AFRA KO AMRAH HAUSA NOVEL

AFRA KO AMRAH 3-4

????3⃣????
Tunda ya fita gidan bashi ya dawo daga gurin meeting d’in ba sai bayan sallar la’asar.

Shigowar sa keda wuya bai zarce koina ba sai 6angaren gwaggwo,
da shigar sa dakin yayi tsaye cike da murmushi yana kallon Afrah kwance sae bacci take ga sweet a gefen ta zube saura kuwa duk ta watse su a tsakiyar dakin kamar yadda tsorayen kalabar ta suka barbaje akan bed.

K’arasawa yayi daga ciki ya zauna tare da gaida gwaggwo dake zaune kan sallaya tana lazimi yace “gwaggwo haka er reonon taki ta 6ata miki daki da sweets?sae da gwaggwo ta shafa addu’a tare da yaye hijabin jikinta tace”hm!ai yau ni qaramar hauka tamin sae fada take dani cikin gwallanniyar su ta kurame,farhan yayi murmushi mai hade da dariya sannan ya kalli Afrah shidai haka kawai baya son yaji an kirata a kurma duk da yasan eh kurma ce,gwaggwo taci gaba da cewa “a cikin gwalaniyar ne take dauko duk abinda ta samu tayi ta jifa da shi nayi rarrashi har na gaji haka ma Amrah tazo ta bata alawa tayi ta rarrashi amma duk d’aya wai mamaci ya karye.
Ita da kanta ta gaji da murmujen ta a nan bakin qofa har bacci ya kwashe ta shine na dauke ta na d’ora kan gado tare da alawar da na fara tsincewa ban samu na qarasa ba naji kiran sallah shine na ajiye aikin tukun idan na qarasa sallah.

Farhan ya nisa yace “ina ce dai bata jiwa kanta ciwo garin murmuje ba kuma bata miki 6arna ba?Aa ko d’aya bana tunanin haka,nan ya tashi tare da fadin to zanje na da’n huta na dawo na dauke ta,gwaggwo tace “to Allah hutar da gajiya” yace “Amin”kafin yake fita daga dakin.

Yana isa 6angaren su ya tarar da Amrah daure da towel gaban mirror tana taje gashin kanta.
Ya jima a tsaye bata san da shi ba sai daga baya ne ta hango shi ta jikin mirror sakar masa lallausan murmushi tayi yayinda ya russuna a hankali ya rungumo ta tare da dora kansa a kafadar ta yana mai shaqar qamshin turaren da ke fita a jikinta, yace “my Amrah na gaji sosai”shafo sajen fuskar shi tayi tace “sorry my uncle”ta fad’i haka ne yayinda yake miqar da ita tsaye yace “muje ina son naci abinci”nan ta cire masa suit hade da fadin bari kayi wanka tukun ko…a gajiye ya kalle ta yace”ba kya da tausayi ko my Amrah sbd ke kinci kin qoshi shine ni sai nayi wanka ko zanci”,,um um uncle ba haka bane ba,, haka ne man gashi har cikin ki ya tasa alamar kinci ki qoshi”ya fadi haka ne yayinda yake shafa cikin ta ya tafi har izuwa qirjinta cike da jin kunya ta cusa fuskar ta a qirijin sa ba tare da ta jaye hannun sa da yake yawo dashi kan qirjin ta ba, tace “Allah uncle ina tausayin ka kasan ulcer nake fama da ita ko naso na jira ka bazan sami damar hakan ba”
Bai ce da ita komai ba sae aikinsa da yake na shafar jikinta wanda komai yana yinsa ne a natse a haka ne har yake qoqarin zame mata towel bata hana shi ba duk da masifar kunyar abinda yake mata da take ji sbd har yanzu bata sake dashi gabadaya ba kuma idan ta hanashi tasan bata masa adalci ba sbd tasan turarukkan da ta shafa qamshinsu ba xai barshi a iya kallonta kad’ai ba.
Suna cikin haka ne tayi saurin jaye jikinta daga nashi tare da daura towel d’in ta da farhan ya fara zamewa hakan yasa farhan
ya d’ago a hankali yana kallon ta,
ganin tana kallon qofar d’akin yasa shima ya maida duban sa a gun.
Afrah ya gani a tsaye riqe da sweet a hannun ta sae dai fuskar ta dauke take da fishi,murmushi yayi wanda ya nuna cike yake da farin cikin ganin Afrah.
qarasawa yayi gurin ta ganin bata da alamar qarasowa,
yaje ya durqusa tare da kama kunnen sa afrah kuwa kauda fuskar ta tayi gefe ta turo baki tare da maqale kafad’a wai bazata haqura ba,kamar qaramin yaro ya nuna kansa yace “nine baza kiyi ma haquri ba”kallon sa kawai tayi sannan ta kalli amrah da ke tsaye tana kallon su nan ta bar shi durqushe ta tafi gurin amrah tare da miqa mata sweet din da ke hannun ta Amrah ta kar6a ta bude mata sweet d’in sannan ta dauke ta,farhan ne ya qaraso gurin su yana cire buttons din rigarshi yaje gefen gado ya zauna tare da jawo stool di’n da kulolin abinci ke kai, Amrah ce ta zuba masa abinci shi kuma sae kallon Afrah yake da ke shan sweet tana kallon shi wanda ya fahimci so take ya d’auke ta nan ya miqa hannu ya kar6e ta ya dora ta kan cinyar sa yana mai fadin an daina fishi da uncle? tsure bakin sa kawai tayi da kallo ta lafe a jikin sa tana mai wasa da buttons d’in rigar sa.

????????????????????????????????????????
[10:19PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [7/11/2016] ????????????????????????????????????
~ AFRAH KO AMRAH ~
????????????????????????????????????

Na
Billy giro???? &Bilqis sidibe????????

????4⃣????
Cike da kulawa farhan ke kallon Afrah da ke wasa da buttons d’in rigar shi wanda ya fahimci akwai yunwa a tattare da ita,
cire sweet d’in da ke bakin ta yayi ya zaro tissue ya goge mata bakin ta, ya zaunar da ita ta yanda zai ji dad’in ciyar da ita.
Sai da ya fara cin abincin sbd yaji idan ba wata matsala ta yaji haka,
kasancewar Afrah bata son yaji ko kadan,
ya kuwa ji abinci dai dai ba wata matsala kuma dama yayi tunanin haka bcs bai ta6a jin wata matsala a abincin Amrah ba ko yanzu ya d’and’ana ne sbd yasan d’an adam ajizi ne ya kan yi kuskure wata rana.
A hankali ya shiga fara bata abincin yayinda take bud’e d’an qaramin bakin ta tana kar6a haka shima yake bud’e d’an madaidaicin bakin sa tana saka mishi,domin Afrah yarinya ce wacce duk abinda farhan ya mata ta kan so ita ma ta mishi haka, duk da cewa yanda take bashi abinci akwai shiririta amma haka farhan ke biye mata wanda wani lokaci idan taje saka mishi spoon yakan d’an karkace abincin ya zuba amma sai dai yayi murmushi yasa tissue ya share ya kuma dai dai ta mata spoon d’in ta yanda zata saka mishi a baki ba tare da abinci ya zuba ba.
Haka suka ci gaba da cin abincin su cike da sha’awa da burge duk wanda ke kallon su.
Bayan sun kammala cin abinci ne ya dauke ta yaje ya mata wanka ya dunqulo ta cikin towel ya kwantar kan bed sannan ya fice toilet domin yayi nasa wanka.
Koda ya fito har Amrah ta shirya ma Afrah cikin kayan da suka yi matuqar daukar ta sai zuba qamshi take.

Bayan wasu kwanaki farhan ne dauke da Afrah a kafadar sa dayan hannunsa kuma kaya ne niqiqi.
Amrah da ke kwance kan 3 seater ta zo cikin hanzari ta kar6i kayan da ke hannunsa suka shiga daga ciki,
Amrah na ajiye kayan Afrah ta shiga bubbud’e su cike da murna tana gwalanniyar su ta kurame tana nunawa Amrah kayan d’aya bayan d’aya,
nan Amrah ta shiga kar6ar kayan tana dubawa,
school bag ce da littafai da kuma sweets,choculate,biscuit,da school basket sannan da kuma lunch box,da ta gama gani ne ta shiga tambayar ta tana mai mata maganar kurame da hannu yayinda Afrah ke bata amsa.

Bayan ta gama tambayar ta ne ta maida dubanta gun farhan da ke jingine kan sofa idanuwansa a lumshe tace”uncle Afrah tace wae gobe zaka fara kai ta school?a hankali ya bud’e idon shi
tare da gyara kwanciyar sa yace eh by tomorrow inshaAllah zata fara zuwa school”to ni zancen tawa school fa?
shiru yayi kamar ba zai ce da ita komai ba can ya nisa tare da fad’in “kar ki damu idan lokacin WAEC da NECO yayi zaki je kiyi amma baza ki koma da zuwa school ba, ba ta ce da shi komai ba,
ba wai don bata ji dad’i ba sai don ita ma haka yafi mata,jin shiru yasa ya tashi zaune tare da yaye hular da ke kansa ya kalle ta da kyau yace”yadai Amrahna baki so hakan ba ne?girgiza kanta tayi hade da fad’in “ai ni uncle haka ma da kayi yafi min”ok dauko min ruwa nasha kinji.
Nan ta tashi ta dauko masa ruwa had’e da lemu mai sanyi.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button