AL’AJABI part 1

Nan fa hankalin kowa ya kara tashi komai ya
kara rikicewa, sai dana shafe tsawon lkc
bansan a inda kaina yake ba.
A cinyar momi na farfado mufida na tsaye a
kaina tana yimin fifita, na cilla idanuna sashe
zuwa sashe lkc guda na dago kaina izuwa
mikewa zaune na zarce da kuka.
Momi ta jawoni jikinta ta fara rarrashina,
daddy da sauran mutane na zazzaune kowa ya
zuba tagumi suma suka shiga bani baki ciki
akan kaddara idan tazo ba yadda aka iya da
ita.
*Kwanaki biyu kacal muka shafe aka sallame
mu muka bar asibitin muka koma gida, daga
nan ne kuma wata sabuwar dagulalliyar
rayuwa ta fara, abubuwa da yawa suka sauya
izuwa bai-bai ba yadda suke tafiya a baya ba.
Aikin da faruk keyi dole tasa ya hakura domin
bazai yiwu babu idanu ba kuma gashi ba kmr
aikin gwamnati ba aikine da idan zaka iya ayi
dakai idan ba zaka iya ba shikenan an ajeka
babu saran samun komai, gashi kuma ummin
faruk bata nan kuma duk wasu kadarori da
dan abinda faruk keda shi suna hannunta.
Hakan yasa a dan kankanin lkc muka fara
shiga matsanancin yanayi sai da takai wani
lkcn abinci ma dakyar muke ci, wani lkcn sai
dai abokan faruk su taimaka mana.
Ina son na sanar da daddy don ya taimaka
mana amma faruk yace Na bari kawai mu kara
hakuri umminsa na gaf da dawowa komai
zaizo karshe, kuma dai nima din bana son
sanar musu sbd ina tsoron abnd ka iya biyo
baya.
Kamar yadda na saba ina ckn kitchen ina
sarrafa dan abnd zamu ci na tsaye nake na
dafa wani table dake gabana na tafi duniyar
dana saba zuwa wato TUNANI, gaba daya
hankalina ba‘a kan girkin ma da nakeyi yake
ba. alamun zamewa data faduwar da naji yasa
na dawo hayyacina tare dayo waje da sauri
izuwa falon, abnd kuwa nake zatone faruk ne
sai dai baije kasa duka ba. Nayi saurin rike
hannunsa nace “sannu! baka ji ciwo badai??“
Ya danyi murmushi tare da fadin “Ah ba abnd
naji karki damu.“ Ya mike tsaye.
Na jawo yar karamar bakar sandarsa na
makala a hannunsa muka tsaya a haka nace
“kayi hakuri laifinane danayi nisa ban dawo da
wuri ba.
Harka gaji da zaman kadaici kayi yunkurin
fitowa.“
Ya grgz kai tare da yin murmushin da koda
yaushe kuma a ko wane yanayi ya saba yi
yace “baki da laifi nine da karambani.“
Nayi masa jagora izuwa kan kujera na dubeshi
nace “bari naje kitchen ko?? mintu biyu kawai.
Ya gyada kai kawai, Na mike na koma.
Bayan na gama ne na zubo abincin wani dan
plate na dawo falon.
Zaune muke faruk nacin abncn muna hira ckn
nutsuwa, mun fuskanci juna ina lura da yadda
yake kai abncn bakinsa.
Ya dago kai yace “da alama fa ba cin abncn
nan kike ba??“
uhm! so nake kai dai ka gama tukunna.“
yayi shiru zuwa can ya grgz kai yace
“HUMAIRA ina tausayinki gsky kina shan
wahala ba karama ba…“
Nayi saurin katseshi nace “ka daina fadan
haka don Allah, abnd nake yima ne zai zama
wahala??
Ban taba klln abinda zanyi maka a matsayin
me wahala ba koyaya yake kuwa sbd ka
cncnci fiye da haka, Zanci gaba kuma da yima
iya iyawata har abada.“
Yayi murmushi kawai kmr zai ce wani abu sai
na kautar da maganar da wani zancen.
Bayan ya gama ne na jawo jarida sabuwa na
fara karanta masa halin da duniya ke ciki, idan
muka zo kan wani lbrn na ban dariya muyi
tare.
Sallamar da muka ji ce ta dawo da
hankalinmu, gabana ya fadi da naga momi ta
tsaya tana yi mana wani kallo ta tako a
hankali izuwa ciki.
Sannu da zuwa momi!!
Na fada dai-dai sanda faruk yayi saurin sakin
fuska da fadin “Ah! momi ce sannu da zuwa.“
A ynyn fuskarta nasan da matsala, sama-
sama suka gaisa da faruk na tashi nayi masa
jagora izuwa daki na dawo falon na zauna.
KE HUMAIRA!!!!!
momi ta fada sanda ta gyara zamanta a kjrr
da take zaune tare da dubana sosai.
Na dago kai nace “Na‘am“.
Momi tace “Wai baki da lafiyane naga duk kin
wani rame kin kanjame kin lalace??“
Na dan dubi jikina nace “rama kuma?? lfyta
kalau momi ba abnd ke damuna.“
Ah karya kike akwai, idan ba rashin lfy ba to
yunwa ko wahala akwai daya.“
hmm… Na gama gane inda ta dosa, na grgz
kai nace “ni dai-dai nake kuma ina ckn farin
ciki sosai.“
Karya kike akwai wani abu, kodai baki da lfy
ko kuma akwai yunwa a tare dake ko kuma
wahala me tsanani.
Na bita da kll kawai, ta dora da cewa
“tsakaninki da Allah kina cin abinci sau uku a
rana??“
Kina samun cikakken hutu koda na awa biyu
ne a rana??
Kina samun wani farin ciki a irin wannan
zaman??“
Nadan yi baya da kaina nace “To momi meya
kawo wadannan tambayoyin kuma??
Koda ina samu ko bana samu nan fa gdn
mijina ne ina da inda yafi nan ne??“
Kina dashi.
Tayi saurin cewa ta zarce da fadin “Duk
zaman dazai zama da kwarar juna irin wannan
to bashi da wani amfani don haka dole a samu
mafita akan haka don ba zamu zuba ido
wahala na neman kasheki a banza ba.“
Wani takaici ya rufeni na dauke kaina nace
“Banyi zaton jin haka daga gareki ba ko kadan,
a zatona kwarin gwiwa zaki bani akan kula da
faruk amma ba wadannan maganganun ba.
Haba momi faruk fa!!
Eh naji faruk sai me??
Ta fada tana dubana.
Na grgz kai nace “Toni bana daga ckn butulu
masu manta alheri a dan kankanin lkc, nidai
naji na gani kuma na gamsu zan iya koda
kuwa zan mu2 ne akan haka.
Momi tace “ke yarinyace da kike da kuruciyarki
sosai kula da makaho a gurinki ba karamar
masifa bace da zata iya sawa ki tsufa 2n kina
yarinya kada ki cuci kanki munyi magana da
daddynki dole ma asan abinyi.
Idanuna suka zaro waje kmr zasu fado, abnd
na dade ina tsoro kenan nasan zaiyi wuya
hakan bata faru ba.
Na sauka daga kan kujerar da nake na sauka
kasa na kwantar da muryata nace “Momi kada
kuyi haka don Allah, ki 2na abinda faruk yayi
mana bai kamata muyi masa haka ba, ni zan
jure koma menene.
Momi ta mike tace “kinga ana auna me zai zo
ne gaba ba abnd ya wuce ba, ba wanda zai
yarda yabar y‘arsa me gata gaba da baya a
yanayin da kike ciki da sake.“
Momi ki tsaya ki fahimceni.
Na fahimceki mana amma kiyi fatan daddynki
ya fahimceki idan ya ganki a wannan yanayin.
Ta fada tare da juyawa ta fice.
Na koma da baya na jingina da kujerar dake
bayana, tunane-tunane suka fara kaiwa da
komowa a zucita.
Abu daya dana sani duk rintsi ba wani dalili
dazaisa na rabu da faruk.
(Hmm za’ai butulci kenan)
Abin ya ma2kar dauremin kai, banyi
tsammanin jin haka daga momi a dan
kankanin lkc haka ba.
Na dade a zaune nayi tagumi kawai abin
duniya ya isheni, dakyar na iya mikewa na
koma daki, faruk na kishingide akan gado
idonsa dake sanye da bakin glass na klln
sama.
Na zauna gaf dashi, meye kike kuka??
Ya tambaya.
Nima nayi saurin tambayarsa da cewa “kuka
kuma??“
Na shafa kuma2na, yes gsky ya fada akwai
hawaye na grgz kai nace “ba kuka nake ba.“
Ya za‘ai momi tazo da magana me zafi, daci
da ciwo irin wannan kice ba zakiyi kuka ba??
ya sake jefo min tambaya.
Na kauda kaina a zcyt nace “dama yaji abnd
ya faru??“
Ya sauke kansa kasa yace “Watakila shikenan
lkcn rabuwarmu yazo, duk ginin da mukai a
baya ya rushe!! Sababbin hawaye sukayi
saurin gangaromin, na kwantar da murya nace
“Faruk idan kana fadan haka sai nayi zaton ko
baka da kwarin gwiwa akaina ne, ina so ka
yarda ba abnd zai rabamu har abada.
Ka yarda da haka. muka danyi shiru na wani
lkc ya gyada kai tare da cewa “Na dade da
yarda amma akwai tarin kalubale akan
yiwuwar hakan.
Sautin kukana ya sake fitowa na kwantar da
kaina kawai.
*BAYAN KWANAKI UKU*
Misalin karfe takwas na dare bayan mun gama
komai faruk ya dubeni yace “kyau kije ki
kwanta ki huta duk yau fa baki samu wani hu2
ba, na kada kai nace “badai ina tare da kai
ba??
Shine morewar tawa ai.“
Duk da haka dai hutu ma wani abu ne.
ya fada.
duk da bana son tashi amma sai da ya
lallabeni na mike na tafi daki, da yake a gajiye
nake sosai ina kwanciya barci ya kwasheni.
Faruk na zaune jim kadan da tashi na kamar
daga sama daddy ya fado da zazzafar
sallamarsa data sanya faruk saurin dagowa
bai iya amsawa ba har sai da daddy ya zauna.
Sannu da zuwa Alhaji.
Ya gyara zama sosai akan kujera ckn gadara
yace “Yauwa“.
Shiru ya gudana tsakaninsu nadan lkc zuwa
can faruk yadanyi kmr zai mike tare da cewa
“bari na taso humairan tana ciki.
A‘A yayi saurin dakatar dashi kana yace
“Wajenka nazo ba ita ba.“
A hnkl faruk ya koma ya zauna tare da cewa
Allah yasa dai lfy?
Ka taba ganina a gdnku??
daddy ya tambaya ya dora da fadin “To 2nda
ka ganni yau ka hakikance dole da dalili.“
Yadanyi shiru yabi da komai da komai na falon
da kallo a wulakance yace “Ah duk halin da
ake ciki lbr yazo kunnena kuma banyi mamaki
ba don nasan dole haka zata faru.
Sanin kanka ne yanzu ka zama misaki,
nakasashshe kuma makaho ba abinda kake iya
yiwa kanka bare kayiwa wani ba.
Hakan yasa ba zaka iya rike humaira ba a
halin da kake ciki kuma kai kanka kasan haka,
Naso ace ku zauna na har abada sbd yadda
kuke son junanku musamman irin halaccin da
kayi mata to amma magana ta gsky hakan ba
zata samu ba.
A matsayinmu na iyayenta ba zamu zuba ido
muna gani y‘armu ta kaskance ta lalace
karshe ta mu2 a wahale ba.
Don haka ina me umartarka da lallai ka
sawwakewa humaira ba tare da bata lkc ko
jinkiri ba.“
sbd grgz a firgice faruk ya dago kai duk da ba
iya ganin komai yake ba amma sai daya mayar
da fuskarsa zuwa inda yake 2nanin cewa anan
daddy ke zaune, fuskarsa ta canja ma2ka
bakinsa na rawa yace “Alhaji! wannan
maganar da kazo min da ita ta ma2kar
gigitani!!
Don girman Allah ka taimakeni kada ka rabani
da humaira, duk duniya Allah ne gatana
humaira ce gatana ita kadai ke taimako na don
Allah….“
Wannan ba wani abin damuwa bane, akwai
kudi dazan baka wadanda sun isheka ka auri
mata hudu ma idan kana so su kula dakai
nidai bukatata ka sakar min y‘ata ban haifeta
don irin wannan wahalar ba.
daddy ya fada.
Faruk ya grgz kai yace “kome zaka bani kuma
komai yawansa baikai muhimmanci da kimar
humaira a idona ba kuma idan ina dashi zan
iya sadaukar dashi akanta, ka rike koma meye
nidai ka barmu tare don Allah.“
daddy ya kara bata rai yace “bawai nazo ne
muyita wani doguwar muhawara dakai ba so
nake yadda kazo gida na dauki y‘ata na baka
to ka dawo min da y‘ata gida.“
faruk ya grgz kai yace “To kuwa bazan taba
iya yin abnd kake so ba.“
Da sauri daddy ya dubi faruk ya maimaita
abnd ya fada ckn salona tambaya, kace ba
zaka iya ba??
daddy ya mike tare da cewa “kuskure mafi grm
da zakai a rywrk shine kaki sakar min
y‘ata.Dama can ba tsararka bace na amince
ka auretane kawai sbd irin larurar data shiga
amma kaima kasani badon ka cancanta ka
aureta bane.
Na baka 24hrs kacal lallai ka dawo min da
y‘ata gida ko kuma kaga abnd zanyi maka.
Idan kunne yaji……“ Ya juya ya fice.
Faruk ya dafe kai ckn tsananin takaici
innalillahi…… bakinsa yama gaza kai karshen
addu‘ar daya faro.
Yadau tsawon lkc a zaune bayan tsawon
min2na ne kuma ya lalubi sandarsa tare da
mikewa ya taho a hankali ya shigo daki, takun
tafiyarsa ne ya tasheni daga barcin da nake,
nayi saurin tashi na bishi da kll, duk da yadda
yake so ya boye damuwar dake ransa sai data
fito.
Yana zama na fara da tambayarsa “meye ya
faru kuma??“
Yadanyi yake da cewa “kinga wani abune??“
Na gyada kai nace “tbbs akwai damuwa.“
Ya dan gyara zama yace “daddynki ne yazo!!“
Nayi saurin zabura, daddy?? me yace??
Ya kukai dashi??
faruk ya grgz kai yace “bai kamata kiji ba sbd
bashi da dadin ji.“
Na sani abu me dadi bazai kawo daddy ckn
gdn nan ba amma duk da haka zanso ji, don
Allah me yace??
Kmr bazai ce komai ba zuwa can yace “Ya
bani wa‘adin awanni 24 lallai na….“
2n kafin ya karasa na katseshi da cewa
“awanni 24??“
hmm… Tayaya yake zaton zama na har abada
za‘a kawo karshensa ckn awa 24??
Kayi hakuri mijina wannan tatsuniyace kawai.“
Duk da yadda naso na nuna ba wani damuwa
amma ni kaina a zuciyata nasan karya nake,
bansan yadda zanyi da wannan kalar masifar
data sake tinkaromu.
*** Sai byn kwanaki biyu da yammaci muna
zaune da faruk muna hira, kamar dirar mikiya
daddy ya fado, juyowa daya nayi muka hada
ido naja da baya a tsorace tare da cewa
“Innalillahi!!“
Meye?? waye??
faruk ya tambaya.
Ubankane!!!!!
Daddy yayi saurin fada 2n kafin nace komai.
Me nace maka??
Yaya mukai dakai??
ya tambayi faruk yana dubansa a fusace, ya
dora da fadin “to yau ko kana so ko baka so
sai y‘ata ta dawo gida tare muke da yan
sanda na shigar da kararka sai munyi shari‘a
dakai.
ya juyo gareni ckn tsawa yace “uban me kike
yi anan?? wuce mu tafi.“
wayyo faruq kadebo ruwan dafa kanka..!
A maimakon na iya cika umarnin da daddy ke
bani sai na tsaya ina binshi da kallo kawai,
idan na dubeshi sai kuma na juya na dubi
faruk dake tsaye ya kasa cewa komai na tbbtr
kunnuwansa a bude suke yaji abnd zan iya yi.
Alkawarin dana daukarwa kaina na kasancewa
da faruk a duk yanayin da yake ciki yasa duk
wani tsoro yakau daga zcyta, ni ban wuce na
tafi kmr yadda daddy ke cewa ba kuma bance
komai ba har sai daya kara buga min tsawa a
karona biyu.
“Ki wuce mu tafi nace“.
Maganar ta daki kwakwalwata, yaune karon
farko da daddy ke daka min tsawa kai tsaye
haka amma maimakon na firgita sai na kara
gyara tsayuwa ma na tsaya kyam nace
“daddy! ka dubi grmn Allah da manzonsa
karkayiwa faruk haka, ka 2na sanda ya
taimakemu ya rufa maka asiri kai kanka dani
daduk danginmu, me yasa yanzu mu kuma ba
zamu saka masa ba??
Idan wai don ni kakeyi don ka samar min da
farin ciki ka rabani da wahala, to ka barni
kawai sbd ni farin cikina anan gdn yake, faruk
mijina ne har gobe kuma zan iya zama dashi a
kowanne yanayi.“
Daddy ya zaromin ido yace “gsky na yarda
baki da hankali, banda haukanki ina ke ina
zama da nakasashshe makaho??
Abin kunyane ma ace kmr ni y‘ata mijinta
makaho ne, abnd yayi mana a baya ya wuce
mu gaba muke hange idan ke baki da 2nani
mu muna dashi kuma bazamu bari wahala ta
kasheki a banza ba, ki wuce nace!!“
Fuskata ta canja ma2ka naja da baya nace
“Ina me baka hakurin cewa wlh ba inda zanje
ba yadda za‘ai na tafi nabar gdn mijina wanda
yaso ni sanda kowa ya gujeni yake kyamatata,
kuma ba akan wani dalili ba.“
Cikin tsananin AL‘AJABI daddy ya bini da kallo
yace “Ni kike gayawa haka??“
Ba tare da tsoro ba nace “Kayi hakuri amma
ya zama dole in fadi hakan sbd kokoluwar
butulci ne abnd kake so kuma banyi halacci ba
idan nayi haka, na zabi na zauna anan har
mu2wa tazo ta riskeni.“
Kin zabi wannan makahon akan mu iyayenki??
Daddy ya fada yana me nuno ni.
Na gyada kai nace “Eh! haka nake nufi sbd
mijina ne ko a wajen Allah hakkinsa a yanzu
yafi naku.
Hakanan dady yajuya yatafi tare da gargadin
bani basu..