AFRA KO AMRAH HAUSA NOVEL

AFRA KO AMRAH 9-10

????9⃣????
Yakai hannu zai cire mata pant,Afrah ta qanqame jikinta sosai tana kuka tana kuma ci gaba da kallon abinda ke tsakiyar qafafunshi a cikin yanayi na mugun tsoro kamar wacce ke masa kallon qatoton maciji.
ganin abin yana qoqarin ta6a cinyoyinta ne yasa ta daddage ta buga wata uwar kuwar da tasa farhan ya wani irin tashi a firgice ya kai duban sa a gun,wanda hakan ne yasa firgicin sa ya qaru sosai ganin tsirif ya rage a lalata masa rayuwar Afrah,
Da qarfin tsiya ya nufi mutumen ya masa uwar mazgar da tasa ya fad’i qasa wanwas.

Haka shima farhan fad’uwa yayi sbd wani irin tari da ya tunkaro shi ya durqushe nan gurin tare da tofar da baqin jini,daga nan bai sake yin tari ba sae dae gabadaya jikin sa ya saki baya iya ta6uka komai sae numfashi da yake sama sama.

Afrah ta zo da gudu ta fad’a jikinsa tana kuka mai tsima zuciya jikinta sae qyarma yake.
Da qyar farhan ya iya kai hannu ya rungumota hawaye masu zafi na fita a idanun shi yayinda yake gyara mata pant,qara rungume ta yayi yana fitar da ajiyar zuciya mai nauyi kamar yadda Afrah ta rungume shi tana fitar da ajiyar zuciya…..uncle! uncle! ya d’aga kansa cikin sauri domin ganin Amrah da ke kiranshi,yayinda luqeqen mutumen da Farhan ya mazga ke cewa ku kwantar min da ita idan ya hana ni da qaramar zanyi da babbar.
A rikice yace “don Allah kar ku ta6a min matata ku min ko ma mene ne amma kar ku ta6a min Amrah da Afrah”

Sam basu bi ta kan farhan ba sae qoqarin kwantar da Amrah suke…….

  "Ku dakata!cewar wani  gaye da tun shigowar su yake zaune kan sofa ya d'ora qafa kan qafa yana shan sigari cikin kwanciyar hankali.
Tashi yayi yaje gun farhan ya durqusa yana mai ci gaba da shan sigari yana busawa Farhan hayaqin sigari a fuska, Afrah da ke maqale a qirjin farhan ta qara cusa fuskar ta sbd ko kad'an bata son ganin fuskokin su.

Yace da Farhan “kaine silar mutuwar mahaifin mu don haka dole ka za6i d’aya daga cikin matan nan,
wacce zamu dauki fansa a kanta domin yau na lashi takobi baza mu bar gidan nan ba har sai munyi kisa a gaban idon ka domin kaji irin zafin da muka ji a lokacin da kasa aka kashe mana mahaifi a gaban idon mu.
Farhan yace “Habib ni ya kamata ku dauki fansa akaina ba akan su ba”

Gayen da farhan ya kira da habib ya shiga kallon farhan cikin yanayi na ka ma raina min da wayo.
Sae dai bai ce da shi komai ba face sigarin sa da ya zuqa yayinda hayaqin sigarin ke fitowa ta bakin sa da hanci cikin yanayin qwarewa,sannan yace “tun farko kai kasa kanka abinda bai gano ka ba,hakan yasa bazan ta6a tausaya maka ba ko na canza ra’ayi,don haka na baka minti biyu ka fad’i AFRAH KO AMRAH wacce zamu d’auki fansa akan ta idan ba haka ba wlh zan harbi wacce naga dama ko kuma na kashe su gabad’aya!

????????????
Farhan ya kalli Habib da mamaki had’e kuma da ganin son kanshi yayi yawa yace”Habib kenan to ni kana nufin mahaifi na da kuka kashe da kuma matar da kuka harba bata ji ba bata gani ba kun ci bulus kenan.
Habib yace “kwata2 ba sa hannun mu a wannan kisa wata qungiya ce da taje fashi gidan sa suka kashe shi ba mu ba,amma wannan matar ni na harbe ta da kaina sbd zafin kashe mana oga da kuka yi wanda muka dauke shi tamkar mahaifi, amma kuka masa kisan da bai ji ba bai gani ba, bcs fitowa yayi domin jin qarar harbi sae kawai kasa aka harbe shi.
Kaga kuwa ba qaramin taimaka maka nayi ba da har nace ka za6i d’aya, amma idan kasa wasa sae na aiwatar da aiki na a cikin rashin tausayi.

Shiru farhan yayi yayinda gumi ke karyo masa ta ko ina, yana tunanin ta yanda zai shawo kan Habib ya haqura,ya za6i wani abin amma banda kashe, AFRAH KO AMRAH domin bai shiryi jin mutuwar ko waccen su a ciki ba, har dai a yanda ya d’auke su matsayin amana.

Shin waye Farhan?
kuma ya akayi Afrah da Amrah suka kasance amana a gare shi?

Muje zuwa domin jin labarin.

Farhan ya kasance maraye ya tashi ne a hannun gwaggwo koda ya tashi bai san su waye iyayen sa ba kasancewar duk sun rasu yayinda suka bar masa tarin dukiya mai yawa sbd shi kadai ne d’a a gun iyayen shi.
Mahaifin farhan yana da qannai guda biyu,
Alhj usman(mahaifin fu’ad) sae gwaggo ita ce qarama a cikin su domin har yanzu ba wasu shekaru ne da ita ba sbd bata haifi warin farhan ba asali ma bata ta6a haifuwa ba,duk tsawon shekarun da tayi da mijinta kafin ya koma ga mahalicci.
Uncle Basheer wato mahaifin JB,ya kasance yaya a gun mahaifiyar farhan.

Marigayi Alhj Sadiq cewa da mahaifin Afrah maqwabci ne a gun su farhan,kuma abokin mahaifin farhan ne sosai,wanda tun daga kan karatun farhan na primary har izuwa high school da yayi a qasashen larabawa shine ya dauki nauyi,duk da irin dukiyar da iyayen farhan suka bar masa bai yarda aka ta6a ko sisi a ciki ba,acewar sa abar masa abinsa idan ya girma ya mallaki hankalin kansa ya fara juya abin sa ta hanyar kasuwanci.

Kuma Alhj Sadiq ya kasance mai tausayin talakawa da taimakon jama’a duk unguwar kowa ya shaida.
Sae dai yana
da kishiyar uwa da duk abin nan da yake bata gani duk da cewa gabakidaya ‘ya’yanta har jikokin ta da ita kanta ba abinda zasu nema a gurin shi su rasa,amma kullum cikin rashin gode masa ta ke,
gashi kusan ince rabin neman sa su yake ma sbd ba shi da d’an uwa ko d’aya kuma mahaifiyar sa bata raye,yana dai da mata qwaya d’aya tal Hajiya Zarah da yake matuqar sonta duk da cewa bata ta6a haifuwa ba kusan shekaru goma da sukayi aure amma kwata2 bai nuna mata damuwar sa ko ya nuna buqatar qaro aure sam ba hakan a ransa ya riga ya barwa Allah komai yayinda suka dage da addu’a shida matar sa Hajiya Zarah.

Hajiya Zarah ta kasance tana samun tsangwama sosai a gun en uwan mijinta sbd rashin haifuwar ta,a yanda suke mata gori kwata kwata kamar sun manta cewa Allah ke bada haifuwa,wanda cikin zagin da suke mata har cewa suke juya baki ganin Annabi,baki haifo ba kin hana shi ya qaro aure ya haifo,
kin magance mana d’an uwa baya ganin kowa da gashi indai zancen ya qaro aure ne sai dai yace haifuwa ta Allah ce shine mai bayarwa,haka duk dukiyar nan tashi sae abinda kika ce yake bamu.
Tun abin baya damunta har yazo ya fara damunta wani lokaci ta shige d’aki tayi ta kuka tana roqon Allah yasa tana da rabon samun haifuwa a duniya,ko zata huta da tsangwamar da dangin mijinta keyi mata.

Da yawan addu’ar da take yi ne wata rana ta tashi cikin tsananin zazza6in da yasa Alhj Sadiq ya shiga damuwa sosai yaje ya kira likita,koda likita yayi en gwaje gwajen sa ya fahimci Hajiya Zarah na dauke da juna biyu.
Sosai Alhj Sadiq yayi farin ciki da jin zancen domin har sadaka sai da yayi.

Tunda dangin sa suka ji labari sukayi baqin ciki sosai domin ba da gaske suke suna son d’an uwan su ya haifu ba,bcs basa son ya samu magaji,
so sukayi su tursasashi ya auri wata er uwar su domin su riqa tatsar sa sannu sannu har dukiyar ta koma hannun su.
Sae dai basu nuna masa baqin cikin su ba sae ma gud’a da suka tarbe shi da ita a lokacin da ya kai musu labari.

Hajiya luba wato Kishiyar uwar sa fantsama tayi gurin bokaye ita da ‘ya’yanta domin su samu su zubar da cikin da ke jikin Hajiya Zarah wacce yanzu komai kawo mata suke na marmari,yayinda Hajiya Zarah ke kar6a tana ci domin ganin take yanxu ba wata qiyayya a tsakanin su kuma bata tunanin cewa suna saka mata wani abu a ciki.
Duk irin barbaden da sukeyi mata a cikin abinda suke kaimata bai sa cikin ta ya zube ba sbd Hajiya Zarah mai yawan addu’a ce ita da mijinta.
Cikin ikon Allah kuwa cikin har ya kai wata tara yayinda en uwan mijinta ke ci gaba da faman fad’i tashi gurin bokaye na ganin cewa an haifu abin bai zo da rai ba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button