AL’AJABI part 1

Ilalliqa’a
muhadu gobe.
Inkarike daure muku
HUMAIRA!!!
Momi ta kira sunanta ta juyo a hnkl, Zo nan.
Momin ta fada.
Ta tako a hnkl tazo gbnta.
Zauna!! momi Ta sake fada tare da yin nuni da
hannunta izuwa kusa da ita.
ba tare da gardamar komai ba humaira ta
zauna.
Momi tamkar me jin nauyin yin maganar abnd
take son fada sai data jima sannan tace
“Humaira!!“
ta kira sunanta tare da dorawa da fadin “Na
fahimci rashin farin ciki da nuna bakin cikinki
karara a lkcn da aka ce daddynki zai samu lfy,
nasan dalilinki nayin hakan amma dole zan
gaya miki hakan da kikai bai dace ba.
Koba komai mahaifinki ne baki da tamkarsa a
duniya kuma baki isa ki canzashi ko
kankareshi daga wannan matsayin ba har
abada.
Na yarda muma munyi kuskure akan abnd
mukayi kuma kema yakamata ace kin dade da
fahimtar hakan kuma kinyi mana uzuri, wlh
mahaifinki nasonki kuma yana kaunarki ma2ka
zan shaidi hkn a ko‘ina, abnd yayi yana ganin
gata ne don ya rabaki da wahala sai dai bai
sani ba ya rabaki da farin cikinki na har abada
ne.
Kiyi hakuri humaira ki maida komai wurin Allah
ina da yakinin ba haka kawai abnd ya faru ya
faru ba lallai akwai wata izinah da Allah zai
nuna mana, amma ki daina dauka cewa
mahaifinki makiyinki ne kinji.“
wasu fararen hawaye suka yi saurin
gangarowa ta kuma2n humaira ta grgz kai ckn
kasa da murya tace “Bawai bana son daddy ko
rayuwarsa bane wlh nafi son inga ya rayu fiye
da kowa sbd bana son a nunani a kirani
marainiya har karshen rayuwata, amma momi
faru..k… duk sanda na 2na bansan inda yake
ba ya mutu ko yana da rai??
A dadi yake ko a wahala??
Nakanji na tsani duniya da duk abnd ke cknta,
lkt a asibiti ya bamu tbbcn akwai yakinin
daddy zai warke yaci gaba da rayuwa ckn
walwala da nishadi, inama kuma ace akwai
wanda zai bani tbbcn faruk na raye kuma yana
rayuwa ckn farin ciki da nishadi???
Dazan samu lbrn hakan kawai ya wadatar dani
amma babu.“
gudun hawayen nata ya karu.
Momi ta kauda kai tayi saurin mayar da
kwallar dake neman kwararowa daga idanunta,
tana tausayawa humaira ma2ka.
Ta dafa kafarta tace “Nayi miki alkawarin daga
sanda mahaifinki ya dawo to duk inda faruk
yake a fadin duniya sai an nemoshi ma2kar dai
yana da rai, koda nawa kuma za‘a kashe akan
hakan.“
Humaira tayi saurin hada hannayenta ckn na
momi ckn sheshsheka tace “Don Allah ku
taimakeni momi… ina son na kara ganin faruk
koda sau daya ne tak a rayu..wata..“
Ta zarce da kuka tare da kwantar da kanta
bisa cinyoyin momi wadda ta shiga
Rarrashinta.
BAYAN WATA DAYA.
A mafi yawancin lkt mutane kan nuna maka
soyayya a zahiri har su rika kokarin wuce
makadi da rawa wajen nuna sunfi kaunarka
fiye da kowa a duniya, amma idan da wata
masifa zata afka maka sune na farko wajen
rige-rigen gudunka.
Duk da irin dukiyar Alh. isma‘il da yadda
mutane da yawa ke cin gajiyarta ta bangarori
da dama, da abokai hamshakai fitattu da yake
takama dasu amma ya gane kuransa sanda ya
shiga rashin lfyr data haddasa kowa ya guje
shi, duk wanda ya ziyarceshi sau daya baya
mararin ya koma musamman idan yaga
matakan da ake dauka kafin shiga inda yake.
Lallai gskyr masu magana da suka ce harka ta
duniya da me rai kuma me lfy ake yinta,
shikam ya yarda da hakan don ya gani da
idanunsa.
byn shafe wata guda curr!! da yayi a kasar
finland ckn nasara aka kuma sa ranar
dawowarsa, nan fa yaransa, ma‘aikatansa da
duk wanda keda alaka ta kusa kota nesa dashi
aka fara dafifin isa airport don taroshi.
**Misalin karfe 11:30 na safe fitaccen filin
sauka da tashin jiragen saman AMINU KANO
INTERNATIONAL AIRPORT din yadau harama
tare da daukar shiri na musamman daga
ma‘aikatansa wadanda 2ni suka fara tbbtr da
shiri ga inda katafaren jirgi saukar farko a yau
zai sauka.
Ba tare da jimawa ba kuwa makeken jirgin na
EUROPE AIRLINE ya dira a tirbar kasa daga
sararin samaniyar daya shafe a awanni yana
shawagi, daya byn daya mutanen jirgin suka
fara fitowa yayinda jami‘ai suka hau kan aikin
don tbbtr da cewa ba wani bata gari daya
shigo ckn jrgn.
Ckn wadanda ke fitowar harda Alhaji isma‘il,
byn komai ya kammalu sun gama gaisawa da
mutanen dake tsaye suna dakon fitowar tashi
ne kuma jerin gwanon tsala-tsalan motocin
y‘an tarbar tasa suka fice daga airport din tare
da darewa bisa kwalta suka nufo gdnsa.
Ya warke sarai tamkar bashi ba tamkar kuma
bazai taba dawowa haka ba, sukan dan taba
hira kadan da wdnd ke tare dashi a motar
msmmn idan yaga wani abu da ya canja masa
a hanyar da suke bi.
Min2na klln suka kwashe suka iso gdn nasa
tafkeken gate din gdn ya bude jerin motocin
suka wuce ciki a jere kmr yadda suka taho.
Ckn min2na biyu kacal alh. isma‘il yayi godiya
ya sallami kowa da kowa duk suka watse, shi
kadai ya juya ya shige ckn gdn nasa.
*MINTUNA TALATIN DA DAWOWARSA*
Zaune yake bisa daya daga ckn kujerun dake
zagaye da makeken tebirin dake zagaye da
kayan abnc kala-kala, Ya dukufa akansa ckn
annashuwa.
Hajiya na tsaye bisa kansa tana tsiyaya masa
juices a kofi ya dago kai tare da cewa “wai
yaushe rabona da cin abnc irin wannan harna
manta.“
Kada dai kace can turai din abncnsu ba dadi.
Momi ta fada sanda ta juya ga plask dake
kusa da ita.
Ya hadiye lomar dake bakinsa yadanyi dariya
yace “hmm.. wai turawa!! wadannan abncnsu
ai jagwalgwalo ne kawai, banda dole madai…
amma abcnsu ba wani ciyuwa yake ba.“
hajiya ta zauna ckn murmushi tace “To da
fatan dai an dawo lfy??
yadan gyara zama yace “alhmdllh!! tfy gashi
tayi kyau sosai, saura kuma cuta daya daban
samu waraka ba har yanzu kuma ta yiwu har
abada.
…Na sani abu ne mawuyaci idan maganin
cutar zai samu, gsky nayi kuskure ma2ka da
har na kyamaci mu2m me karamci da mu2nci
akan wata larura sai gashi ni naci karo da
wadda tafi ta. Ina ma ace zan…..“
Isowar da humaira tayi wajen tare da dafa
daya daga ckn kujerun wajen ta ari murmushi
ta yafa a fuskarta, daddy ya dago tare da
dakatawa da cin abncn.
Humaira tace “You are wellcome my dad.“
Daddy yace “my daughter yanzu nake shirin
tambayarki ashe kina ckn gdn ma.“ Ina nan
daddy ai banji shigowarka ba sai danaji hira
tayi yawa…“
Ya katseta da cewa “Eh mana gata nan tasani
a gaba sai zuba muke,“ Suka danyi shiru
nadan lkc daddy ya bita da kll yace “Ya 2nanin
faruk kuma???“
Lkc guda fuskarta ta fara sauyawa daga
murmushin data kakala a baya, a hankali kuma
hawaye suka fara ciko idonta har izuwa sanda
suka gangaro bisa kumatunta.
Ta juya da sauri tabar wurin.
Daddy ya ture abncn dake gbnsa tare da dafe
kansa yace “wai ba abnd ya ragu game da
ita??“
Sai dai abnd ya karu.
Momi ta fada. Daddy ya grgz kai tare da cewa
“gsky hajiya mun cuci yarinyar nan, ban taba
zaton abin nan zai zama haka ba,“ yakai
karshen maganar yana me grgz kai tare da yin
ajiyar zuciya.
Tunanina kawai yaushe ne zan dawo mata da
farin ciki??
Tayi dariya ta gaske bata karfin hali ba??
Yaushene walwalarta zata dawo kmr yadda
take 2n asali??
Domin idan har bamuyi taimaketa da hakan ba
zuciyarta ba zata taba yafe mana ba ko ta
daina kllnmu a wadanda suka kawo karshen
farin cikin rayuwarta wanda ni kuma bana son
hakan, ina so ko byn raina tayi alfaharin cewa
ni mahaifinta ne, amma ta yaya??“
Momi taci gaba da klln inda idanunta suke kmr
me yin nazarin wani abu jim kadan tace
“Hakan na iya yiwuwa idan da rabon zai yiwu,
muna da damar da zamu iya yi mata hakan ta
hanyoyi da dama saura kuma mubarwa Allah
yayi zabinsa.“ Daddy ya gyada kai tare da
cewa “A yadda nake ji a shirye nake na kashe
ko nawa ne don dawo da farin cikin y‘ata, sai
dai bansani a ina FARUK yake??
Tsorona ace ya mutu don hkn na nufin
dorewar bakin ckn y‘ata har abada.“
Insha-Allahu ma bai mutu ba yana nan da
ransa kuma zamu sameshi na tbbtr shima duk
inda yake tunaninsa yana nan shima, ka cgb
da cin abncnka yana wucewa fa.
Ta fada sanda ta mike ta cgb da shirya kayan
dake ajiye bisa kayataccen faffadan tebirin,
yadan dago daga dafe kan da yayi “Au ni
harna manta wlh.“
Ya fada sanda ya jawo plate din daya ture
dazu.
Byn dan lkc ya dago kai tare da cewa “Yauwa
idan an jima da daddare zamu je AMK hospital
dukkanmu.“
Ta dago kai da sauri da cewa “Baka gaji da
kwanciya a gadon nasu ba kenan??“
Yayi dariya yace “Allah ya tsaremu da
kwanciyar gadon nan, kinsan dole sun cncnci
jinjina ta musamman kuma bata baki kawai
ba….“
Yauwa dama ban gaya maka ba, jin dadi da
farin ckn dana shiga sanda naji lbrn yadda
akai bansan sanda na bawa su hukumar
asibitin ten millions ba sbd muma yadda akayi
mana ayiwa wasu.“
Ya mayar da kansa ga plate din dake gbnsa
tare da cewa “Kin kyauta ma2ka da haka,
amma akwai wadanda nake son zanyiwa
kyauta ta bajinta sannan kuma ina bukatar a
hada ni da masu gidauniyar nan.“
Momi tace “FISABILILLAH FOUNDATION!! ance
fa basa bukatar asansu ko ayi musu godiya
bare a basu tallafi, duk abnd sukeyi don Allah
ne kuma suna da yakinin sunfi karfin hakan, ni
a yadda nake gani ko su waye ma amma ba
kananan mutane bane suna da arziki na wuce
misali.“
Nima ina tsammanin hakan amma ina so naga
waye??
wacece??
ko kuma su waye??
Ina sha‘awar ace nima an hada gwiwa dani
wajen aikata kyawawan ayyuka irin
wadannan.“
hajiya tayi murmushi tare da juyawa izuwa
dan karamin firjin dake ajiye nesa kadan da
inda suke.
Hakan nada ma2kar kyau kuma tunani ne me
kyau kayi dama a kllm duk abnd ya faru ga
mu2m ilimi yake karawa indai yana da hnkli,
mafi kyawun dukiya itace wadda ake sadaukar
da ita ga wadanda basu da hali, ake taimakon
masu bukata kuma ake amfani da ita wajen
saukakawa wadanda ke ckn matsi.“
Hira ckn nutsuwa taci gaba da gudana a
tsakaninsu.