BAKAR INUWA 14

Chapter Fourteen
………….A gidan Ummi komai ya canja. Gaba ɗaya ya ranta sun bar walwala. Sun daina fara’a. Sun daina zaman hira, abinci ma kaɗan suke tsakura. Idan tai magana suce sun ƙoshi. Ta ko ina ta gaza gane kansu.
Da farko tayi biris da su, duk da kuwa ta fahimcesu tsaf. Sai dai ganin abin nasu bana ƙare bane sai itama lamarin ya fara damunta. Dan ita kanta sun jefata a cikin kaɗaici. Hatta da Hibbah ƴar karamarsu itama ta ɗauke mata wuta. Saboda wannan abun daya faru ma ta tattara ta koma makaranta duk da Yaya Abubakar ya hanata zuwa da.
Duk da ta ɗan fuskanci ƙalubale a wajen mutane a ranar data koma saboda tafiya da itan da ƴan sanda sukazo sukayi ranar haka ta daurema zuciyarta ta cigaba da zuwa. Bakuma ta sanarma kowa ba. Dan a ganinta da zaman gidan su tana cigaba da ganin Abba da baƙinsa gara kallon da ƴan makarantar zasu mata.
Tunfa Ummi na ɗaukar lamarin nasu wasa sai ƙara girmama ya keyi. Dan kwanakin nan biyu ma basa dawowa gidan sai sun dai-daici tayi barci sannan. Hankalinta sosai ya kuma tashi. Ga damuwar yaranta, ga damuwar auren da aketa ƙulle-ƙullen nana musu na son zuciya. Wanda tsaf ta gama fahimta da gane ina hakan ya dosa. Sarai ta gane manufar Abbah akan son ƙulla auren ƴaƴanta da nashi, manufar kuma duk ɗaya ce tsakaninsa da hajiya mama.
Gaba ɗaya ta rasa ina zata saka kanta taji sanyi, babu uwa babu uba, babu abokin shawara a cikin ƴan uwa, babu wanda zata kaima ƙara ya duba matsalarta ya share kukanta. Gudun abinda zaije ya dawo kuma ke sakata kwaɓar ƴaƴanta akowane lokaci. Bata son abinda zai rabata da su. Bata son a cutar mata da su. Dan sune hope ɗinta, sune murmushin fuskarta. Sune masu share hawayenta da tun tana ƴar ƙanƙanuwarta suke kwaranya a bisa kumatunta. Tasan nuna ƙarfinsu ya kawo kuma zai iya zama sanadin da komai Abba zai iya aikatawa a garesu domin samun cikar burinsa, kuma kamar yanda yasha faɗa koda ya salwantar da rayukansu babu mai yarda shine ya aikata. Wasu hawaye ne masu zafi suka silalo mata saman fuska.
Wata banzar dariya Abba da ke shigowa cikin sashen ya shiga tuntsurawa yana tafa hannaye. Cike da izgili ya dubeta sheƙeƙe yana faɗin, “Kuka kuka kuka! Ai kuwa yanzu kika fara kuka Asiya. Yo ina jarumtar taki ne yau? Shin har kin fara zuwa ƙasa ne tunkan ma a ɗaura auran manufarsa kuma ta tabbata?. Tunda har kikace ni ban isaba Asiya, to wlhy kema bazaki taɓa isa ba. Yau ina wanda kike gadar da shi? Ya tafi tamkarma ba’ayisa ba. Abinda kika hanashi yay mana ta hanyar zagon ƙasa ya dawo hannunmu a lokacin da ko ido baki isa ɗagawa akai ba. To suma ƴaƴa mazan da kike ɗagawar kin haifa masa zasu mamaye komai tafin hannunmu zasu cigaba da zama ballagaza kawai. Zaki iya tashi kuma mu shige ciki dan ina bukatar haƙƙina. Inba hakaba kuma zan ƙwata anan cikin falon babu ruwana….”
Hanyar bedroom ɗinta ya nufa yana gama faɗa alamar ta biyosa. Ummi da ke jin wani ƙullutun abu yazo ya tokare maƙoshinta ta shiga karanto duk addu’ar da tazo mata a saman harshe saboda jin numfashinta na fita a gwagwgwame. A hankali sanyi ya rinƙa shiga cikin ƙashinta, yayin da jikinta ya fara wani irin rawa, har haƙwaranta na haɗuwa waje guda. Hannu takai domin lalubo wayarta da ke saman centre table. Sai dai hakan ya gagara sakamakon gushewar gani da ta risketa a lokaci ƙanƙani. Hannunta ya goce da ga lalube wayar, sai gata ƙasa wanwar da ga saman kujera…..
A dai-dai wannan lokacin Hibbah ta shigo tana masifar bibiyarta da kullum Shuraim keyi babu fashi balle nuna gajiyawa duk da yarfatashin da take yi a kulum. Data fita da ga gida zuwa makaranta yana biye da ita. Hakama idan ta dawo sai ya rakota har gida ta hanyar bibiyarta. Zuwa yanzun tun lamarin nasa na bata mamaki har ya koma takaici da al-ajab. Har tabbayar kanta take shin baida aikinyi ne ko mi?. Wannan takaicin nasane ya sata yau ana saukesu a napep taje tai masa knocking glass. Yana saukewa ta balbalesa da masifa batare data yarda sun haɗa ido ba dan karma yay mata kwarjini. Sai dai abin ALLAH wadai da takaici, harta gama masifar tata ma bai nuna yaji haushi ba. Sai ma murmushin da ya nema rikita mata lissafi ya sakar mata yana wani narkewa a cikin kujera.
Wani uban kara ta ƙwalla tana isa inda Ummi ke kwance wanwar tana wani irin tari dake fita da ƙyar. Kiran sunanta ta shigayi tana girgizata hankali tashe. Sai dai ina Ummi ta fita hayyacinta. Dabarar rarumar wayar Ummin ce tazo mata a rai. Batare data nutsu wajen ganin wanda ta kira ba kawai tai dailing numbern farko, dan tasan su ne dai kawai suke yawan kiran no din Ummin tasu a koda yaushe.
“Yaya dan ALLAH kazo gida, Ummi…Umminmu. Na shiga ukuna. Ummi dan ALLAH ki tashi. Wlhy kika mutu nima mutuwa zanyi. Dan ALLAH Ummi na roƙeki karki mutu. wlhy bazamu sake yin fushi da ke ba. Mun tuba Ummi, mun daina. Mun yarda zamu auresu Ummi…….”
Sambatu taketa faman yi tama manta da waya a kunnenta. Kukanta ya fiddo Abba da ga ɗakin Ummi ɗin wando a hannu. dan harya cire kaya ya baje a gado yana jiran jakarsa ta shigo ya murza a wulaƙance. Ido huɗu sukai da Hibbah da ke sake ƙwala kuka tana kiran Ummi da girgizata. Ai sai ta sake fasa wata ƙarar ganin a yanda ya fito, saboda bai saka wandon dai-dai ba an samu mishkila wajen bayyanar jikinsa.
Sakin Ummi tai ta fita a guje da ga sashen baki ɗaya jikinta na rawa. Tana da yayu maza manya. Amma tunda take da su ko zama da singlet da boxers basu taɓa yi a gabanta ba balle a yanayin da Abban ya fito wanda bata taɓa ganin wani mahaluki a yanayin ba.
Jikinsa ta faɗa dai-dai maigadi ya buɗe masa gate ya shigo, dan Hibbah wayarsa ta kira saboda shine na ƙarahe da ya kira Ummi yaji yaya jikinta? Dan ya kwana biyu baizo gidan ba. Duk yanda yaso ganin ya janyeta a jikin nasa hakan ya gagara, sai sake ruƙunƙumesa takeyi jikinta na rawa, yayinda taketa faman son ɓoye fuskarta a ƙirjinsa duk da tsahon nata gaba ɗaya iya ƙirjin nasa ta tsaya.
Cikin zafi-zafi ya shiga tureta yana girgizata. “K Muhibbat nutsu, muje inga Ummin gani nazo”.
Jin muryar da bata yayunta ba ya sata saurin ja da baya tabar jikinsa. Isma’il da ya samu ta rabu da jikin nasa da sassarfa yay gaba abinsa zuwa sashensu har yana haɗawa da ɗan gudu-gudu. kusan cin karo sukai da Abbah da ya koma ya ɗakko kayansa saboda ihun da Hibbah tayi ya farga da halin da yake a ciki. Duk da ya kuma ga Ummi a yashe a ƙasa sai kawai firgici biyu ya kamashi. Na farko kar wani yazo ya gansa a yanda yake sakamakon ihun Hibbah a zata wani abu yaso mata har Ummi ta shiga halin da take ciki a yanzu. Dan haka ya fito dan ya gudu salin alin, idan Hibbah ta sako sunansa a ciki kuwa yasan ta yanda zai kare kansa ai.
Haka kawai zuciyar Isma’il ta raya masa irin abinda Abban ke gudu. Dan haka yasa ƙafa ya taɗesa sai gashi a ƙasa tim. Takan kafafun Abba yabi da shaggun takalman ƙafarsa, ji kake ƙasss ƙashi na bada sautin karyewa ko tsagewa. Wata iriyar wahalalliyar ƙara Abba ya saki tare da ɗaukewar numfashi na wucin gadi. Ko waiwayensa Isma’il baiyiba ya ida afkawa cikin falon inda ya hango Ummi a ƙasa itama babu alamar rai tattare da ita.
“Ummi!… Ummi! Ummi!!” ya shiga ƙwala mata kira da kama hannunta yana girgizawa. Sai dai babu alamar motsi tare da ita sam. Mikewa yay da sauri ya ciro wayarsa yay kiran Yaya Umar da yasan shine mafi kusanci da gida. Sai dai bai ɗaga ba. Tunawa ana sallar la’asar yanzu haka ya sakashi cije lip ɗinsa na ƙasa ya cusa wayar a aljihu. Batare da tunanin komai ba ya ciccibi Ummi gaba ɗayanta yay waje. Sai lokacin Hibbah ta nufo falon sabida hango abinda Isma’il ɗin yay ma Abba.
“Muje asibiti” yace mata kawai yana nufar hanyar gate. Babu musu ta bisa tana kuka da riƙe hannun Ummi ɗin da ya ɗakko. Sai lokacin kuma Hajiya mama ke fitowa da ga sashensu itama. Ta bisu da wani irin kallo mai ma’anoni da yawa saboda ganin baƙon fuska ɗauke da Ummi ɗin. Dan duk zuwan da Isma’il ɗin keyi gidan ba taɓa haɗuwa sukai ba. Wahalallen ihun da Abba ya saki ne ya fargar da ita halin da yake a ciki, babu shiri ta runtuma a guje kansa tana ƙwala kiran sunansa…….