BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 18

18

……….Sosai idanunta ke faman marmari ga ƙwalla na ƙoƙarin taruwa a cikinsu.
      “Juwairiyya!! Wlhy! wlhy! daga yau na sake ganin yaron nan ko wani ya ɗaukeki a motarsa koya kaiki gida sai na miki mugun dukan da zaki kasa tashi, kuma ki koma gidana da zama stupid kawai”. Ya ƙare maganar da ture fuskar tata gefe.
     So take ta fashe da kuka amma tana ƙoƙarin son dannewa, sai dai hakan bai hana rawar jikinta bayyana ba. A tsawace ya sake faɗin, “Get out of my car! Kafin na marmashe ƙashinki anan stupid”.
     Da sauri ta ɓalle murfin ta fice tamkar mai jiran umarnin nasa dama. Yaja dogon tsaki da figar motar yay gaba, badan titi bane da sai ya bula mata ƙura, murfin ma sai da yay gaba kaɗan yaja abinsa ya rufe.
     Duk yanda taso ƙoƙarin danne komai hakan ya gagara. Dole ta samu wani dutse a gefen titin ta zauna ta fashe da kuka. Duk abinda kaga Anam ta zauna yima kuka lallai ya taɓata sosai, dan tsiwarta da giringiɗishi bai cika barinta maida abu serious ba, ga kuma yanayin rayuwar data tashi a ciki, ita kaɗai a gidansu sannan a ƙasar da kowa kansa ya sani kawai.
     Ring da wayarta ta farane ya sata share hawayenta ta daga dan tasan su Mamie ne, a kullum tana waya dasu a irin wannan lokaci da kuma in zata kwanta. Video call ne, dan haka ta shiga son ɓoye damuwarta da murmushin farin cikin ganinsu. “Good morning my sweetheart”.
        Dukansu babu wanda ya amsa mata, dan duk da ƙoƙarin da take na ɓoyewa idanunta sun tabbatar musu tayi kuka. Abie yaja numfashi a hankali yana sake kafeta da ido. “Mamana mi yake faruwa da ke? Waya saki kuka? Ko baki da lafiyar ne har yanzu? A ina kike nan?”.
      A karan farko ta saki murmushi dan jin tambayoyin mahaifin nata a jajjere. Samun kanta tai da kasa faɗar gaskiya duk da ƙarya ko ɓoye-ɓoye ba halinta bane, ta sake share hawayen da suka ciko mata ido tana murmushi, “Abie ba komai fa, kawai kewarkuce har yanzu ALLAH. Kuma a wajen aiki nake ban dai shigaba ka gani”. Ta juya masa wayar yanda zai iya hango gate ɗin wajen.
     A jiyar zuciya suka saki shida Mamie, kafin su shiga lallashinta duk da ita Mamie a ranta bata gama yarda da cewar har yanzu kewar tasu bace. Amma sai ta barta a hakan dan tasan Anam da rashin ɓoye-ɓoye koma miye wataran da kanta zata sanar musu. Sai da suka tabbatar sun sakata farin ciki tana ƙyalƙyala dariya kamar ba ita ba sannan sukai mata sallama Mamie na faɗin ta gaida mata Yaseer. Farin cikin waya da iyayenta ya taushe abinda Shareff yay mata ta shiga wajen aikinta da walwala kamar yanda ta saba ko yaushe.

      MALAYSIA

“Humairah waye naji kina faɗin Mamana ta gaida miki?”.
Cikin rashin damuwa Mamie tace sirikinka ne duk da dai naga ɗiyar taka bata son a gane hakan…..”
Cikin sauri ya ɗago yana kallonta, har ya kasa dannewa sai da ya ambaci “Suruki kuma?”.
Ƴar dariya Mamie tai, “Eh bashi kake fatan ganiba daman?, bayan shi ma ai akwai wasu. Yaron nan Muzzaffar da kuma wani abokin Shareff Jamal. Amma naga hankalinsu yafi zuwa ɗaya da Yaseer ɗin nan kamar”.
Jin shiru baice komaiba ta ɗago ta kallesa, kallonta yake kamar mai nazari ko tunani, ta ɗan taɓashi, ajiyar zuciya ya sauke. “Abien Anam akwai matsala ne?”.
Kai ya ɗan jinjina mata yana gyara zamansa, “Babbama kuwa Humairah, miyasa tun muna Nigeria baki sanar min hakan ba.”
Sosai maganar tasa ta sakata kafesa da ido dan mamaki, amma ta kasa cewa komai. Fahimtar hakan ya sashi jinjina mata kai, “Basai kin tambayeni komai ba Humairah, amma idan lokaci yayi ko baki tambayeni ba zan baki amsa da kaina”.

Gaba ɗaya kanta ya ƙara ɗaurewa ita kam, sai dai rashin sabo dayi masa dagiya yasa ta kasa cewa komai ta bisa da kallo kawai ganin ya miƙe yana kai waya kunensa. Yana gab da shigewa ɗakinsa taji ya ambaci sunan Yaya (tasan Daddyn Shareff yake kira da hakan). Jitai kamar ta tashi ta bisa amma sai ta dake kawai, zata bisa a sannu dan tasan dalilinsa na son hana Anaam ɗin tsayawa da samari bayan kuma duk fatansu kenan ita da shi tunkan ta wuce Nigeria…..

   ★★★★
 
Sauraren sakatariyarsa kawai yake batare da yana fahintar abinda take faɗa masa ba, idanunsa ma gaba ɗaya nakan kula ɗin daya shigo dashi, wadda baya raba ɗayan biyu Anam ce ta manta ta…
     “Kinga jeki zan nemeki”.
Ya faɗa cikin katse sakatariyar da ke faman zuba bayani cike da yanga da kwarkwasa. Bataso hakan ba, sai dai sanin shi sam baya wasa yasata bin umarninsa. Sai da ta fice da kusan minti ɗaya ya sauke kakkauran numfashi tare da furzar da shi, yakai bayansa kwance jikin kujerarsa yana mai lumshe idanu. kusan mintuna uku ya ɗauka a hakan kafin ya bude idanun, kular ya ɗauka ya buɗe. Ya tsirama abinda ke ciki idanu tamkar mai irgawa ko lissafa abinda aka sarrafashi da shi. Abincine irin na ƴan ƙasar malaysia, shima yana bala’in son sa a lokacin da ya rayu acan, ko yanzu kuma da yake a Nigeria yakan je takanas ya siya a inda yasan zai samu. Hannu yakai ya ɗauka spoon ɗin dake ciki ya ɗiba dan tabbas wannan ɗin da gani an masa haɗi da girki na musamman ne. Sosai ya lumshe ido lokacin da yake taunawa, koda ya haɗiye sai ya sake ɗiba yakai baki, kamar da wasa sai gashi ya cinyesa tas dan dama bai karyaba ya fito gidan, shayi kawai ya sha, shima sai da Fadwa ta ɓata rai dayin korafin ganin saurin da yake faman yi duk da ta fahimci shi mai fitar wuri ne office sannan ya sha a tsaitsaye ya barota tana tura baki gaba…….
      Shigowar Fharhan ta sashi ture kular gefe yana goge bakinsa da tissue. Fharhan dake kallon kular da murmushi ya kai zaune yana faɗin, “Ɗan gatan madam, abincin ma sai an baka kazo office kuma ba gayyatar masu tayaka ci ka kulle office kai kaɗai”.
     Murmushi kawai yay yana miƙa masa hannu sukai musabaha. “Kai ka cika sa ido wlhy, ka hucema kanka takaici kai auren kaima sai a ringa baka kana zuwa da shi kana hanamu”.
       “A’a karka damu alhaji, ai abun bana gori bane muna hanya da iznin ALLAH”.
    “Haka muke so ai muma. dan kun ishemu a tituna”.
        Dariya sosai Fharhan yake da maganar ta Shareff, yace, “Kaima yaushe kabar titin. Ba komai zan rama”.
          Shima ƴar dariyar yayi. Cikin komawa serious yace, “Yanzu nake duba saƙonka ta email ai. Mutanen nan ya zasu mana haka kuma?”.
    “Wlhy nima abin ya ɗauren kai, jiya badan karna takurakaba da a daren zanzo na sameka gida tun shigowar saƙonsu, na kira wayoyinka kuma duka switch up”.
            “Mtsoww! Kabari kawai, wlhy ban san madam ta kashesu ba sai da asuba na gani. Amma gaskiya abun nan nasu yayi tsauri, anya kuwa bazamuce mun janye ba”.
     “Amma janyewar sai nake gani kamar akwai matsala Musty. Sakamakon company na buƙatar babban aiki irin wannan a halin yanzun, na biyu mun riga munyi zama da su har munyi signing akan agreement ɗin, kasan kuma turawan nan dai musamman chines ɗin nan da basa wasa da damarsu”.
      Huci ya ɗan furzar yana mai komawa jikin kujera ya kwanta. Har ga ALLAH abubuwa masu yawa ne ke masa kaikawo a cikin rai. Amma duk sai ya haɗiye abunsa yana sake fuskantar Fharhan dake kallonsa. “Ni gaskiya da tafiyar ta zama nine dole zanyi shine matsalata Fharhan”.
      “Oh saboda amarya?”.
Hararsa Shareff yayi, “Ko saboda ita ma ɗin ai inada hujja”.
   “hhhh hakane ango kafa ɗan ɗana. To mizai hana kaje da ita kawai”.
            “Zan so hakan nima, sai dai bazai yuwu ba”.
    “Mi yasa?”.
Shiru kamar bazai amsa ba, sai kuma ya girgiza kansa da furzar da iska ya sake komawa jikin kukera ya kwanta yana ɗan juyata. “Ina hasashen Fadwa nada shigar ciki, sai dai ko ita kanta bana jin ta sani. Yin tafiya da ita a irin wannan gaɓar zai iya zama haɗari”.
         “Masha ALLAH! Alhmdllhi. Lallai wannan angon da gaske sharp shooter ne. ALLAH ya inganta mana”.
      Shareff ya ɗan murmusa da faɗin “Amin” akan laɓɓa. Cigaba da tattaunawa sukai, daga ƙarshe dai shawara ta zauna akan shi zaiyi tafiyar tunda dai wata uku ne kawai insha ALLAH.
       Bayan fitar Fharhan ya buƙaci shigowar sakatariyarsa, daga haka ya cigaba da ayyukansa har zuwa lokacin break….

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button