AL’AJABI part 1

.
Tun ina da shekaru hudu aka saka ni a nursery
ta musamman ba kamar saura ba, me tsadan
gaske ce da kudin da ake biya a shekara daya
kawai ya isa a dauki nauyin karatun yayan
talakawa guda uku tun daga primary har zuwa
jami’a. Direrba aka tanada don kaini kuma ya
daukoni, idan ya kaini baya tafiya har sai an
tashi ya dawo dani. Shekaru biyu kacal nayi
aka matsar dani izuwa hamshakiyar
makarantar da duk wani dan me akwai ke
burin ganinsa a cikinta, wadda tun daga
sunanta kasan tafi karfin talaka koma uban
talaka, makarantar nada kyan yanayin data
burgeni har yakai ban taba korafi da ita ba.
Ina daya daga cikin dalibai abin alfahari a
makarantar sbd kwakwalwata ta saurin gane
abu wanda hakan ke kara min girman kai
matuka. Duk da cewa makarantar kowa naji da
kansa domin ba dan talaka a cikinta kowa ka
gani daga gidan arziki yake, amma fa nawa
girman kan yafi na kowa domin ko kawa daya
ban yi ba sbd a ganina duk babu me aji dai dai
dani. Sai dana shafe shekaru goma sha biyu
anan primary & secondary, da shekaruna 18 na
gama ta.
.
A dai- dai wannan lokacinne kuma kari kan da
ZUNZURUTUN KYAU ya kara bayyana,
Wohoho!!!!!!!!!!! Kai idan ka ganni sai ka rantse
da Allah ni balarabiya ce domin kadan zubi na
bana hausawa bane, kamar yadda ake fada
kuma nake gasgatawa a duk sanda na dubi
kaina babu kamata a wannan zamanin indai
fagen kyau ne. Nasha jawo accident idan ana
tafiya dani a mota ban daga glass ba, nasha
jawowa mutane karo da juna idan ina tafiya,
duk wadda ke ji da kanta idan ta ganni sai ta
fashe da kuka don taga karshen kyau, wasu
fashewa suke da kuka suna cewa ina ma su
sami 1/10 kyawu na. Kwalliya ma bata wani
dameni ba sbd a cewata idan kyau bai cika
bane ake neman kwalliya ta karasa cikashi
amma idan kyau ya cika babu bukatar hakan.
Mafi yawa harkar sharwoliya bata dameni ba
koda a shigata nakanyi kokari na rufe jikina,
mafi yawa kayan da nafi sawa ba wadanda
basu kamata bane sbd ni ako yaushe na yarda
na tsare mutuncina kuma a ko’ina. Bayan na
kammala secondary a nigeria mahaifina ya
nema min admission amma fa a oxford
university dake kasar england, nayi murna
sosai sbd ina da buri na bar kasata izuwa
wata musamman kasashen turai. Da yake
harka ce ta kudi nan da nan komai ya
kammala kuma aka saka ranar tafiyata domin
fara degree na farko a fannin kimiyar tattalin
arziki wato (economics) da kuma lissafi. Ana
gobe zan tafi ne bayan komai ya gama
shiryuwa zaune nake nasa tafkekiyar
televission din dake manne a jikin bango nesa
kadan dani a cikin katafaren falon alfarma na
gidanmu, cikin kwanciyar hankali nake kallon
ba wani abu dake damuna. kaso 99% na
hankali ya tafi ga kallon film din na DHOOM
yadda jarumin film din ke raina hankalin yan
sanda da dabaru daban daban, wucewar da
daya daga cikin yan aikin falon tayi ta gabana
yasa banga karashen abinda ya faru ba abinda
ya tunzira ni kenan wulakancina ya motsa na
kira sunanta da karfi.
.
HANNE!! Ta juyo da sauri tana kyarma, nace “
Zo nan” Ta fara matsowa a hankali a hankali
na daka mata tsawa nace ” gidan uwar wa
zaki je??” Tace ” uhm… haji..ya ce ta kira…ni.
“. Nace harareta nace ” kuma don ubanki shine
ta gabana zaki wuce ko? Duk nan ba hanya
bace??” Tayi shiru kawai tana makyarkyata
bata ankara ba na zabga mata mari hade da
fadin ” ba tambayarki nake ba??”. Karfin marin
sai daya sa ta fadi kasa lokaci guda ta zarce
da kuka.” Ahmad ya kauda littafin daga
karantawar da yake yace ” Lallai wannan
wulakanci har na siyarwa kina dashi ya gyara
kwanciyarsa tare da mayar da idonsa ya dora
da karantawa…….
.
Karar data kwalla ne ya jawo hankalin mum ta
fito da sauri tana tambayar lafiya kuwa?? Ta
tsaya kawai tasamu a gaba tana kallo hade da
hararata cikin takaici…….
AL’AJABI part 6
NA ABUBAKAR A. MUHAMMAD
wth———>
Aßu Fer’ezerh
MUM ta dade tana kallona cikin takaici jim kadan
tace ” Me tayi miki kika mareta??”
Na koma kan kujera na zauna nace ” zuwa… tayi
ta giftani ina kallo ta kare min ban gani ba kuma
tambayarta tayi min shiru.”
ta kada kai tace ” lallai humaira rashin mutuncin
naki yakai, kawai daga na kirata ta gifta ta
gabanki shine abin duka??”
Na zunburo baki nace mum ” kare min fa tayi
kuma…….”
Ta katse ni da cewa ” ke dalla can rufa mana baki
kice kawai wulakancinki ya motsa to kin daketa
kinji dadi, idan kinfi karfinta ai akwai Allah.”
Ta nufi inda hanne ke zaune har yanzu bata tashi
ba sai kuka da take yi.
Na dan kara bata rai tare da gyara zama nace “
ni mum wlh bakya yimin adalci a komai ba zaki
taba goyon bayana ba kullum nice me laifi a
wurinki akan wadannan banzayen.”
Nakai karshen maganar da kauda kai.
Mum tace ” anki a goya miki bayan wace gsky
gareki?? Ke ko kunya baki ji ba don Allah?? ki
rasa wacce zaki zage kwanjinki akanta sai yar
aikin gdnku wadanda yakamata ace kin jasu a
jikinki ki nuna musu kauna.”
Na kalli hanne na zabga mata harara nace “
wadannan shashashan matsiyatan zanja a
jikina?? Allah ya kiyaye.
Mum tace ” to tunda ba zaki kyalesu susha iska
ba ba ruwanki dasu basu shiga rayuwarki ba kada
ki kara shiga tasu idan kuma kika ku wlh zan
basu dama idan kika dakesu su rama suyi miki
dan banzan duka ai ba karfinsu kika fi ba. Taja
hannunta suka wuce, nabi mum da kallon
mamakin jin abinda ita kanta tasan bazai yiwu
ba, nace ” Su dakeni fa kika ce?? “
Ta juyo da sauri tace ” Eh don ubanki “.
Nabita da kallo ganin abin ya dau zafi da yawa ta
juya suka bar falon da nake a zaune.
Na gyara zama na hade rai nayi kicin-kicin kamar
na fashe da kuka, wai ni ake zagi akan wannan
banzar yar aikin? lallai zamanta yazo karshe a
gidan nan bari dady ya dawo.
BAYAN AWA DAYA naji motsin dawowar dadyna
na kakalo sabon fushi da takaici, dady yana
shigowa yayi ido hudu dani cikin fushi, yayi saurin
ajiye jakarsa tare da tunkaro inda nake zaune “
my daughter ( daya daga cikin sunayen da yake
kirana dasu ) menene ya faru haka? waye ya taba
min ke?”
Nayi shiru na kara hade rai kawai na juyar da
kaina.
Dady ya zauna gaf dani cikin kasa-kasa da
murya yace ” fada min mana waye ya taba ki?
uhummm?”
Cikin shagwaba na mirgina kai nace ” ba mum
bace…….”
Me kuma tayi miki??
Ya tambaya da sauri.
nace ” wai….. zata sa yan aiki su rinka dukana “
dady har wani dan babban motsi yayi tare da
mai-maita abinda na fada ” su dakeki??”.
na gyada kai.
Ya juya da sauri ya fara kwallawa mum kira.
Hajiya!!!!! Hajiya!!!!!
Da saurinta ta fito izuwa falon da faddady yace “
Me yasa kika batawa humaira rai, wai ke hajiya
me yasa kike haka ne don Allah…. to to yanzu
me kike nufi yar aiki tafi yar da kika haifa da
cikinki kenan??”
Mum ta tabe baki tace ” au wai da akan wannan
ne kake kwala min kira haka sai kace wani tashin
hankali??”
Au kina nufin shi wannan ba komai bane kenan??
kinga hajiya ran kowa zai baci a gidan nan fa.
Mum tace ” rainin nata ne yayi yawa nace zansa
a dai daita mata zama.
Na tsandara ihu nace kaji ko dady??
Dady ya kara rudewa ya fara zabga bala’i ta inda
ya shiga batanan yake shiga ba.
Zuwa can nace ” dady kawai a kori yan aikin nan
dukansu “.
dady ya juyo yace ” kwantar da hankalinki, abinda
za’ai kenan suna ina ne??”
Mum tace ” Wai suwa za’a kora?? bazai yiwu ba
sbd duk cikinku ba wadda kuka dauka kuma baku
kuke biyansu ba nice don haka babu me korar
minsu ina jin dadin aiki dasu……
Munji tafi kici gaba da harkokinki kada ranmu ya
baci duka, Allah ya baka hakuri.
Ta juya ta nufi sashinta, dady ya juyo gareni ya
fara rarrashina ni kuwa sai wani kara hade rai
nake.
Kinga manta dasu kinji humaira na, ba wanda ya
isa ya taba ki duk wanda ya kara bata miki rai
wlh tamuce ni dashi.
Kada ki manta fa gobe iwar haka kina kasar
birtaniya kin bar musu kucakar kasar tasu zaki
fara rayuwa cikin turawa ba wanda zai takura
miki inda iskar da zaki shaka ma ba irin wannan
bace.
Jin hakan da nayi yasa nadan saki raina kadan,
yace ” to danyi murmushi mana “
Na saki rai sosai yace ” Yauwa ko ke fa! gobe kiyi
kokari ki tashi da wuri sbd jirginki na safe ne an
gama duk wasu shirye-shirye kina zuwa direct
zaku daga shuuuuu!!! sai london.”
yakai maganar da murmushi.
Na dan tabe baki cikin shagwaba nace ” dady nifa
dakai zamu tafi idan muka je sai ka dawo.”
Ya dubeni yace ” to ke banda abinki ina naga
lokacin binki har london kuma na dawo? kedai
karki damu jirgin na musamman ne zaki samu
duk abinda kike bukata kuma za’a kula daku
sosai musamman ma ke yar lele.
Nayi murmushi kawai.
Daddy ya mike ya dau jakarsa bari na shiga ciki
ko?
“To dady” Na fada idona na kasa ya wuce.
Na daga kaina na dubi katafaren agogon dake
manne a jikin bango karfe 6:15pm sallar
magaribar ma ai da saura na mayar da kaina ga
t.v din naci gaba da kallo.
$$$$$$$$$$$$
in Alhaji lfy irin wanWashe gari misalin karfe
8:00am na safe zaune muke mu uku, mum da
dady na zaune a kujeru daf da juna yayinda nake
zaune a kujerar dake fuskantarsu.
faffadan tebirine a gabanmu kayan abinci kala-
kala jere bisa kansa wadanda suka dace da karin
safe, babu wanda ke magana a cikinmu.
Humaira!!!!!!!!!!!!!
dady ya kira sunana, na dago a hankali na
dubeshi.
yace ” misalin 11:30 na safen nan zaku tashi,
abinda nake so dake shine kibi a hankali kuma ki
kula sosai sbd kasar da zaki je ba taki bace ba
wadda kike ciki bace kuma ba wadda kika saba
da ita bace, kiyi abinda yakai ki kawai shine
karatu ki samo abinda zanyi alfahari dashi sbd
ina da comfidence 100% akanki kuma ba zaki
bani ba.
Insha-Allahu dady. Na fada tare da mayar da
kaina ga kofin tea dake hannuna.
Daddy ya mike yace ” bari inje na shirya na fita
ina da meeting karfe tara hajiya ina takardun nan
dana baki ajiyansu jiya??
Ta dago kai a karon farko tace ” Suna nan cikin
lokar sama.” Ok ” ya fada tare da dubana yace “
yar lele na Allah ya kiyaye hanya, da zarar kun
sauka zanyo miki waya.”
To dady na fada ya juya nudi dakinsa.
Na mike na koma kan kujerar dake gaf da mum
nace ” Momina banji kince komai ba.”
To me zance???
Ta fada kanta na duban abinda take ci.
Nace yakamata kice wani abu saboda kinga tafiya
zanyi ta shekaru da yawa kodai bakin cikin
rabuwa dani kike yi da yawa haka har ya hana ki
magana??”
A’A ta fada tare da cewa ” nifa haushinki kawai
nake ji “
Na bita da kallo lokaci guda nayi yar gajeriyar
dariya nace ” da gaske??”
ta gyada kai kawai.
Na kwantar da kaina a jikinta nace ” sorry my
mum ai nasan da wasa kike ba zaki taba jin
haushi na ba, uhmm! mum pls sarkar nan don
Allah ki bani zanyi amfani da ita acan.
Ta girgiza kai tace ” kefa kika nuna halin ko in
kula da ita sai yanzu zaki ce kina so??”
Mum dama can ina sonta wlh zan kula da ita,
Zaki bani??
nakai karshen maganar da kwantar da murya.
Mum ta dubeni kadan ta kauda kai tace ” Zan
baki “.
Na saki fuska hade da alamar jinjina nace “
Thank you MUM bari naje na fara shiri. “
Na nufi dakina.
Misalin karfe goma 10:00am mufida tazo kawowa
momi sako ta iske ina gaf da gama shirina ta
tayani muka karasa na tilasta mata ta tsaya don
yimin rakiya izuwa airport.
MUFIDA y’a ce a wurin haj. jameela kawar mum
kuma aminiyarta, mufida ce kadai zan iya cewa
kawata a duniya don da ita kawai na yarda muyi
kawance sbd ta wasu bangarorin halinmu yazo
daya duk da muna da banbanci da ita sosai a
wasu bangarorin.
Misalin karfe 10:15am Nayi sallama da momi da
sauran wadanda zan iya sallama dasu sauran yan
aikin gidanmu kuwa da rashin mutunci muka rabu
don ban hakura ba sai da nayi final.
A jibgegiyar mota kirar PRADO muka fito, mufida
na gefena sai kuma mutum biyu har direba dake
gaba.
Mukanyi hira jefi-jefi da mufida, kaina sai wani
kumbura yake waini zani kasar turai.
Cikin kankanin lokaci muka isa AMINU KANO
international airport, tunda naga jirgin dazai daga
damu na yarda bana yara bane saboda
haduwarsa, ya isa a nunashi a ko’ina.
Ban dauki lokaci ba aka gama tantanceni na juyo
na karbi jakunkuna na mukai sallama da mufida…