AL’AJABI part 1

Shigata jirgin ya tabbatar min da abinda dadyna
ya fada, tsaruwarsa daga ciki yafi yadda nake
ganinsa daga waje domin ya wuce duk yadda
nake tsammani.
kai tsaye sit dina na wuce na zauna duk da cewa
yaune karon farko dana shiga jirgi irin wannan
amma ban yarda na nuna hakan ba don kada
wadanda ke cikin jirgin su raina ni.
Abinda na lura dashi shine kowa naji da kansa a
cikin jirgin sbd daga manyan attajirai masu tafiya
kasuwanci sai yayan attajirai masu zuwa karatu
irina, babu ma zaton samun dan talaka a ciki
bare a samu din. Kamar yadda aka shirya
11:00am dai dai jirgin ya daga kai tsaye izuwa
birnin london tafiya mafi tsawo dana fara yi a
rayuwata, jami‘an cikin jirgin kuwa sai nan nan
ake damu duk abinda muka bukata ba bata lkc
ake bamu.
Awanni nata shudewa 2n ina sha‘awar tafiyar har
sai dana gaji amma bamu iso ba, duk na kosa
sbd wannan ne karon farko dana taba yin tafiya
irin wannan daga karshe madai wani nannauyan
barci ne ya kwashe ni ban farka ba sai AIRPORT
na birnin londôn, A hankali daya bayan daya
muka sakko daga cikin jirgin.
wowwww!!! Nan fa naga abin mamaki domin ba
birnin ba airport din kadai abin kallo ne ban taba
tsammanin akwai wuri me kyau da kawatuwa irin
wannan lallai duk yadda ake bada lbrn birnin nan
ya wuce nan, duk yadda nakai da ji da kai sai
dana zama kamar wata yar kauye a wurin.
saukowarmu keda wuya jami‘an filin jirgin suka
yo kanmu nan fa aka shiga secreening kala-kala
harda wanda ban taba ji ba ko a lbr, bayan na
cika duk wani sharadine aka bani damar ficewa
daga airport din, ban jima ba kuwa wata
jibgegiyar mota me matukar fadi da tsawo ta iso
like take da banner din OXFORD UNIVERSITY
bamu dauki tsawon lokaci ba ta debemu tare da
mutane daban-daban da muka zo daga wurare
da kasashe maban-banta, Anan ne fa naji kwalta
tamkar ita ta shimfida kanta, duk inda motar tabi
titine luwai-luwai ba gargada bare rami.
Shuuuuuuu!!!!! A haka motar ke tafiya tamkar
jirgin sama ban-bancin kawai ita wannan a kasa
take tafiya ba‘a sama ba.
Gefe guda tsarin gine-ginen birnin wanda keda
matukar tsayi tamkar zasu tabo can kololuwar
sama sun kawatar dani matuka.
gashi kowa irin rayuwar da nafi so yake yi ta ba
ruwan kowa da wani, kowa ka gani harkar
gabansa yakeyi. jim kadan muka iso katafariyar
jami‘ar daya daga cikin mafi girma, daukaka da
suna a duniya, bayan komai ya kammalu kuma
kai tsaye aka yimin jagora izuwa masaukina.
Ni kadai ce a sashin nawa wanda ya kunshi duk
abubuwan da nake bukata.
*** Nan fa na shiga karatu
gadan-gadan kasancewarsa wajene da ko baka
so sai kayi karatu, da farko na dauka a nigeria ne
naci gaba da jiji dakai da takama sai naga ina!!
domin a banza wajene da kowa keji da duk
abinda nake ji dashi shima. Dole tasa na sakko
na fara maraba da kowa nan da nan kuwa na
tara kawaye masu yawan gaske tamkar bani ba,
na saki jiki da mutane sosai. Da yake ba karatu
ne irinna na nigeria ba cikin shekaru biyu kacal
na kammala degree na na farko a hakan ma don
mun sami dan tsaiko ina daya daga cikin
wadanda suka sami sakamako me kyan gaske
hakan yasa makarantar ta bani damar yin
masters degree kyauta kasancewar ina jin dadin
zaman yasa na amince na zarce cikin ba tare da
jinkiri ba. shekara daya kuma na kammala
masters, degree biyu cikin shekaru uku kacal,
wannan shine tarihin kara2na da yadda na samu
masters degree a kasar birtaniya.
“hmmm….. Lallai gskyr Bahaushe da yace ‘Talaka
bawan Allah‘ domin talakan nigeria ne zai kwashe
shekaru hudu yana neman diplomer bai samu ba“
Ahmad ya fada sanda ya kauda kansa daga kan
littafin lkc guda ya mayar da kansa ya dora.
kammaluwar komai tasa na tattaro inawa-inawa
nayo nigeria, ranar laraba misalin 12:00pm
jirginmu yayo nigeria.
dirarmu keda wuya dady ya iso tare da wasu
daga cikin yaransa aka daukeni direct mukai gida,
nan fa girman kai, takama, gadara da raina
mutane ya dawo sabo fil. Na fara jin nifa yanzu
nafi kowa kuma samun kamar ni sai an tona kai
zaiyi wuya ma a samu mace kamar ni da tattara
abubuwan da nake dasu…..
Hmmm’un yanxu akapara shirin..!
BARKAN KU DA ASUBAH..!
Bayan kwanaki uku da dawowata ina kwance
bisa doguwar kujera hannuna na rike da wani
novel daya daga cikin abokan hirata a london
me suna HAPPINESS DAY na prof. christiana
wolein dan kasar holland, kyakykyawar fuskata
nakan littafin wanda fararen idanuna ke kallo,
hankalina, tunanina da duk wani nazarina ya
tafi ga karanta daddadan lbrn da nake yi
wanda nake matukar son karasashi ko don naji
yadda karashen lbrn zai kasance.
Magribar da nake ganin ta doso yasa na kara
kaimi, Momi ta fito daga sashinta rike da wani
dan madai-daicin kaskon turare wanda wani
daddadan kamshi ke tashi ta hanyar farin
hayakin dake fita daga kaskon, ta fara zagaye
faffadan falon domin kanshin ya isa ko‘ina
kafin ta dawo ta ajiye shi a tsakiyar falon.
A dai-dai lkcnne dady na ya dawo, cikin fara‘a
yayi sallama kasancewar ya ganni a falon, ya
karasa ya aje jakarsa tare da zama. Kamar
hadin baki nida momi muka amsa sallamar, na
dago daga kwanciyar da nayi tare da aje novel
din a gefena nace “Wellcome back my dady“.
Yauwa yar lele na da fatan dai komai normal
ko? na gyada kai kawai, momi dake gefe ta
bimu da kallo tare da jinjina kai tace “uhm..
gsky ina ganin kabilanci a gidannan, wato
Alhaji yarka kawai ka sani ni ba mu2m
bace??“ Daddy ya kyalkyale da dariya yace
“kinji ki hajiya da wani zance gani kikai na
tashi daga nan bance miki komai ba??“ Da
sauri tace “zaka iya don ba karamin aikinka
bane kace bama ka ganni ba 2nda ka shigo
sai da nayi magana.“ Dady ya sake yin dariya
yace “ A haba sai kace wani makaho? kawai
dai……..“ Y‘arka ce a ranka!! momi ta karasa
masa zancen.
ya gyada kai yace “anji muje a hakan“. Momi
tace “gashi kuma duk daran dadewa sai ka
shigo falon nan ka tarar batanan koka manta
macece dole ka aurar da ita??“ Dady yayi
murmushi yace “kinga hajiya duk takaicinki
kyayi ki gama ai ba akuya bace ita bare kice
zan kaita kasuwa na siyar mun rabu kenan har
abada.“
Duk muka fashe da dariya, dady ya kwantar da
kansa jikin kujerar yace “ yauwa ni na tuna
ma, humaira!!
Na dago kaina a nitse domin nasan indai dady
ya kira sunana kai tsaye to maganar da yake
son yimin me muhimmanci ce.
Yace “kasancewar kinyi kara2 me tsada a wuri
me tsada kuma akan abu me tsadan gaske
izuwa yanzu na sami request daga wurare
daban-daban akan anaso ayi aiki dake, daga
ciki akwai central ban.k da me gwamnan
bankin da kansa ya rubuto min takarda akan
cewa suna bukatar karin kwararru da suke da
sani akan tattalin arziki, akwai FIRST BANK,
GTI BANK, DIAMOND BANK da sauransu.
Ma‘aikatar kudi ta tarayya ma na bukatar kiyi
aiki dasu, sannan jami‘o‘i kamar B.U.K, A.B.U
da sauransu na bukatar kiyi musu aiki a
matsayin lecturer, ke harda wasu hukumomi
daga kasashen waje sai kin zaba kin darje.
A maimakon nayi farin ciki sai na hade rai,
dady ya dubeni tare da gyara zama yace “Ah
ya naga kin bata rai?? lafiya??“
Na dan kumburo baki nace “dady nifa bazanyi
wani aiki a duk wuraren nan ba.“
dady yace “sai a ina?? ko a bankin duniya kike
so kiyi aiki??“
Na girgiza kai nace “ A‘A ni bazanyi a ko‘ina
ba.“
Kafin yace wani abu momi tace “ba zakiyi ba
kina nufin duk kara2n da kikai ya tashi a
banza kenan??“
Dady ya dubeta yace “haba hajiya kibita a
hankali mana, ya juyo gareni yace “Yar lelena
me yasa bakison kiyi aiki??“
Nace dady nifa banyi kara2 don na wahalar da
kaina ba, nawa ne duka albashin da za‘a
biyani? duka fa bai kai kudin da gyaran gashi
na keci ba.
Yayan talakawa da matsiyata sune keyin kara2
don su sami aiki amma ba irina ba.“
Daddy ya kyalkyale da dariya kamar zai
tuntsiro daga kan kujerar yace “gskyrki fa
y‘ata.“
Momi tace “ Au wai kaima ka biye mata a
hakan??“
Daddy yace “To karya tayi??, ya juyo gareni
yace “ yanzu ke me kike so ayi??“.
Na tabe baki kamar ba zance komabi ba daga
bisani nace “ daddy nifa a duniya ba abinda
ban iya ba irin kwamfuta don haka ina son na
samu certificate akanta.
Cikin sauri daddy yace “Tooo!!! a germany ko
japan ko america zabi daya……
Na tabe baki nace “NO daddy duk basai ankai
ga haka ba, anan kano nake so nayi.“
Daddy yabini da kallo yace “kina nufin a
makarantar matsiyata??“ Dariya ta kwace min
na girgiza kai nace “ a‘a akwai wata reshen
AL-KHRAMY ta kasar saudiya da suka bude
anan kano next week za‘a fara lecture,
MUFIDA ma can zata fara zuwa kaga na sami
abokiyar tafiya.“
Daddy ya gyara zamansa yace “kwarai naji
lbrnta, to karki damu my daughter a ckn satin
nan za‘a shirya miki komai next week dake
za‘a budeta.“ Nayi murmushi nace “Thank you
my dad“.
Daddy ya mike “bari in karasa ciki, ya juyo ga
momi yace “a ina kika saka min jakar nan ta
jiya??“ Har yanzu takaicine akan fuskarta tace
“ tana nan cikin lokar dakinka“. daddy ya sabi
jakarsa ya wuce. Ni kuwa wani farin ciki ya
lullubeni, gsky daddy na sona ni kaina nasan
haka.
Hararar da momi keyi min ce tasa ban takalo
wata hira da ita ba na jawo novel dina tare da
kwanciya bisa luntsimemiyar kujerar da nake
kai na cgb da kara2n da nakeyi a baya.