Labarai

Allah Akbar Rai Bakon duniya, Fasinjoji (14) Sun Kone Kurmus A Wani Mummunan Hadarin Mota daya Faru a Jahar Kan

Allah Akbar Rai Bakon duniya, Fasinjoji (14) Sun Kone Kurmus A Wani Mummunan Hadarin Mota daya Faru a Jahar Kano

Daga gaya zuwa Wudil  wani hatsarin mota ya faru da kirar Toyota Hummer da wata mota kirar Hyundai jeep wanda hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Kasa FRSC ta tabbatar wa jaridar SOLACEBASE.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa motar bas mallakin Kano Line ta taho ne daga jihar Gombe a yayin da ta yi karo da wata motar kirar jeep, da misalin karfe 7:30 na daren ranar Lahadi.

Kwamandan hukumar FRSC reshen jahar Kano, Zubairu Mato ya shaida wa majiyar jaridar Alkiblah ranar Talatar nan cewa jami’an kiyaye haddura sun isa wurin da hadarin ya afku a kauyen Rege da ke Antukuwani, kan hanyar Kano zuwa Gaya da karfe 7:45 na yamma.  “Fasinjoji 13 ne suka kone kurmus nan take tare da jikkata wasu mutum 6 a hadarin An kuma sanar da rasuwar karin mutum daya daga cikin fasinjojin, macen da ta rasu a safiyar ranar Litinin a asibitin koyarwa na Aminu Kano, (AKTH) a sashin Intensive Care Unit.

Kwamandan hukumar FRSC ta alakanta hadarin da Gudu na wuce gona da iri, Ya kuma bukaci direbobin da su tabbatar da amfani da na’urar da za ta iya kayyade gudu a kodayaushe tare da kaucewa gudun wanda bai kamata ba.

A karshw muna yiwa wanda Aka rasa Addu’a Allah yaki kansu da rahama ameen.

Kalli Cikakken vedion anan

Jaruma Maryambooth tayi abun mamaki

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button