AL’AJABI part 1

¤¤ Ahmad dake karanta lbrn yayi saurin juyo
shafin da yake karantawa sakamakon zuwa
karshe da yayi, yayi saurin bin faffadan littafin
dake hannunsa da kallo. Iyakar inda aka tsaya da
rubuta labarin kenan, zuciyarsa ta fada masa.
Ya saki lttfn tare da kauda kai kmr ya fashe da
kuka amma ai ba shikenan ba da saura sai meye
kuma ya faru daga nan??
Ya tambayi kansa, ya shafi fuskarsa sannan ne
yaji hawayen daya dade yana yi ashema kuka
yake yi bai sani ba.
Tunda yake bai taba jin lbr na abin al‘ajabi da
tausayi kmr wannan ba yayi saurin sake jawo
lttfn ya bude farkonsa ya kurawa hotunan dake
manne a farkon littafin ido, hoton musamman
hoton faruk din dake gefen na humaira, Allah
sarki!!
Ga kyau ga haiba ga annuri na tashi a fuskarsa,
dukkansu farare sol tamkar larabawa sun dace
ma2ka.
Ya dubi dan zanen da akai a tsakiyar ho2nan,
hoton alamar LOVE mashi ya shiga ta tsakiya
kasa kadan an rubuta:
littafin ya subuce daga hannunsa ya dafe kai
kawai. Allah sarki!! Ashe ba banza ba humaira ta
kasance koda yaushe ckn damuwa, shine dalilin
da yasa ta zama wata iri harma ya kasa gane
kanta.
Ahmad ya daga kai ya kalli agogon dake manne a
dakin nasa karfe 3:12 na dare, safiyar ma da
saura kenan!!
Ya fada.
sbd yadda yake ji kmr ya jawo safiyar tazo, so
yake kawai ya ganshi a gbn humaira sbd akwai
tambayoyi masu dimbin yawa da yake son yi
mata.
Dukan kofar dakin nasa da akeyi a hankali
yasashi dawowa hayyacinsa ya mike tare da
takawa izuwa bakin kofar.
Waye??
Ya tambaya ba tare daya bude ba.
Nice.. Fatima ce.
Ya bude kofar a hankali ya dubeta tare da cewa
“Menene ya faru??“
Tadan dafa bakin kofar tare da cewa “Yaya
lafiyarka kuwa??
Ina kwance a daki 2n dazu nake jiyoka kana
surutai kai kadai fa.“
Kai!! zancen zucin da nake dama a fili nake yinsa
kenan??
Ya tambayi kansa a zcyrsa.
Ya juyo tare da cewa “a‘a.. kin… Waya nake yi
ne da wasu abokan business dinmu muna
magana ne akan yiwuwar wata yarjejeniya mu da
su, bawai….wani abu bane…“
Waya har karfe 3:30 na dare??
Ta tambaya tare da cewa “gari na wayewa kuma
karfe 8:00 ka fita, Allah yaya mutanen nan fa idan
ka biye tasu zasu haukata ka!!
HAUKA????
yayî saurin tambaya.
Ya dora da fadin “kawai daga ina ayyukana sai
hauka ko kuwa an gaya miki kwakwalwar mu
maza irin taku ce??“
fatima Tayi dariya tare da cewa “To! Yanzu dai
duk ba lkcn wannan bane don Allah ka kwanta
kayi barci ka huta, ka kyale mutanen nan gobe
sai ku karasa.“
Ya gyada kaî tare da cewa “To!! dama mun
gama.“
Taja da baya da fadin “Sai da safe.“
OK!! ya fada sanda ya mayar da kofar ya rufe
tare da takawa ya dawo kan gadonsa ya kwanta
amma barcinma gagararsa yayi, 2nani kawai yake
ta yadda zaiyi ya iya shawo kan humaira ta
karasa masa lbrn nan.
Sai byn tsawon lkc barci ya daukeshi ba kuma
wani dadewa yayi ba aka kira sallar Asuba.
*Tunda ya tashi bashi da wani 2nani sai asibitin
da humaira take, 2ni ya mayar da komai ckn jakar
tata kmr yadda take badon-badon ba da 2ni ya
fice da sassafe amma dole tasa ya hakura.
Misalin 8:30 na safe suna zaune bisa kujeru su
uku sunsa faffadan tebirin cin abinci a gbnsu
wanda ke dauke da abinci kala-kala akansa,
Ahmad da sauri yake kai abncn bakinsa burinsa
kawai yaga ya kammala ya fita, Fatima ta kofin
tea dake hannunta ta dubeshi tace “Yaya don
Allah kaci a hankali, Mum jibi wani cin abnc da
yake yi don Allah.“
Ya bîta da kll tare da cewa “Ina ruwanki??
Kin ganki…“
Mum din tace “gsky ta fada ai irin wannan cin
abinci kmr zaka tashi sama??“
Ya dan daga kansa yace “wlh mum akwai abnd
nake so naje nayi ne da gaggawa..“
Aiki ko??
Ta tambaya ba tare data dubeshi ba.
fatima tayi saurin cewa “Shine mana mum ai kllm
zancensa kenan.“
To!! Fadi ba‘a tambayeki ba.
Ya ture kwanon dake gbnsa ya mike tare da cewa
“Mum daga daki wucewa zanyi sai na dawo.“
A dawo lfy Allah ya bada sa‘a.
Mum ta fada ahmad ya amsa da ameen tare da
takawa.
Fatima tace “A dawo lfy yayana na kaina.“
Ya waigo tare da cewa “Allah yasa kanwata ta
goshina.“
Fatima ta kyalkyale da dariya.
Mum kanta sai data murmusa tare da cewa
“kudai abin dariyarku yawa gareshi.“
ahmad da sauri-sauri ya dauki abubuwan daya
saba dauka hade da jakar ta humaira da key din
motarsa ya fice daga gdn.
Tafiyar da yakeyi akan kwalta kanta ba irin ta
kllm bace hakan yasa a y‘an kalilan min2na ya
iso asibitin, ya karasa da motar tasa inda aka
tanada yayi parking kai tsaye ya wuce ciki.
Allah yasa ta farfado ta dawo hayyacinta, Allah
yasa ta yarda ta taimakeshi da abnd yake son ji.
A hnkl ya 2ra kofar dakin wanda ya kasance na
musamman a asibitin ya shiga, Ido hudu sukai da
ita yayi saurin canja tafiya.
Alhmdllhi! ya fada a ransa ganin yadda ta dawo
tamkar ba ita ya bari a wani hali jiya ba.
Ya karaso a hankali tare dayi mata sallama sanda
ya iso gaf da ita ya zarce ga kwantaccen
tsukakken tebirin dake jikin gadon da take ya
jingina zuwa can yace “Sannu humaira, ina fatan
saukin jikinkinki ya wuce yadda nake gani a zahiri
Sannan da fatan zaki yi hakuri da abnd ya faru
nasan nine na jawo miki.
Ya zanyi? dole na hakura mana, na hakura rabin
jiki na ma ya tafi nake zaune da rabi!!
bare wannan.
Ta fada tare da yi masa nuni daya bata jakarta
dake hannunsa.
Ya tako ya dawo yana me cewa “banga kowa ba
sai ke kadai??
Momi na ce kawai dama kuma ta fita amma zata
dawo yanzu.
Ya mika mata jakar yana me dubanta lkc guda
yace “Naji faruk ya tafi kin suma a wancan lkcn
daga nan sai me kuma ya faru??
Humaira ta saki jakar dake hannunta tare da
binsa da kll tace “Abnd nake gudu sai daya faru
kenan??
Ina ruwanka da jakata??
Meye na bude min??
Da izinin wa kayi hakan??
Ahmad ya grgz kai tare da cewa “kiyi hakuri
nasan bai kamata bude miki abin sirri ba amma
Allah ya kaddara ta hakan zansan lbrnki, naga
abbwn AL‘JABI da yawa a cknsa ki taimaka ki
kawar da dubunnan tambayoyin dake min yawo a
zuciyata.
ckn fusata humaira tace “Ba za‘a fada maka ba
to! Sbd banga wani dalili ba da zaisa dole sai
kasan komai gameda rayuwata ba 2nda idan ma
ka sani ba abnd zaka iya yi.“
ka daina taso min da tsohon ciwo ka fita ka tafi
kawai.
Ta nuna hanyar fita..
Uhmm mumadai dabe karanbanin budewaba da
bazamusan labarinkiba humaira..
Kuma muna buqatan aqarashemana..kobahakaba
abokai..!??
SABAHUL KHAIR
Dan samun posting dinmu akodayaushe
Ahmad yabita da kallo kmr ya fashe da kuka
don takaici, ba’abin da yake so a ransa kmr jin
karashen lbrn daya dauko jinsa amma ya
yanke amma gashi bisa alama bazai samu ba,
yadan gyara tsayuwa kadan yace “Amma
humaira…..“
Tayi saurin katseshi da fadin “Ahmad!!
idan kana yiwa Allah ka fita ka tafi! Karka
manta duk abnd ka sani ma bada izini na bane
bada yarda ta ba don idan da don nice ba
zaka taba sanin komai gameda dani ba har
abada.
Ahmad ya juya baya daga inda yake tsaye
yadan taka a hnkl ya dafa kujera dake gaf
dashi ya juyo yace “Shikenan humaira kina da
dama da ikon bani ko hanani abnd ya zama
naki ba, kuma banga laifinki ba sbd wannan
abune da ba kowa za‘a budewa ya sani ba.
Is ok!! Na fahimceki kuma na gane abnd kike
nufi da hkn, koda akwai wadanda zasu iya
sanin komai gameda ke ni bana daya daga
cknsu.
Na gode Allah iya abnd na sani da kuma ilmin
dana samu dangane da rayuwar duniya daga
lbrnki, nayi dariya a wasu wuraren nayi
murmushi a wasu wuraren, naji haushi a wasu
wuraren sannan nayi kuka me yawa a wurare
da yawa. Ya dakata da maganar jim kadan
yace “Baki so ba kuma baki ji dadin sanin
lbrnki danayi ba amma kiyi hakuri, Sai anjima.“
Ya juya a hnkl tare da takawa zai fita.
Humaira tabishi da kll lkc guda taji bata
kyauta ba idan tayi haka, Ahmad mtm na farko
daya nuna damuwarsa akanta kuma yake son
sanin wani abu game da ita, kuma Ahmad
nada kamala sosai yarda dashi ba wata
matsala bane.
AHMAD!!!!
lkc guda ta kira sunansa, ya tsaya cak! a inda
yake tare da juyowa ya dawo ya dubeta a hnkl
yace “Yadai?? Da wani abune??“ Ta dan kauda
kai kadan tace “Kana da ma2kar girma a
wajena kuma ganin kimarka sosai akwai
abubuwa da yawa da kayi min wadanda zan
dade ina 2nawa, bai kamata ka nemi abu naki
yi maka kai tsaye ba.
Zan baka karashen abnd ya faru ckn shekaru
biyu daga wancan lkcn har zuwa yanzu, amma
ba yau ba sbd har yanzu kwakwalwata a rikice
take amma nayi maka alkawarin zaka sani
wataran.
Ahmad ya jawo kujerar dake gaf dashi tare da
yin murmushi byn ya zauna yace “Na dade da
sanin kina da karamci don na gani a lbrnki, a
shirye nake na jira komai tsawon lkc kuma
komai dadewa kodon na karasa jin AL‘AJABI
mafi girma daban taba jin irinsa ba, soyayyar
da ko lbrn littattafai da fina-finai ban taba
ganin irinta ba.
Ya mike tare da cewa “Nasan may be ba wani
dadewa zakuyi a asibitin nan ba ko??
Ta gyada kai da cewa “A yau dinnan ma zamu
tafi gd, Suman da nayi ba wani tsatsauran abu
bane a wajena don hkn ya saba faruwa.“
Ya saba faruwa?? amma ba wani mataki da
kuka dauka akai??
Meke sawa kina shiga wannan yanayin??
Ba zaku nemi magani ba??
Ahmad ya tambaya ckn mamaki.
Hawaye sukai saurin gangarowa ta kuma2n
humaira tace “Da baka san komai game dani
ba to bznyi mamakin wadannan tambayoyin
ba.
Wane magani??
byn maganin cutar ya dade da tfy!!
Yana raye koya mu2 ma waye ya sani??
Allah ne kadai yasan a halin…da.. yak….“
Kuka ya hanata karasawa.
Ahmad yadan kauda kai hade da tambayar
kansa, kenan 2nda faruk ya tafi bai dawo ba
har yau??
Yayi saurin dawo da kansa tare da cewa “Ki
daina fadar haka ki rage yawan damuwa
komai yayi zafi maganinsa Allah, gashi momin
ta barki ke kadai har yanzu bata dawo ba.“
Ya kautar da zancen.“
Ta jingina kanta da bango tare da cewa “Zata
dawo….ne ina 2nanin suna magana da doctor
ne don data dawo tfy zamuyi“.
Ahmad ya mike tare da duban agogon
hannunsa yace “bari na tafi kada nayi late da
yawa kinsan yau aikin mu2m biyu zan fara ga
nawa ga naki, fatan karin sauki da kwarin jiki
sai nazo dubiya.“
Ya fada tare da juyawa ya fice, humaira ta
kara jingina kanta a jikin bangon taci gaba da
abnd ta saba, kukan zuci dana fili.
Tayi saurin dakatawa da kukan da takeyi
sakamakon FARUK da taga ya shigo dakin da
saurinsa ya tsaya a bakin gadon da take ya
bita da kallo yace “humaira meye ya faru dake
haka??
Ya naga kin zama haka??
Tayi saurin dago kanta tace “Faruk!! dama
kana nan??
Ashe kana raye??
amma ka tafi ka barni ka manta dani baka
waiwayata.“
Yayi saurin cewa “Na dawo gareki humaira zan
daukeki mu tafi, zo mu tafi.“
Ya fada tare da miko hannu, ta mika hannunta
har sai da hannayensu suka kusa haduwa
bat!!! ya bace.
Dama tasan ba‘a gaske take ganinsa ba gizo
yake yi mata kuma ba yau fara ta fara hakan
ba.
Ta saki hannayen nata suka je kasa tabi
gadon ta kwanta ta rushe da kuka wanda hkn
yayi dai-dai da shigowar momi wacce ta
karaso dakyar ta tsaya akan humairar zuwa
can ta zauna gaf da ita tayi tagumi kawai,
tasan dalilin kukan kuma koma meye 2n asali
sune suka ja don haka bata da bakin takurawa
humaira akan dole saita hakura.
Har tayi iya yinta tayi shiru sannan suka
shirya suka fita daga asibitin, driver yaja su
suka nufi gida.