AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 11-22

Wurin shirinta ta nufa tajanyo wasu hadandin tufafi, kananun kayane riga da wando, kayan sunyi matukar mata kyau,
Tana tsaye tana kallon kanta ta madubi tajiyo sallama a falo, da sauri takarasa bakin gado tadauko wayarta, sannan tafita falo,
Kawarta AMEERA tagani wadda suke kira da Amrah,
Suka rungume cikin jindadi da farin ciki, Amrah tafito daga jikin ameela tatsaya tana kare mata kallo tayi dariya tace ” bakida dama kawata kinga wani kyau da kika kara kuwa, lallai auren nan ya karbeki, su haske manya” ameela ta yamutse fuska ” ke dalla banson shashanci, wane aurene ya karbeni, nida ko morar first night dita banba” amrah ta zare ido “toh fa meya hana “
Ameela tayi murmushi tace “aikinsani mutum ne mana chart yadaukemun hankali, zoma kigani” taja hannun amrah suka zauna, ameela ta fitar da wayarta, tashiga ciki number nan HMM, tafara nunawa amrah photon guy din,
“Kinga wannan shine nake gayi miki jiya lokacin da muke cikin mota za’a kawoni gidan nan, shine guy dinda yadaukemun hankali jiya mukayita chart har kusan karfe 3 nadare, kinga pic dinsanan yacemun dan kaduna ne”

Amrah idonta nakan photon tace “aikuwa nasan za a rina wannan ai sai kaduna, ammafa ya hadu”

Ameela tayi murmushi “yace nima natura masa nawa”

Amrah tajuyo ta kalleta da mamaki “to tura masan zakiyi”

Ameela tace “eh mana to miye a ciki bafa a gari daya mukeba balle kice mijina zai iya ganin pic din, ni barima kigani, Ameela ta mike tsaye tana gyara dress dinta, tayi wata irin tsayuwa tace ” yimin pic a wayata nashirya”

Amrah tace “a a ameela banbaki shawarar kitura masa photon kiba, kifa tuna akwai AMANAR AURE akan kifa”
Ameela ta tsuke fuska ta harare amrah “Amanar taci ubanta, ina ruwanki nidai kimun pic nace komai yafaru ai baruwanki, ruwanane, nidai kawai idan zakimun kimin, idan kuwa bazaki minba naji ahe”

“A a zamma yimiki, gyara tsayuwar zan dauka” amrah tafada bayan tashiga camera, tadaidaita fuskar ameela nan tafara bata flasher, ameela sai chanza style ake, wani style ko budurwa bazata yisa balle ita datakeda aure,

Bayan tayi dauka takai goma sannan ta karbi wayar tazo tazau kusa ga amrah "gyara muyi selfies" amrah ta gyara badama suka fara snapping din pics masu kyaun gaske., 

Bayan sungama selfies
Ameela tana murmushi cike da jindadi tace ” yau dp zaici ubansa, domin idan nafara dura pic dinnan saiā€¦” Amrah tana rike dawayar tace “kawata kinga wannan pic dinnan kuwa wlh yayi bala’in kyau” ta nunawa ameela daya daga cikin pic dinda taimata ne, Ameela tace “wow kamar baniba, dan Allah bani nadaurasa a dp” Amrah ta mika mata wayar, ameela takarba tadaura pic din a dp, sannan taturawa HMM sauran pics din kusan goma tatura masa, daga kasan pic din tarubuta gasunan”
Sannan ta rufe data tajuyo sukaci gaba da fira ita da amrah,

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button