AFRA KO AMRAH HAUSA NOVEL

AFRA KO AMRAH 1-2

????1⃣????
Zaune yake a office dauke da kyakkyawar yarinya maqale a kafadar sa wacce shekarun ta baza su wuce four to five yrs ba sai bacci take abin ta shikuma yana faman cike ciken wasu takardu.

Gayen ya hadu sosai wanda kallo daya zakayi masa kasan dan hutu ne.
Kuma komai na sa a natse yake yinsa.

Wani gaye ne ya shigo office d’in da sallamar sa shekarun sa baza su fi 27yrs ba duk dai en tsara ne kuma da alama en uwan juna ne sbd suna dan da kama.
shigowar gayen keda wuya ya ajiye aikin da yake tare da amsa sallamar sa yayinda fuskar sa ke dauke da alamar murmushi.

Wanda ya shigo ne ke cewa “Doctor farhan sae aiki kake ta faman yi da Afrah maqale a kafada,se faman bacci take baza ka ajiye ta ka huta ba”
doctor farhan yayi murmushin da ke qara masa kyau yace “fu’ad kenan ai kasan Afrah haka take ko yaushe tana maqale a jikina har dai idan zatayi bacci ba makawa sae kan jikina take samu baccin ya dauke ta.
Kuma zancen ajiye ta na huta ko naso hakan idan baccin ta bai yi nisa ba zata farka ne idan taji zan ajiye ta,sauqi na daya Afrah bata da nauyi abin har mamaki yake bani dmn komai tsawon lokacin da nayi dauke da ita bana jin na gaji, idan kaga na ajiye ta ba wai don na gaji bane se don zanyi wani aiki.
Fu’ad ya nisa hade da fadin lallai Afrah najin dadin ta,inace dai bata hana ka sake wa da amaryar ka Amrah? Nop ko daya.
Yauwa haka nake son ji ace Afrah na bata takura kowa,ya fadi haka ne tare da d’ora ledar sweet kan desk yace ga sweet na saya ma sweet Afrah ita kadai bada Amarya ba dmn bana
son a sakawa Afrah rani, idan amarya na buqata angonta ya saya mata,farhan yayi murmushi yace “bazan siya ba kuma sae ta sha na Afrah,kai ita ma zata fara sha kafin Afrah.
Fu’ad yace “cab bazan yarda da haka ba Afrah dai zata fara sha” ya fadi haka ne tare da kiran sunan Afrah kusan sau uku bata motsa ba.
Farhan yayi murmushi yace “tank God da yasa yau en jin basa kusa da ka tayar min da ita,kamar ya en jin basa kusa? Kai fu’ad kar ka ce min baka san Afrah bata ji ba she is deaf,au haba meyasa idan aka mata magana take dagawa mutum kai alamar taji?eh tana ji wani lokacin amma rashin jin ta yafi yawa kuma d’aga kan da take,
ka fahim ce ta da kyau idan kana magana bakin ka take kallo ta hakan ne take samu ta baka amsar abinda kace,
ikon Allah to kace tana ji wani lokaci,
kenan har da magana tana yi a wannan lokaci? Bata iya magana kawai dai bakin ta na motsi kamar tace wani abu se ta kasa,amma idan tana kuka ka rantse da Allah tana ji,kukan tsaf yake fita kamar ba na deaf ba haka ma dariyar ta.
Fu’ad yace Allah sarki to baza ka kaita a duba ta ba,,fu’ad ai kasan bazan bar Afrah haka kawai ba, abun ne ya faskara amma ko yaushe cikin shan magani take,kamar Amrah.

Ka ce dai blind & deaf kake fama da su a gidan ka…kai! waye blind?ai ka fini sani, au dama cin mutunci ne ya kawo ka a office dina,wane cin mutunci ai gaskiya na fada Amrah bata gani sae da glass,to shine zaka kirata blind,bazan kirata blind ba kuwa tunda da zarar ta cire glass bata ganin komai,….wa ya gaya ma Amrah kam tana ganin shadow,….ahaf shadow din da ko ta gan shi kwata kwata bata fahimtar na mene ne,to na dai ji koma yaya ne ina sonta a hakan,ai an san kana son ta a hàkan tunda ka aure ta,ya fadi haka ne tare da miqe wa tsaye yace “ni zan tafi na san patient na can na faman jira na,idan kaje a gaida amarya,
farhan ya gyada masa kai yace inshaAllah zata ji sannan fu’ad ya fita.

Fitar fu’ad keda wuya Afrah ta fara motsawa a hankali.
Farhan ya maida ta kan cinyar sa,
tayi saurin sauka tare da jawo hannun sa tana nuna masa toilet hakan yasa farhan ya fahimci fitsari take ji.
Ya tallabeta cak yakai ta toilet tayi fitsari suka fito.
Ya dora ta kan cinyar sa tare da jawo food flask,ya zuba mata abinci ya shiga bata a hankali har taci ta qoshi ya bata ruwa tasha hade da zaro tissue ya goge mata dan qaramin bakinta.
Ya lotsa en yatsun sa kan kumatun ta se kawai naga tayi murmushin da ya bayyanar da dimple in ta,sannan ita ma ta kai hannu ta lotsa en yatsun ta a nasa kumatun shima yayi murmushin da haqoran sa farare tas suka bayyana.
Mayar da Ita yayi kan desk suna fuskantar juna ya dauko ledar sweet ya miqa mata tare da fadin uncle fu’ad ne ya ce a baki,
Shiru ta mishi tana kallon shi sbd bata fahimci me yace ba, sake maimata maganar yayi yayinda ta tsure bakin sa da kallo,a nan ta fahimci me yake cewa,yayinda ya dauko dayan sweet yana bude mata.

Cike da murmushin jin dadi irin nasu na yara ta kai hannu ta kar6i sweet din da farhan ya bude mata ya miqa mata ta kar6a.
Ta hade tafukan hannyen ta alamar thank u sannan ta saka sweet din a bakin ta se shillo take da en qafafuwanta,farhan ya kai hannu ya gyara mata tsorayen kalabar ta da ke reto kan fuskar ta.

Da dare guraren qarfe tara farhan ne da Afrah a kwance kan bed cikin shirin su na bacci suna game da waya Afrah se qyalqyatar dariya ta ke……uncle!uncle!! kiran yana fitowa cikin murya mai dadin sauraro.

Farhan naga ya tashi a natse ya nufi toilet ya same ta riqe da towel bata riga ta daura ba ta dai kare qirjinta da shi,sae faman lalabe take.

Towel ya kar6a ya daura mata sannan ya tattara sumar ta da ta jiqe shar kaf da ruwa ya mayar a baya ya shiga dube dube a toilet din bai ga abinda yake nema ba, ya jawo dan qaramin towel tare da jawota jikin sa,ya shiga tsane mata gashin kanta da ya gama ne ya dauko ta cak se kan bed kafin yake kai duban sa kan mirror ya hango eye glass din ta,yace “Amrah me yasa kika shiga toilet ba glass a idonki? Oily eyes din ta ta dago tana kallon inda take sa ran fuskar sa ce,
in kaga hakan zakayi zaton tana gani sbd yanda ta saka qwayar idonta a cikin nashi wanda ni billy & Futha munyi mamakin kallon amma shi farhan da alama ya saba ganin haka shiyasa bai yi mamaki ba ko kadan
tace”uncle ina so ne na fara koyon yanda zan riqa zuwa wani gun ba sae da glass ba,yace no ki daina haka ina tsoron ya zama had’ari wata rana,ta gyada kanta kafin farhan ke tashi ya dauko mata eye glass ya saka mata.

Tace “tank u” sannan ta tashi tana tafiya cikin dabara,
farhan sae kallon qafafun ta yake cike da tausayi.

Gaban mirror taje ta shafe jikinta da turarukka masu qamshin dadi.
Sannan ta nufi wardrobe yayinda Afrah ta mirgino kan jikin farhan tayi pillow da cinyar sa tare da miqa masa wayar sa.
Gashin kanta ya shiga shafawa a hankali sbd ya fahimci bacci take ji.

Koda Amrah ta gama shirin baccin ta har Afrah tayi bacci,
qaraso wa tayi ta zauna a dayan gefen sa tare da d’ora kanta a kafadar sa, farhan ya shafo gashin kanta ya kalle ta cike da kulawa yace”ya jikin naki?duqar da kanta tayi dauke da alamar jin kunya tana wasa da zoben hannunta kafin take cewa “naji sauqi”

????2⃣???? Murmushi yayi wanda ya qara masa kyau sbd yanayin yanda Amrah keyi idan taji kunya yana birge shi sosai,
shafo gefen fuskar ta yayi kafin yake dora Afrah kan kafadar sa da tuni baccin ta yayi nisa yaje a hankali ya shimfide ta kan d’an maidaidaicin gadon ta.
sae da ya jima yana tofe ta da addu’o’i kafin yake barin gurin.
Amrah kuwa ba abinda take face kallon sa wanda ako yaushe bata gajiya wa da hakan.
Ba ita ta daina kallon sa ba sai da yazo gab da ita ya zauna tare da jawo ta jikin sa hade da lakuto hancin ta yace wannan kallon fa sae kace yau ne farkon haduwar mu.
Bata ce dashi komai ba face lumshe idon ta da tayi hade da d’an guntun murmushi,farhan kuwa ya kashe musu wutar dakin suka kwanta sae bacci.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button