wa Mummy ba. Sanda ta ke shiryawa sai ta ga shi ma yana shirin fita. Ta tambaye shi zai je wani wuri ne, ya yi mata shiru don ya ji haushin abin da ta yi masa dazun a gaban ‘ya’yansa, amma dubi kamar ba ita ba, yanzu wai har ta manta. Kananan kaya ya saka wadanda suka zaftare shekaru ashirin daga hamsin din da yake da su kai ka ce balaraben kasar Misra ne. Zulaiha kasa jurewa ta yi, ta yi azama ta rungume shi ta baya yana dab da ficewa daga dakin. Hakuri ta shiga ba shi ta ce tana bisa umarninsa, za ta yi duk abin da ya ce ta yi. Kwace jikinsa ya yi, ta sake kamo shi.
“Daddy please…†Ta marairaice masa yadda ta san ba ya iya jurewa. Ya ce,
“Na nawa kuma Zulaiha? Sau nawa za ki yi min laifi ki ce in yi hakuri in hakura, amma gobe ki sake? Wait, I want know your problem(ina son sanin menene matsalarki) cikin kwanakin nan. Da fari kin ce zaman Aalimah ne da yaranki, you then come and said you regretted hurting me with this, you accepted her. And now, what’s bothering you? I failed to get you right, please make it clear to me (kika dawo kika ce kinyi nadamar bata min rai akan hakan, kin karbe ta cikin ‘ya’yanki, yanzu kuma, me ke damun ki? Na kasa fahimtar ki daidai, don Allah ki fahimtar dani abinda ke ran ki)â€.
Hakurin dai ta ci gaba da ba shi kwando-kwando. Bayan shi ba ta san da wacce kalma za ta yi masa bayani ya fahimta ba. Ya fahimci she doesn’t want a STRANGER close to her family (bata son BAKO cikin iyalin ta). Cewa zai yi Aalimah is not a stranger she’s part of him. Ita kuma ‘Da’ in ba ita ta haife shi ba, to ba Da ba ne a gurinta, tunaninta daban, ra’ayinta daban da na kowa. Kai ka ce haifaffiyar Amurka ce iyaye da kakanninta sabida dabi’u da akidojinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button