AFRA KO AMRAH 5-6
????5⃣????
Domin sae ajiyar zuciyar ta ke fita a hankali,
cike da kulawa farhan ke ci gaba da kallon er fuskar ta mai kyau wacce d’igon hawaye ke kan eyelashes d’inta,
yasa yatsan sa ya share mata tare da kwantar da ita a tsakiyar su,
cike da shagwa6a ta farka tana fad’in”uhm uhm”tayi saurin shigewa jikin sa kamar wacce ke jin tsoro har dai yanda ta cusa fuskar ta a qirjin sa ta qudundune guri d’aya.
Addu’a ya shiga yi mata lokaci mai tsawo, sannan ya kalli matar sa Amrah wacce har yanzu bacci take gashin kanta duk ya barbarje a kan pillow har ma ya d’an rufe mata fuska,
bai yi yunqurin gyara mata ba sea surar jikinta da yake bi da kallo yana cikin haka ne yaji wani irin fad’uwar gaba wanda ya sa shi saurin daina kallon ta ya tashi a hankali yana mai karanto addu’a yaje gab da ita ya yaye mata gashin kanta da ya rufe mata fuska kafin yake zuwa toilet ya d’oro arwala yazo ya saka jallabiya kasancewar d’an guntun wando ne kad’ai a jikin sa.
Sae da ya shimfid’a carpet sannan ya kabbarta sallah.
Da asuba Amrah ce ta fara tashi miqa takeyi a hankali tare da tattara gashin kanta ta d’aure guri d’aya,
ta kai hannu ta d’auko eye glass d’inta da ke kan drawer ta saka sannan ne ta iya hango farhan da ke jingine jikin wardrobe riqe da casbi sae dai da alama bacci yake.
Yaye bedsheets d’in da ke jikinta tayi ta zamo daga ita sai er rigar ta ta bacci fara tas da ita iya guiwa mai siririn hannu.
Saukowa tayi kan gadon ta nufi gun farhan ta zauna kusa da shi tare da jinginawa a jikinsa tace “uncle ka tashi an fara kiran sallar asuba,kaji uncle”da qyar ya iya bud’e idonshi sbd wani irin bacci mai nauyi da ke fizgar shi,
ya sakad’o hannun shi ta bayan ta ya rungomo ta sosai,kamar qaramin yaro yace “my Amrah bacci nake ji sosai”to uncle ka bari idan kayi sallah sai ka koma baccin ko”gyad’a mata kai yayi kafin yake
janye jikinsa daga nata ya tashi ya nufi toilet yayi arwala ya fice masallaci haka ita ma taje tayi arwala tayi sallah.
Bayan ya dawo daga masallaci ne ya hau kan bed da niyar ya kwanta sai ya tuna yau Monday zai kai Afrah school,
hakan yasa ya fasa baccin da yayi niya,ya tashi yaje ya fara tsara littafai a cikin school bag d’in Afrah.
Amrah tazo tare da kar6ar aikin da yake tace”uncle je kayi baccin ka kawai tunda yanzu 5:40am to 7:00am sae na tashe ka yayinda ni kuma na gama had’a komai na buqatar zuwa makarantar Afrah,
Cike da jin dad’i ya gyada kansa ya shafo gefen fuskar ta tare da fad’in “tank u my wife” murmushi kawai tayi taci gaba da aikin,
shi kuma yaje ya kwanta wanda a nan take bacci ya d’auke shi.
Qarfe bakwai dai dai ta tashe shi koda ya bude idonshi har ta shirya ma Afrah cikin uniform d’in makaranta sky blue and white,
riga ta kasance fara mai dauke da necktie sky blue,aka mata stocking da skirt wanda ya kasance sky blue mai layin fari a qasan shi,
tsayin sa iya guiwa yayinda fararen socks d’in ta suka tafi har izuwa guiwar ta,se hular kanta sky blue wacce ta mata bala’in kyau har dai yanda aka d’an d’age ta gashin kanta sae ya baje a bayan ta,takalman qafafun ta kuwa tums ne baqaqe haka ma school bag d’inta baqa ce.
Ba qaramin kyau ta ma farhan ba domin ta yanda yake kallon ta kad’ai ya isa ya ganar da kai hakan,
wanda hakan ya nuna bata ta6a masa kyau irin na yau ba.
Cike da murmushin jin dad’i ya kalli Amrah yace “sannu da qoqari my wife”ya fad’i haka ne yayinda ya dauki Afrah cak ya d’aga ta sama yana juyi da ita sae faman dariya suke, sannan daga bisani ya dora mata kiss a kumatu tare da lotsa yatsun sa akan kumatun ta wanda hakan ya qara fad’ad’a murmushin da take yi sae dimple d’inta suka qara lotsawa sosai.
Haka ita ma ta masa kiss a kumatu hade da lotsa en yatsunta a kumatun shi,
Yayi mata tsadadden murmushin da ba ko wane lokaci yake yinsa ba,
domin duk cikin murmushin da yake yi wannan yafi qara masa kyau da haiba.
Ya kalli Amrah da ke riqe da towel tana ta faman kallon su cike da murmushi,
ajiye Afrah yayi tare da kar6ar towel d’in da ke hannun Amrah ya nufi toilet domin ya gaggauta yin wanka.
Koda 7:30am tayi har ya kammala shirin sa tsaf ya ciyar da Afrah ba tare da yayi nasa break fast ba sbd gudun kar su makara da yawa duk da cewa makarantar kusa da su ta ke.
Koda suka isa makarantar sun samu ana assembly da yake founder d’in makarantar yasan da zuwan su kasancewar sa d’an uwan farhan hakan yasa yana hango fitowar su daga mota ya qarasa gurin su,farhan ya durqusa cike da ladabi ya gaishe shi wanda cikin gaisuwar ne naji ya kira sunan shi da uncle Basheer.
Sai da suka gama gaisawa ne uncle Basheer yaja hannun Afrah suka tafi sae bye bye take ma farhan kamar zata yi kuka.
Uncle Basheer na isa da ita assembly ya dora ta kan step tare da fad’in sunan ta da kuma class d’in da zata kasance wato nursery one.
Yayi haka ne sbd haka ake yi a makarantar duk aka sami newcomer akan d’ora sa a step a fad’i sunan shi da class d’in da zai shiga,akan yi haka tun daga kan d’an nursery, primary &secondary bcs makarantar ta qunshi nursery,primary & secondary.
Tun da aka d’ora Afrah kan step take kallon mutanen makarantar a wayen ce ma’ana ba wani d’ar d’ar ko noke noke akasin wasu da ko fuskar su basa bari a gani sae suyi ta faman noke noke.
Hakan da Afrah tayi ya burge mutanen makarantar sosai musamman ma wani hadadden gayen malami da tunda aka dora ta yake kallon ta har izuwa yanzu.
Kamar sa sak da founder makarantar wato uncle Basheer da alama jinin sa ne.
Ana gama assembly uncle Basheer yaja Afrah sae zuwa class d’in da zata zauna bai fito class d’in ba sae da yaja musu kunne kan kar yaji ko ya gani ana takarar ta ko nuna banbanci akan kasancewar ta kurma,
wanda duk zancen nan da uncle Basheer yayi yana kunnen hadadden gayen malamin nan,da shima yazo ne domin shiga class d’in riqe da attendànce register,
Sai dai jin Afrah kurma ce bai sa yaji burge shin da take ya ragu ba sae ma abinda ya qaru.
Domin a maimakon ya zauna ya kira register sae ma daukar Afrah yayi ya dora ta kan desk ya shafi gefen fuskar ta tare da sake mata lallausan murmushi yana mai qara jin son Afrah a cikin ransa fiye da yanda yake jin son sauran yara sbd gayen ya kasance mai son yara ne sosai.
Kar6ar school bag in ta yayi ya fitar da littafan ta ya fara rubuta sunan ta kamar yadda yaji uncle Basheer ya ambaci real name d’in tà a gaban assembly [ 7/12/2016] ????????????????????????????????
~AFRAH KO AMRAH ~
????????????????????????????????
Na
Billy giro????&Bilqis Sidibe????????
????6⃣????
Bayan ya gama ne yaja hannun ta yakai ta layin tsakiya seat din gaba ya zaunar da ita tare da kallon wata yarinya da ke zaune a 6angaren seat d’in, wacce kallo d’aya zakayi mata kasan tana da wayo sosai,
yace da ita”Amrah ga qawa na miki amma banda fada da tsokana sbd kan fadan ki ne yasa kowa baya son zama a kusa da ke”kan ya qarasa maganar sa wacce ya kira da suna Amrah ta wani turo baki cike da masifa tana kallon shi, tace”uncle JB……..shiii! na da gai gaya miki,mtsw qaramar yarinya da ke sae masifa,cike da alamun zata yi kuka ta kalle shi ta le6ace baki tace “masifa”……no kar kiyi kuka bazan sake kira miki masifa ba amma kar kiyi fada da ita kinji,
yanzu zanje office na zauna ina hango duk abinda kike yi da zarar naga kin tsokane ta zan miki bulala kuma daga yau ba ruwana da ke na daina shiri da ke gabadaya ,girgiza kanta tayi cikin sauri ta ce”ni bazan ma tsokane ta ba,sannan ta riqo hannun Afrah tace “daga yau ke qawa ta ce ba fada a tsakanin mu ko?murmushi Afrah tayi tare da gyada kanta wanda hakan ya bawa JB mamaki,har yana magana a zuci.