AL'AJABI

AL’AJABI part 1


BAYAN SATI DAYA


Misalin karfe 4:20 Na yamma Ahmad ya fito
daga ofis dinsa yahau motarsa tare da bin
doguwar shimfidaddiyar kwaltar data nufi kudu
daga inda yake, yasan ya fito da wuri ma2ka
amma dalilin hakan yana son zuwa gdnsu
humaira yau kodôn cika alkawarin daya dauka
na zuwa dubata har gd.
Da address daya dade da sani daga gareta
kawai ya dogara akan zai iya kai kansa gdn
nasu, A hnkl ya shigo unguwar tasu wacce
take sabuwa mallakar gwamnatin tarayya.
Ya fara ratsa tsala-tsalan gdjn ckn nutsuwa,
har izuwa sanda ya iso gdn daya tbbtr nan ne
gdnsu humaira yaci birki.
Yana daga ckn abnd yake son ji daga
karashen lbrn humaira, meye ya dawo dasu
wannan sbwr unguwar kuma sabon gd daga
SARAUNIYA STREET da suke acan baya??
A hnkl ya danna worn me kula da gate din ya
leko ta karamar kofa ya koma tare da bude
tafkeken gate din Ahmad ya wuce da motarsa.


*Hajiya ce zaune a daya daga ckn kayatattun
kujerun falon alfarmar ta zubawa T.V dake
manne a jkn bango ido, hafsa ta shigo ckn
ladabi tace “hajiya kunyi bako.“
Ta dawo da kllnta gareta tace “Wanene??“
uhmm!! Yace sunansa Ahmad.
hafsa Ta fada.
Ahmad..Ahmad!!
hajiya ta fada ckn salo na nazari.
Ok!! abokin aikin humaira.
kace ya shigo.
y‘ar aiki Hafsa ta juya tare da fita, jim kadan
Ahmad ya shigo, manyan bakin yamma.
Ahmad yayi dariya kawai ya karasa ya zauna
suka gaisa da momi, ta mike tare da cewa bari
na 2ro maka humairar ko?
To hajiya nagode. Ta wuce kawai. Ahmad ya
daga kansa ya dubi tafkeken falon da
kawa2warsa da yadda yake, gskyne dole ma
ya yarda humaira a gdn girma take kamar
yadda ya dade da sani a lbrnta. Arziki kam
akwai shi don rubuce yake karara 2n daga
bakin gate izuwa ko‘ina na gdn, komai na gdn
na daban ne. A hnkl kansa yakai ga kyawawan
ho2nan dake manne a jkn bangon dakin
zagaye dashi wadanda suka kasance manya
sosai ckn kyakykyawar dauka. Senior na
dubiyar ce sai yau byn na gama warwarewa
harna manta ma da zancen wani ciwo??
Ta fada dai-dai sanda ta zauna.
kafin yace komai daya daga ckn y‘ar aikin gdn
ta iso dauke da wani kyakykyawan faffadan
faranti dauke da ruwa da kuma juices gamî da
wasu kananan kofuna ta dire a gbnsa ta mike
ta juya.
ya danyi murmushi yace “Wlh kinsan ayyuka
sun hadu sun cunkushe gashi kema din kinki ki
dawo ofis bare ki rage wasu abubuwan, yau
din ma gudowa nayi kawai don na cika
alkawari amma badon na gama ba.“
Humaira tace “Ahmad kenan kana kokari sosai
da aiki yana da kyau a samar maka wani ko
wata ta rike ofis dina kodon rage maka wasu
abubuwan.“ Yayi saurin ajiye kofin hannunsa
yace “Ke kuma fa?? ko shikenan ba zaki sake
dawowa ba??
Ta gyada kai da cewa “gsky bazan dawo ba
ahmad sbd ni banga wani amfani ba, ina aikin
nan ne wai don na rage damuwa anma ba
abnd ya ragu, kuma ni ba don kudi nake yi ba,
ba wani alfanu da hakan keyi min ba wani
dalili da zaisa naci gaba da wahalar da kaina.
Na zabi dana zauna ni kadai a haka a gd na
karasa rayuwata da bakin cikin daya riga yayi
aure ya tare a zuciyata, yayi tsatso tare da
fitar da y‘ay‘a masu yawa.
Ahmad ya bitada kll yace “amma nidai banji
dadin haka ba, kenan daga yau shikenan ko??“
Zan iya cewa haka sai dai kuma idan ka kawo
ziyara irin wacce ka kawo yau.
Humaira ta fada.
Ahmad ya gyara zama yace “2nda may be yau
itace ranar karshe zanso ki karasa min lbrnki
kmr yadda kikai min alkawari, sai me kuma ya
faru??
Faruk ya dawo??
ko har yanzu??“
Fuskar humaira tayi saurin canjawa daga dan
walwala da take ciki kadan izuwa takaici, kmr
ba zata ce komai ba zuwa can hawaye suka
gangaro mata ta gyara zama ta fara:
“Daga nan sai komai ya kara tabarbarewa, ya
lalace bawai gareni kawai ba ga dukkanmu.
Gskyr faruk da ya fadawa daddy “idan yayi
hakan ne don ya samu farin cikî to bazai samu
ba, domin kuwa 2n daga wannan lkcn rayuwar
bakin ciki ta bude sabon shafi a gdnmu.
Ni kaina bansan dalilin irin rikicewar da nayi
ba, na susuce tmkr wata mahaukaciya haka na
zama a wannan lkcn.
Ko abnc bana iya ci duk na rame iya karshen
ramewa tamkar bani ba, magana kuwa babu
zancen ta fito daga bakina sai dai 2nani, kuka
kuwa na fili dana boye na ido dana zuci ba
wanda bana yi.
Ba abnd nake 2nani face FARUK!!!
wanda ya nuna min son da duk duniya ba
wanda yayi min rabinsa, ya fifitani fiye da
kansa, ya soni sanda kowa ke guduna.
Amma gashi an rabamu, ya tafi baisan inda ya
dosa ba baisan inda zashi ba, ga lalurar rashin
gani ba lallai ya samu wanda zai taimakeshi
ba…..“
( sheshshekar kuka )
…..“Ina zashi??
Kuma wajen wa??
Shi kansa bai sani ba amma a hakan ya zabi
ya ajiyeni a gd ckn aminci shi yasha wuyar shi
kadai.
Wannan kawai SO ne da dole zan rinka 2na
faruk dashi har abada.
Munyi aure dashi amma bamu san meye
dadinsa ba, wata mu‘amala irin ta auratayya
bata shiga tsakaninmu ba har muka rabu kllm
ckn jiyyar junanmu muke.
(Wannan ne dalilin da yasa idan aka
tambayeni game dani budurwa ce ko
bazawara ko matar aure nake cewa ban sani
ba.)
Idan nace ni bdrw ce sai na tuno nayi aure,
idan nace bazawara ceni amma kuma ai
bansan wani da namiji ba a dny, Ta wani
bangaren ma sai inga ina matsayin sakin da
aka tilastawa mu2m yayi??
Hkn nasani a ckn rudani.
Bayan wata daya da faruwar abin ne aka tbbtr
zaiyi wuya rywt ta dore a haka ba tare da
dayan biyu ya faru ba, kodai na mutu kn kuma
na haukace.
dole tasa aka shiga neman faruk ido rufe aka
yita nemansa baji ba gani, har kyauta daddy
yasa ga wanda ya kawo lbrn inda faruk yake
amma har aka gaji ko alamar za‘a sameshi
babu.
Bai bar wata kofa koda daya da zata bada
dama asan inda yake ba.
A raina banji faruk ya tafi har abada ba shi
yasa har gobe ina mafarkin dawowarsa.
gdn da muke kansa dole tasa muka barshi sbd
halin da nake shiga, a duk sanda na kalli inda
faruk ya taba tsayawa, wannan shine dalilin da
yasa muka dawo wannan gdn da muke ciki.
Kuma 2n daga wancan lkcn har zuwa yanzu
abubuwa da yawa sun faru wadanda zasu fadu
dama wadanda ba zasu fadu ba…“
Tayi shiru kawai.
Ahmad ya gyara zama tare da cewa “Wato
wasu abubuwan ban zaci zasu iya faruwa a
gaske haka ba sai da naji lbrnki, ALLAH SARKI
HUMAIRA!!
gsky kinga abbw da yawa a rywrki na ban
mamaki, amma kuwa daddynki ance ya rasu
ko??“
Ya tambaya dai-dai sanda ya dago kai ya
dubeta.
Humaira tadanyi shiru jim kadan tace “Haka
duniya ta dauka.“
ckn rashin fahimta Ahmad yace “ba haka bane
kenan?“
humaira tace “magana ta gsky ba mu2wa yayi
ba da ransa amma na tbbtr halin da yake ciki
shi kansa ya kwammace ya mutu…..“
Subhanallahi!! meye ya sameshi haka??
Ahmad ya tmby cike dason jin amsa.
wasu sabbin hawaye suka gangarowa Humaira
tace “Yana asibitin kwararru mallakar
gwammatin tarayya (federal hospital).
Watanni shida da suka gabata ne ya kamu da
wata irin cuta da likitoci kansu suka tbbtr a
garin nan dai ba‘a taba samun me irinta ba,
hakan yasa a duk kasarnan ba inda suke da
masaniya akan cutar bare su bada mgnnta,
barînsa shi yafi kokarin neman magani don
inma anyi a banza.
inji kwararrun likitoci.
Yana can magana, ji da gani ba wanda yake
iya yi.
Sakayyan faruq ne…
Barka da sauka jum’ah..


Jikinsa baya motsi tamkar gawa, an killaceshi
a inda ba kowa akalla tazarar meter 300 da
inda wasu mutanen suke.
Shakar numfashi ma sai da kundun robar
oxygen yake yi, ba wanda ke iya shiga inda
yake sai da tsauraran matakan kariya gudun
kamuwa da cutarsa ta alakakai. Yana
mawuyacin hali ma2ka da gaske, munyi iya
kokarinmu akansa ta hanyar amfani da dukiya
ta wuce misali amma a banza, mun karyata
asibitoci masu yawa da manyan likitoci masu
yawa amma duk inda muka je ba abnd yake
sauyawa daga abnd likitocin farko suka fada
mana.
Dole tasa daga karshe muka hakura muka
dawo dashi nan AMK TEACHING HOSPITAL
inda muka guda 2n farko, abnd kawai lktcn
suka gaya mana shine cutarsa sabuwar ce har
yanzu masana na duniya bincike sukeyi
akanta, da zarar an samu ingantacciyar hanyar
maganceta zasu sanar damu domin sunsan
kudi ba matsalarmu bane ko nawa ne zamu
iya kashewa kai tsaye.
Sai dai rashin lfyr daddy zai wuya ya tash….“
Kuka ya kwace mata wanda ya haddasa ta
kasa karasa dogon zancen data dauko.
Ahmad ya grgz kai tare da cewa “wato
humaira duk wanda ke korafi akan yawan
damuwarki to baisan tarihinki bane, Ashe
wannan ma na daya daga cikin wani yanki na
damuwarki??
Humaira tace “bazan ce maka A‘A ba amma
magana ta gsky ban wani damu da halin da
daddy na ke ciki ba sbd shine ya jawa kansa
koma meye, sun rufe ido sanda suke da dama
sun sakawa wanda yayi musu alheri da sharri.
Sbd kawai wata jarabta da Allah yayi masa
gashi kuma shi ya kamu da wadda tafi ta
faruk din, halin da daddy ke ciki a matsayin
skyy na daukeshi.
Bazan manta sanda faruk ke fadawa daddy
cewa ‘Na tafi kmr yadda kake so amma ka
sani idan wai kayi haka ne don ka samu farin
ciki to ba zaka samu ba, kuma ka saurari taka
UKUBAR don dole sai tazo….
domin guguwar kaddarar data 2nkaro ba
wanda zata bari.‘
Allah sarki gsky faruk BAWAN ALLAH ne gashi
dai duk abubuwan daya fada suna ta bayyana,
dalili daya ne kawai yasa nake son daddy ya
warke, sbd na kalli ckn idanunsa snd zanyi
masa wata tambaya guda daya tak!!
Amma badon haka ba ya…..“
Ahmad yayi saurin katseta sanda tare da grgz
kai sanda ya fahimci abnd take son fada, ya
bita da kallo zuwa can yace “bai kamata kice
haka ba mahaifinki ne fa!!
Koba komai yakamata yaci darajar wannan,
duk dan adam ka iya aikata kuskure a
rayuwarsa.
Na tbbtr shi kansa ya dade dayin dana-sanin
akan abnd yayi, abnd yakamata kiyi yanzu
kawai shine kiyi masa addu‘ar samun sauki.
Sannan kuma humaira ki rage yawan damuwa
da 2nanin da kikeyi sbd ba komai zasu haifar
miki ba face matsala babba, wasu lktn sai kin
manta rywr baya kafin ki iya shimfida sabuwar
rayuwa.“
Humaira ta gyara zamanta tare da mayar da
kanta izuwa inda take fuskanta tace “Nagode
da shawarar daka bani,“ ta juyo ta kalleshi
tare da cewa “amma ka sani bazan taba iya
cire tunanin Faruk a ckn zuciyata ba dashi zan
mutu na koma kabarina.“
Humaira ta riga tayi nisa ba zata ji kira ba.
Ahmad ya fada a zcyrsa lkc guda ya mike tare
da duban agogon hannunsa yace “yamma na
dada yi bari na tafi, nagode sosai humaira da
kasancewata mu2m na farko da kika bawa
dama nasan abubuwa da yawa game da ke.“
Humaira ta dago kai tare da cewa “bari na kira
maka momi kuyi sallama mana!!“
Ahmad ya grgz kai dai-dai sanda yadan taka
gaba kadan yace “A‘A basai ma kin kirata ba
idan ta fito ki fada mata na tafi.
Nagode.“
Ya karasa fada tare da dunkule hannunsa a
kirjinsa ya juya ya fice.
Ta mike tare da komawa kan kujera ta kwanta,
hafsat ta shigo ta dauke farantin juices data
kawo.
Humaira na daga kwancen take canja tashar
da take kallo da remote din dake hannunta
yanayin da momi ta fito dashi yasata
dakatawa tare da tambayar lfy kuwa momi??
Ta karaso jknta a sanyaye tace “daga Asibitine
can inda daddynki yake aka kirani wai ana
bukatar ganinmu da gaggawa, anya….“
Humaira ta cgb da harkar gbnta tare da cewa
“meye ai bazai wuce kudi suke bukata ba
wadancan sun kare ko kuma sun gaji da
ajiyarsa anan zasu bukaci a daukeshi akaishi
wani wurin.“
Momi tayi shiru tana me klln humaira kmr
tahau kanta da duka, can tace “wai ke wace
irin mu2m ce??
mahaifin naki na ckn hali irin wnnn amma
bakya nuna wata dmwrk akai ko?
To ki shiga hnklnk wlh.
Kuma ki shirya zamu tafi yanzu,“ Ta juya
izuwa ciki.
Humaira ta dago kai tare da cewa “Tare
dani??“
Momi tayi saurin juyowa a fusace da fadin “Eh
don ubanki, ko ba zaki bane??“.
Humaira ta mayar da kanta kawai tare da
cewa “Allah ya wuci zuciyarki“.
Tayi tsaki ta juya izuwa ciki.
*Mintuna ashirin kacal suka kwashe suka fito
daga gdn, zundumemiyar mota kirar Toyota
PRADO suka hau direban ya tuka su suka bar
harabar katafaren gdn nasu suka hau titin
dazai sadasu da asibitin.
Momi duk ta rude sai salati kawai takeyi
fatanta kawai Allah yasa ba mutuwa yayi ba.
Zaiyi wuya idan lfy a irin kiran da aka yi mata.
Innalillahi wa inna ilaihir-raji‘un.
Abnd take ta maimaitawa kenan.
Humaira kuwa a zahiri nuna tayi ko a jknta
kmr yadda ta saba yi, kalle-kallenta kawai
take.
A haka har suka iso harabar tafkeken asibitin
kwararrun, ta ko‘ina mutanene ke shiga da fita
wasu da marasa lfy wadanda ke iya iya shiga
da kansu da wadanda ake dauke dasu, grmnsa
ya wuce yadda ido ka iya hango karshensa.
Kll daya zaka yiwa asibitin kasan ya wuce
tsarar karami ko matsakaicin asibiti sai ka
kirashi mafi kurewar girma.
Kwararrun ma‘aikatane kawai ke kaiwa da
komowa duk ta inda ka ratsa, asibitin AMINU
KANO TEACHING HOSPITAL kenan daya daga
ckn mafiya girma, shahara da kwarewa a fadin
africa.
A hankali momi da humaira ke ratsa sashe-
sashe na asibitin izuwa sashen da nasu
patient din yake, ofis din da zasu je don jin
halin da ake ciki.
Akan hanya suna gaf da shiga wani jami‘i ya
taresu “inane kuna zuwa??“
Ya tambaya ckn dagulalliyar hausarsa.
Momi tayi saurin cewa patient dinmu ne a
sashen an kiramu ana nemanmu.“
Mu2min ya grgz kai tare da cewa “No baku da
kowa anan yanzu an dauke kowa daga nan,
babu wani patient naku.“
Momi najin haka ta dafe kai tare da cewa
“shikenan ya mutu sun daukeshi muje
mutuware kawai, zata sulale kasa humaira ta
tarota tabi jikin humaira izuwa kasa ta zarce
da kuka ALHAJI ya tafi, innalillahi wa inna
ilaihir raji‘un…
Abinda take nanatawa kenan 2n ckn kuka me
tsanani, dan katon mutumin dake tsaye ya
dubesu tare da cewa “Alaji??
which Alaji??
Kuna nufi me cutar nan daya dade anan??
Humaira ta dago kai tare da cewa “Eh..Ehh
shi.“
Ya daga kansa tare da cewa “wannan ba
mutuwa yayi ba.“
Momi da humaira sukayi saurin dago kai
kukan da momi keyi ya tsaya, To yana ina??
Meya faru??
Momi ta tambaya.
Ehh! an fita dashi anan wurin.
Ya fada.
Me yasa to??
Humaira ta sake tambayarsa.
Ya dauke kai yace “Oho!! bana nan don a
tambayeni kuje ofishi ku tambayesu mana.“
Momi tayi saurin mikewa suka koma da baya
izuwa ofis din dake gaf dasu kai tsaye momi
taja hannun humaira suka fada.
Doctor meya faru??
ina patient dinmu??
Bangaren da yake ma gaba daya a kulle me
yake faruwa??
Momi tayi saurin tambayarsa.
Dan siririn farin mu2min dake zaune bisa
kujera yasa faffadan tebiri a gaba dake dauke
da files akansa.
Ya gyara zaman glass dinsa da dan yatsa
yace “Alhaji isma‘il mahmud??“
Humaira da mominta suka dubi momi tayi
saurin cewa “Eh.. shi muke nufi doctor.“
To bismillah ku zauna ko??
Ya fada tare da yi musu nuni.
A hankali suka karaso tare da zama bisa
kujerun dake fuskantarsa cike da zakuwa da
jin abinda zai fito daga bakinsa.
Kafin yace komai saî murmushi mai kama da
dariya ta kwace masa yace “Ta ina ma zan
fara??
To magana ta gsky Alhajinku ba mu2wa yayi
ba hasalima an tafi neman lfyrsa da yakinin
samun sauki da yardar Allah.“
Ban fahimta bafa doctor.
Momi ta fada. Ya gyara zama tare da cewa
“Ah! dama kamar yadda kuka sani ne mun
fada muku duk sanda aka samu sahihiyar
hanyar da za‘a bi ta neman lfyrsa zamu sanar
daku, akalla sati biyu da suka wuce muka
samu rahotanni daga wani Babban asibiti a
kasar finland akan sunyi gwajin aiki akan cutar
kuma sunyi nasara gagaruma. Toda muka
tbbtr da hakan munyi iya kokarinmu akan mu
sameku sai ya zamana lambar da kuka bane
da address mun nemesu mun rasa, akalla
wajen kwana goma kenan sai yau muka gani
muka kiraku.
Lkcn da muka rasa yadda zamu yi ne
kwatsam! sai ga wata gidauniya me suna
FISABILILLAH FOUNDATION da suka ji abinda
ke faruwa da kuma halin da ake ciki na
bukatar aiki da gaggawa sai suka dauki gbrr
daukar nauyin fita dashi bama tare da kun
sani ba, sune suka dauki dawainiyar komai
kuma yanzu haka ina tbbtr muku sun isa
finland harma an fara aiki kuma komai zai
kammala ya kuma warke ras a kasa da wata
daya.
Amma badon anyi haka ba a hasashen da
mukai bazai kai yanzu da ransa ba Allah ne
kawai yayi da kwanansa a gaba, ta silar
wannan gidauniya.“
hawayen dake idon momi ya hade da
murmushi daya ziyarci fuskarta yanzu ta juya
suka kalli juna ita da humaira, humaira ta
wani dauke ba wani alamun jin dadi data
nuna.
Momi ta juya gareshi tace “Alhmdllh!! bansan
irin godiyar da zanyi garesu ba dama ku kanku
gsky kunyi mana kokari sosai, FISABILILLAH
FOUNDATION!!
Ta fada tare da yin shiru tace “Na dade ina jin
lbrnsu wajen aikata abubuwa irin wannan
kuma kmr yadda sukayi mana muma munyi
alkawarin daukar dawainiyar kashe linkin abnd
aka kashe akanmu ga wasu marasa lafiyan
dake bukatar taimako.
Idan da hali ina so a sadamu da wannan
gidauniya donyi musu godiya, idan kuma da
wani tallafi da suke bukata don ci gbnsu muna
iya basu tallafi muma.“
Mu2min ya gyara zama yace “maganar gsky
gidauniyar nan ba zasu taba yarda asan su
bama bare aje ayi musu godiya ko wani abu
makamancin haka, amma ba2n kashe kudi
akalla Alhajinku an kashe kusan miliyan biyar
akansa…“
Mu kuma zamu bada naira miliyan goma,
samu masu bukatar aiki da basu da hali ayi
musu har sai kudin sun kare.
Farin mu2min ya gyara zama yayinda
murmushinsa ya kasa boyuwa yace “Hajiya
wato da ace za‘a rinka samun irin hakan da
ba karamin nasara za‘a samu ba, sbd sau tari
zaki ga wadansu akan wasu kudi da basu taka
kara sun karya ba wlh sai dai patient dinsu ya
mutu sbd basu da yadda zasu yi.
Zaki zubar da hawaye idan kika ga rai ya
salwanta akan rashin kudi naira dubu ashirin
ko goma ke kasa da haka ma, kuma mafi
yawan wadanda yakamata su taimaka basayi.
Momi ta gyada kai tare da cewa “Mun dauki
izinah daga abnd ya faru kuma insha-Allahu
zamu dage wajen aikata ire-iren abubuwa irin
wadannan.
Ah idan mun isa gida zan aiko maka da chak
din kudin da kuma… dan ladan albishir naka
kaima.“
Takai karshen maganar tana murmushi.
Likitan me lambar kwarewa mafi kololuwa ya
gyara zama ckn murmushi yace “A madadin ni
kaina da duk wadanda wannan taimako zai
shafa dama hukumar wannan asibitin muna
mika godiyarmu, Allah ya saka alkhairi.“
Momi da humaira suka mike momi tace “ Mun
gode sosai sai yan aiken nawa sun karaso“
To hajiya muma mun gode.
Ya fada.
Suka juya tare da ficewa ya mayar da kansa
ga abnd yake yi.
Motarsu suka hau kai tsaye suka nufi gd momi
nata farin ciki da annashuwa.
Suna isowa gd worn daya direban yayi
tafkeken gate din ya fara budewa jim kadan
motar tasu ta wuce izuwa harabar gdn, momi
da humaira suka fito daga cknta kai tsaye
suka wuce izuwa ckn gdn.
Tafiya kadan sukayi suka iso katafaren falon
alfarmar gdn nasu, humaira ta cire mayafin
dake jikinta ta wurgashi kan kujera ta taka ta
tafi da nufin wucewa izuwa dakinta.
HUMAIRA!!!
Momi ta kira sunanta ta juyo a hnkl, Zo nan.
Momin ta fada.
Ta tako a hnkl tazo gbnta.
Zauna!! momi Ta sake fada tare da yin nuni da
hannunta izuwa kusa da ita.
ba tare da gardamar komai ba humaira ta
zauna.
Momi tamkar me jin nauyin yin maganar abnd
take son fada sai data jima sannan tace
“Humaira!!“
ta kira sunanta tare da dorawa da fadin “Na
fahimci rashin farin ciki da nuna bakin cikinki
karara a lkcn da aka ce daddynki zai samu lfy,
nasan dalilinki nayin hakan amma dole zan
gaya miki hakan da kikai bai dace ba.
Koba komai mahaifinki ne baki da tamkarsa a
duniya kuma baki isa ki canzashi ko
kankareshi daga wannan matsayin ba har
abada.
Na yarda muma munyi kuskure akan abnd
mukayi kuma kema yakamata ace kin dade da
fahimtar hakan kuma kinyi mana uzuri, wlh
mahaifinki nasonki kuma yana kaunarki ma2ka
zan shaidi hkn a ko‘ina, abnd yayi yana ganin
gata ne don ya rabaki da wahala sai dai bai
sani ba ya rabaki da farin cikinki na har abada
ne.
Kiyi hakuri humaira ki maida komai wurin Allah
ina da yakinin ba haka kawai abnd ya faru ya
faru ba lallai akwai wata izinah da Allah zai
nuna mana, amma ki daina dauka cewa
mahaifinki makiyinki ne kinji.“
wasu fararen hawaye suka yi saurin
gangarowa ta kuma2n humaira ta grgz kai ckn
kasa da murya tace “Bawai bana son daddy ko
rayuwarsa bane wlh nafi son inga ya rayu fiye
da kowa sbd bana son a nunani a kirani
marainiya har karshen rayuwata, amma momi
faru..k… duk sanda na 2na bansan inda yake
ba ya mutu ko yana da rai??
A dadi yake ko a wahala??
Nakanji na tsani duniya da duk abnd ke cknta,
lkt a asibiti ya bamu tbbcn akwai yakinin
daddy zai warke yaci gaba da rayuwa ckn
walwala da nishadi, inama kuma ace akwai
wanda zai bani tbbcn faruk na raye kuma yana
rayuwa ckn farin ciki da nishadi???
Dazan samu lbrn hakan kawai ya wadatar dani
amma babu.“
gudun hawayen nata ya karu.
Momi ta kauda kai tayi saurin mayar da
kwallar dake neman kwararowa daga idanunta,
tana tausayawa humaira ma2ka.
Ta dafa kafarta tace “Nayi miki alkawarin daga
sanda mahaifinki ya dawo to duk inda faruk
yake a fadin duniya sai an nemoshi ma2kar dai
yana da rai, koda nawa kuma za‘a kashe akan
hakan.“
Humaira tayi saurin hada hannayenta ckn na
momi ckn sheshsheka tace “Don Allah ku
taimakeni momi… ina son na kara ganin faruk
koda sau daya ne tak a rayu..wata..“
kai wannan love haka..
Allah ban wadda xatasoni kaman haka..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button