Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
AFRA KO AMRAH HAUSA NOVEL

AFRA KO AMRAH 3-4

Da dare guraren qarfe goma sha biyu kowanen su bacci yake abinsa cike da kwanciyar hankali.

A hankali farhan yake bude idon shi sbd yanda yaji jikinsa kamar wanda aka d’ad’d’aure,
gabadaya yaji sa a tamke ga kuma yawan motsi da yake ji a d’akin yunqurawar da zai yi ne yaga tabbas kuwa a d’aure yake har ma ba ta yanda za’ayi ya iya wani qwaqqwaran motsi,kallon d’aurin da aka masa yake cike da tsananin mamaki shin ta yaya hakan ta faru,waya masa haka ⁉
Idon sa yakai kan gadon Afrah wayam ba kowa ya kuma kalli gefen sa ba Amrah sosai hankalin sa ya qara tashi kan yayi wani yunquri yaji kukan Afrah an fito da ita a dayan daki aka shigo da ita d’akin da yake tare da kunna wutar dakin,
Afrah na ganin shi ta fara kuka sosai tana zille zille tare da miqo hannunta tana so farhan ya cece ta,
su kuwa sai janta suke zasu bar d’akin da ita,yayinda farhan ke yunqurin ya kunce kansa amma ya kasà gashi kad’an ya rage su fita da ita hakan yasa ya fad’o kan bed yana son yaja jikinsa da sauri yaje ya kar6o Afrah,
amma hakan ya gagare shi sbd hannayen sa a baya suke kuma a daure haka ma qafafuwansa a daure suke,
da qarfin tsiya ya yunqura hade da wani irin nishi yayinda aka kashe wutar dakin wanda yayi dai dai da tashin qarar bindiga………kamar had’in baki farhan da Afrah suka tashi firgigit daga bacci wanda hakan ya nuna kowanen su ya tashi daga mummunan mafarki,a rikice farhan ya kai dubansa kan gadon Afrah kamar yadda ita ma Afrah take kallon nasu gadon,
Da gudu ta sauko kan gadon ta nufo gurin shi tare da fad’awa kan jikinsa,
jikinta sae qyarma yake shi kuwa farhan jikinsa ne yaji ya mutu ya qara matse Afrah a qirjin sa ya shiga shafa sumar kanta a hankali sae dai tunani ne fal a ransa yayinda yake tuna fuskokin mutanen da ya gani a cikin mafarki tabbas a zahiri yasan wad’annan fuskokin, kuma yasan mugun nufin su a kanshi,
shiyasa ya shiga fargaba sosai kar mafarkin sa ya zamo gaskiya”saukar hawaye yake ji kad’an kad’an a qirjin sa tare da jin sautin kuka,
wanda shine ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yake ya kalli Afrah da ke lafe a qirjin sa hawaye na ta faman zarya a kumatun ta,
tana kuma fitar da sautin kuka a hankali,
sannu a hankali farhan yakai hannu yana share mata hawaye yana kuma tunanin shin ita kuma Afrah wane irin mafarki ne ya firgita ta har take yin kuka.
Gashi bai iya maganar kurame ba bare ya tambaye ta,
Amrah ce ta iya kuma bacci take.
Lallashin ta kawai ya shiga yi ta hanyar bubbuga bayan ta,
har ya samu tayi shiru ta kuma qara lafewa a qirjin sa alamar tayi bacci.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button