AL'AJABI

AL’AJABI part 1


Shekara daya kenan banga wajennan ba, duk
inda na baya kawai nake 2nawa sanda aka
kawoni magashiyan na rikito daga bene yau
kuma gani na dawo da kafata. kai tsaye
bangaren da aka kwantar dani shekara daya
data wuce sanda larura ta sameni muka wuce,
muna isa kuwa aka taremu nan fa wasu
likitoci mata su biyu suka sani a daki aka fara
gwaje-gwaje da aune-aunen kafata 2n daga
sama har kasa, na jima kafin daga bisani su
kammala.
babban lktn ya umarcemu muje ofis dinsa mu
jirashi, haka kuwa akai muka shiga ofis din
tare da zama a kujeru biyun dake fuskantarr ta
kujerar likitan.
Addu‘o‘i kawai nake mai-maitawa a raina
Allah yasa karshen matsalarmu yazo gaba
daya, Allah yasa muji tbbcin komai ya dai-
daita kmr yadda muke da yakini.
Bayan tsawon lkcn da muka kwashe a zaune
likitan ya shigo da saurinsa tare da yi mana
sallama, muka amsa faruk ya mike suka gaisa
ckn girmamawa suka zauna a tare.
Likitan ya dubemu tare dayin murmushi yace
“FARUK*HUMAIRA ko??“
muka gyada kai kawai mudai abnd ya kawo
mu kawai muke son ji.
ya kada kai tare da zaro wata sabuwar
takarda daga gaban aljihunsa ya dubemu ya
sake yin murmushi yace “humaira sannu fa,
kinsha wahala amma gskyr hausawa da suka
ce komai yai farko zaiyi karshe, Allah me
magani.“
Muka dubi juna fuskarmu tadan kara saki.
Likitan ya gyara zama ya mayar da idanunsa
ga faruk yace “a baya kmr yadda mukayi
maganar da mahaifinta akan larurar data
sameta idan ban manta ba na sanar dashi
cewa matsalar data samu bata din-din-din
bace lkc zaizo da zata warke kwata-kwata sai
dai babu yakinin ko yaushe ne.
Ah wato duk yadda nake da yakini akan cewa
zata warke amma ban taba 2nanin abune da
zaizo da sauki koda wuri ba.
Yadan dakata tare da rike baki kadan yace
“Abin ya bani mamaki da AL‘AJABI ma2ka da
gaske ni kaina ban taba 2nanin zata warke a
dan kankanin lkc haka ba, Allah ya nuna
ikonsa!!
Ina me tayaku murnar kin warke babu wani
kafarki ta dawo kamar ta kowa kina da damar
takata zuwa duk inda kike so ba wani sauran
ciwo a tare da ita.
Mukayi gaggawar duban juna nida faruk ido
cikin ido a hankali murmushi ya fadada a
fuskokinmu, faruk ya matso gaban kujerar da
yake kai tare da fadin “ina me bakin cikin kasa
yi maka komai a matsayinka na wanda ya bani
albishir mafi dadi a rayuwata, hakika da ace ni
me tarin dukiya ne da kudi yau sai ka gaji da
cewa a barsu haka, sai na cika maka harabar
gdnka da motoci, na gina maka manyan gdje
na gani na fada, kana duk shekara sai kaje
aikin hajji da umara.
Doctor yayi dariya tare da cewa “faruk kenan
da abin dariya kake, yin Allah kenan a kiyasce
shekara biyu na daukarwa al‘amarinnan gashi
Allah yayi ckn shekara daya kacal.“
yakai karshen maganar yana dubanmu.
Faruk ya dubeni mukayi farr da ido a tare
muka zarce da yalwataccen murmushi tamkar
zamu 2ntsire da dariya.
Mun dade munayi masa godiya kafin mu fito.
Tare muka jero muna fitowa na ciro wayata na
fara kiran mufida na sanar mata, jinta kawai
nayi amma nasan bata taba farin ckn da tayi
yau ba.
Muka karasa jkn mota faruk ya dubeni yace
“hmm… lallai kina ji da kawarki irin wannan
lbrn ba‘a fara sanar da momi ko daddy ba sai
ita???
suma duk zasu ji ai lambarta ce ta fara zuwar
min a farko.
Na fada kawai amma a zuciyata nasan dalili,
mufida tayi min halacci duk abnd ya faru baisa
ta watsar dani ba tafi kowa kula dani idan ka
cire faruk.
Tsayar da dan tasi din da faruk yayi ne ya
bani mamaki nace “a mota muka zo fa koka
manta??“
Ya grgz kai yace “Ina sane kuje gd a wannan
motar zan tafi a tasin nan zuwa wajen aiki
akwai wani documents da suke nema ni kadai
nasan inda yake kinga sun yimin text yafi guda
ashirin.
Amma faruk….
Ya katseni da fadin “karki damu!! ko awa daya
bazan kai ba na dawo gdn, ya juya ga salih
yace “ku koma gd nima ina tafe, amma wlh
kabi min sarauniyata a hankali.
salih yayi murmushi kawai ya amsa da TO.
Bari nayi sauri inje ko??
Ya fada.
Na gyada kai kawai na bishi da kallo har yayi
gaba sai kuma ya dawo ganin kallon da nake
masa.
Yadai?? menene??
Ya tambaya.
Na dan gîrgiza kai nace “ba komai.“
Nayi saurin fada.
To jeki ku tafi sai nazo.
Ya juya ya shige tasin suka tafi nayi ta kallon
motar har sai data bace min.
Na juya na shiga motar da muka zo da ita
salih ya juyata muka bar wajen.
Wani iri naji da faruk ya fadi zai je inda ya tafi,
amma ai na saba jin haka duk sanda zamu
rabu da faruk.
hakan yasa na share kawai.
Bayan mun iso gd ina isowa dan karamin
falonmu wani tsallen farin ciki nayi na fada kan
kujera.
(akwai masu cewa basuga wani part ba da
mukawuce me buqata se ya shiga wannan
pagedin(y) ßADI ßA RAI.
dan samu complete)
Rayuwa sabuwa yau akwai shagali, dawowar
faruk kawai nake jira.
Na tashi na shiga nan na fita nan nayi ta
kewaya gidan sai yanzu na kara gane gdn, da
yawa sai yanzu naga wasu abubuwan.
Na shiga bathroom nayi wanka na fito na caba
kwalliya irin wadda na manta rabo na da nayi
irinta, jina nake kawai na dawo wata sabuwa.
Na wuce kitchen kuma na shirya hadadden
girki na dawo falo na zauna na kurawa wani
hotonmu nida faruk ido wanda aka hadashi
mun yi kyau sosai.
Ina nan zaune Bayan akalla min2na talatin
wayata tadau ringing na dagota nayi arba da
faruk nayi murmushi nace DAN HALAK ina
ambatonka a raina kana kirana a waya, na
daga nakaita kunnena fuskata cike da annuri.
Na karasa kai wayar kunnena yalwataccen
murmushi na tashi daga fuskata, sai dai tayi
saurin canjawa daga annuri zuwa rashin
fahimta sanda naji muryar dana tbbtr ba tashi
bace.
..inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un..nafada..
Kome ke faruwa..!
Na karasa kai wayar kunnena yalwataccen
murmushi na tashi daga fuskata, sai dai tayi
saurin canjawa daga annuri zuwa rashin
fahimta sanda naji muryar dana tbbtr ba tashi
bace.
Idan har a yadda muka fahimta dai-daine Ga
alama kece matar me wayar nan ko??
Ckn y‘an sakannin da yayi na maganar 2n
kafin yakai karshe fuskata ta rikide daga yadda
take a baya zuwa mummunan yanayin daya
wuce misaltawa nayi saurin cewa “Eh…eh nice
la..fiya meye ya faru??“
ka2war muryar tamkar ana buga diro dake
magana tayi shiru zuwa can tace “To kiyi
gaggawar zuwa asibitin SABO TAIWO
HOSPITAL mijinki ya samu mummunan
accident…“
Iya abnd kunnuwana suka iya jiye min kenan
suka dauke dif ma‘ana suka daina jin komai,
wani duhu ya ziyarci idanuna na daina ganin
inda nake tsaye ma bare nesa. Kaina kuwa
wata irin juyawa ya fara yi kwatankwacin
yadda belt din inji ke juyawa sanda yake aiki,
wani gumi me zafi ya fara ketowa ta ko‘ina
daga jikina tamkar an watsa min ruwan zafi.
(wani yasaman yacemin wai ina tsalleke..to ni
ban tsallake duk wanda be gani haq qarke to
se ya koma ta opera zegani har inda mu ka
tsaya..)A tsaye nake na kasa gaba na kasa
baya, a takaice dai gaba daya na dauke wuta,
ni kaina banyi yunkurin motsawa ba don nasan
faduwa ce zata biyo baya saima mika hannuna
da nake yi wai ko zanji bango na dafa amma
babu. Na shiga yanayi mafi muni 2nda uwata
ta haifeni yau sanadin MUMMUNAN ALBISHIR!!
Bansan sanda wayar ma dake hannuna ta
subuce zuwa kasa ba, tana dira kuwa ta
tarwatse komai nata ya rabu da dan uwansa,
na dade a tsaye tamkar gunki dafe da kaina
dake juyawa.
Zuwa jimawa kadan dana ji dan dama-dama
na yunkura da karfi daga inda nake tsaye wani
jiri ya kwasheni ta gefe nayi kasa sai dai bisa
sa‘a jina kawai na fado akan kujera, na
dunkule kaina na fashe da kuka hawaye na
zuba tamkar ruwan sama.
Zaiyi wuya in ban rasa faruk ba. 2nanin da
nayi kenan wanda yasa nayi gaggawar mikewa
duk da ban gama dawowa dai-dai ba na jawo
mayafina, takalmina da mukullin motar faruk
duk na rikesu a hannuna nayo waje da gudu.
Banma yi yunkurin tsaida kukan da nakeyi ba
don nasan bame yiwuwar tsayawa bane.
ganin a yanayin dana fito yasa salih tasowa
tare da tambayar “hajiya lfy??
ya na ganki haka??
me ya faru kike kuka kuma??
Na daga baki dakyar nace “Faruk ne.. sunyi
accident yanzu haka suna…asibiti…“
Nakai karshen maganar dakyar.
Subhanallahi!! Accident??
shima ya fada a gigice, hankalinsa ya tashi
ma2ka.
Yayi saurin amsar mukullin dake hannuna ya
bude min kofar motar, muna shiga ya juyar da
ita muka fice.
Duk da gudun da salih keyi iya krfnsa amma
na raina gudun ji nake kmr na sauka na ruga
da gudu, kuka kawai nake rusawa 2n salih na
bani hakuri har ya gaji ya daina.
Muna isowa harabar asibitin kukana ya karu
2n kafin ya gama tsayawa nayi ready na
sauka, yana tsayawa nayi yunkurin fita yayi
saurin dakatar dani da fadin “hajiya kiyi hakuri
ki rage kukan nan don Allah ki samu nutsuwa
ko yayane, dubi yadda kike fa!!
Nabi mayafina da takalmina wadanda duk suke
rike a hannuna nabi shi da kallo kawai na saki
takalmin zuwa kasa na zirashi ckn kafata na
yafa mayafin akan kafata kawai nayo waje
nayi saurin tsayawa sakamakon motar dana
gani a nesa kadan dani na ganeta motar tasin
da faruk yahau ce, gaba daya tayi raga-raga
lallai ba karamin accident bane.
Nan fa na sake rudewa da firgici me tsananin,
‘IHHH!!!! bakina ya furta dai-dai sanda
hakorana suka fara karo na sama na dukan na
kasa ji kake KAF! KAF! KAF! jikina yadau
tsima.
nasan zaiyi wuya wanda ke ckn motar nan ya
fita da rai, na juya da gudu izuwa ckn asibitin
bangaren Emergency na nufa don nasan bazai
wuce can ba, 2n kafin na karasa naga an fito
da wani daga daki bisa irin gadon nan da ake
2rawa an lullube jikinsa alamun ya mu2.
kawai ji nayi kafafuna sun dakata, SHIKENAN!!
ya mutu!!
kukana ya canja salo, da sauri na tari gaban
wadanda ke 2ra dan siririn gadon na dire a
gabansa tare da bude mayafin dake rufe da
fuskarsa.
Nadan yi baya a zaune KAI! ba faruk bane!! na
ganeshi direban tasin ne.
Nayi wata juyawa a haka na mike tsaye da
gudu na doshi dayan dakin dake kusa da
wanda naga an fito da wancan.
Kai tsaye na fada da yake dakin nada zurfi
zarcewa nayi zuwa tsakiyarsa, tfyt tayi saurin
cnjw na koma tfy a hankali sabanin gudun da
nake yi a baya.
Har na karaso gbn gadon da yake kwance,
kwance yake idonsa a rufe tamkar meyin barci
gaba dayan kansa na nade da farin bandeji,
hannunsa dama kafarsa.
Numfashinsa na hawa da sauka a hankali, y‘ar
farar kyakykyawar fuskarsa na klln sama.
Na tsaya akan gadon nasa na zuba masa ido
da yanayin da yake ciki, nabi pipe na ledar
karin jinin dake jone a jikinsa da kallo sama
inda take rataye.
Wasu hawaye da suka banbanta da nadaa
suka zubo min, Bai mutu ba.
Abinda na baiwa kaina tbbs kenan.
Na cake gwiwoyina a kasa na dora kaina bisa
gadon gefensa kadan na zarce da kuka me
tsanani, wanda duk wanda yaji sai ya tausaya
min.
Na jima a haka ko sau daya ban dago kai ba,
ji kawai nayi an dafa bayana a hnkl na dago
kai muka hada ido da wata siririyar farar nurse
dake sanye da fararen kaya, tayi murmushi
tace “am sorry dan matsa kadan zan cire
masa wannan ledar.
Na bita da kll da jajayen idanuna kawai na
mike wani jiri yaja ni zan fadi nurse din ta taro
ni da fadin “hankali zaki fadi fa.“
Na lallaba na zauna a kujerar dake gaf da
gadonsa na kwantar da kaina a jkn bango
hawaye suka cgb da sintiri a kuma2na.
Nurse din ta cire ledar jinin ta jona masa ledar
karin ruwa, tadan tako kmr zata wuce sai
kuma ta tsaya ta dubeni tace “kiyi hakuri kinji
shi ai nashi yazo da sauki ma2ka, karki damu
da yawa.“
Takai karshen maganar tare da dafa kafata ta
wuce.
hmm… wane kwantar min da hankali ma zata
iya yi??
Tayaya hankalina zai kwanta da wannan
bala‘in??
Daga wannan sai wannan, murna ta koma ciki
kenan takaici yaci uban nadaa.
Wannan wace irin KADDARA ce?? wane irin
bala‘i ne??
yaushene zamuyi rayuwa kmr kowa??
ire-iren 2nanin daya mamaye kwakwalwata
kenan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button