AL'AJABI

AL’AJABI part 1


faruk ne xaune abakin gado yana tatunanin
dani kaina bansan me yake tunawaba..
Gyaran murya yayi alamun yanason yace wani
abu naisaurin dago dakaina..yace
HUMAIRAH.!! Nace na’am yace kishirya gobe
zamuje gidanku.”!
Yinme? natan bayeshi..zamuje muba dady
haquri akan abin daya faru..
Da SAFE WAJEN KARFE 10;00 ranar asabr…..
Tsawon min2na talatin muka dauka sannan
muka gama shirye-shiryen tafiya, abinda ya
bani mamaki yadda faruk keyi tamkar zamu
inda ba zamu dawo ba.
Bayan mun gama kuma yace na rufe duk wasu
kofofin gidan na ko‘ina, cikin rashin fahimta
nace “wai faruk ina zamu ne??
Ina tsammanin cewa kayi gdnmu zamu mu
dawo??
Meye kuma na sai mun garkame kofofi??
Faruk yadan hade fuska yace “ba gdnku zamu
ba siyar dake zanje inyi.“
Duk da yanayin da nake ciki sai da nayi dariya
na kada kai tare da cewa “Ba haka nake nufi
ba faruk abin ne kawai ke bani mamaki,“Na
dan taka daga gbnsa izuwa kan kujerar da
hijabina yake, na kara yin dariya a karona biyu
nace “wai ka siyar dani, ashema zaka iya siyar
da kanka kenan??“
Naja sandarsa muka wuce kai tsaye izuwa
waje tare da cgb da hira har muka fito izuwa
harabar gdn muka zarce izuwa inda motar
faruk take, na budewa faruk kofar ya shiga na
mayar na rufe tare da zagayawa na shiga na
tuka motar muka tafi.
Ckn nishadi muke tafiya ina sanar dashi duk
wani wuri da muka gifta ko wani abu daya faru
dai-dai sanda zamu gifta, a haka har muka iso
tsaleliyar katafariyar unguwar, SARAUNIYA
STREET!!
makeken Allon dake kafe yayi mana maraba.
2n daga nan fuskata ta fara canjawa shekara
daya curr kenan rabona da mahaifata na fara
tuno rayuwar data faru dani a baya, na fara
2no lokutan baya sanda a wannan hanyar ake
tukani a tsaleliyar mota, sanda nake takama
ina fankama, nake ji da kaina.
Ba yanzu da rayuwa ta canja ni ta karfin tsiya
ba. A hankali muka cgb da ratsa kyawawan
gine-ginen dake hamshakiyar unguwar da duk
wanda ka gani a cknta to ya wuce raini, har
muka iso tsalelen gdn namu.
hmm… birki naci kawai a gbn gidan ina
kallonsa, da ace wani zaizo wucewa yaga
motar danake cknta da yadda na koma idan
zanyi rantsuwa nan gdnmu ne bazai yarda ba.
A hankali na danna worn har sau uku a hankali
karamar kofar ta bude me bude gate din yabi
motarmu da wani wulakantaccen kallo naji
sanda kasa-kasa yake cewa “Bafa kowanne
talaka ke shiga gdn nan ba.“
Waye ne??
Ya tambaya.
Na sauke glass din motar a hnkl na leko da
kaina waje, 2n kafin nace komai yaja da baya
adan tsorace ‘ranki ya dade!!‘
Ya juya da sauri ya koma, jim kadan tafkeken
gate din ya fara budewa.
Naja motar izuwa harabar gdn nayi parking
tare da fitowa ina me bin harabar gdn da kll
sashe zuwa sashe.
Abubuwa da yawa suka fara dawo min, duk
inda na kalla sai wani abu ya fado min wanda
faru a dai-dai wajen.
Idona ya ciko da kwalla.
Dai-dai lkcn ne faruk ya fito daga ckn motar
wanda hakan ya dawo da hankalina gareshi na
tako naja sandarsa muka nufi ckn gdn.
Ma‘aikatan gdn kuwa sunyi dandazo sai
gaisheni suke duk wanda na gifta ta kusa
dashi, wasu ma harna fara manta sunansu.
Da sallamarmu muka shigo tafkeken
kayataccen falon, ba kowa sai hafsa y‘ar aiki
tsaye a gbn plasma dake kafe tana y‘an goge-
goge.
Ta amsa sllmr tare da juyowa muna hada ido
ta dafe kirji, LAH! aunty humaira!.
Hajiya! Hajiya!!
Ga humaira tazo.
Da sauri momi tare da daddy suka fito, momi
ta dubeta tace “meye??“
hafsa tayi nuni damu.
Dukkansu sukai turus suna kllnmu, momi ta
dubi hafsa tace “To na gansu jeki.“
Hafsa ta ajiye duster dake hannunta ta juya
tare dan dago min hannu tana murmushi, na
gyada mata kai kawai ta fice.
Daddy wanda ya kllmu ya dauke kai yaci gaba
da gyara maballin rigarsa lkc guda ya dago kai
ckn tsawa yace “uban me kuka zo yimin a
gd??
Meya kawo ku??“
Na dan kara matsawa gaf da faruk nace “ka
fada masa abnd kace kazo ka sanar masa
kawai mu tafi.“
Faruk ya gyara tsayuwa yace “Zuwa nayi don
na sanar dakai abnd nasan dole sai kayi
dariya, abnd nasan shi kake so kaji kuma shi
kake so ya faru.
Insha-Allahu daga yau ka daina tsanata kuma
komai yazo karshe.“
Faruk yaja hannuna izuwa kan kujera muka
zauna.
Momi da daddy ma suka zauna kunnuwanmu
duk a bude so muke kawai muji me faruk zai
fada.
faruk yace “Alhaji na sani duk duniya ba
wanda kake so kamar y‘arka guda daya wato
humaira, sannan kuma ba wanda ka tsana kmr
ni faruk sbd dalilai da yawa, musamman yanzu
da dalili me karfi ya karu akan nada.
Banga laifinka ba don kana son kwatowa
y‘arka yanci donta rayu ckn rayuwa me dadi
da nayi 2nani ma sai naga hakika kafini gsky.
Nayi iya nazarin da zanyi na gano cewa
zamana da humaira babu komai a ciki face
takaici da damuwa….“
Na katseshi da karfi nace “FARUK!!“
ya daga min hannu da fadin ‘ HUMAIRA! minti
daya.‘
ya dora da cewa “akwai cutarwa kwarai kmr
yadda kake fada idan naci gaba da zama da
humaira a haka kuma nima bazan so ta rayu
har ta mu2 da bakin ciki ba don haka gata na
dawo maka da ita har gida kmr yadda ka
nema kuma zan tafi na…..“
Nayi saurin mikewa tsaye nayi dawurwura a
guri daya naja da baya da sauri na fizgo wata
sharbebiyar wuka na dan yanki hannuna kadan
jini yayi tsartuwa kai tsaye na wuce da ita
wuyana.
daddy da momi suka mike da sauri tare da
zaro ido, momi tadanyi kara da fadin “iohhh!!!!!
humai…“
Faruk ya mike tare da cewa “humaira me kika
dauka??“
Ba tare da tsoro ba nace “WUKA!! wuka ce
faruk! kuma zan kashe kaina idan har ka tafi
ka barni.“
Ya tako izuwa inda yake jin motsina ya tsaya
cak a gabana yace “Karkiyi haka!! duk
tsananin tashin hankali da ukuba kada kiyi
yunkurin kashe kanki domin tashin hankalin da
zaki tarar yafi wannan, zaifi ki nemi wata
mafitar amma ba wannan ba.
Ya miko hannunsa tare da cewa “bani wukar.“
Nabi fuskarsa da kallo wadda keda tasirin
saurin sani ko hanani da kallo na saki wuka
kasa na rike hannunsa nace “Karkayimin
haka??
Nice fa humaira koka manta ne??
Kace ba zaka tafi ba don Allah kaji??
Kace da wasa kake faruk!!
Ya banbare hannuna daga nasa yaja da baya
yace “bakin alkalami ya bushe ba yadda muka
iya, don kin rabu dani ba yana nufin shikenan
ba.
Kece dai humairar nan ta baya zaki samu
wanda yafini kiyi rayuwar farin ciki.
Ki manta da ba2na kawai ki dauka baki sanni
ba a rywrki ki shimfida sbwr ryw, nina tafi.“
Ya kai karshen maganar ya juya ya nufi
hanyar fita…
Natausayama faruq..!
Koya rayuwanshi xata kasance..? Ko
yararuwan ita humaira zekasance…?
Sekucigaba da binmu
Dan samun sauran labarin. sekashiga blue
rubutunnan kayi like(y)
L‘AJABI part 20
with—–>Aßu Fer’ezerh
Daddy yace “Yayi kyau faruk kuma ka birgeni
akwai kudin da nayi maka alkawari zan baka ka
tsaya ka karbi cheque din.“ Faruk ya juyo hawaye
suka kwararo ta kasan glass din dake sanye a
idonsa yace “ka rike kudinka bana bukata.“
Ya sake binmu da kallo wanda ya kara rikitani ya
juya ya fice.
Innalillahi wa inna ilaihir-raji‘un.
Abin da AL‘AJABI sai kace almara!! Faruk da
kansa ke furta rabuwa dani?? Da kafarsa zai fita
daga inda nake??
Idona yakai ga fuskar daddy wanda keta
murmushi yana annashuwa.
Da sauri na nufi hanyar fita inda faruk yabi nabi
bynsa duk da kiran dasu momi keyi min baisa na
dakata ba.
A guje na karaso inda yake tuni har ya fito
harabar gdn duk da cewa da ma‘aikata masu
yawa suna ta kaiwa da komowa bai hanani tarar
gbnsa ba, na rike sandar dake hannunsa zafafan
hawaye suka kwararo da idanuna ckn
sheshshekar kuka nace “Faruk kana nema rana
ka cnz min daga hakikanin yadda nasanka izuwa
wani daban, ko a mafarki ban zaci haka daga
gareka ba. Yanzu ma a haka tayaya zaka tafi??
Faruk ya grgz kai yace “indai don ta tfy ne karki
damu na tbbtr salih yazo??
Yayi nuni da inda motar da muka zo take. Na
juya na kll inda ya nuna, kwarai yazo kuwa. zcyt
ta fada min.
Ya dora da fadin “Na gaya masa dama ya biyo
bynmu zai daukeni ban bari kin sani bane sbd
kada ki gane akwai wani abu.“
Na kara gyara tsayuwa nace “amma faruk
yakamata ka tausaya rywta a karona biyu ka
sani idan ka tafi ba lallai na dauki dogon lkc ba
zan bakin ciki da takaici zasu kasheni, idan ma
wani wuri kake so kaje na yarda zan bika muje ko
ina ne kuma duk rintsi da wahalarsa zan iya
jurewa….“
Ba inda zaki bini humaira kuma baki isa ki fita
daga ckn gdnnan tare dani ba, na hakura dake na
hakura da tarayyarmu 2nda ba wahayi akayi
mana dole sai mun zauna tare ba.
Ya fada yana me daga murya.
Bakina yadau rawa na dan taka kadan izuwa
gfnsa nace “faruk!! nice fa!! ni kake gayawa
haka??
Anya kuwa kasan abnd kake fada??“
Ya gyada kai tare da cewa “kwarai!! da hnklna
kuma duk abnd nake fada shine abnd nake nufi
har ckn zcyt.“
Tfyr hawayena ta canja izuwa kara sauri nace “A
takaice kana so kace duk irin kaunar da kake
yimin a baya yanzu babu ita??
Duk yadda alkawuran da mukai zaka karya su??
kenan soyayyar da muka dade muna raina ta
mu2, yanzu babu ita 2nda har zaka iya tafiya ka
barni…“
Yayi saurin juyowa yace “EH! babu ita na dade da
kankareshi daga zuciyata wanda shine ya bani
krfn rabuwa dake.
Dai-dai lkcnne daddy da momi suka karaso.
Na dubeshi nace “idan ka tafi kai da kanka sai
kayi dana-sani me girma…“
dana-sani??
Ya tambaya yana dubana ya dora da cewa “Ai na
gama dana-sani 2nda na yarda na aureki,
wannan shine kuskuren da nayi mafi girma a
rywt.“
Kaina ya sara da karfi Bansan sanda nace “karya
kake faruk!! Ni nasan baka isa ka tafi ka barni
har abada ba ko ka daina so na ba.“
Ya juyo yace “Kece makaryaciya humaira amma
ni duk abnd na fada gskyne, zan tafi na barki
kuma bazan taba dawowa ba har abada.“
Ya yunkura zai tafi nayi saurin rike rigarsa ya
juyo muka dubi juna nace “Ka daina zaton ni kmr
kowa ce a gareka, nasan maganar da zaka fada
ta gaske da wadda bata gaske ba.
Nasan abinda zai yiwu a wurinka da wanda
bamai yiwuwa bane, abnd kake fada yanzu har
abada bazai yiwu ba.
Nasan kana fadan hakane sbd kawai kana son na
kyaleka ka tafi, idan kuma har da gaske kake ka
juyo ka rantse min da Allah Ka daina sona kuma
zaka iya tfy ka manta dani har abada!!“
Ya tsaya kawai ya kasa motsawa.
Na katse shirun ckn daga murya da cewa “Ka
fada mana idan zaka iya“.
jimawa kadan ya juyo a hnkl tare da grgz kai
yace “humaira kinsanni ma2ka fiye da kowa a
duniya, kinsan abnd zan iya yi da wanda bzn iya
ba.
Nayi karya idan nace “Zan iya cire sonki daga
zcyt kona manta dake a tsawon rayuwata.“
Yayi kasa da murya yace “Amma ina so ki
fahimta yau ba zabi bane a garemu, dole ne mu
rabu.
Bashi da wani alfanu cgb da zama a yadda muke
sbd kowa baya son zamanmu tare kuma ba wnd
keda shirin taimaka mana, duk daren dadewa
dole wataran zamu gaza watakila sanda lkc ya
kure mana.
RABUWA itace kawai maslaha a garemu koda
bama so amma dole mu hakura.
Kin sani bazan taba son mu rabu haka kawai ba,
dalilaina nada ma2kar karfi wanda suka sa ni
kaina naji na gamsu mu hakura da juna ba sonki
nayi ba idan na barki kika bata da iyayenki
akaina, na dawo dake garesu shine Kokoluwar
son da zanyi miki sbd koda yaushe ryw aunata
ake akan mizani, dole na fada nayi kuskure tun
farko dana yarda na bata da kowa akan SOYAYYA
kuma bazan so abnd nayi kema ki maimaita
irinsa ba.
Kiyi hakuri ki fahimceni humaira don Allah.“
Na jinjina kai sanda sautin kukana ya kara fitowa
nace “yanzu meye madogara a gareka ina
zaka??“
yace “Allah ne kawai madogara ta gareshi na
mika al‘amurana na tbbt bazan taba tozarta ba.“
Ya juya inda ya tbbtr anan su daddy ke tsaye
yace “Alhaji yau mun rabu da y‘arka kmr yadda
ka nema, ni kuma na tafi kmr yadda kake so,
amma ka sani idan wai kayi hakan don ka samu
farin ciki to ina me bkn ckn sanar dakai kayi
bnkwn dashi har abada.
Na tbbt GUGUWAR KADDARA dake binmu tana
gaf da zuwa kanka.
Alkhairi nayi amma ban tsira ba bare kai daka
shuka mana sharri, ba fata nake maka ba amma
kaji tsoron taka UKUBAR don dole sai tazo.“
Daddy murmushin keta kawai yayi don wasa ma
ya dauki zancen.
faruk ya juyo gareni yace “Kada ki manta idan
kika so nan da dan lkc kina da damar kîyi wani
auren ba takunkumi akanki ya jinjina kai ya juya
da fadin “ Na tafi humaira!! Sai wata rana idan
muna da rabon saduwa.“
Bani da ikon hanashi a yanzu dole tasa nabishi
da kallo har izuwa sanda motarsu ta fice daga
ckn harabar gdnmu, a hankali kuma idanuna suka
fara duhu kwakwalwata ta rikice, idanuna suka
fara lumshewa a hankali ban ankara ba na sulale
kasa sumammiya…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button